x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 58 - CUTARWA

  • 171001 words
  • 174000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 519

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
menene?"

"Haba dan Allah, tayaya zan iya haɗa ido da Alhaji, kuma sai azo duba ni, da ka yi shiru ba wanda ya sani sai mu biyu shikenan"

Raihan ya yi murmushi ya ce "Kunya ki ke ji ace kin yi ɓarin cikin ƙaninki" yayi maganar yana wani irin miskilin murmushi.

Murguɗa masa baki tayi, shi kuma ya din ga dariya, ganin duk yadda ta damu.

Ko awanni biyu ba ayi ba, sai ga Hajiya tare da Alhaji har da abinci, suka zo duba ummi.

Raihan ko a jikinsa, ita kuwa ummi kamar tayi fuka-fukai ta gudu dan kunya.

Bayan sallar magariba aka sallame su, suka koma gida.

Washegari da safe sai ga Abdul tare da noor, dan raihan ya gaya wa Abdul.

Sai dai duk zuwa dubiyar nan, ko da wasa farida ko a waya ba ta yi wa ummi sannu ba.

Abun ya din ga damun ummi, tare da jinjina irin ƙiyayyar da farida take yi mata, da ma ba ta saka ran ganin mami ba ma.

Dr. Kuwa dama yana uganda, ya je yin wani course a ƙoƙarin sa na zama professor.

Sai da noor ta kwana uku a gidan ummi, sannan ta koma gida.

Abun da ya ƙara bata kunya da Salim ya zo dubata shi ma, gashi raihan a gabansa yake nuna irin soyayyar da yake yi wa ummi.

Duk wanda ya zo duba ummi ya san tana samun kulawa daga mijinta.

Cikin ikon Allah ummi ta warware, sai dai kullum sai raihan yayi zancen dama cikin nan bai zube ba, kuma sai ya roƙi Allah ya kawo musu wani.

Sai dai a wannan halin mami ba ta ɗaga wa raihan ƙafa ba, wurin cigaba da ƙwarzabarsa a kan yin aure, tare da barazanar raba shi da ummi. Duk da mami mahaifiyarsa ce, ya ji takaicin rashin jajanta wa ummi abun da ya same ta, ko ba komai a sanadin ɗanta lafiyarta ta taɓu, ko asarar jininta da ta yi ya ci ayi mata sannu, amma mami ba ta nuna hakan ya dameta ba, balle tayi mata sannu.

Kasancewar weekends ne, raihan yana gida, ummi ta sha kwalliyar ƙananan kaya, tana aiki a kitchen tana waya da Abdul tare da sanar masa cewa raihan ya ce ya je main branch ɗin su na Kano, game da batun bashi aiki.

Abdul ya ce "Ummi ina fatan ba takura masa ki ka yi ba, kuma kar hakan ya cigaba da haifar miki da matsala tsakaninki da sirikarki"

"Kar ka damu yaya, ya ce ba wani abu, ai ban taɓa roƙonsa wani abu makamancin haka ba"

"To shikenan ummi, zan je in sha Allah, Allah ya saka miki da alkhairi"

"Haba yaya meye na godiya kuma, ka ce wa noor da an yi hutun makaranta ina jiranta dan Allah ta zo mu zauna"

Yayi murmushi ya ce "Zan gaya mata, ina ji tana cewa idan aka cigaba da takura mata za ta bar musu gidan ta dawo gidanki, kin san mutuniyar taki"

Ummi ta yi dariya ta ce "Zuma ga zaƙi ga harbi ba" suka yi dariya sannan suka yi sallama.

Har ta ajiye wayar, ta ji kamar ana kallonta, tana waiwayawa ta ga maryam a tsaye tana yi mata wani irin mugun kallo. Ras! Gabanta ya faɗi, dan tun da ta auri raihan ba su haɗu ba, mijinta a kudu yake aiki, suna can tare.

