Yanayin sintiri da nacin da headmaster yake yi mata, abun har mamaki yake bata, kamar ya ɗauketa ya kaita gidansa ya ajiye.
In da Allah ya rufawa ummi asiri, aikin nan nata, tana ɗan samun salary, idan tayi girki ta gama farida sai ta hanata abinci, tayi ta janyo mata masifa da bala'i da miyagun alkaba'i, tare da fatan ta sha wahala a rayuwa kamar yadda ta wahalar da ita a gidan aurenta.
Ummi a ranta ta ce 'Wahala waccece ban sha ta ba, kuma ban cutar da ke ba a zamanmu ke ki ka cutar da ni!"
Tun da dr. Ya zo gida, headmaster yake sintiri, a kan zai kawo kuɗin, dr. Ya ce ya ɗan ba shi lokaci tukuna.
Hatta wurin aiki manager ya lura yanayin ummi ya sauya, kamar wani abu na damunta, amma dai yayi shiru bai ce mata komai ba.
Dr. Ya kira ummi ya tambayeta ko tana son malam Isa, ummi ta ce eh.
"Ummi, kar takura ko damuwa ta sanya ki kai kanki ga halaka, rauwar aure ba rayuwar gida ba ce da babu nauyin kowa a kanki, kar ki kai kanki in da zaki yi dana sani, mutumin nan babban mutum ne, kar ki zo daga baya azo a samu matsala, ki dai je ki sake tunani" ummi ta amsa masa da to, ba dan ta so ba, ita fatanta kawai dr. Ya amince.
Kasancewar yau babu coustomers, ummi ta bar reception ta koma in da take zuwa ta yi salla ta ci abinci ta kwanta, tana cigaba da duba chat's ɗin su da raihan.
Ƙamshin turaren raihan ne ya fara yi mata sallama, ta zaci hallucinating kawai take yi, sai dai ba ta gama tunanin ba, ta ganshi a tsaye a kanta.
A zabure ta tashi zaune, tana bin sa da kallo.
Wani irin kwarjini ta gani a tare da shi, wanda ba ta taɓa gani a tare da shi ba, fuskarsa a matuƙar haɗe, kamar ba ya dariya.
"Raihan" ta kira sunansa a hankali.
Ya nemi wuri ya zauna, ya ƙura mata ido sannan ya ce "Salma wannan shi ne tukuicina daga gareki ko? Ko rabuwa ki ke son mu yi, yanke alaƙa da ni kai tsaye ba tare da wani dalili ba kina ganin shi ne mafita? Bafa a rana ɗaya muka gina alaƙar nan ba, ummi dama zaki iya wulaƙanta ɗan Adam har haka kamar yadda ki ka yi mini?"
Cikin rauni ta ce "A'a raihan, ba haka bane ba, dan Allah ka fahimce ni" nan ta gaya masa bayan dawowarta gida abun da ya faru, yadda farida tayi mata bincike ta nuna wa dr.
"Raihan wulaƙanci ba halina bane ba, ina ma naga ƙarfin gwiwar da zan iya wulaƙanta wani? Raihan ba kowa zan yi wa bayanin alaƙarmu ya kalli abun da idon basira alaƙar ta yi masa ma'ana ba, bana son zargi ya shiga ran dr. Duk da ya goya mini baya, amma ban san ta yaya zan wanke kaina ba, kafi ƙarfin wulaƙanci a wurina raihan, ban yi haka dan wulaƙanta ka ba"
Ya girgiza kai ya ce "Ban yadda ba ummi, duk a ƙoƙarinki na guje mini, ki ke shirin kai kan ki ga halaka, zaki auri shugaban makarantar ku ko? Malam isa"
A zabure ta kalli raihan, ya aka yi ya san wannan maganar?
"Mamaki ki ke yi ma? Ni zaki juya baya rana tsaka ummi, har ki yi shirin aure ban sani ba? Ina bibiyar rahuwarki fiye da yadda ki ke tunani, gani nake ko yaya na kawar da kai a kanki wani abu zai faru da ke, rabuwa da ni ba mafita bane"
"Raihan haka ne kawai mafita a wurina, matar gidanmu ta matsa mini da yawa, ƙalubale ko ta ko ina, ba zaka gane a mawuyacin halin da nake ba...
