tafi, saboda zai daina ganinta a kai-a kai, sai dai yayi mata alƙawarin zuwa ya gaida mama.
Haka zalika ya tura mata kuɗi a account ɗin ta, ya ce idan ya tashi zuwa maiduguri zai taho mata da kayan fitar biki.
Suna zane suna hirar, wayar ummi ta fara ringing, ta ɗaga wayar, sai ya ga ta yi shiru tana kallon sa, amma ba ta ce komai ba.
Kawai sai ya tsargu, ya karɓi wayar ya saka a hansfree.
Muryar Safiyya ya ji, tana ta zazzaga rashin mutunci, da kalaman muzantawa ga ummi.
Jin ummi ba ta ce komai ba ya sanya safiyya cewa "Malama ba magana nake yi miki ba?"
"Da raihan ɗin ki ke magana ba ummin ba" hankali a tashe ta kashe wayar, tana salatin Allah ya rufa mata asiri.
Ya kalli ummi ya ce "Dama haka take kiranki tana ci miki mutunci ba ki gaya mini ba?"
Ummi ta ce "To me zan ce, kullum sai in ƙare a kan ƙara, ni ba zan iya ba tun da ka ji yanzu da kanka shikenan, dan Allah idan zaka aureta ka aureta amma ni ta daina zagina"
Ya jinjina kai ya ce "Ina fatan dai ba shiru ki ke yi mata ba?"
"Ni mu bar wannan zancen bana so" tayi maganar tana zumɓura baki, ya ɗan ƙura mata ido, kishin ne yake damunta, dan haka yayi mata shiru kawai.
Daga wurin ummi da niyyarsa ya je gidan su safiyya, sai dai ya fasa ya tafi gida kawai.
Ummi ta tattara muhimman kayanta, ranar tafiya ta je yi wa farida sallama, amma ta ka da baki ta ce mata Allah ya raka taki gona.
Mami na ta sake maimaitawa raihan idan ya kuskura ya kashe kuɗi sosai a harkar auren ummi, sai ta ci masa mutunci fiye da yadda yake zato.
Kwana biyu da tafiyar ummi maiduguri, Raihan ya je gidan su safiyya, anty rakiya har ta fara yashe baki, tana cewa "Babban mutum barka da zuwa, yau kai ne a gidan namu?"
Ya ce "Eh, safiyya fa"
Ta ce "Ahh wurin mutuniyar aka zo kenan, to bari na yi mata magana"
Kasancewar Safiyya ta san abun da ta aikata, ya sanya gabanta faɗuwa ta ce ba zata ba.
"Dan ubanki abun da muke neman zaki ce ba zaki ba?"
Kamar za ta yi kuka ta ce "Ni fa tsoro nake ji, na gaya miki abun da ya faru"
"To sai ki bari kanki ya kulle, ba mace ba ce ke? Guda nawa raihan ɗin yake banda ma ya jajibo aure? Tashi ki je dalla"
Har ta shiga falon tv yake kallo, bai ko ɗaga kai ya kalleta ba, sai da ta zauna ta fara gaishe shi ya amsa, ya tambayeta ya makaranta ta ce masa lafiya ƙalau, sannan ya kalleta ya ce "Safiyya na san kin san abun da ki ka aikata, to ki sani, ba zuwa na yi bin ba'asi ba, kuma ba wani ya gaya mini ba, ta gaya mini na farko na kawar da kai, ban zaci irin wannan zagin ki ke yi mata ba, to ba sa'arki ba ce ba, kuma hakan da ki ke yi ba zai canza komai na batun aurena da ummi ba, wallahi idan ki ka sake kira mini mata ki ka ci zarafinta sai na gwada miki waye raihan, ba ruwana da wani zumunci sai na ɗaureki an ci tarar ki, na gaya miki. Ni ba ƙyale-ƙyale nake bi ba, mutunci, tarbiyya da soyayyar da nake yi mata ya sa zan aureta, kalli jikinki kowa ya gama gani, ba shigar mutunci a tuninki wannan ce wayewa safiyya? Dan an ce miki matar da zan aura kidahuma ce, ni a wurina hakan ne wayewa, kar ki bari abun da ki ka yi ya taɓa zumuncinmu, dan bana magana biyu, idan kuma Anty na da kuɗin belinki ki cigaba da kiran Salma kina ci mata mutunci tun da baki da kunya" bai ko tsaya yin sallama da anty rakiya ba, ya tashi yayi tafiyarsa.
