x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - CUTARWA

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 510

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
dai jini yaƙi tsayawa, ƙarshe aka ce tiyata za a shiga da ita da gaggawa a cire mata cikin, dan ta fara jijjiga ga jini ya ɓalle.

A daren aka shiga da ita tiyata, aka ciro ƴa mace, sai dai ba ta san in da kanta yake ba, har aka fito da ita.

Ita kanta yarinyar taƙi yin kuka, aka yi ta fama, sai dai tayi kaɗan tayi shiru, ga rashin isashiyar oxygen a jikinta sai da aka saka mata oxygen.

Rahama ta din ga kuka, tare da ɗora zargin hakan a kan ummi, sai dai ta yi shiru ba ta gaya wa baban su Abdul abun da ya faru ba.

Abdul kuwa a gida aka bar shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye, mussaman yadda ya kasa manta ganin jini na zuba a jikin.

Ummi bacci sai ɓarawo ya kwasheta, shi ma a rigingine ta kwana.

Da asuba ta tashi tayi salla, fatar cikinta duk ta ɗaga tayi wani iri, saboda ƙuna.

Bayan ta idar da sallar, ta lallaɓa ta fito falon, ta tarar da wurin duk jini, ga kayan gugar duk a watse a wurin, tsaf ta gyara wurin ta kwashe kayan gugar, ta shiga kitchen, ta ɗora ruwan shayi, sai lallaɓa jikinta take yi, saboda raɗaɗin da take ji a cikinta.

Ta sake fitowa falo, ta tarar da Abdul a tsaye yana kallonta.

Ta kalleshi ta ce "Yaya Abdul".

"Na'am, ya jikin wurin ya ƙone?"

Ta ce "Eh, amma ba sosai ba".

Ya ce "Maama fa a asibiti ta kwana"

Zaro ido ummi tayi ta ce "Meya sameta?".

"Faɗuwa tayi" yayi maganar cikin damuwa.

Sai a lokacin ummi ta tuna taga farida ta zame ta faɗi, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, to yanzu ya jikinta?".

"Nima ban sani ba, tun da suka tafi basu dawo ba".

Ummi ta ce "Allah ya sa tana lafiya".

Ya amsa da amin.

Suna tsaye suna jajantawa, sai ga Abba yayi sallama, duk suka zura masa ido suna yi masa sannu da zuwa.

"An yi wa mamanku aiki, an ciro baby girl, sai dai dukkannin su, they are under special care, duk basu da lafiya"

Ummi ta ce "Subhanallah, Allah ya basu lafiya".

Ya amsa da "Amin, ummina na san kin yi breakfast, ki zuba wani a flask a kai musu asibiti, ku shirya na ajiye ku a makaranta, ina su kausar?"

"Ba su tashi ba"
"Kamar yaya, ƙarfe bakwai saura, ba zasu makaranta bane?" A fusace ya nufi ɗakinsu, ya taso su da bulala.

Ƙarshe dai sai da suka makara, jin mamansu na asibiti, ya sanya suka din ga kuka, haka ya kai su makaranta ya wuce asibiti.

Gumin da ummi take ta yi, ya din ga taɓa wurin ƙunar nan, ga kuma rigar makaranta, hakan ba ƙaramin takurata yayi ba.

Sai dai duk da abun da farida da ƙamwarta suka yi mata, tunaninta yana kan yaya jin faridan yake.

Kasancewar rahama ce a can asibiti tare da farida, sai ya zamana kusan kula da ragamar gidan yana hannun ummi, kai ba ka ce babu mace a gidan ba, duk aikin gida ita take yi, har kawunta sai da ya yabawa ƙoƙarin ta tare da jinjina mata, dan hatta abincin da za a kai asibiti ita take dafawa.

Gefe guda Abdul ne yake takawa su intee burki, dan tana yi musu wahala amma ba sa gani, dan sai suka tsiri cewa ai anty rahama ta ce musu, ummi ce ta saka mamansu ta faɗi, su yi ta yi mata rashin mutunci da wulaƙanci.

