x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 47 - CUTARWA

  • 138001 words
  • 141000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 541

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
shi da aure har abada, ga babansa ya ce idan aka fasa zai aureta, na shiga uku ina na kama? Kin ga suna nema su haukata ni, raihan kafiya da taurin kai kamar ubansa, idan ya ƙi aure ya lalace yaya zan yi?"

Anty Rakiya ta ce "Ai kawai ki dage ki samu ya dawo tukuna, ki kira shi a waya"

"Wayoyin da duk ya kashe su, ina zan yi?"

"To ki koma ki samu babansa ki lallaɓa shi, ya dawo da shi kar a rasa wannan damar kuma ta kasuwancin nan "

Mami tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, zan kira ki mayi magana anjima" ta katse wayar ta ajiye tana wani irin haki, ita ba mai asma ba.

***
Dr. suna tafe a mota da shi da ummi, ya ce "Mamana zaki ga zamu yi doguwar tafiya, ba sayar da ke zan yi ba abun alkhairi ne"

Ummi ta yi murmushi ta ce "Idan sayar da ni ɗin ma ka yi ai na saidu kawu"

Yayi murmushi ya ce "Idan na sayar da uwata ina na kama? Yakamata ace kin yi azumin farinciki kan mu yi tafiyar nan"

"To Ubangiji ya tabattar mana da dukkanin alkhairin da yake cikinta"

Ya amsa mata da "amin"

Ummi ta gaji da zaman motar nan sosai da sosai, sai dai tun da taga symbols da sunan borno, jikinta ya fara sanyi, har ta rasa tunanin me ma za ta yi ne?.

Kawu kuma ya mayar da kai sosai a kan tuƙinsa, sai lokacin salla ya tsaya suka yi salla, ya saya mata abinci.

Ta tuno lokacin da ya ɗaukkota daga gagarwa a wahale, ba sutura ga ciwo, ko ba komai ta samu alkhairi a dalilin riƙonta da yayi

A ranta ta ce "Allah sarki kawuna, baba ya tafi amma ya bar mini Allah, Allah kuma ya bani kai, Allah ya kula da kai da zuriyarka".

Duk da ba ga saba baccin mota ba, gajiya ta sanya wani irin nannauyan bacci yin awon gaba da ita.

"Mamana tashi mun zo" a hankali ummi ta motsa tare da buɗe idonta, har suka fito daga cikin motar, ba ta iya cewa komai ba, sai bin wurin da kallo.

Ƙofar wani gida suka tsaya, dr. Ya ciro wayarsa ya ɗan daddana ya kara a kunnensa ya ce "Gamu mun zo"

Wani matashin saurayi ya leƙo ya durƙusa ya gaida dr. Sannan ya ce su shiga.

Suka shiga cikin gidan, ummi ta zubawa dattijon da suka tarar a tsakar ido, yana zaune a kan buzu, da Alƙur'ani bugun warshi a gabansa.

Dattijon ya miƙe tsaye yana yi musu maraba, tare da bin ummi da kallo, ba ta ɗaga niƙabin fuskarta ba, sai dai ta shagala da kallon sa ta san shi, amma a ina? Ta kasa tunawa.

Yayi musu jagora har wani matsakaicin falo, yana ta yi musu sannu da zuwa.

Suka gaisa da dr. Ummi ta gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa, sai dai bai tambayi wacece ba, kuma ya kasa daina kallonta.

Dr. Ya ce "Ina mutuniyar kuwa?"

"Wai sun fita barka a nan bayan layi, jikin ne ma ya ɗan motsa, amma Alhamdilillah mun gode Allah, bari azo a ɗora muku girki, ai bamu san zaku zo ba"

Dr. Ya ce "Ai alƙawarin da na ɗauka na zo cikawa, zuwan babu cikekken shiri, bari mu yi salla kafin su dawo".

Ya ja dr. Suka fita, bayan nuna wa ummi banɗaki, tayi alwala ta yi salla, ta nemi wuri ta kashingiɗa tana hutawa, saboda gajiyar da tayi.

Ummi ta ɗan jima a zaune, sannan dr. Ya shigo, shigowar ta sa yayi daidai da shigowar matashin da ya yi musu iso, ya kawo musu nono mai sanyin gaske, da nama fal malam ya ce a kawo musu da ruwa, dan azo a ɗora sanwa.

Ummi dai ta kasa sakewa ta ci, dr. Kuma sai hira suke yi da malam.