Cikin dakiya ummi ta ƙaƙalo murmushi, duk da ba ta ji daɗin yadda maryam ɗin ta ganta ba, yanayin shigar jikinta mijinta kawai yakamata ya gani.

"Babbar baƙuwa ce haka yau ta sauka, ba sanarwa balle in yi shirin karɓar ki"

"Dalla rufe mini baki, asararriya tun da ba gidan ubanki bane kin isa na sanar miki da zuwa na gidan ƙanina, wadda ta bawa abun kunya gaba ba baya ba"

Ummi ta ce "Haba Maryam me yayi zafi?"

A hasale maryam ta ce "Ban sani ba, kwaɗayyiya mayyar abun duniya, kodayake barewa ba ta gudu ɗan ta yayi rarrafe, na samu labarin a garin mugun son abun duniyar babarki, babanki ya mutu, ita kuma ta hukace"

Ummi ta girgiza kai ta ce "Cin mutuncin har ya kawo kan iyayena, Allah ya baku haƙuri maryam daga ke har mami, aurena da raihan ba shirina bane, Allah ne....

Maryam ta ɗaga mata hannu ta ce "Yi mini shiru, ba ki da wata magana da zaki kare kanki malama, kalleki dan Allah wai raihan ƙanin bayanki, shi ki ka aura wai saboda shi ki ka yi wannan shigar ko? Kuma saboda baƙin abun kunya har ki ɗau cikin raihan, saboda tsabar abun kunya raihan fa, ni ban ma san yadda aka yi ki ka yi wannan gogewar ba, ko rantsuwa zan yi ba zan kaffara ba, bokaye ki ka bi ki ka aure shi, kuma wallahi tun da na zo garin nan kin shiga uku, sai kin gudu da ƙafafuwan ki, mummuna dangin kwaɗayi da asiri, kuma ba zaki taɓa haihuwa ba ki haifo mana mahaukata da munana ba"

Ummi ta yi murmushi mai ciwo, ta tattare gashin kanta, ta mayar bayanta, tare da goge hawayen fuskarta, ta din ga tuno maganganun raihan na ƙwarin gwiwa da ƙoƙarin kare kanta a duk lokacin da wani ya ci zarafin ta, ta kalli maryam ta ce

"Maryam! Da aurena da naki duk sunansu aure, wataƙila nawa ya ɗara naki, tun da ke da ki ke kyakywar ma ba a baki sadakin da aka bani ba. Kuma cikin raihan yanzu na fara ɗauka sai na tarawa raihan zuriya, ko zaki mutu, dama na shiryawa arangamata da ke, idan kin isa maryam ki saka raihan ya sake ni, ki zo ki aure shi. Batun bin bokaye kuma kema da zaki samu irin bokana na tabatta zaki bi, dan wasu sai su shekara suna asirin bai ci ba"

Buɗe baki maryam tayi tana tunanin anya wannan ummin da ta sani ce? Yaushe ta waye tayi baki, ummi ta fice ta barta a wurin.

Tana shiga ɗaya falon ta tarar da raihan ya fito da dogon wandon bacci a jikinsa fari, yana ganinta ya rausayar da kai ya ce "Ke na fito nema, baki tashe ni in karya ba"

Ba tare da ta nuna masa wani abu ba ta ce "Na fara shirin ɗora abincin rana ne, barka da fitowa maigidana na kaina" ta nufe shi, ya buɗe hannayensa ta shiga jikinsa ta rungume shi.

Ya saka hannunsa ɗaya ya riƙe ƙugunta, ɗaya kuma ya shafa kanta ya ce "You look cute baby" sai dai bai kai ga aikata abun da yayi niyya ba, maryam ta faɗo falon.

Mamaki ne ya kama raihan, dan bai san ta zo ba, ummi ma ta yi pretending da ba ta san da zuwanta ba ta juya da sauri tana kallon in da maryam take.

"Maryam, wannan ai saɓa dokar addini ce, ai a main falo yakamata ki tsaya ki nemi izini, kawai sai ki faɗo mana haka babu ko sallama?".