Kwanan farida biyu a asibiti, aka samo kanta da ƙyar, kawu yahaya ya ɗauki su ummi ya tafi da su asibitin dubata.

Sai dai yanayin kallon da ƴan uwan farida ke yi mata, ya sanya ta sha jinin jikinta, dan ko sannun da tayi wa faridan ba ta amsa ba. Tana kwance jaririyar a kusa da ita, ana ƙara mata jini. Sai dai kasancewar babansu Abdul yana wurin, ba su iya ce wa ummi komai ba.

Ummi fa ƙuna ta din ga jagwalewa, ga ƙaiƙayi tana yi mata, ta tuna ta taɓa ƙonewa a ƙafarta lokacin tana ƙauye, na'ima ta din ga shafa mata zuma, dan haka ta cewa baban su Abdul, ya sammata zumar da yake shan shayi.

Yayi murmushi ya ce "Zumar da gata nan kaya guda, ai ba sai kin tambayeni ba ummana" ta samu abu ta tsiyaya take amfani da ita a ƙunar, dan har wurin cibiyarta ta ƙone.

Kwanan farida biyar a asibiti aka sallamo su, babu tsammani ummi ta dawo daga makarantar boko ta dawo ta tarar an cika gidan.

Ta ƙarasa falon ta durƙusa tana gaishe su, sai dai basu amsa ba, rahama ta janyo hijjabinta har tsakiyar falon ta ce "Kun ganta nan azzaluma, ita ta kusa kashe anty farida, ita ta kayar da ita"

"To ai da farida cewa tayi mai aikinta ce".

"Ba ƴar aiki ba ce ba, ƴar wan maigidan nan ce".

Ƙanwar babansu farida ta ce "Kuma shi babu matakin da ya ɗauka?"

Farida na daga kwance ta ce "Wane matakin zai ɗauka, kin ga faman da nayi a kan ba zan zauna da ita ba ya dage, ni kuwa na samu ƴar aiki"

"Aikuwa idan baki yi hankali ba ta kashe ki wataran".

Ummi tayi shiru ta sunkuyar da kai, wata yayar su ta dunƙule hannu, ta ɗirka mata duka a tsakiyar ka ta ce "Wallahi da kin kasheta, sai kin yi prison daga ke har ubanki".

Rahama ta ce "An ce ubanta ya mutu ai".

"Matsiyaciyar yarinya da ya bar wata tsiyar, da ba a ganki a nan ba, har ki ke ƙoƙarin kashe mana ƴa, ni wannan anya ma ba mayya bace ba, kalli ƙwayar idonta fa".

Wata a gefe tayi caraf ta ce "Wace iri ce? Turo mini ita nan, ai ni ina gane maye"

Matar ta ja ummi kamar tana jan shara, ta dungurarwa da ɗaya matar ita, tuni ummi ta fara kuka, ga zafin duka ga na cin mutunci.

"Ke ɗago idonki na gani"

Ummi ta sunkuyar da kai ta kasa ɗagowa.

"Ba zaki ɗago ba sai na mareki" ummi ta kasa ta sake fashewa da kuka.

Aikuwa matar nan babu tsoron Allah, ta sauke wa ummi yatsunta a fuska iya ƙarfinta, sai da ta hantsula gefe.

"Wallahi zata iya yiwuwa mayya ce, tun da ta kasa haɗa ido da ni, shegiya ga baƙi kamar ƴar maƙera".

Suka ciwa ummi mutunci son ransu saboda abun kunya, da yawansu zasu haifi ummi, amma kasancewar ba ƴar su ba ce ba, suka din ga muzanta ta suna aibata ta.

Tayi kukan da tun da aka kawota gidan ba ta yi irin sa ba, har ta fara tunanin ko roƙon kawu yahaya za ta yi, ya mayar da ita ƙauye.

Sai dai gabanta ya faɗi, da tuna irin azabar da ta sha a ƙauye, da sauri ta girgiza kanta, har da istigfari, ta fara ƙoƙarin auna zaman nan da na can wanne yafi sauƙi.