Ya katseta da cewa "Kuma sai ki kai kan ki ga halaka, mutumin da ya saki mata sun kai biyar, ya saki wata ke ma zai aureki ya biya buƙatar sa ya sake ki, ba irin wannan mijin nake roƙa miki ba"
Ta ce "Raihan alkhairi nake fata"
"Yi mini shiru" yayi maganar a hasale, galala take bin sa da kallo.
"Yakamata mu daina yaudarar junanmu, daga ni har ke, idan saboda ki rabu da ni ne, ki ke ƙoƙarin yin wannan auren, kin riga kin makara, ba za ayi shi ba. Ban damu da koma me wani zai yi zargi ba, ba zaki iya rabuwa da ni ba, kin riga kin makara. Ke banda rashin lissafi ma me zaki yi da wannan dattijon, shekarunsa nawa ke naki nawa? Me zai tsinana miki, ko ke ba kya wannan lissafin, ko an ce miki ci da sha ne kawai aure? Kodayeke ai kin san me nake nufi" kai ka ce gunki haka ummi ta koma, yau raihan ya zama wani abu na daban.
"Salma, ki yi haƙuri ba zan iya barin wani ya aureki ba, saboda ni nake sonki"
Tamkar ya jona mata shocking ta zabura ta ja da baya tana kallon fuskar raihan, yadda farar fatarsa ta koma ja, da irin kallon da yake yi mata, ya sanya ta tabattar da ba ƙarya yake yi ba.
"Ummi ki yi tunani, wace irin alaƙa ce a tsakani na da ke?"
Kamar zata fashe da kuka ta ce "Raihan, ni fa ƙanina na ɗauke ka, ƙanin ƙawata ce kai, mutum ne kai mai muhimmanci ne a gareni, amma ba irin wannan alaƙar ba".
Tashi yayi ya taka, ya je gabanta ya durƙusa, ya ɗan tsura mata ido ya ce "Bamu haɗa alaƙa da ke ba, ta uwa ko ta uba ba, kuma tarayyar mu da muka yi da ke ta wuce yadda ki ke tunani, ta kuma wuce gurbin da ki ka ajiyeta. Salma son juna muke yi. Lokacin nan da muka ɗauka ba ma tare, ki ka yanke alaƙarmu, kin sani a mummunan yanayin da yakamata ki ce na yafe miki, na shiga matsananciyar damuwa"
Da sauri ta girgiza kai ta ce "A'a Raihan, ina ganin mutuncinka, babu wannan maganar a tsakanin mu dan Allah a barta, kar ka sake yin ta bana so"
Ya shafi gefen fuskarsa, yana jin zafi a zuciyarsa, ya kalli ummi ya ce "Na gode Salma" ya tashi ya fice daga wurin.
Ummi ta takure tana ajiyar zuciya.
"Salma, ki yi haƙuri ba zan iya barin wani ya aureki ba, saboda ni nake sonki" shi ne abun da ya din ga yi mata kai kawo a zuciyarta.
Manager ne ya biyota yana tambayarta me ta yi wa ƙaninsa ya ga ya fita rai a ɓace, ummi ta ce masa babu komai.
Kwanaki biyu a tsakani, headmaster ya daina kiranta a waya gaba ɗaya, messages ɗin ma da yake tura mata ya daina.
Sai dai ko a jikinta, tunanin ya raihan yake yafi tsaya mata a rai.
Gashi ya ce halin da ta saka shi a ciki, yakamata ta nemi yafiyarsa.
Ganin ba ta da mafita, ya sanya ta neme shi a waya, amma shiru ba ya ɗagawa.
Tana cikin jimamin lamarin, dr. Yayi sallama a ƙofar ɗakinta, ta amsa sannan ya shiga.
