x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 48 - CUTARWA

  • 141001 words
  • 144000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 524

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
abun kunya ne ma a gare shi ace bai yi wa ummi kayan lefe ba. Haka yayi ta wasi-wasi yana nazarin abun a ransa.

Farida ba ta damu da in da ummi take ba, sai dai tana tambayar dr. Tana fatan ummi ta tafi kenan, amma yayi mata banza ya ƙyale ta.
Noor kuwa sai bin sa take tana tambayar sa, wai yaushe ummi za ta dawo, ita fa gidan babu daɗi idan ummi ba ta nan, ya ce mata zata dawo nan ba da daɗewa ba.

Ummi a gabanta aka fara haɗa kayan turarukan wutanta, wai akwai turarukan da sun fi shekara a binne a ƙasa ana tsuma su.
Yaya maryam ta kasa zama, kullum tana yawon kasuwa ita da mama, matar malam wurin yi wa ummi sayayyar kayan aure.
Ita babban abun da yafi faranta mata, bai wuce kasancewar ta da babarta ba.

Mami ta ƙara matsanta wa raihan, ga gefe guda kuma, Safiyya sai ta wani kira shi wai za ta gaishe shi, duk rashin son wulaƙanta ɗan Adam irin na raihan, ƙarshe sai da yayi blocking ɗin ta, dan ta daina damunsa da kira.

Ya cewa ummi zai zo Maiduguri ya ganta, ya kuma gaida mama, amma gudun matsala ya sanya ta ce masa ya bari ta kusa dawowa.

***
Sai da ummi tayi sati uku cif, sannan dr. Ya koma ɗaukar ta, kamar ta ce masa dan Allah ya barta a nan, amma sai ta ji nauyin hakan ta kasa, kayanta ƙwaya biyu da ta je da su, sai da aka ɗinka mata kusan kala goma a can, kuma tuni suka haɗa kayan gyaran jiki masu haɗe da turarrruka, ummi ta fara amfani da shi.

Yaya maryam sai jaddada mata take yi, kar ta yi wasa da kayan gyaran da aka ba ta ta yi, da sabulan da aka haɗa mata.

Mariya ta kalli dr. Ta ce "Ka yi mini alƙawarin ba wurin Iya zaka mayar da ita ba?"

Yayi murmushi ya ce "Ai aronta na ce ki bani, ba zan kai miki ita wurin Iya ba"

"To ai zaka dawo da ita ko?"

"In sha Allah"

"To dan Allah ka kula mini da ita sosai da sosai, kar ka bari ta yi kuka"

"In sha Allah zan kula da ita sosai da sosai"

Ta kalli ummi ta ce "Kar ki yi musu kuka kin ji ummi, ban da ƙyuya da kuka, ba ruwanki da yara, kar ki je su din ga dukanki kin ji ko?"

Ummi ta riƙe hannunta ta ce "To mamana, me ki ke so na taho miki da shi idan zan dawo?"

Ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Bakomai, ni dai kawai ki dawo, ba dan ina jin kunyar kawu yahaya ba, ba zan bashi ke ba"

Ummi ta cigaba da kallon mariya tana jin daɗi.

Da ƙyar suka rabu suka nufo hanyar Kano.

Duk rashin surutun ummi, haka ta sake ta din ga yi wa kawu hira tana bawa kawun labarin mamanta.

Bayan azahar suka sauka a kano, noor kamar ta mayar da ummi cikin ta, dan murnar ta dawo.

Ummi ta shiga har falo, ta ce wa farida sun dawo, ta amsa mata a yatsune, sai dai fuskar inteesar kawai ta kalla ta san matsala ce ta kawota gida.

Ummi ta koma ɗakinta, suka din ga hira ita da noor tana bawa noor labarin mamanta.

Noor ta ce "Kuma ki ka yadda ki ka dawo, wallaahi idan ni ce ba zan dawo ba, amma na san saboda yaya raihan ki ka dawo ko?"

Ummi ta ce "Ban sani ba"

Suka din ga dariya, noor ta ce "In gaya miki, Inteesar mijinta ya ɗauki amaryarsa sun tafi umara, shi ne take kuka wai ba a tafi da ita ba"

"To waye ya tambaye ki?"

Noor tayi shiru tana ƙifta idanu.

Haka nan take murna, ta san yau za ta ga raihan, ta rasa dalilin da ya sanya take murna.

Haka nan ta samu kanta da yin shirin haɗuwa da shi.

Ta ɗauki kayan tsaraba da ta zo da su, har da su kayan turaren wuta ta kai wa farida, ta karɓe ba tare da godiya ba.