Aikuwa kan ya je gida, tuni sun sanarwa da mami, yan zuwa ta dirar masa da masifa tare da kashedi iri-iri, ciki har da barazanar sanyawa a fasa auren sa da ummi, tare da jaddada masa cewar aurensa da safiyya ba fashi.
Ummi kuwa yadda su yaya maryam suke kula da ita da gyarata, har gajiya ta fara yi, a murza mata wancan, a shafa mata wannan, gashi aka hanata aikin komai, kullum tana kauwwame a wuri ɗaya, daga ci sai sha, banda kayan magungunan gyaran da ake ta yi mata.
Tulin turarukan wutan da ake ta haɗawa kuwa, kai ka ce ci za ayi, ga uban kayan kitchen.
Ummi har hawayen daɗi tayi, saboda irin so da ƙaunar da dangin mahaifiyarta ke nuna mata, gashi dai ba wani ƙarfi ne da su ba, amma sai zuciya da ƙoƙari.
Ga isasshen lokaci da ta samu tare da mama, ga isasshen abinci mai kyau, komai na ta daban.
Saura wata guda biki, raihan yana ta shirin zuwa maiduguri, yana zaune suna shawara da hajiya, a kan yadda abubuwa zasu gudana, ya haɗa akwati guda na kayan fitar biki kawai.
Salim yana zaune sai dai bai tsoma musu baki ba.
Sai daga baya ya ce "Wannan akwatin ɗaya kawai zaka kai sai ka ce tsiya, ba zaka yi lefe ba?"
Cikin sanyin jiki ya ce "Mami ta hana, ta ce bazawara ce, wai kuɗin auren da aka kai ya isa, shi ne na ce bari na yi mata kayan fitar biki, lefen idan ta je gidana na yi mata, amma kalli kayan ka gani masu kyau ne fa" yayi maganar yana buɗe masa akwatin.
Tabbas manyan kaya ne sosai da sosai na alfarma.
Salim ya yi ajiyar zuciya ya ce "Idan ka kai musu sai dai ka yi musu bayani, na ji ka ce maiduguri zaka kai mata, ana yi wa iyaye akwati fa su ma, dole ka yi ƙoƙarin fitar da su kunya, aurensu da tsada sosai"
Hajiya ta ce "Kai a ina ka sani?"
Ya amsa mata da "Abokina umar ɗan can ne ai, kuma ƴar can ya aura, ni da shi muka din ga shirin bikin ai"
Cikin marairaicewa raihan ya ce "To ka taimaka mini mana nima"
Ya girgiza kai ya ce "Bana son babarku ta zo ta ce ba a kyauta ba"
Hajiya ta ce "Ba ƙaninka bane ba? Babu abun da za ta ce"
Haka kuwa aka yi, dan sai da suka sake sayen akwati, aka zuba atamfofi da shadda, wanda ake yi wa iyaye, sannan ya gaya masa zai bayar da kuɗin turaren wuta.
Gwiwar raihan ba ta yi sanyi ba, dan shi a ganinsa komai zai kashe wa ummi bai faɗi ba.
Yadda raihan ɗin ya din ga yi wa salim biyayya, ya sanya da Hajiya ta lallaɓa shi ta ce su tafi tare maidugurin bai yi musu ba.
Can Maidugurin ma da ummi ta ce musu raihan zai zo, aka din ga shirye-shiryen tararsa, dan bai gaya mata da Salim zai zo ba ma.
Mami ta so hana tafiyar nan, amma Alhaji ya taka mata burki, ya ce babu abun da zai hana raihan zuwa maiduguri, tun da matarsa a can take.
Kasancewar ana idar da sallar asuba suka tafi, ƙarfe sha ɗaya na safe suka sauka.
Suka bi adress ɗin da ummi ta basu har gidan suka je.
Kasancewar sun yi shigar kamala, daga shi har Salim, hakan ya ƙara musu kima a wurin ƴan uwan ummi.
Sai rarraba ido kawai yake yi ya ga ummi, aka kawo musu abinci na alfarma.
