x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - CUTARWA

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 486

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
mijinki kenan, ki kasa zama da shi a yadda yake, ki hura masa wuta ya tafi ajali ya riske shi, kuma gashi an ɗora miki, an ce ke ce sila. Mariya kin ɓata wayonki, wannan ba tarbiyyar gidanmu ba ce ba, kuma ahalinsa ba zasu taɓa mantawa da abun da ki ka yi ba". Kasancewar yana cikin manyan yayyenta, kuma tana bala'in tsoronsa, dan haka ba ta iya kare kanta ba sai kuka, ga shi a gaban mutane ya din ga yi mata faɗa, mariya ta rasa da wanne za ta ji.

Iya kuwa ta samu damar cigaba da ƙullawa mariya sharri a wurin yayanta.

Yahaya ya tsawatar, saboda shi ɗan boko ne, ya ce ba zai yiwu a saka mariya a gaba ace ita take aikata duk wannan laifukan ba. Idan ma haka ne tana matsa masa kan ya rasu yanzu yana ina? Kuma ai mijinta ne, tana da right na ya yi mata abun da take so.

Ɗakinta ta shiga ta zauna, tayi kuka, tayi kuka, har zuciyarta ta fara raya mata ko kashe kanta zata yi ta huta da wannan azabar.

Ummi ta zo tana kuka ita ma, dan tun ana yi mata faɗan nan ummi take tayata kukan, ta din ga share mata hawayen tana cewa "Mama ki yi haƙuri, ki daina kuka" ita kanta yayar mariya, ta san mariya ba za ta aikata haka ba, yadda iya ke yi wa mariya a gaban su, ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba. Sai dai su al'adar gidan su, muddin ak kawo ƙararka daga waje, ba a taɓa goya maka baya, balle kuma a gidan aure, idan miji gutsurar namanki yake yana ci, sai ace ki je ki cigaba da haƙuri, wataran sai labari, kowa haƙuri yake yi.

Maryam ta tambayeta ina samirunya, ta ga duk babu? Mariya taƙi gaya mata, ta shashantar da zancen.

Bayan kwanaki uku da share zaman makoki, ƴan nesa suka watse, sai masu shigowa jefi-jefi gaisuwa, yayar ta ta zauna da ita, ta ɗan din ga ɗebe mata kewa, zuwa kwana arba'in, aga meye abun yi.

Gaba ɗaya mariya ta gama fita daga hayyacinta, kai daka ganta ka san tana cikin alhini, ko abincin kirki ba ta iya ci. Salla kawai take iya yi, wanka kansa sai ta yi da gaske take iya yi.
Daga kwanciya sai kuka, amma hakan bai sanya ta tsira daga tashin hankalin Iya ba, ga kyarar ummi da take yi kamar ba jininta ba, wanda hakan ya fara tunzura yayar mariya maryam.

Kwanan bashir goma sha huɗu da rasuwa, rabi'u ya zo yayi sallama, suka amsa ya sake yi musu gaisuwa.

Ya ce wa iya "Ina mariya, ina son zan yi magana da ku ne"

Iya ta ce "Dole ne sai ta nan? In dai abun da ya shafi ɗa na ne, gaya mini kawai ina jinka"

"Wane irin a gaya miki kawai? Ai tana da hakkin sanin menene ita ma, tun da mijinta ne" yaya maryam tayi maganar a zuciye kamar ta kife iya da mari, saboda a zamanta ɗin nan ta gane lallai mariya tayi zaman haƙuri.

"Rashin kunya zaki yi mini?"

"Ba wani rashin kunya, maganar gaskiya ce ai. Ke mariya fito za ayi magana"

Jiki a sanyaye mariya ta fito cikin hijjabi, ta zo ta samu wuri ta zauna.

Suka sake gaisawa da mariya, yayi mata gaisuwa, Sagir yayi sallama ya shigo suka amsa masa, shima ya samu wuri ya zauna.

Rabi'u ya ce "Yauwwa, dama ni na yi masa magana tun da yana gida na ce masa ya shigo, Iya kamar yadda ki ka roƙi na tafi da bashir lagos, ya nemo arziki, to mun sauka Lagos lafiya".