Bayan sallar magariba ummi ta saka rigar atamfa bubu, tana ta fama ta ɗaura ɗankwali, abu ya gagara saboda ba ta saba ba, ƙarshe noor ce ta ɗaura mata da ƙyar, shima gashin ya ƙi rufuwa, sai da ta saka hula sannan aka ɗaura ɗan kwalin.

Ta yafa mayafi, tana ta rufe-rufe tana tunanin anya za ta iya fita a haka? Kiran wayarsa ta gani, ta tashi ta kalli noor ta ce "Anya in fita a haka kuwa?"

"Wallahi kin yi kyau, kin rufe ko ina kuma"

Da ƙyar ummi ta iya fita, tana ta kare jikinta, ta ƙarasa in da yake.

"Oyoyo sweetheart, long time"

Tayi murmushi ta zauna, tana kawar da kanta gefe.

"Congratulations once again, ya ki ka baro mini maman?"

Ummi ta yi murmushi ta ce "Tana lafiya ƙalau"

"Kin bata labarina kuwa?"

Ummi ta ce "Idan na yi mata babu lallai ta gane ma"

Ya ce "Ba ki yi niyya ba dai, zan je da kaina mu gaisa ai"

"Ka gama yajin?"

Yayi murmushi ya ce "Ke ma haka zaki ce?"

Ummi ta ce "To ba yajin ka yi ba, ko kunya ba ka ji ba?" Yayi dariya ya ce "Na samu mafita ai, kin yi kyau sosai da sosai wallahi, Allah ya nuna mana ranar nan lafiya babyna" ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kanta.

Kausar ce ta nufo in da suke zaune, dan haka yayi shiru yana kallon ta.

Cikin mamaki take kallon raihan, yanzu wannan ne zai auri ummi? Wannan yaron, amma kuwa tayi asara, ko kuma shi yayi asarar kyakykyawan matashi kamar wannan ya auri ummi. Ta yi maganar a zuciyarta

Cikin gadara ta ce "Ke ki zo maama tana kiranki, wa ki ka barwa yin abincin daren da haryanzu baki ɗora ba," tayi maganar cike da son wulaƙanta ummi a gaban raihan.

Raihan ya ce "Tana magana da mijinta ne, idan kun matsu ku ci, ku dafa, tana buƙatar hutu, tun da yau ta dawo daga tafiya, kuma ina buƙatar yin magana da ita"

Zare ido ummi tayi ta ce "Na shiga uku, raihan"

"Shhh" ya ɗora yatsansa a kan lips ɗin sa yana zare mata ido.

Ya sake kallon kausar ya ce "Ki koma ki ce ba za ta yi ba"

Ayshercool
08081012143.


FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

*CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

35

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe

35

Galala kausar ta buɗe baki tana kallon raihan.

"Ko ba ki ji me na ce ba ne?" Yayi maganar yana kallon kausar.

Ta kalli ummi, ta ce "eh lallai, zaki shigo zaki haɗu da maama"

Raihan ya ce "Idan ta shigo kar ku bar ta da rai" kausar ta juya fuuu ta tafi.

A rikice ummi ta ce "Raihan, meyasa zaka yi haka? Ka san me zaka jan yo mini ne?"

Ya ƙare mata kallo ya ce "Idan kin koma gidan, ki tsaya ki zuba musu ido su illata ki, ummi ba fa kowanne lokaci ne haƙuri yake maka amfani ba, meyasa da ba a ce sai kin yi girkin ba sai da na zo? Dole ki rage wannan shirun naki, kuma ki shirya tsaf, domin akwai ƙalubale a zaman da zamu yi, zaki fuskanci challenge daban-daban dole ki din ga ƙoƙartawa, a yanzu dai duk abu ba zaki daku ba, dan haka kar ki bari wani abu ya baki tsoro, idan ma dukkan ne ki rama, ki daina zama ana cin kashi a kanki, tun da kin kusa bar musu gidan"

Ummi ta yi shiru tana nazarin matsalar da raihan ya jefa ta a ciki.

Ya basar ya ce "Baki bani labarin Maiduguri ba, ya ki ka ga garin, ya kuma ki ka ji da ki ga mama?"
Duk da a tashin hankali take, sai da ta yi murmushi, ta ɗan saki jiki, ta bashi labarin yadda ta ga garin, da abubuwan da suka faru.

Har ta fara mantawa da matsalar da raihan ya jefata a ciki.