"Sallama, ni ka ke gaya wa haka raihan, saboda wannan mummunar yarinyar da ka aura, me ka gani a jikin ummi da babu a jikin matan garin nan ka aureta dan asara?"

Raihan ya sosa kai yana murmushi ya ɗago ummi daga jikinsa ya ce "Abubuwa da yawa mana, next time karki sake shiga wurin ma'aurata anyhow please, ba girman ki bane"

Ummi ta yi murmushi ta ce "Sannu da zuwa Maryam, yau ina da babbar baƙuwa"

"She ruin my enjoyment" yayi maganar a taƙaice.

Maryam kuwa ta ɓarke da masifa ta babu gaira babu dalili, tana alwashin sai ta raba auren nan, dan asiri ummi ta yi wa raihan.

Ummi ta yi shiru, zuciyarta na yi mata zafin cin zarafin da maryam ke yi mata, kuma ta ƙi ɗaga jikin raihan.

A hankali ya ce wa ummi "Go and get some rest, kin san baki gama warkewa ba" ta jinjina masa kai, ta nufi ɗaki.

"Dubeta dan Allah, ko kunya ba kya ji"  sai dai abun da Maryam ba ta sani ba, har da hassada ta kamata, gidan da raihan ya saka ummi ya fi nata haɗuwa, kuma gaba ɗaya yau ta nemi munin ummi ta rasa, a dire take ba abun da wata ƴa mace za ta nuna mata. Ga wani irin ƙamshi da take yi, yau ta ga ainihin kyawun surar da Allah ya yi wa ummi. Dan da ta juya baya ma tana tafiya, ga gashin ta ya kwanta a bayanta, kamar ba bahaushiya ba, dole yaro ya rikice ta faɗa a ranta.

Ummi na barin wurin ya haɗe rai ya kalli Maryam ya ce "Idan har kin san zaki zo gidana ki ci mutuncin matata kar ki sake zuwar mini gida ki ɗaga mini hankali, Mami idan tayi ta isa ne, ke kuwa kin yi kaɗan duk rashin mutuncin da na yi miki ke ki ka saya".

"Ni ka ke cewa kar na sake zuwar maka gida? Kodayake ba laifinka bane ba, an kai sunanka gaban bokaye an mallakeka"

"Bakomai, ni bokan ya taimakeni da ya mallake mata ni, kar ki sake zuwar mini gida ki ɗaga mata hankali, definitely na san sai ta yi kuka cin mutuncin da ki ka yi mata".

Maryam ta ja numfashi ta jinjina kai ta ce "Bayan cin mutuncin da ta yi mini, kai ma ka ɗora naka, sai na nuna wa Salma haryanzu kanta a kwano yake, yarinyar da na taimakawa a baya mara galihu irint...

"Kema ta taimaka miki, dan a irin daƙiƙancinki, ba dan taimakon nata ba asarar kuɗin tara za ayi a banza, dan haka juna ku ka taimaka" suka yi wa juna kaca-kaca suka yi faɗa ta tafi ta bar gidan.

Ummi kuwa ta din ga saƙe-saƙe a ranta, tabbas yanzu tun da har ta riga ta yi aure ta bar gida, raihan ne kawai ya rage mata source of happiness, idan ba ta yi da gaske ba, Maryam za ta iya aikata abun da ta ce, dan ba mutunci ta cika ba, dan haka a wannan karon ba ta tunanin za ta iya ɗaga wa maryam ɗin ƙafa.

Raihan ya bi ta ɗaki ya din ga rarrashin ta. Sai dai ta kasa daurewa, sai da ta din ga yi masa kuka yana rarrashinta.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ga sunan Yaya Salim, ya ɗaga suka gaisa, Salim ya ce "Ina waje"

Raihan ya ce "Yaya ka shigo falo, gani nan" ya ajiye wayar ya ɗauki jallabiyarsa ya ce "Yaya ne ya zo, ki wank fuskarki ki zo"

"Allah ya sa ba laifi na yi masa ba"

Ya girgiza kai ya ce "Haba dai, yaya Salim ya ce ke ƙanwarsa ce, da ya karɓo amanarta a wurin mama, idan ban kula da ke ba, ni da shi ne" Ummi ta yi murmushin yaƙe, ta sanya kaya suka fito.