Ya nemi wuri ya tsaya, sannan ya dube ta ya ce "Ummi, baya fa ta haihu, mutumin nan malam Isa ya kirani a waya, ya ce mini ya janye maganar aurenku, kuma hakan yayi mini dai-dai, dan kuwa ko bai janye ba, ba zan bashi aurenki ba, binciken da na yi a kansa bai yi mini daɗi ba, dan haka ki cigaba da addu'a, Allah ya kawo mafi alkhairi" har kawu yahaya ya fita, ummi na tunanin me raihan ya yi wa headmaster ya fasa aurenta, kenan da gaske yake yi sonta yake, ba zai bari kowa ya aureta ba!?
Gabanta ya faɗi tare da tabattarwa da kanta ba ta ga ta zama ba, idan ba raihan da rigima ba, ai ya san zaren ba kalar yadin bane ba, ina shi ina ita? Kyakkyawan matashi kamarsa me zai yi da ita, ga uwa uba ta girme shi, dole ta lallaɓa shi su rabu lafiya.
Sanin baya ɗaga wayarta, ya sanya washegari da ta shirya, ta tafi office ɗin su raihan.
Sai dai ba a bari ta shiga ba, sakataren shi yayi mata sannu da zuwa, tare da tambayarta raihan ya san da zuwanta?.
Ta ce "A'a, amma ace masa ummi ce"
Sakataren ya tashi ya shiga cikin office ɗin raihan, ya dawo ya ce mata ta jira, zai neme ta.
A ƙalla ta shafe awanni biyu tana jira, bai fito ba, ba kuma dan yana abun da ya fi ganinta muhimmanci ba, sai dan ya sanya ta yarda da alaƙarsu soyayya ce.
Yana office ɗin sa, ya kira waya ya saka aka kai mata ruwa da lemo da snacks.
Ya koma ta window ya tsaya yana kallonta in da take zaune, fuskarta duk ta faɗa, tana ta wasa da yatsun hannunta.
Ji yayi ya kasa jurewa, ya nufi ƙofa ya fita, tana hango shi ta tashi ta tsaye, sakataren ya fara yi masa bayanin ita ce baƙuwar da take son ganinsa, ta daɗe a wurin. Buɗar bakin raihan sai cewa ya yi ta rubuta a rubuce tana son ganinsa, idan yayi approving ya bata date da time ya fice ya bar ummi.
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
31
Har raihan ya bar harabar gidan bayansa ummi take kallo, ko sau ɗaya bai waiwayo ba, ita kuma ba ta daina zubar da hawaye ba, gani take kamar kallon ƙarshe take yi masa, ba zai sake dawowa rayuwarta da sunan yana son ta ba.
Ta tashi jiki babu ƙwari, ta tafi ɗakinta, ta rufe ɗakin ta saka sakata, saboda kar noor ta zo ta isheta da surutu.
Ta zauna ta din ga kuka, ta ma rasa kukan me take yi.
Ta yi shiru tana tuno irin rayuwar auren da ta yi a gidan idiris, ta kasa manta irin wulaƙantar da ta yi a gidan idiris, irin tozarcin da ya yi mata, tamkar ya auri mushen dabba ba ɗan Adam ba, kuma ɗan Adam ɗin ma ƴar uwarsa.
Ta tuna yadda abokansa suke zunɗensa da angon ɗoɗɗoya, ba zata manta tonon asiri da wulaƙantarwar da Idiris yayi mata ba.
'To idan kuma haryanzu ban warke ba fa'?" Ta tambayi kanta.
Ta dafe ƙirjinta tana zancen zuci, ita dai tun da Allah ya sa kawu yahaya ɗaukkota, yayi ta ƙoƙarin saya mata magunguna, cikin ikon Allah ba ta sake jin wannan matsalar ba, ko maƙiyinta ba ta fatan Allah ya haɗa shi da bala'in da yake cikin larurar sanyi.
