amma za ta maimaita a gaban Allah, amma wallahi ba zan yafe ba, na ji labarin azabtar mini da ummi ta yi, amma yaya ɗan lami ka ƙi dagewa ka karɓo mini ummina"
Dr. Ya ce "Haba maman ummi, ki yi haƙuri abun da ya wuce ai ya riga ya wuce, ki yi haƙuri dan Allah" yayi maganar yana haɗa hannayensa.
"Ai kai na ce na yafe maka, tun da ka kawo mini ummi, kuma kana saya mini magani da abun da nake so, har yaya ɗan lami na yafe muku, amma ban da iya da wanda suka ci zalin ummina, bani da abun da zan gani na tuna da bashir sai ummi, amma ta ƙwace mini ita dan ta wulaƙanta ni"
Dr. Ya ce "Ba gani a gabanki kina kallona ba?"
"Yaya Yahaya ne fa ba Bashir ba, na gane ka yau" yayi murmushi ya fahimci memoryn na ta yana yi yana seizing ne.
Sun sha mamakin yadda ummi ta girma, ummi kuma kallon mamanta take yi, kamar ba ita ta haifeta ba, haryanzu shar da ita, gashi gaba ɗaya ba sa kama, sai kaɗan, kamar ya da ƙanwa ba uwa da ƴa ba.
Dangin mama kamar su cinye ummi, a yamamcin nan suka din ga zaryar ganin ummi, sai dai ta ɓoye ummi a bayanta, kowa ya zo sai dai ya hango ummi daga nesa wai kar a ɗauketa a mayar da ita wurin Iya.
Ummi ta ga ƙauna da soyayya, mariya ta din ga zuba mata hira, wata tana ganewa, wata ba ta ganewa, ummi space take son samu, ta kira raihan a waya ta sanar masa.
***
Raihan yana zaune a falon hajiya Aisha yana kaɗa ƙafa, yana danna wayarsa cikin damuwa, ya kasa samun ummi a waya.
Falon ta shigo cikin takunta na ƙasaita, ta samu wuri ta zauna ta kalli raihan ta ce "Kai, babanka ya kasa samunka a waya, yana ta ƴar murya a lallaɓoka ka koma fa"
Raihan ya gyara zamansa ya ce "Wallahi ko dan saboda Alhaji ban so na taho ba, mami ce taƙi tsayawa ta fuskance ni, na rasa yadda zan yi da ita wallahi, taƙi fahimta ta kuma anty rakiya ce take zigata"
"Kai dalla can, na kirata mun yi magana da ita, ba abun da za ta sake yi a kan maganar, ita ba a auren aka aureta? Mu ba auren zumunci ake a danginmu ba, babanka shi ya fara karya mana wannan ta'adar, ya aurota daga nan kowa ya samu ƴancin yin hakan, sai yanzu ita kuma ta ce ba za a auro wata ba?"
Raihan ya ce "Abun kuma har da gori?"
"Eh an yi mata gorin, da ai ba ayi ba, siyama na nemanka wai ka je ta girka maka menene oho mata"
Yayi murmushi ya ce "Nifa yanzu abincin kowa ya daina yi mini daɗi sai na matata"
"Ka ga fitsararre, amma dai da namun ka ke ci ko? Wai wani matarka ka ga idan ba ka rage rawar kan nan ba a kak yarinyar nan, haka zaku yi ta faɗa da babarka"
Raihan ya miƙe ya ce "Ni kaina na sani, ina ƙoƙarin ragewa wallahi, amma hannun ummi akwai maggi ta iya girki sosai"
Hajiya Aisha kawai ta yi murmushi ta girgiza kai, tana sake jinjina wautar mami, a irin wannan stage ɗin, ba a saka pressure wurin cewa lallai sai an tanƙwara namiji, sai nasiha da rarrashi idan ma so take ta soke auren.
Da daddare mariya da kanta, ta gyara katifarta, ummi ta kwanta, ta kawo abun rufa ta lulluɓe ummin, sannan ta rungumeta.