Sai dai tun da suka fito yake bin su da kallo, suka zauna ummi ta gaishe shi, ya amsa tare da cewa idan ina ganinku taren nan, sai na ji kamar nima na yi auren nan.

Da sauri Raihan ya ce "Yaya da gaske, dan Allah ka yi"

Salim yayi murmushi ya ce "Ya ƙarfin jikin naki" raihan ya ce "Ta ji sauƙi sosai"

"Kai na tambaya?"

Raihan ya ce "Allah ya baka haƙuri".

"Meyafaru ne? Na ga kamar fuskar ku da damuwa, mussaman ummi".

Ummi ta ce "A'a yaya, komai lafiya ƙalau"

Salim ya gyara zamansa ya ce "Yadda ku ke ɗin nan gwanin sha'awa yayi wuri ace kun fara samun saɓani, duk da ma bana tunanin hakan ne, na san akwai abubuwa marasa daɗi a ƙasa, amma ku yi haƙuri da juna".

Raihan ya ce "In sha Allah babban yaya"

Ya ce 'Masha Allah, dama zan wuce ne na ce bari na zo na sake dubata, amma Maryam ta zo gidan nan ko?"

Gaba ɗaya suka kalle shi a tare.

Raihan ya ce "Eh ta zo"

"Tun da na ganta a gida jiya na san za ta zo, kuma yanayin ta ya nuna mini ba zuwan arziki tayi ba, ta yi miki wani abu mara daɗi ko?"

Ummi za ta yi magana raihan ya ce "Haka ne yaya, amma in sha Allah i can handle it"

Salim ya miƙe ya ce abun da nake son ji kenan, bai sake ce musu komai ba ya fice.

"MD meyasa zaka gaya masa haka?"

"Wai dan kin ga yana shiga sabgar aurenmu? Idan na yi masa ƙarya a gabanki zai zageni, ba a ayi masa musu, na gaya miki kallon ƙanwa yake yi miki,ko na ɓoye masa idan ya gano na kaɗe"

Ummi ta ce "Ni dai duk da haka da baka gaya masa ba, ai na san da ta tafi shikenan.

Salim kuwa fitar maryam ya gani a mota, ya samu nihal ya ritsata ya tambayeta ina maryam ta tafi daga zuwanta jiya? Ba ta ɓoye masa ba ta gaya masa gidan raihan ta tafi.

Maryam kuwa bayan komawarta gida, ta samu mami ta zayyane mata abun da ya faru da wanda bai faru ba, wanda hakan ya ƙara tunzura mami, mussaman da maryam ta gaya mata baƙaƙen maganganun da ummi ta faɗa wanda suka ba ta mamaki.

Bayan la'asar Salim ya shiga sashin mami, wanda rabonsa da sashin, yayi shekaru. Mami na cin abinci maryam kuma na kallo yaranta na ta wasa a falon.

Ya tsaya a kan Maryam ya ce "Zuwa na yi nayi miki gargaɗi, idan ki ka sake taka ƙafarki a gidan raihan, ki ka ci zarafin matarsa wallahi sai na casa ki, ba soja ba ko bindiga ki ke aure tun da ke mahaukaciya ce"

Mamk ta miƙe tsaye ta ce "Saurara kai a wa?".

"Ni a wanta, wanda na isa na saka na isa na hana, wallahi ba zan yi kaffara ba, na sake jin labarin kin je masa gida kin yi masa hauka, sai na ci.... Ya ɗirka mata ashar mai zafin gaske.

"Shaye-shayen ka yi zaka zo ka sauke iskancinka a nan?"