Sun kai a ƙalla awa guda, yaya maryam ta tsare ummi, ta hana ta zuwa, sai daga baya ta shirya cikin lafaya mai kyau, sai ƙamshin turare take yi, hujin hancin da suka yi mata, ta saka barimar azurfa, sai ƙyalli take yi a kan baƙar fuskarta.
Da tayi sallama tare suka ɗaga kai suka kalli ummi, babu kunya raihan ya kafe ta da ido.
Salim ya jinjina kai a ransa ya ce "Lallai yaron nan akwai tsaurin ido"
Ummi ta wani ƙara cika sosai, ga wani irin ƙamshi da ya cika ɗakin.
Durƙusawa tayi har ƙasa ta gaida Salim, ya amsa mata fuskarsa babu yabo ba fallasa.
Ta juya wurin raihan ma ta gaishe shi, ya amsa yana washe baki.
Ya ce "Tun da ga yaya salim, akwai kuɗi a jikina, sai a ɗaura yanzu kawai" hararsa tayi ta samu wuri ta zauna.
Salim ya mayar da hankali a kan wayarsa, kamar bai san suna wurin ba, raihan kuwa ya rasa control ya din ga zuba a gaban Salim, ummi kuma kunya kamar ta nutse.
"Baby me mama take baki ne? Kin ƙara ƙiba, kalli skin ɗinki"
"Ni fa bana son ƙibar nan" ta faɗa a hankali.
"Ni kuma ina so, baki ga kyan da ki ka ƙara ba, kin ji ƙamshin da ki ke yi kuwa? Anya zan iya jiran lokacin nan, Innalillahi kin ganki kuwa? You look take away, ko dai in yi zamana a nan"
Dukan da Salim yayi masa a ƙeyarsa ne, ya sanya shi yin shiru yana sosa kai.
Ummi ta yi masa gwalo, ta ce "Bari na je n yi wa mama magana, mu shiga ku gaisa" ta tashi ta fita.
Tana fita Salim ya ce "Kai dan ubnka a gidan sirikai fa ka ke? Wannan da bamu zo tare ba me zaka yi?"
Raihan ya ce "Bakomai"
Yayi ƙasa da murya ya ce "Zaka ƙara da kuɗin gyaran jikin da ake yi mata, kara fa aka yi maka da duk ba ta tambayeka ba, zaka saki bakin aljihu tun da ɗiyar ƴan maiduguri zaka aura"
Raihan ya ce "To ai duk ba ta gaya mini ba"
Salim ya ce "Ni yanzu na gaya maka, kuma wannan ginin da ka ke yi, ka je ka ce wa Alhaji ya saya ko ka bashi jingina, ka samu gida mai kyau ginanne ka saya"
Raihan ya ce "To ai ina son gidan sosai "
"To ka ce wa Alhaji ya baka gudunmawar bikin, ka ƙarasa"
Raihan ya yi dariya ya ce "Haka za ayi yaya"
Ya ɗaga masa gira.
Ummi ta ce "Bisimillah ku shigo"
Suka tashi suka shiga, suka din ga gaisawa da mutanen gidan, ummi tana gabatar musu da kowa.
A ɗakin mama suka yi sallama, suka zazzauna, ta din ga murmushi tana amsa musu gaisuwar.
Ta kalli yaya maryam ta ce "Yaya, wannan suwaye?"
"Sirikanki ne, wannan ne zai auri ummi"
Sai tayi dariya ta rausayar da kai ta ce "Ummin za a yi wa aure yanzu? Ai tayi ƙarama da yawa"
Maryam ta ce "Wai ke ummin haryanzu a kan cinyarki take ne tsawon shekaru ba ta girma ba?"
Ta kalli raihan ta ce "To kai ba ka ga munin na ta ba? Iya ta ce mummuna ce babu mai aurenta"
Raihan ya ce "Haba mama, ummi ba mummuna ba ce ba, kalleta fa ki gani tubarkallah masha Allah"
Ta ce "Yauwwa, da ma na faɗa, wani zai ce yana son ummi a haka, amma iya ta din ga yi wa ummi ba'a, har sauran yaran gidan, su yi ta ce mata mummuna ko wasa da yara ba ta yi, kuma duk iya ce ta janyo, da ta tsawatar ai ba za su yi mata ba ko?"