Da zai tafi ya zura hannu a aljihunsa, ya ajiye mata kuɗi, ya ce "Na san ba zaki rasa buƙatunki ba, sannan ranar monday zamu je banki a buɗe miki account, zan saka miki kuɗin kayan lefenki a ciki"

Ta kalli tudun kuɗin da ɗan yawa, ta ce "Ka bar kuɗin nan mana, hidima ce a gabanka sosai"

Ya girgiza kai ya ce "Kar ki damu, ai ba wani kyautar kuɗi nake yi miki ba, kina buƙatar kuɗi kuma na san ba tambayata za ki yi ba, abu na gaba kuma shi ne, saura ki shiga cikin gidan nan, su yi miki magana ki zauna kina kuka, ina da cid na kin sani, idan ki ka bari noor ta ce mini kin zauna kin yi kuka, ni da ke ne, ki kula mini da kan ki amaryata" Ummi ta yi zuru da ido tana tunanin irin tashin hankalin da zata iya fuskanta.

Kausar kuwa jiki na tsuma ta je ta sanar wa farida abun da raihan ya ce, babu kunya a gaban ƴaƴanta ta kuza ashar ta miƙe tsaye jikinta yana tsuma.

"Wai wani ɗan iska ne ma wanda za ta aura ɗin? Wani matsiyacine ne, bari in je in ga ɗan gidan uban waye na ci mutuncin sa daga shi har ita".

Kausar ta tare ta ta ce "Wallahi wani ɗan yaro ne, dan dai yana da jiki ne, amma wallahi ba ki ganshi ba"

"A'a bari na ƙarasa na je na ga wani shegen ne, ita ma ba ta isa ba balle shi"

Kausar ta ce "A'a maama, ba mutuncinki bane ba ba girmanki bane, ai kin fi ƙarfin haka, dan Allah kar ki je, ki jira ta shigo ki ci ubanta"

Noor ta ƙyalƙale da dariya, har da tuntsurawa, ta ce "Hmm wallahi maama baki san yaya raihan ba, ba fa matsiyaci bane da ki ka faɗa, ranar da aka kawo kuɗin auren anty ummi, kin ga motar babansu kuwa?"

"Rufe mini baki kan na zo na tatsile ki, munafuka kamar na saka da ke" noor ta tura baki tare da yin shiru.

Sai da ummi ta nufo shigowa cikin gida, ƙirjinta ya tsananta bugawa, wani irin tsoro ya shige ta, ta din ga tunanin yaya za ta yi.

Ganin har ta shiga ɗakinta babu wanda ya ganta, ya sanya ta rufe ƙofarta ta ciki, tana fargabar abun da hakan ka iya haifarwa.

Farida na zaune na jiran shigowar ummi, dan ta san dole za ta shigo ta ce za ta yi girkin, dan haka ta yi niyyar wulaƙanta ummi, sai dai shiru babu ummi babu dalilinta.

A fusace farida ta kasa jurewa, ta tafi harabar gidan, kausar tana riƙeta tana ƙoƙarin hanata.

Sai dai suka tarar da kujerun babu kowa, ta tambayi mai gadi, ya ce mata tun ɗazu suka shiga cikin gida. cikin zafin rai da zage-zage ta nufi ɗakin ummi, tana wani irin bugun ƙofar kamar za ta hau iskokai.

Noor ta fito ta ce "Maama maƙwabta fa suna jin ki, kina ta ɗaga murya"

Banza ta yi wa noor, ta cigaba da bugun ƙofar ɗakin ummi, tana ɗura mata ashar kamar bamagujiya.

Ummi kuma wani irin tsoro ya kamata, ta kasa buɗewa tsoro take ji, ba ta san me faridan za ta iya yi mata ba idan ta buɗe.

Sai da farida  ta ji ƙarar motar dr. Sannan ta saurara da bugun tana huci, dr. ya ƙaraso ya tarar da su a tsaitsaye, ya ce "Lafiya kuwa?"

Farida ta ce "Ina fa lafiya? wallahi na gaji, wai ba wurin uwarta ka kaita ba, meye na dawo da ita gidan nan, to wallaahi barin gidan nan za ta yi, ko a kan bola uwarta ta take, ta je su ƙarata"

Dr. Ya ce "Wai meyafaru ne?"

"Sai ka yi magana ta buɗe ƙofar ɗakin ka tambayeta ka ji, tun da kai ka isa da ita, ni tana ganin sa'arta ce"

Dr. Ya bubbuga ƙofar ɗakin ummi ya ce "Mamana ni ne buɗe ƙofar"

Cikin tsoro da fargaba ummi ta buɗe ƙofar, kallo ɗaya yayi mata ya san a tsorace take.

"Meyake faruwa?" Ya sake tambaya.