Salim ya ce "Ras nake, sai dai da sannu zaki gane manufata, let her make another scene zaku gani" fuuu ya fice kamar zai tashi sama.

"Yaushe yaron nan ya samu kusanci da raihan, har yake shiga cikin lamarinsa haka?"

Maryam kamar tayi kuka ta ce "Mami ƙarata suka kai masa kenan? Mami raihan ya fifita matarsa a kaina, mami ki yi wani abu a kai tun kafin raihan yafi ƙarfin control ɗinki".

Babu tunanin komai, ta hau kan maganar ta zauna.

Ummi tana sallar magariba a bedroom ɗin ta, ta ji yo hayaniya a falo, wanda ko tantama ba ta yi muryar mami ce, mamin da tun da aka yi bikinsu ba ta taɓa takowa gidan ba.

Bayan ta idar da sallar, cikin tsananin fargaba da tashin hankali ummi ta fita falon, raihan yana ta ƙoƙarin shawo kanta daga masifar da take yi.

"Mami sannu da zuwa" riƙe sannu da zuwanki, idan kin so ma ki kirani da bilki, dan ban haifeki ba, saƙon da ki ka bawa maryam na ji, na zo kuma in nuna miki na isa da ɗa na, kai kuma ka aiwatar da abun da na ce"

"Mami dan girman Allah ki yi haƙuri, mai zai sanya na aikata haka babu wani dalili".

"Ni ka ke gaya wa haka? To ka saka a ranka zaka canza wata uwar bani ba, kai ba ka isa ba ma, wallahi sai ka saketa raihan na riga na rantse maka, ko in yi maka abun da ba ka zata ba" tayi maganar tana watsa masa biro da takarda.
Tuni jikin ummi ya fara rawa, ta ji numfashin ta kamar zai ɗauke, da sauri ta bar falon, ta tafi ɗaki, lallai tsuguno ba ta ƙarewa rayuwarta ba.

Ta ɗauki ƙaramar akwatin ta, ta zuba kayanta, ta buɗe wurin da raihan yake zuba kuɗi ta ɗiba ta zuba a jakarta ta ɗauki ATM ɗin ta ta fito, tana zubar da hawaye.

Ta tarar da raihan a zaune ya dafe kansa, cikin tashin hankali bai yi zaton mami zata aikata masa haka ba.

Tana ganin ummi ta ce "Ita akwatin ai na san ba daga gidan ubanki ki ka zo da ita ba, dan haka ajiyeta" ummi ta durƙusa ta kwashe kayanta ta ajiye akwatin.

Raihan ya miƙe yana kiran sunanta.

"Wallahi ka taka ka bita ban yafe maka ba!!!. Ummi ko waiwayawa ba ta yi ba ta fita.

"Kuma ka san duk yadda zaka yi ka kareni a wurin babanka, wallahi ka kuskura ka gaya masa umarnina ne ka rabu da ita sai na saɓa maka, ba zan zuba ido ka zama soko ba"

Zuciyar sa na tafasa ya ce "Mami kina ganin wannan hukuncin shi ne farincikin ki ko? Ni kuma kin ƙuntata mini, shikenan tun da haka ki ka yanke kin isa ne, na gode"

Ƙura masa ido ta yi ta ce "Raihan kuka zaka yi dan na rabaka da masifa" ya kalleta hawaye na gangarowa daga idonsa, ya san komai zai ce mata ba zata fuskanci irin son da yake yi wa ummi ba.

A falon gida ummi suka yi karo da farida, da ita da kausar da alama ba su daɗe da dawowa daga unguwa ba.

Ta ƙarewa ummi kallo da kaya a hannu ta ce "Lafiya?"

"Ya sake ni ne" ta faɗa a hankali.

Kawai farida ta rafsa guɗa ta ce "Har an yi an gama? Soyayyar da ɗaga hancin ya ƙare? To wallahi ba zan riƙe bazawara har karo biyu ba, ki nemi wurin zuwa ba dai nan gidan ba!!!.

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE,
End Ads