Sai da ta tabattar da mariya tayi bacci, sannan ta tashi zaune ta kira wayar raihan.
Aikuwa a take ya ɗaga ya ce "Ina ki ka shiga ne? Tun safe nake kiran wayarki amma shiru"
Ummi ta ce "Albishirinka"
"Goro fari ƙal"
"Na haɗu da mama"
Yana kwance ya tashi tsaye, ya ce "Wace maman?"
"Mamana mahaifiya, ashe kawuna ya san in da take, wai dan kar in gudu in ƙi zama na yi karatu ya sanya ya ɓoye mini"
Adduoi na nuna godiya ga Allah ya din ga jerowa, yana hamdala can kuma ya ce "Congratulations to both of us ummi, dan wallahi da al'amarin nake kwana nake tashi, ina tunanin ta ina zamu fara nemanta, Alhamdilillah Ala mun gode wa Allah"
Tare suka din ga murna da raihan a waya, suka gama ta ajiye wayar, ta rungume maman tsam a jikinta, tana tuno irin rabuwa da suka yi, da irin so da ƙaunar da maman nata ta nuna mata.
Bacci suka yi sosai da sosai, babban abun da ya burge ummi, ya ƙara sanyata nutsuwa, duk da rashin lafiyar da maman take fama, tana yin salla, sai dai wasu lokutan akwai kura-kurai sosai a sallar ta ta, amma duk da haka tana kamantawa.
A washegari kawu ya ce zai koma Kano, nan da sati biyu zai dawo ya tafi da ummi.
Yaya maryam ta ce "Dr. Ka tafi da ita kuma, kusan shekara goma sha takwas, ba sa tare kuma ace nan da sati biyu za a zo a ɗauketa a tausaya mana dan Allah"
Dr. Ya ce "Eh ai ban gama maganar bane ba, abu na farko ummi tana aiki, in da take aikin kuma sun jin daɗin zama da ita, abu na gaba kuma an saka mata rana watanni huɗu, kun ga za ta yi shirye-shirye ita da mijinta, daga kano ace ya din ga zuwa maiduguri yayi masa nisa, duk da dole zai zo ya gaisheku"
Anty maryam ta yashe baki tana faɗin "Masha Allah, Alhamdilillah"
Malam ma ya din ga murmushi yana sanya albarka.
"To amma, akwai ɗan shirye-shiryenmu da muke yi wa yaranmu na aure, ai da an bar mana ita mun yi mata"
Dr. Ya ce "Nan da watanni biyu zuwa uku sai ta dawo nan, ku yi duk shirye-shiryen ku a tsanake"
Yaya ɗan lami ya ce "Amma ba za a ƙara mana ko wata ɗaya ko biyu ya zama nan da wata shida ba, mu gama shirinmu mu ma"
"A'a kar ka damu, in sha Allah babu wani abu da zai gagara, manyan mutane ne, idan muka ce a ƙara zasu ga bamu kyauta ba, hakan ma in sha Allah babu abun da zai gagara"
Suka kammala tattaunawa, suna ta yi wa kawu godiya, ya kama hanya ya koma kano.
Ummi taga gata da ƙauna, babu kyara, babu hantara babu cin zarafi, duk ba a rasa wanda sukan yi maganar cewa ummi ba ta kama da mariya, mariya ta fita kyau da haske, maryam ce ma a tsaye take faɗan kar wanda ya sake yi musu wannan zancen.
Ummi murmushi kawai tayi, dan da ta san abun da tayi going through, da wannan bai ɗaga mata hankali ba.
***
A ka yi bikon raihan da ƙyar ya koma kano, Alhaji sai tsokanarsa yake "ni zaka yi wa yaji ko? Zamu gauraya da kai ne".
Hajiya ta ce "Raihan ba a fushi da iyaye, nan gaba kar sake aikata abu makamancin haka"
Raihan ya ce "Hajiya ba fushi na yi ba, na tafi ne dan na je na samu nutsuwar zuciya, amma in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba"
Cikin tsananin fargaba ya tashi ya nufi sashin mami, ba addu'ar da bai karanta ba, saboda ya san dole ne zuwansa ya tarar da sabon ɓacin rai.