Maryam ta ce "Amma ki ka ce mariya ce ta ce lallai sai ya tafi neman kuɗi"

Iya a fusace ta ce "Wai wace irin mara tarbiyya ce, ƙarya nake yi kenan, matsin da take yi masa ya sanya na yi masa magana, ya tafi da shi"

Maryam ta ce "Amma ai ba haka ki faɗa ba, ki ka saka yayanmu ya din ga ci mata mutunci a gaban mutane, wallahi ki ji tsoron Allah"

Rabi'u ya ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ku saurare ni ku ji, bayan zuwanmu Lagos, mun fara sana'ar fawa da balarabe, kasancewar ba shi da account, yake tarawa a account ɗina, ya ce mini mariya ta sayar da kayanta, ta bashi kuɗin, amma shi a bashi ya karɓa, zai mayar mata da kuɗinta, dan haka ba laifi ya tara kuɗi, riba kawai kusan dubu sittin, uwar kuɗin sa da ribarsa da komai, kusan dubu ɗari biyu, basussuka da sauran su, duk na biya masa dubu ɗari da arba'in ne suka rage, mun taho gida da niyyar idan mun zo na cire kuɗin na bashi.

A hanya ƴan fashi suka tare mu, suka ƙwace mana kaya, da kayan tsarabar sa, har sun yi gaba ya tashi kan su ƙarasa barin wurin, shi ne suka harbe shi a ƙirjin sa, kan ya rasu ya ce: kar a raba gado, sai an biya mariya kuɗinta na kayanta, da sauran kuɗin da take bin sa" Ya kalli ummi da ke zaune tana bin su da kallo, sannan ya kalli mariya ya ce "Ya ce; ki kula masa da ummi, sannan ki yafe masa" yana faɗar haka mariya ta sanya tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka.

"Ni bai ce maka komai a kai na ba?" Iya tayi maganar tana kallon rabi'u.

"Yana cikin maganar yayi kalmar shahada, ummin dai ya fi nanatawa"

Ta share hawayen da ke shirin zubo mata sannan ta ce "Ba wani zancen tana bin sa kuɗi, ni ban yi wannan maganar da shi ba, dan haka ka je ka ɗebo kuɗi ka kawo mini"

Maryam ta ce "A kawo miki kuɗi kiyi me da su? Ai kuɗi na magada ne, kuma sai mariya ta gama idda za a raba gado, saboda a tabattar da babu ciki".

"Ba dai ciki ba, shekara nawa rabonta da haihuwa, tun daga wannan mummunar yarinyar fuska kamar turotso, ba ta sake haihuwa ba, ba haihuwa take ba, dan haka ba ta da wani ciki. Wa ya sani ma ko balaraben baya haihuwa"

"To me ki ke nufi, ummin ba ƴar ku ba ce ba? Wai ke matar nan anya musulma ce ke? Kin yi imani da Allah kuwa?"

Sagir ya ce "Ke malama kar ki sake ki zagar mana uwa, na gaya miki" miƙewa maryam ta yi ta ce "Na zageta ɗin, ka yi abun da zaka yi. Azzalumar tsohuwa mara imani da tausayi, ashe ke ki ka ingiza ɗanki ya tafi neman kuɗi, amma kin saka yarinya a gaba, kina ta yi mata sharri, to wallahi dan kanki, ummi kuma idan ba ƴar ku ba ce, sai ki fita neman ubanta" nan da nan hayaniya ta ɓarke.

Mariya ta tashi ta ce "Dan Allah yaya maryam ki yi haƙuri, in dai kuɗi ne, ni babu bashi tsakanina da baban ummi, na rasa mijina balle abun duniya? Tumunin takabar ma na yafe, a bawa ummi hakkinta, in ɗau ƴa ta in koma in da na fito dan Allah" tayi maganar cikin matsanancin kuka, tare da jan hannun ummi ta tafi ɗaki.

Shi kansa rabi'u yayi mamakin rashin arzikin Iya, kawai ta ɗorawa mariya karan tsana.
Ta sake jaddawa rabi'u ya kwaso kuɗi ya kawo mata, me balaraben ya mutu ya bari, da za a tsaya wani rabe-raben gado.

Maryam kuwa da kanta ta tafi tasha, ya bayar da saƙo zuwa gida, a kan lallai a cewa yayansu ya zo, akwai matsala.