Raihan ya ce "Gaskiya ne, amma ummi ai mai kyau ce, ga ilimi da tarbiyya, ta cancanci a so ta"
Yaya maryam ta ce "Dan Allah ki daina zancen nan da ya wuce"
Salim ya ce "Kamar tana jin daɗin hirar, ki ƙyaleta"
Mariya ta sake cewa "Ka san har malaman makarantar su ummi, wai su yi ta ce mata baƙa, na yi ta kuka, ko ace idonta irin na mayu, da ta fita yara su yi ta cin zalinta, shiyasa ni da babanta mu yi ta sonta, ba ka ga yadda yake son ta ba"
Raihan ya ce "Allah sarki, mu ma muna son ta sosai"
Ta kalli Salim ta ce "Ka ga yadda kakarta ba ta son ta ko? Amma bayan mutuwar baban ummi, matar nan ta ƙwace mini ummi, ba fa iya kula da ita take yi ba, an ce sun azabtar mini da ummi sosai da sosai" tayi maganar tana share hawaye.
Salim ya ce "Ki yi haƙuri ki daina kuka dan Allah".
Ta kalli raihan ta ce "To ka ga dai yarinya ce, dan Allah ka kula da ita sosai, ka din ga ba ta abinci, idan magariba tayi a saka mata kayan sanyi, cikin dare ma a tashe ta tayi fitsari"
Ya ce "Duk za ayi mama, ai ummi yarinya ce kyakkyawa, duk za a din ga kula da ita"
"Eh, to amma ban bar maka ita ba fa, zaka dawo mini da ita"
Mama ta din ga zuba, suna hira da raihan da Salim, duk rashin sakin jikin salim, suka din ga hira da mama, wani abun idan tana gaya musu, sai tayi kuka, wasu abubuwan ma duk ummi ba ta san sun faru ba.
Har da tambayar maryam, wai anya Salim da raihan ba su ne jaririn da suka haifa ba aka ya ce ya mutu.
Gashi dai ba ta da cikakken hankali, amma a nutse take, malam kakan ummi, ya din ga yi musu nasiha, tare da gaya musu muhimmancin riƙe addu'a.
Salim suka ba su kayan da suka zo da su, Malam ya ce ai ba su suka riƙe ummi ba, dan haka babu buƙatar kawo wannan kayan.
Malam akwai kwarjini, ya kasa magana, Salim ne ya tausasa harshe tare da nuna masa cewar ba su takura ba, duk abun da suka yi wa ummi ta cancanta.
Kuɗin turaren wuta da na gyaran jiki, suka danƙawa yaya maryam masu kauri.
Mama har bakin mota ta raka su, suna cigaba da hira.
Ummi ta ji daɗin karamcin da suka nuna wa mama, mama har da tambayar yaushe zasu kuma zuwa? Su faɗi abun da zata dafa musu.
Yaya ɗanlami ya ce "Ban da larura ma, yaushe mutum zai zauna ya yi ta zuba da sirikai"
Su raihan suka koma kano, cikin farinciki da tausaya wa mama da irin abubuwan da ta din ga faɗa game da rayuwar ummi.
Har suka je gida ummi na kiransu na jin yaya suka je gida?
Mama sai zancen su raihan take yi, ko sunansu ba ta sani ba, tun da Allah ya sa ta haɗu da ummi, bakinta ya buɗe tayi ta surutu amma da ummi take yi, sai kuma su Salim da suka zo.
Da daddare bayan su raihan sun sauka kuwa, ya takurawa ummi da waya, dan duk taka tsantsan ɗin sa sai da ya kusa kauce hanya, sai dai ummi ta yi masa shiru.
Kwana biyu da komawar raihan kano, Salim da kansa ya samu Alhaji ya tsutsiye shi, wai me zai bawa raihan na gudunmuwa.
Alhaji ya ji daɗin kulawar da Salim ya bawa raihan a kan aurensa, kuma ya lura raihan ɗin ne bai canza masa daga biyayyar da yake yi masa ba, duk da yana da wani muƙami ba.
Alhaji ya ce "Ni za a yi wa solidarity?"