Duk zaluncin iya, ba ta taɓa ƙonata da wuta ba, illa iyaka duk laifin da tayi jikinta zai gaya mata.
Nan kuma duk rintsi, ko ba a bata abinci sau uku ba, ba zata kwana da yunwa ba, kuma tana da kayan makaranta da na sawa duk da babu yawa, kuma tana da takalmi da sauran abun da ba a rasa ba.

"Mama meyasa ba so na ne? Laifin me nayi, meyasa idona yake ba kalar na mutane ba? Duk abun da nayi mutane sai sun tsaneni, ko a gida ko a makaranta?" Tayi maganar tana ganin fuskar mariya a idonta, tana jin tamkar ta ga mamanta ta bayyana.

Tayi kuka ta gaji, ta duba sabulun wankanta ya ƙare, tayi wankan a haka, ta shirya islamiyya, ta fice ba tare da kowa ya sani ba.

Dama kuɗin motar zuwa islamiyyar ma, idan kawu yahaya yana nan, yana bata ko ya bawa farida ta bata, idan ta ga dama ta bata, ko taƙi bata wanda zai ishe ta shima saboda ta na biyawa ɗaukko su intee daga ta su makarantar islamiyyar, dan Abdul ba lokaci ɗaya suke tashi ba, sai ƙarfe shida, su kuma tun huɗu da rabi ake tashin su.

Dan haka ummi tafiyar ƙafa ta sha, kan ta je makarantar, nan ma da ta je sai da aka daketa dan ta makara.

Zama tayi, tayi shiru a ajin, dan kamar yadda ta saba, bata da ƙawaye, dan ba ta son shiga cikin su su tsokane ta.

Haka kurum ta ɗan shagala da kallon yarinyar da take jin tsoro a ajin, mai suna maryam saboda hantararta da take yi tana kyararta, da nuna mata tsana ƙarara a fili.

Tubarkallah maryam fara ce sol, irin fulnin nan masu dogon hanci, sai azabar iyayi da iya gayu, da yawa ƴan ajin na tsoronta, saboda azabar masifarta da rashin son rai ni.

Ba tsammani ummi ta ji ta ce "Ke lafiya ki ke kallona kamar zaki cinye ni?"

Da sauri ummi ta ɗauke kanta tare da cewa "Yi haƙuri"

"Da haƙurin ta mutu sadakar nawa ki ka bayar? Bana son kallo"

"Ai na ce kiyi haƙuri" ta faɗa a sanyaye.

A ranta ta ce 'Dama nima fara ce, wataƙila da ba za a tsane ni ba. Amma ai akwai baƙaƙe da yawa da ake son su, ni meyasa ba a sona?' ta tambayi kanta, wasu hawayen na rige-rigen zubowa.

Maryam ta zauna a kusa da ummi, ko a jikinta ganin ummi ta kifa kanta.

Sai da malami ya shigo ajinsu sannan ta ɗago kanta, ya yi musu karatun da zai yi musu, sannan ya basu class work.

Sai dai fa maryam ba ta iya komai ba, ta din ga rarraba ido, ga malamin ya jaddada cewar duk wanda ya faɗi sai ya zane shi.

Ganin lokaci ya kusa cika, ya sanya ummi buɗe mata takardarta ta ce "ki kwafa ya kusa karɓa" babu kunya maryam ta kwafe duk abun da ummi ta rubuta.

Lokacin sallar la'asar yayi, ɗalibai na ta ƙoƙarin fita daga ajin, ba tare da tuna alkhairin ummi ba, maryam ta hankaɗeta zata fita, bisa tsautsayi ummi ta faɗi ta fama ƙonuwar da take cikinta.

Ƙara ta saki, tana girgiza kanta, duk ɗaliban suka tsaya suna kallon ummi, ganin jini yana tsatstsafowa a rigar uniform ɗin ta.

Maryam a tsorace ta ce "Na shiga uku" ta durƙusa ta ɗago ummi, a zaton ta ko cikin ummi ne ya ɓule.