Tun da farida ta dawo daga gidan inteesar, tamkar ita za ayi wa kishiya, kamar za ta yi hauka, domin kuwa da ita da wasu daga ƙannenta suka dawo gidan, suna ta bata haƙuri, a kan sai ta daure ita ma, idan ba haka ba inteesar ba zata kwantar hankalinta ba.
Sun cika falo suna mayar da yadda aka yi, noor kuma na ta kokowa da remote tana ƙara volume ɗin tv.
"Wai ke noor baki da hankali ne? Ba ni san meya samu yayarki Inteesar ba ne?"
Noor ta juyo ta kalli mai maganar ta ce "Mutuwa ta yi ne?"
"Wane irin mutuwa, ke ko gidan nata ma baki je ba, balle a haɗu a rarrasheta da ke, kina kallon mahaifiyarku hankalinta a tashe, ita ma can muka baro ta tana kuka, amma ke kina nan kina ƙure wa mutane kunne da ƙarar tv"
Noor ta taɓe baki ta ce "To tun da dai ba mutuwa tayi ba ai barkanta, wanda ba shi da kunya ai dole ayi masa kishiya, haka wata malama ta ce rannan a tv, na ce ashe saura maama"
"Ke uwar taki ki ke cewa ayi wa kishiya?"
Kausar ta ce "Mama hadiza, ki ƙyale yarinyar nan kar ta saka hawan jininki ya tashi, ba isasshen kai ne da ita ba, yanzu sai ta yi miki rashin kunya, kuma ba kowa ne ke zigata yana koya mata wannan iskancin ba, ban da ummi, idan ba haka ba ta yaya ɗa zai yi fatan a yi wa uwarsa kishiya, banda shashasha mara hankali"
"Ni dai ban saka da daƙiƙi a maganata ba, mutum ya bari ya fara gane karatu" kausar ta ja bakinta tayi shiru, idan ta cigaba da tankawa noor, sai noor ta kunyata ta a gaban mutane.
Nan kuma akalar hirar ta koma kan ci wa ummi mutunci, da ziga farida a kan lallai yakamata ummi ta bar mata gida, tun da ta tsofe a gidan babu aure.
Suka gama soko burutsunsu, suka bar gidan.
Ummi kusan kwanan zaune tayi, tayi ta salloli tana kaiwa Allah kukanta, wayarta kuwa ta dubata babu adadi, amma babu saƙon raihan ɗaya da ya sake shigowa cikin wayarta.
Ƙasan zuciyarta ya shiga tabattar mata da sun rabu da raihan kenan.
Bayan ta idar da sallar asuba, message ya shigo wayarta, wani website da raihan ya saka ta shiga, ta yi submitting cv ɗin ta, an kira su screening ciki har da ita, wani sabon gidan talabijin da ba a daɗe da fara shirye-shirye a cikin sa ba.
Yau da safe aka ce su je wurin, ba ta ga saƙon ba sai yanzu, cikin sauri ta tashi ta haɗa credentials ɗin ta, agogo ta kalla, muddin ta ce za ta jira ta yi musu girki, to fa zata makara, dan haka ta dudduba jakunkunanta, ta samu kuɗi ta fito, ta turawa Abdul message na in da ta tafi.
Ko da ta je wurin ta tarar da mutane da yawa, haka nan ta fara bin layi ita ma, ta din ga duba wayarta tana tunanin raihan, shi ne mutum na farko da yakamata ta kira, ta sanar masa da an kirata screening, sai dai ba ta da wannan damar a yanzu.
"Dama na sani, babu lallai ka dawo gareni raihan, amma duk da haka ba zan ga laifinka ba, ina yi maka fatan alkhairi a duk in da ka ke".
Farida tamkar ita aka yi wa kishiyar, ko bacci gagararta yayi, ta taso da nufin ta tarar da abincin safe, Abdul ya shigo ya sanar da ita saƙon ummi, tana fara zage-zagenta, ya fice ya bar mata falon.
Raihan yana zaune yana ta juyi a kan kujera a office ɗin sa, ya kasa taɓuka komai, ya juya kai nan ya juya kai can, in aka jima sai ya ciro wayarsa ya duba ya mayar ya ajiye.