Dr. Ya ce "Malam ba ka ganni da baƙuwa ba ne? Baka tambayeni wacece ba"

Malam yayi murmushi ya ce "Tun da baka gaya mini ba, bai kamata na yi shishshigi ba ai, na ma zata ko mai ɗakinka ce, shiyasa ban yi magana ba, kuma na ganta sanye da niƙabi"

Dr. Yayi murmushi ya ce "Aishikenan, mama malam ne fa, baki gane shi ba?"

Ummi ta ce "Na sanshi amma na manta a ina?"

"To ki cire niƙabin ko zai gane ki"

Ummi ta jinjina kai tana ƙoƙarin cirewa, aka  yi sallama.

Bayan matar farko ta biyun ma tayi, a nan take ummi ta daskare, ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, ta ji tamkar numfashin ta zai bar ƙirjinta, wata irin tsuma ta ji ta fara yi, amma ta gaza motsawa.

Malam ya ce "Daga zuwa barka kun yi zamanku, gashi kun yi baƙi tafiyayyu daga kano"

Ta ce "Baban ummi ne?"

Malam ya ce "Eh shi ne, tun da shikaɗai ki ka sani a kanon ba"

Shigowa suka yi tare, tana riƙe da mayafinta a hannu, hannunta kamar amarya an yi mata lalle yayi jawur.

Ba ta kalli baban ummi ba, kai tsaye ummi ta zubawa ido, yayin da ummin ma ta zuba mata ido, tana jin yadda ƙirjinta ke lugude. Gaba ɗaya suka zuba musu ido, kai tsaye ta nufi ummi ta zauna a gabanta, tana cigaba da kallon ummi ta niƙabinta.

Ta miƙa hannu a hankali ta ɗaga niƙabin ummin, tayi tozali da fuskar ummin da a duniya bata ganin kyan komai, kamar yadda take ganin kyawun wannan fuskar.

A gigice ummi ta yi mata wata irin runguma ta fashe da matsanancin kuka, saroro mariya tayi, ta kasa taɓa ummi sai hawaye da ya fara zuba daga idonta.

Mama ta miƙa hannu tana faɗin "Ki yi mata a hankali ba ta da cikakkiyar lafiya"

Mariya ta buge hannun maman da ƙarfi, ta ruƙunƙume ummi, tana wata irin ajiyar zuciya kamar za ta fita daga hayyacinta.

Ta miƙa hannu ta warware mayafinta, ta lulluɓe da ummi da shi, ta ɗaukko mafici kuma tana yi mata fifita tana kuka.

Sai a yanzu suka gane wacece, malam ya sunkuyar da kai yana hawayen tausayin ƴar sa.

Ya zura hannu a aljihunsa ya ɗaukko wayarsa, ya kira Maryam a waya da kuma yaya ɗan lami.

"Ummina, kina cin abinci kuwa? Naga duk kin rame, iya tana yi miki wanka? Ko dai zazzaɓi ne a jikinki?" Tayi maganar tana ɗora hannu a goshin ummi.

Wasu irin jijiyoyi suka ɗaɗɗaga a goshin ummi, wani irin riƙo take yi wa mariya, tana jin kamar an sanyata a wata ni'ima.

Sun fi mintuna talatin a haka, sun ƙi sakin juna, mariya sai kakkare ummi take yi, kar wani ya taɓa mata ita.

Dr. Yayi gyaran murya ya ce "Yau na cika alƙawari ko?"

Ta jinjina masa kai, tana kuka ta ce "Wallahi ba zan taɓa yafe wa iya ba, Allah ya saka mini zaluncin da ta yi mini, ta ƙwace mini ummi bayan ba son ta take yi ba, ta ce ni na kashe mata ɗa, kalli yadda duk ummi ta rame, haka zan kwanta in yi ta mafarkin ummi tana kuka, tana cewa na zo na tafi da ita"

Ta ɗago ummi tana goge mata hawaye ta ce "Ki daina kuka kin ji ummana, ba zan sake bari a mayar da ke wurin iya ba, na san ba ta sonki ba ta ƙaunarki, ban san me ki ka yi mata ba, wallahi ba zan yafe mata ba, yaya ɗan lami yaƙi dagewa ya karɓo mini ƴa ta, kullum sai na yi kuka saboda ummi, yaya maryam ma ta hantare rannan wai kamar nikaɗai ce me ƴa, ki daina kuka kin ji ummina, da kaina zan din ga yi miki wanka, ina baki abinci, katifata zata ishemu mu din ga kwana tare, ba zan sake bari a kai ki wurin iya ba kin ji mamana"

Ummi ta ƙura mata ido, yadda mama ke wannan surutan daga wannan zuwa wancan tare da kasa gane ummi ta girma yanzu, ya tabbatar wa da ummi cewar mariya bata da lafiyr ƙwaƙwalwa.