Ummi sai yarfe hannu take yi tana kuka, ɗalibai suka taru a wurin, malamin da ya fita daga ajin ya dawo ganin ɗalibai a wurin yana tambayar meyafaru, aka gaya masa maryam ce ta hankaɗeta ta faɗi.

Cikin tashin hankali ya ce a kai ummi ofishin malamai, ita ma maryam ta bisu sai an hukunta ta.

Cikin tashin hankali malamai mata suka ɗaga rigar ummi, ana ƙoƙarin gano menene yake jini a cikinta, sai dai ba kyan gani, suka tarar da ƙonuwar ta jagwale, ga ruwa ga jini ya dame da zumar da take sakawa.

Maryam na ganin haka ta fashe da kuka, ta zata duk faɗuwar ce ta janyo haka.

Shugaban makarantar ya dubi Maryam ya ce "Wato maryam ba kya ji ko? Zaki gane kuskurenki, sai kin daku yau ɗin nan, makauniya ce ke da zaki tureta ta faɗi".

Malamin ya dubi ummi ya ce "Ke ya aka yi ki ka zo da wannan ciwon makaranta, meya sameki haka?"

"Ba maryam ce ta ji mini ciwon ba, dama na ƙone a gida"

"Da me ki ka ƙone, kuma an kai ki asibiti?"

Ta ce "Eh an kaini"

"A'a wannan da an kai ki asibiti, da ba ta jagwale haka ba, kuma da ba a bari kin saka kaya ba, ki gaya mini gaskiya da me ki ka ƙone?" Malamin yayi maganar cikin zare ido.

"Da ruwan zafi"

"Mamanki ta san kin ƙone?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"Meyasa baki gaya mata ba?"

Cikin kuka ta ce "Ai ban san in da take ba"

"A'a to ina mutanen gidan da ki ka ƙone ɗin, ba ƴar gidan dr. Yahaya bace ne?" Ta ɗaga kai alamar eh.

"Malama zuhra, a nemo abun hawa a kai yarinyar nan asibiti a dubata, ke kuma maryam mu je office ɗina sai na hora ki"

Maryam ta fashe da kuka tana magiya, cikin ƙarfin hali ummi ta ce "Malam dan Allah kayi haƙuri, ba ta san ina da ciwo ba, na yafe mata ai"

Ya ce "To zan duba, tashi a kai ki asibiti, daga nan a mayar da ke gida".

A asibitin ma, ma'aikaitan sun yi faɗa sosai a kan sakaci da lafiyar ummi, dan da ƙunar zata iya zama infected ta taɓa sauran sashin jikinta, bayan ta zama gyambo.

Suka ce lallai a kula da ummi, a samu ƙunar ta warke, kuma a zurfafa bincike dan wannan ƙunar ba tayi kama da ta ruwan zafi ba.

Ummi ta sha kuka, saboda yadda aka dirje ƙunar nan tas, aka saka magani, aka bata magungunan sha.

Sai dai da malama zuhra ta ce ta kwatanta musu gidansu a mayar da ita ta ce "A'a a mayar da ni makaranta, idan aka tashi zan ɗaukko ƙannena daga islamiyya"

"A haka da wannan ciwon" malamar tayi maganar tana kallon ummi.

Ummi ta jinjina mata kai.

"A'a ba zai yiwu ba, mu je gidan naku, a saka wani ya ɗaukko su".

Kuka ummi ta fara tana yi wa malamar magiya, a kan ta ƙyaleta a tashi ta ɗaukko su daga makaranta.

Ba ta da zaɓi, suka koma islamiyyar ta gaya wa shugaban makarantar duk abun da ya faru.

Suka yi waya da kawu yahaya, suka tattauna, ya ce a mayar da ummi gida, zai yi waya makarantar yaran, su jira yayansu sai su taho tare.

Da ƙyar ta yadda da hakan, saboda tana tsoron abun da ka iya biyo bayan rashin ɗaukko su daga makarantar.

Cikin sa'a malamar ta fuskanci yanayin da ummi take ciki na tsoro, dan haka a ƙofar gida suka yi sallama ummi ta shiga.