Ko abinci ba a basu, maryam ita ta din ga cefane tana ciyar su.

Yayan su mariya ya dira a garin, Iya sai da ta yi mamakin ganinsa, maryam ta ja shi, ta ce masa akwai matsala cigaba da zaman mariya a gidan nan, tana kallon irin zaman da mariya take yi a gidan, nan ta kwashe komai ta gaya masa.
Abun ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba, wani irin tausayin mariya ya kama shi, karon farko da ya ji zai goyi bayan ƙanwarsa, dan haka ya yanke cewa kawai zasu ɗauki mariya da ummi su tafi.

Dan haka ya je ya samu iya ya ce mata, washegari da safe zasu yi sammako su tafi Maiduguri, yaso su zauna su cigaba da gaisuwa, tayi takaba a ɗakin mijinta, amma wasu dalilai ya sanya sun yanke shawarar su tafi da ita gida kawai.

Iya ta ce "Shikenan babu laifi"

Mariya ta wani fannin ta ji daɗi zasu koma gida, wani ɓangaren wata irin kewar ɗakinta da mai ɗakik wato baban ummi, ta sake mamaye mata zuciya, har take jin anya ba za ta ce a bar ta a ɗakin nan ba, za ta cigaba da haƙuri da ita, kawai dan ya din ga gurbin da bashir yake dabdala.

A daren Maryam ta taimaka mata, ta harhaɗa kayanta, abun da zasu buƙata, Maryam ta ce daga baya azo a sayar da sauran kayanta, dan ba zasu iya dakon kaya zuwa Maiduguri ba.

Da sassafe maryam ta yi wa ummi wanka, suka yi wanka suka karya, ummi tana murna zasu tafi su bar gidan nan, tana fatan Allah ya sa idan sun je can babu yara masu tsokanar ta, ko dukanta.

Sun fito maryam na ce mata, ta yi sallama da mutanen gidan, ta nemi afuwarsu, Iya na tsaye tana kallon su.

Iya ya ce "Ummi zo mana mu yi sallama". Saroro ummi tayi tana kallon iya, ta ɗaga kai ta kalli mariya, mariya ta ce "Je ki Iya na kira"

Ummi ta tafi sannu a hankali, ta ƙarasa gaban iya.

Caraf iya ta sanya hannu ta riƙe hannun ummi, sannan ta kalli mariya ta ce "To, Allah ya raka taki gona, ummi dai ba da ita ki ka zo ba, kin san wannan, dan haka a sauka lafiya"

Mariya tayi turus tana kallon iya, dan ganin abun take kamar almara.

Maryam ta ce "Ban gane ba, yarinyar da ki ka ce ba taku ba ce ba"

"Ɓacin rai ne ya sanya ni faɗar hakan, ba zan bayar da ita aje ayi mata gurguwar tarbiyya ba, ta tashi tana sa'insa da manya ba, dan haka ni zan riƙe ummi, ita kaɗai ya haifa, na rasa ɗa na, ina buƙatar ganin jinin sa a gabana".

Cikin kuka mariya ta ce "Dan martabar Allah kar ki yi mini haka iya, ba zan iya jure zama babu ummi a kusa da ni ba, idan ma tafiyar ce na fasa, dan Allah ki bani ƴa ta".

"A a, a kan me zan hana ki tafiya, haifarki na yi, na rasa ɗa na balle wata ke, Allah ya raka taki gona"

Ƙoƙarin ƙwacewa ummi ta fara yi, tana kiran sunan mama.

"Nutsu dan ubanki" Iya tayi mata tsawa.

Yayansu mariya ya shigo, yana cewa su fito kar su yi rana, amma ya tarar da sabuwar dambarwa.

Juyin duniya, Iya ta ce ba zata bayar da ummi ba.

Mariya ta zube a kan gwiwoyinta, tana gursheƙen kuka, a kan iya ta bata ƴar ta, ta din ga cewa mutanen da suka taru, su saka baki iya ta bata ƴar ta, amma matar nan mirsisi taƙi.