A bedroom ɗin ta ya tarar da ita a zaune, cikin ladabi ya durƙusa ya ce "Mami barka da gida"
Maimakon ta amsa sai ta ƙure shi da ido, da har sai da ya fara tsarguwa.
"Ai gara in ƙare maka kallo, in tabattar da ni na haifeka kuwa? Ba matar ubanka ce kuwa ta haifeka ba ko har ubanka? In haifi ɗa a cikina ya janyo mini zagi da cin mutunci, raihan kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ka sani sarai matar nan ba ƙaunata take yi ba, ka je ka sameta ka kai ƙara ta ta kira ni ta ci mini mutunci"
"Wallahi mami ba ƙararki na kai ba"
"Yi mini shiru tun kan na fasa maka baki, ka kyauta ba dai wannan mummunar yarinyar ba ce ba, ka je gaka nan gata, amma ka sani babu yawuna babu saka hannuna a aurenka raihan, kuma bayan ka aireta sai ka auri safiyya. Kuma ban lamunci ka yi mata kayan lefe ba, tun da bazawara ce, dubu ɗari biyar ɗin ta isa komai da komai"
Cikin damuwa raihan ke ƙoƙarin yin magana, amma ta dakatar da shi, tare da bashi umarnin ya bar mata ɗaki.
Kansa har wani sarawa yake yi, wai ita safiyyan nan dole sai ya aureta kamar wahayi? Baya son ta ba ya ƙaunarta amma an dage sai ya aureta, ga kuma wata magana, wai ba zai yi wa ummi kayan lefe ba, to iyayenta ne zasu saya mata sutura da kayan kwalliyar da za ta yi masa a gidansa? Kuma a wannan marrar nawa dubu ɗari biyar take, da har za ta isa ayi wa ummi kayan lefe, nauyin ai sai ya yi wa iyayenta yawa, shi abun kunya ne ma a gare shi ace bai yi wa ummi kayan lefe ba. Haka yayi ta wasi-wasi yana nazarin abun a ransa.
Farida ba ta damu da in da ummi take ba, sai dai tana tambayar dr. Tana fatan ummi ta tafi kenan, amma yayi mata banza ya ƙyale ta.
Noor kuwa sai bin sa take tana tambayar sa, wai yaushe ummi za ta dawo, ita fa gidan babu daɗi idan ummi ba ta nan, ya ce mata zata dawo nan ba da daɗewa ba.
Ummi a gabanta aka fara haɗa kayan turarukan wutanta, wai akwai turarukan da sun fi shekara a binne a ƙasa ana tsuma su.
Yaya maryam ta kasa zama, kullum tana yawon kasuwa ita da mama, matar malam wurin yi wa ummi sayayyar kayan aure.
Ita babban abun da yafi faranta mata, bai wuce kasancewar ta da babarta ba.
Mami ta ƙara matsanta wa raihan, ga gefe guda kuma, Safiyya sai ta wani kira shi wai za ta gaishe shi, duk rashin son wulaƙanta ɗan Adam irin na raihan, ƙarshe sai da yayi blocking ɗin ta, dan ta daina damunsa da kira.
Ya cewa ummi zai zo Maiduguri ya ganta, ya kuma gaida mama, amma gudun matsala ya sanya ta ce masa ya bari ta kusa dawowa.
***
Sai da ummi tayi sati uku cif, sannan dr. Ya koma ɗaukar ta, kamar ta ce masa dan Allah ya barta a nan, amma sai ta ji nauyin hakan ta kasa, kayanta ƙwaya biyu da ta je da su, sai da aka ɗinka mata kusan kala goma a can, kuma tuni suka haɗa kayan gyaran jiki masu haɗe da turarrruka, ummi ta fara amfani da shi.
Yaya maryam sai jaddada mata take yi, kar ta yi wasa da kayan gyaran da aka ba ta ta yi, da sabulan da aka haɗa mata.