Har ta tafi ɗakinta ba wanda ya san ta dawo, saboda ana ta hada-hada a gidan, ƴan barka na shige da fice.

Ta kasa fitowa daga ɗakin, saboda tsoron kar su kuma dukanta.

Sallamar kawu yahaya ta ji a ɗakin, ta tashi da sauri, tana gaishe shi.

"Ya jikin naki?"

"Da sauƙi"

"Mu ga ciwon" a hankali ta ɗaga masa cikinta ta ƙonu sosai da sosai, ya zubawa ƙunar ido sannan ya kalleta ya ce "ya aka yi ki ka ƙone?"

"Da ruwan zafi" ta faɗa tana ƙiƙƙifta ido, saboda ta san ƙarya tayi.

"Meyasa baki gaya mini ba?" Tayi shiru ba ta ce komai ba.

Wannan ƙunar ba ta yi kama da ta ruwan zafi ba, ki gaya mini gaskiya.

"Da gaske nake..." Ba ta ƙarasa ba ya ce "Shaidar iron tayi, kalli yadda shape ɗin ƙonuwar ya tafi, ki gaya mini gaskiya".

Ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Idan na gaya maka ba zaka gaya wa maman su Abdul ba?"

"Ba zan gaya mata ba"

"Ina guge Abdul ya ce zai tayani, ya ƙonawa mamansu riga, ta zata nice shi ne anty rahama ta danneni, suka ɗora mini iron. Dan Allah Abba ka gaya musu bani na saka anty farida ta faɗi ba, sun ce ni na kusa kasheta wallahi ba ni ba ce, fitsari na yi da na ji zafi, shi ne ta zame ta faɗi" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Ayshercool
08081012143
What's app only please 🙏
                         *CUTARWA*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

P16

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI

P16


Ƙurriii kawu yahaya ya yi wa ummi da ido, abun ya girmame shi, bai taɓa zaton mugunta da zaluncim da farida za ta yi wa ummi zai kai haka ba.

Ya sauke numfashi da ƙyar ya ce "Ya isa haka ki share hawayenki, ki daina kukan ya isa ba zan gaya mata ba, kuma na san ba zaki taɓa iya cutar da kowa ba, duk wanda ya cutar da ke, shi ma Allah ba zai bar shi ba, ki yi haƙuri ummi, in sha Allah gobe in Allah ya kaimu zamu koma asibiti, tun da yau an yi dressing ɗin.

Mun yi magana da malaman islamiyyar ku, na biya kuɗin maganinki, sannan sun ce ki zauna a gida sai kin warke".

Ummi kamar ta ce masa gara ta cigaba da zuwa a haka, dan ta san zamanta a gidan nan ba hutawa za ta yi ba, amma ta dake ta ce "To kawu na gode sosai"

"Kar ki damu, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana ummana"

Murmushi ummi tayi, tana so ta ji ya kirata da ummana ko ummina, hakan yana yi mata daɗi, kuma yana tuna mata da maman da babanta.

Ya ce "Au, na manta ban gaya miki ba, mun kusa komawa sabon gida fa, bamu taɓa zuwa kin gani ba ko"

Ta faɗaɗa murmushin ta ta ce "Allah ya nuna mana, wannan wa za a barwa, na ga shima mai kyau ne"

"To ko in bar miki, tun da kin fi son nan?"

Murmushi ta yi ta ce "Ai ni macece ba zan iya zama a gida nikaɗai ba, amma ina son gidan nan"

"Can yafi kyau ai, idan muka koma zaki gani"

"To Allah ya sanya albarka, to nan su iya ne za su dawo su zauna?"

Sai da ya ƙara kallonta da sauri, ya ce "Su iya kuma?"

Ta ce "Eh, su baro ƙauye su shiga makarantar islamiyya, makarantar mu har da matan aure da tsofaffi suna zuwa asabar da lahadi"

Bakomai a ranta ta faɗi hakan, kawu yahaya yayi murmushi saboda magana tayi cikin magana mai ma'ana,
End Ads