Ya kifa kansa a kan teburin gabansa, yana jin yadda kansa yake masa wani irin zafi.
Jin motsin an buɗe ƙofa ya sanya shi ɗaga kai ya ga me shigowar, babu tsammani ya ga safiyya, tana sanye da doguwar riga straight gown, sai mayafinta a kafaɗa da jakarta, ta shigo bakinta ɗauke da sallama.
Ya amsa mata tare da mayar da kansa ya kifa.
"Yaya raihan, barka da rana?"
"Yauwwa sannu"
Ta nemi wuri ta zauna ta ce "Gidan su wata ƙawata na je, a nan tsukin ne, na ce bari na biyo mu gaisa"
Yayi shiru bai ce mata komai ba.
"Are you ok?" Tayi maganar tana kai hannu goshinsa, ganin yana gumi duk da akwai sanyi a office ɗin.
Rau ta ji goshin nasa ya ɗau zafi, ta ce "Subhanallah, yaya raihan baka da lafiya ne? Jikinka zafi"
Ya ɗago a hankali ya ce "Safiya, ki tafi gida Please, ki ƙyale ni"
"Amma ya zan tafi na barka a wannan halin?"
Kallonta yake yi, yana tunanin dama ummi ce a zaune a gabansa take yi masa magana yanzu.
"Ki tafi na ce" yayi maganar a ɗan hasale, tare da jin haushin yadda ya ta tsare shi da ido, saɓanin ummi da ba ta iya ƙura masa ido haka, sai tana yi tana kawar da kai.
Safiyya ba ta fi shekaru goma sha tara ba, ummi ta girmeta sosai, sai dai shegen iyayi da rawar kai, duk in da ta zauna ba ta da aiki sai hira da samari a waya, ga shegiyar kwalliya kamar ƴar tsana.
Ta razana da tsawar da yayi mata, ta tashi da sauri, har ta kusa fita ya ce "Kar ki sake biyo ni office, office wurin aikina ne ba shirme ba" tayi sauri ta fice tana waiwayensa.
Ummi kuwa ta galabaita a ranar, dan bayan screening, aka ce su jira aka tura musu waɗanda suka yi nasara a waya, ciki har da ita, aka ce su jira ayi musu interview.
Kuɗin hannun ummi ba zasu kai ta ci abinci ba, ga yunwa ta isheta, haka nan suka cigaba da jira.
Ba a zo kan ummi ba, sai kusan biyar na yamma, da farko bayan shigarta studion aka fara yi mata interview, a ɗan tsorace take, ga yunwa tana ji, ɗaya daga cikin masu interview yana cewa masha Allah muryarta mai daɗi.
Ɗayan ya ce "Jin ta ya fi ganinta, wannan da radio ce irin su ne masu sauraro ke ɗokin gani"
Shugaban wurin ne ya shigo, ma'aikatan suka din ga gaishe shi, yana hura hanci, ya dubi ummi ya ce "Wannan fa?"
"Dan Allah ku zaɓo wanda za su yi attracting ɗin mutane, ba wanda sai mun yi ta faman sanya filter muna fafutuka kan mu haska su ba, wannan shirin talabijin ne, ba na gidan rediyo ba!"
Tsit mutanen wurin suka yi, ba wannan ne karo na farko ba, amma a duk lokacin da aka yi mata, jin abun take kamar sabo, sum-sum, ta tattara kayanta, tayi waje, duk suka tsaya suna kallon ummi, shi kuma ko a jikinsa ya cigaba da maganar sa.
Ita ba ta san ma yadda aka yi ta isa gida ba, abubuwa daban-daban cunkus a ranta, ta ɗaukko gajiya da baƙin ciki, tana zuwa gida farida ta dira mata nata tashin hankalin.
"Raihan ka gani ko?, ka kori wanda zai aureni, kaima ka tafi ka bar ni, komai yayi mini zafi"
Tayi kuka-kuka iya yin ta, har ta gaji tayi shiru.