Mariya ta kalli dr. Ta ce "Ka yi mini alƙawarin ba wurin Iya zaka mayar da ita ba?"
Yayi murmushi ya ce "Ai aronta na ce ki bani, ba zan kai miki ita wurin Iya ba"
"To ai zaka dawo da ita ko?"
"In sha Allah"
"To dan Allah ka kula mini da ita sosai da sosai, kar ka bari ta yi kuka"
"In sha Allah zan kula da ita sosai da sosai"
Ta kalli ummi ta ce "Kar ki yi musu kuka kin ji ummi, ban da ƙyuya da kuka, ba ruwanki da yara, kar ki je su din ga dukanki kin ji ko?"
Ummi ta riƙe hannunta ta ce "To mamana, me ki ke so na taho miki da shi idan zan dawo?"
Ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Bakomai, ni dai kawai ki dawo, ba dan ina jin kunyar kawu yahaya ba, ba zan bashi ke ba"
Ummi ta cigaba da kallon mariya tana jin daɗi.
Da ƙyar suka rabu suka nufo hanyar Kano.
Duk rashin surutun ummi, haka ta sake ta din ga yi wa kawu hira tana bawa kawun labarin mamanta.
Bayan azahar suka sauka a kano, noor kamar ta mayar da ummi cikin ta, dan murnar ta dawo.
Ummi ta shiga har falo, ta ce wa farida sun dawo, ta amsa mata a yatsune, sai dai fuskar inteesar kawai ta kalla ta san matsala ce ta kawota gida.
Ummi ta koma ɗakinta, suka din ga hira ita da noor tana bawa noor labarin mamanta.
Noor ta ce "Kuma ki ka yadda ki ka dawo, wallaahi idan ni ce ba zan dawo ba, amma na san saboda yaya raihan ki ka dawo ko?"
Ummi ta ce "Ban sani ba"
Suka din ga dariya, noor ta ce "In gaya miki, Inteesar mijinta ya ɗauki amaryarsa sun tafi umara, shi ne take kuka wai ba a tafi da ita ba"
"To waye ya tambaye ki?"
Noor tayi shiru tana ƙifta idanu.
Haka nan take murna, ta san yau za ta ga raihan, ta rasa dalilin da ya sanya take murna.
Haka nan ta samu kanta da yin shirin haɗuwa da shi.
Ta ɗauki kayan tsaraba da ta zo da su, har da su kayan turaren wuta ta kai wa farida, ta karɓe ba tare da godiya ba.
Bayan sallar magariba ummi ta saka rigar atamfa bubu, tana ta fama ta ɗaura ɗankwali, abu ya gagara saboda ba ta saba ba, ƙarshe noor ce ta ɗaura mata da ƙyar, shima gashin ya ƙi rufuwa, sai da ta saka hula sannan aka ɗaura ɗan kwalin.
Ta yafa mayafi, tana ta rufe-rufe tana tunanin anya za ta iya fita a haka? Kiran wayarsa ta gani, ta tashi ta kalli noor ta ce "Anya in fita a haka kuwa?"
"Wallahi kin yi kyau, kin rufe ko ina kuma"
Da ƙyar ummi ta iya fita, tana ta kare jikinta, ta ƙarasa in da yake.
"Oyoyo sweetheart, long time"
Tayi murmushi ta zauna, tana kawar da kanta gefe.
"Congratulations once again, ya ki ka baro mini maman?"
Ummi ta yi murmushi ta ce "Tana lafiya ƙalau"
"Kin bata labarina kuwa?"
Ummi ta ce "Idan na yi mata babu lallai ta gane ma"
Ya ce "Ba ki yi niyya ba dai, zan je da kaina mu gaisa ai"
"Ka gama yajin?"
Yayi murmushi ya ce "Ke ma haka zaki ce?"
Ummi ta ce "To ba yajin ka yi ba, ko kunya ba ka ji ba?" Yayi dariya ya ce "Na samu mafita ai, kin yi kyau sosai da sosai wallahi, Allah ya nuna mana ranar nan lafiya babyna" ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kanta.