Ummi na kuka mariya na kuka, yayan su ya hasala ya kalli mariya ya ce "Ke tashi mu tafi, in dai ƴa ce su cinye, tashi mu tafi"

"Yaya ka taimake ni, ba zan iya rayuwa babu ummi ba, dan Allah kar a rabani da ƴa ta, dan girman Allah ku yi mini rai, da wanne zan ji, na rasa mijina ƴar ma a ƙwace mini? Dan Allah ku bani ummina"

"Sai dai kiyi kukan jini kuwa"

A fusace ya daka wa mariya tsawa, ya ce ta wuce su tafi.

Iya tayi tsaki ta ce "Aikin banza, ban da rashin tarbiyya, wai a kan ƴar fari take wannan abun"

Idris ya shigo, Iya ta ce "Kai kuma mun yi magana ka ɓata mini lokaci, ɗauke ta ka tafi da ita in da na ce maka"

Ya ƙarasa babu walwala, zai danƙi hannun ummi, ummi ya rirriƙe Iya, tana wani irin kuka, dan a rayuwarta, ta tsani ko haɗa hanya su yi da idris, ta ƙarfin tsiya ya danƙi ummi, tana kuka tana kiran mama, mariya ta bi bayansu da gudu tana kiran "Ka zo ka bani ƴa ta, ku bani ƴa ta ba ƙaunar ta ku ke yi ba, ku bani ƴa ta. Yaya maryam ki karɓo mini ƴa ta, ke shaida ce ba son ummi suke yi ba"

Cikin tausaya maryam ta ce "Zaki kashe kanki ne? In dai ummi ce Allah zai kula miki da ita" shiru ta yi tana kallon maryam, ana gobe bashir zai tafi yake cewa Allah ga ƴa ta da mata ta Allah ka kula mini da su.

"Wuce mu tafi, su je su cinye ta, kema kina da masu sonki" auwwalu ne ya bi bayansu da warin takalmin mariya, dan takalmi ɗaya ne a ƙafarta, hawaye ne kawai yake zuba daga idonta, can ƙarshen hanya ta hango ummi tana ɗaga mata hannu tana kiran mama cikin hawaye!

Iya ta ce "Ba dai ke tsagera ba, daga ke har yayar taki dai-dai nake da ku, ummi ce dai tana hannuna, ba wani uban gado da za a raba, a baki ku cinye, gayyar tsiya arna a idi".

*Page ɗin nan sadaukarwa ne, ga duk matar da ta rasa mijinta ko aurenta, kuma aka zo aka rabata da ƴaƴanta, we know is difficult to endure, ku yi haƙuri, ku yi haƙuri, ku yi haƙuri 🙏 Allah ya shiga lamarinku, ya kula muku da yaranku*


Ayshercool
08081012143
       *CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
What's app 08081012143

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)


*BRIGHT PENS...* _suna mara ba da masu buƙatar a tallata musu kasuwancinsu, masu siyar da turarruka, kayan sawa, magani komai da komai, cikin sauƙi za a tallata musu a cikin duka littafan guda uku🤙🏼 *CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI*_

Tsari👯🏻‍♀️
Duk page ɗaya 200
Duka littafin kuma 600
Shafi biyar a littafi ɗaya 1000
A littafai uku kuma 3000
Domin ƙarfin bayani sai a yi wa wannan number magana 08164069385🤙🏼👯🏻‍♀️🫶🫶🏼

P5

Har suka je tasha, jan ƙafa kawai mariya take yi, dan bata gane komai, hankalinta yana kan ummi, wace irin rayuwa ummi za ta yi a wannan gidan? Tana nan ma a ya aka cika, balle yanzu da babu idonta, kuma ya zamana ba ayi rabuwar arziki ba.

"Allah ka kula mini da ƴa ta, Allah kar ka sanya ƴa ta ta lalace, Ubangiji Allah ka duba mini ita, ka tsare mini ita, Allah kai ka san dalilin da ya sanya, ka karɓi mahaifinta ka rabani da ita, Allah ka kula mini da ita. Haka ta din ga wannan addu'ar, jin abubuwan take tamkar a cikin nannauyan bacci, da take fatan ta farka.

Har suka shiga mota suka kama hanya, duk wata nasiha da maryam ke yi mata, ba ji take ba, balle ta fahimta.