Ya ce "A'a ginin da saura ne, kuma saura wata guda biki, za a kai mahaifinta ya ga gida, kuma da kai da hajiya bamu ga gudunmawarku ba"
Alhaji ya yi murmushi ya ce "Na tsaya na ga iya gudun ruwan sa ne, kuma yayi ƙoƙari sosai da sosai, kuma babban abun da ya burgeni, duk faɗi tashin da yake yi, bai nemi taimakona ba, bai kuma ci amanar da na bashi ba, ya ɗaukar mini kuɗi babu izinina ba, dan haka za a san abun yi, kar ka damu"
Ya ce "Ok, mun gode, dan Allah a bashi da kauri sosai"
"Za a duba, Salim na ji daɗin ƙoƙarin da ka ke yi masa, ka yi playing role ɗin ka na babban wa, saura kuma kai ma ka nutsu ka yi naka auren"
Salim ya ce "Raihan, duk da wasu abubuwan da mahaifiyarsa take yi, ina kallon yadda yake ɗawainiya da mahaifiyarmu, duk da yadda muke ɓata mata rai wasu lokutan, shi sanyin idaniyarta ne, yana ƙoƙari a kan mahaifiyarmu sosai, amma a cigaba da yi mana addu'a" bai jira me Alhaji zai ce ba, ya fita.
Alhaji ya ce "Tabbas raihan babban mutum ne, amma akwai dattaku kam"
Da Alhaji ya tashi, a account ɗin Salim ya tura masa kuɗin gudunmuwar auren raihan, kuɗi masu kaurin gaske.
Nan da nan aka ƙarasa ginin raihan, suka kai Alhaji tare da Dr. Rana ɗaya suka gani.
Jikin dr. Yayi sanyi, gado biyu ya yi wa ummi, da dining da kujeru saiti ɗaya.
Sai dai falukan ummi uku, bedroom huɗu, sai kitchen da sauransu.
Alhaji ya ja dr. gefe ya ce masa "kar ka damu, ka saka abun da Allah ya yassare maka, zan ƙarasa ba tare da kowa ya sanu ba, ai ana ƙoƙari sai godiyar Allah"
Saura sati biyu biki, Raihan ya koma maiduguri ya kai wa ummi katin biki, ya ce ko akwai wanda za ta rabawa a kano ta ce ita ba wanda za ta bawa.
Raihan ya tafi da kwana ɗaya, dr. Ya je, ya ɗauki ummi zuwa gagarawa, ta kai musu katin bikin da kanta, in da ta ji daɗi, sai ya tafi da noor.
Kamar kullum, tarbar da ta saba samu ita ta samu, sai dai sai kallon ummi suke yi, ta yi kyau sosai da sosai, a nan dr. Ya gaya wa iya cewar ya gano garin su mariya, kuma ummi tana can, sai da suka yi faɗa sosai da iya a kan hakan.
Ummi suna zaune, wata yarinya ta shigo za ta yi sa'ar noor, kallo ɗaya ummi tayi mata ta gane ta, saboda kamar da take yi da hindu matar Idris.
Iya ce ta hau zagin yarinyar tana tambayarta daga ina take?.
Cikin fitsara yarinyar ta ce "Tasha na bi sajida sayar da shinkafa da wake na tayata ta san mini"
"Saboda matsiyaciya ce ke, sai kin tona mana asiri?"
"Tun da aka bar ni da yunwa, ba a ƙaunata dole na ciyar da kaina".
Ganin da Yarinyar ta yi ummi na kallonta, ya sanya ta ce wa ummi "Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau ya ki ke?"
Ta ce "Lafiya ƙalau"
Ummi ta ce "Zo mana" ta ƙarasa gaban ummi ta durƙusa.
Ummi ta ciro kuɗi a jakarta ta ce "Ungo, yo cefane sai mu yi girki mu ci, amma ki daina zuwa tasha ba mutuncin ƴa mace bane, kamata yayi ace kina makaranta duk da an yi hutu"
Yarinyar ta ce "Ni da bana zuwa makaranta, ko abinci basa bani, sai idan babarmu ce ta bani, kowa ya tsane ni, ni ya zan yi ni na ce a haife ni haka?" Yarinyar tayi maganar tana kuka, duk da ba ta san ummi ba, amma ta ji hankalinta ya nutsu da ita.