"Dole ka ce meyake faruwa tun da ta riga ta raina ni, wallahi ba zan cigaba da zama da yarinyar nan ba, ka mayar da ita wurin uwarta wallahi ba zan cigaba da zama da ita ba"

Cikin zafin rai ya ce "Dan Allah ki nutsu ki yi mini bayani, ummi ba ta taɓa yin haka ba, me ki ka yi mata?"

Cikin takaici farida ta ce "Au tambayata ma ka ke yi me na yi mata?"

"Dr. Maama ce fa ta aika anty kausar, wai ace ummi ta zo tayi girki alhalin yaya raihan ya zo, aikuwa ya ce ba za ta zo ba, anty kausar ta je ta yi girkin, ko su kwana da yunwa"

Gaba ɗaya suka tsaya suna kallon noor, da ke wassafa abun da aka yi.

Ummi ta yi saurin cewa "Dan Allah anty ki yi haƙuri, wallahi ba ni na faɗa ba, kuma tsoron abun da ya faru da rashin sanin abun da zan ce miki ya sa na rufe ƙofar, kunya ma nake ji, dan girman Allah ki yi haƙuri"

Dr. Ya ce "Ummi wuce ki je ki kwanta, Allah ya yi miki albarka"

Ya kalli Farida ya ce "Ai gara da ya nuna miki ɗan zamani ne shi, kuma gaskiya ya faɗa miki, idan ba zaku girka ba ku zauna haka, dan ba baiwar ku ba ce ba, banda zubar da kai da son nunawa duniya rashin sanin ciwon kanki, su ƴaƴanki haka ki ke yi musu, shikenan yarinyar nan babu damar ta huta, har a gaban mijin da ta aura sai kin yi yinƙurin tozarta ta? Meye na wani ta zo ta yi girki, a bari ta dawo mana"

Babu kunyar idon ƴaƴansu farida ta din ga zuba wa dr. Rashin mutunci a gaban yaransa.

Yayi ƙoƙarin danne zuciyarsa ya shareta.

Har da iƙrarin ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, tun da ya fifita ummi a kan ta, sai ya ware mata kitchen ɗin ta ya raba musu kwana kuma.

Sosai ummi ta yi kuka, ba kowa ya ja wannan abun ba sai raihan.

Tun daga ranar takun saƙa mai zafin gaske ya shiga tsakanin ummi da farida, idan ta taho kausar ta taho, sai ta bangajeta, sabon wulaƙanci da tozarci iri-iri.

Farida har da iƙrarin in dai dan ta samu mijin aure ne, ta fara take-taken iskanci, sai gidan mijin ya zame mata gida mafi azaba da tashin hankali.

Ummi ta mayar da hankali a kan addu'a, tare da yaƙinin ko da raihan zai wulaƙanta ta bayan, ba zai kai yadda Idris ya ci zarafinta ba, tun da shi mutum me mai ilimi.

Can gida ma raihan Mami ta sake sako shi a gaba,  duk ta in da ya motsa idonta na kansa, gashi sai cigaba da tura masa safiyya take yi, ɓangaren anty rakiya da safiyyan ma sun riƙe wuta sosai da sosai.

Ummi kullum sai sun yi waya da mama da su yaya maryam, maryam tayi ta gaya mata shirye-shiryen biki da suke yi, ummi sai dai ta yi murmushi ba ta iya cewa komai saboda kunya.

Ana tsukin wannan tashin hankalin, jami'ar bayero suka kori kausar daga makaranta, saboda rashin kawo points ɗin da ake buƙata, ga Inteesar gidan miji ya ƙara yi mata tsanani, saboda abokiyar zamanta ta samu ciki, da mijin da danginsa duk sun juya mata baya ta amarya suke yi.

Hakan ya saka ummi ta ɗan samu sassauci, kamar yadda farida ta ce ta daina shigar mata kitchen, abinci sai ta ɗan sai abu ta ci, da ta ga babu sarki sai Allah idan an yi girki ba ya ciyuwa, sannan ta ce ai ita da yaranta ba bayin ummi ba ne, ita ce yakamata ta zama baiwa, tun da tana cin albarkacin su, dan haka dole ta fito ta yi musu girki su ci.

Duk wannan abun bai damu ummi ba, dan ko a jikinta, farida ta shiga cikin tashin hankalin yadda za su sanar da dr. An kori kausar daga makaranta.

Wani irin kyau da sheƙi fatar ummi ta din ga yi, tayi kyau sosai da sosai, ga wani irin ƙamshi na mussaman da yake ratsata.

Raihan daga ya dawo daga office, sai mami ta tsiri kirshe shi ta hana shi fita,wai dan kar ya je wurin ummi, abun da ba ta sani ba shi ne,
End Ads