Kausar ce ta nufo in da suke zaune, dan haka yayi shiru yana kallon ta.
Cikin mamaki take kallon raihan, yanzu wannan ne zai auri ummi? Wannan yaron, amma kuwa tayi asara, ko kuma shi yayi asarar kyakykyawan matashi kamar wannan ya auri ummi. Ta yi maganar a zuciyarta
Cikin gadara ta ce "Ke ki zo maama tana kiranki, wa ki ka barwa yin abincin daren da haryanzu baki ɗora ba," tayi maganar cike da son wulaƙanta ummi a gaban raihan.
Raihan ya ce "Tana magana da mijinta ne, idan kun matsu ku ci, ku dafa, tana buƙatar hutu, tun da yau ta dawo daga tafiya, kuma ina buƙatar yin magana da ita"
Zare ido ummi tayi ta ce "Na shiga uku, raihan"
"Shhh" ya ɗora yatsansa a kan lips ɗin sa yana zare mata ido.
Ya sake kallon kausar ya ce "Ki koma ki ce ba za ta yi ba"
Ayshercool
08081012143.
*CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
34
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
Wani irin gumi ne ya dinga gangaro wa mami, duk da yadda sanyin AC ke ratsa ko ina a falon.
Raihan ƙararta ya je ya kai wa wannan masifaffiyar yar uban nasa kenan? tuno maganar Alhaji Tahir, da tuni ya bar falon da yayi ya sanya ta jin wata muguwar gudawa, saboda yadda cikinta ya murɗa mata.
Afujajan ta fita ta nufi sashinsa, har da tuntuɓe.
"Wallahi Baka isa ka gaya mini maganar da zata hana ni sukuni ka fice ka bar ni ba, kai yanzu saboda abun kunya goɗai-goɗai da kai sai ka auri yarinyar da ɗan ka ya ce yana so?"
Alhaji Tahir ya ce "In dai haka shi ne mafita a gareni me zai hana? Ku mata ku kuka san wani abun kunya, mu maza abu in dai mu yayi mana ba ruwanmu da abun kunya, kuma ina sake tunatar da ke, bana magana biyu, wallahi da gaske nake, sai dai idan na aureta wanda ba zai iya zama da ni ba ya ƙara gaba, shawara ta rage ga mai shiga shiga rijiya" ya ƙarasa maganar tare da ɗaukar wayarsa ya fita.
Kamar wadda ta zare, haka ta sake kwasa har da gudu, ta tafi ta kira Anty rakiya a waya.
Rakiya na ɗagawa mami ta fashe da kuka, "Anty rakiya na shiga uku na lalace"
"Wane irin kin shiga uku, meyafaru ba yanzu muka gama waya lafiya ba?"
"Ashe raihan bauchi ya tafi, ya je ya haɗo ni da wannan masifaffiyar matar yayar babansa, kin ga yadda ta ci mini mutunci kuwa? shi kuma Alhaji wai idan ban bari an yi auren ba, wai shi zai aureta ya kawota gidan nan a matsayin matarsa"
Anty Rakiya ta ce "Kai haba, dalla rabu da shi, barazana ce kar ki fasa wallahi, kar ki yadda a kawo miki bazawara a matsayin sirika"
"Anty Rakiya waye ya gaya miki Alhaji Tahir yana barazana ne? Magana ɗaya yake yi ko ta yi maka daɗi, ko kuma akasin haka, har rantsuwa yayi mini, na shiga uku, kuma wai raihan ya ajiye aikin nan ina na kama?"
Anty Rakiya ta ce "Taɓ, lallai raihan ba shi da hankali, to wallahi idan ki ka zuba masa ido, haka zai aurota ya fi ƙarfinki, tun da har ya san yayi miki yaji, ki kira shi ki ce lallai ya dawo dan ubansa"
Mami cikin takaici ta ce "Lamarin fa ya wuce yadda ki ke tunani, kin san taurin kan raihan kuwa? To cewa tayi wai ba zai dawo ba, ya bar aikin kenan, ya kuma ce idan aka karɓo kuɗin auren nan,