Mariya ji take tamkar ta sauka daga cikin motar nan, ta koma ta rayu da ummi, ta san ummi wahala kawai za ta sha, dan iya ba ƙaunarta take yi ba.
Tunawa da tayi da cin zarafin da aka yi wa ummi, ya sake karya mata gwiwa, ta sake fashewa da kuka mai sauti.

"Idan ba zaki rufe mana baki ba, a tsaya ki sauka ki koma, ki je duk uban da za su yi miki, su yi miki, sai ka ce a kanki aka fara haihuwa, duk cin zarafin da suka yi miki bai isheki ba, ba dai ƴa ba ce su je su cinye ta, ai ta su ce da ma, dangin uba su ke da ɗa" tun da ya fara yi mata masifar ƴan cikin motar suka yi tsit, sai da ya gama ake bashi haƙuri.

Maryam ta san abun da mariya ke ji, dan haka ta rungume ta tana rarrashinta, haka tana ji tana gani ta bar garin da duka goma da ashirin, ga rashin miji ga rashin ƴa.

Ummi kuwa sai can daf da magariba aka saka yara suka rakata gida, dan can gidan wata ƴar uwarta ta sanya aka kai ta.

Ta ci kuka ta ƙoshi, sai ajiyar zuciya take yi, ana zuwa gidan da sauri ta shiga ta nufi ƙofar ɗakinsu, sai dai ta tarar da shi da ƙaton kwaɗon da su mariya suka rufe ɗakin da shi.

Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar ɗakin, ta cigaba da rera kuka.

Babu wanda ya saurareta, balle ya kula da ita ya rarrasheta.

Sa'adatu ce tayi sallama, ta kawo wa iya tuwon dare.

Ta ajiye mata suka taɓa hira, ta tashi fito, tana daf da shiga sashinta, ta ji ana bin ta a baya, ta tsaya ta waiwayo taga ummi.

"Ke, lafiya ki ke bina?"

"Dan Allah ina mama? Haryanzu ba ta dawo ba, ta buɗe mana ɗaki in yi salla, sanyi nake ji"

Sa'adatu ta yi shiru tana kallon ummi, sam ba ta ga dalilin da zai sanya iya raba mariya da ƴar ta ba, ta san iya ba iya riƙe ta zata yi ba, saboda tsabar mugunta da rashin imani.

"Ummi babarki ba zata dawo ba, ki tafi wurin iya ki je ki kwanta, gari da sanyi"

"Ita ma maman ta mutu? Ba zata dawo ba kamar baba?"

"Ba mutuwa tayi ba, nan kusa dai ba zata dawo ba, ki yi addu'a Allah ya sanya ta dawo ta tafi da ke, can in da aka kai ki kin ci abinci?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "Mama ta hana ni cin abinci a gidan mutane"

Sa'adatu ta ce "Kenan wuni ki ka yi baki ci abinci ba, tafi na kai wa iya abinci, ki je ta zuba miki" ummi ta ce "To"

Ta juya jikinta a sanyaye, ta koma sashinsu, ta zauna a ƙofar ɗakin su, tana kallon ƙofar ɗakin Iya, kuka take a hankali tana jin kewar mahaifiyarta, da yanzu mama ta yi mata wanka, ta shafa mata mai ta saka mata kayan sanyi.

Tana nan zaune a ƙofar ɗakin, sanyi sai ratsata yake yi, ga ƙanan ƙwari na bin ta.

Gani tayi an hasketa da fitila, ta saurin rintse idanuwanta, saboda hasken fitilar, bai ɗauke fitilar ba, har ya ƙaraso kanta ya tsaya.

"Me ki ke yi a nan?" Jin muryarsa ya sanya ta tashi a razane ta ja da baya jikinta na rawa, dan ita duk wani namiji tsoro yake bata.

"Me ki ke yi a nan?"

"Mama nake jira ta dawo"

"Kuma sai ki zauna a nan ga sanyi, ki tafi ɗakin iya ki jirata mana"

Ta girgiza kai ta ce "Zan zauna a nan"

"Wuce ki tafi dalla!" Yayi maganar cikin tsawa. Da sauri ta nufi ɗakin Iya, ya bi bayanta.

Sai da iya ta ga ummi, sannan ta tuna ta ce da yamma a dawo da ita.

Iya ta ce
End Ads