Ta miƙa hannu ta ɗaukko ledar pure water, ta buɗeta ta saka wa ummi a baki tana faɗin "Na san ƙishirwa ki ke ji ummi, sha ruwa kin ji"

Babu wanda tausayin ummi da mariya bai kama a wurin ba, uwa kenan duk da ciwon ya motsa ba ta hayyacinta, amma hakan bai hanata gane ƴar ta ba, duk da shekarun da suka shafe basu haɗu ba.

Dr. Yayi gyaran murya ya ce "Alhamdilillah ala kulli halin, na gode Allah da ya sanya ummi da mahaifiyar ta suka haɗu, ba tare da ta Allah ta kasance ba. Ummi na yi miki laifi, kuma na yi muku duk da ina godiya da fahimta ta da ku ka yi.
Ummi ban ƙi sada ki da mahaifiyarki dan baƙanta miki ba, a lokacin da na ganota, tana cikin halin larura sosai, ba komai take ganewa ba, na yi fargabar haɗuwarku ba za ta yi daɗi ba, idan ku ka haɗu ta kasa gane ki, abu na gaba kuma ina tsoron halin da ki ke ciki, ya sanya ki ƙi zama ki dawo wurinta, alhalin kina tsaka da karatu, dan duk wanda yake ruwa, ko takobi aka miƙa masa zai kama, dan haka a matsin nan da ki ke, duk da kasancewar ki mai biyayya, zaki iya bujirewa ki zaɓi dawo wa gaban mahaifiyarki, ba tare da kin yi acheiving wani abu ba.
Wanda a lokacin babban burina da fatana, ki samu nagartaccen ilimi, da zaki iya tsayawa da ƙafafuwanki, ina fatan zaki yafe mini daga ke har mahaifiyar ki" yayi maganar a sanyaye.

"Ai dama kai na yafe maka, baka cuceni ba, amma iya iya iya, ban san me na yi mata ba, amma za ta maimaita a gaban Allah, amma wallahi ba zan yafe ba, na ji labarin azabtar mini da ummi ta yi, amma yaya ɗan lami ka ƙi dagewa ka karɓo mini ummina"

Dr. Ya ce "Haba maman ummi, ki yi haƙuri abun da ya wuce ai ya riga ya wuce, ki yi haƙuri dan Allah" yayi maganar yana haɗa hannayensa.

"Ai kai na ce na yafe maka, tun da ka kawo mini ummi, kuma kana saya mini magani da abun da nake so, har yaya ɗan lami na yafe muku, amma ban da iya da wanda suka ci zalin ummina, bani da abun da zan gani na tuna da bashir sai ummi, amma ta ƙwace mini ita dan ta wulaƙanta ni"

Dr. Ya ce "Ba gani a gabanki kina kallona ba?"

"Yaya Yahaya ne fa ba Bashir ba, na gane ka yau" yayi murmushi ya fahimci memoryn na ta yana yi yana seizing ne.

Sun sha mamakin yadda ummi ta girma, ummi kuma kallon mamanta take yi, kamar ba ita ta haifeta ba, haryanzu shar da ita, gashi gaba ɗaya ba sa kama, sai kaɗan, kamar ya da ƙanwa ba uwa da ƴa ba.

Dangin mama kamar su cinye ummi, a yamamcin nan suka din ga zaryar ganin ummi, sai dai ta ɓoye ummi a bayanta, kowa ya zo sai dai ya hango ummi daga nesa wai kar a ɗauketa a mayar da ita wurin Iya.

Ummi ta ga ƙauna da soyayya, mariya ta din ga zuba mata hira, wata tana ganewa, wata ba ta ganewa, ummi space take son samu, ta kira raihan a waya ta sanar masa.

***

Raihan yana zaune a falon hajiya Aisha yana kaɗa ƙafa, yana danna wayarsa cikin damuwa, ya kasa samun ummi a waya.

Falon ta shigo cikin takunta na ƙasaita, ta samu wuri ta zauna ta kalli raihan ta ce "Kai, babanka ya kasa samunka a waya, yana ta ƴar murya a lallaɓoka ka koma fa"

Raihan ya gyara zamansa ya ce "Wallahi ko dan saboda Alhaji ban so na taho ba, mami ce taƙi tsayawa ta fuskance ni, na rasa yadda zan yi da ita wallahi, taƙi fahimta ta kuma anty rakiya ce take zigata"

"Kai dalla can, na kirata mun yi magana da ita, ba abun da za ta sake yi a kan maganar, ita ba a auren aka aureta? Mu ba auren zumunci ake a danginmu ba, babanka shi ya fara karya mana wannan ta'adar, ya aurota daga nan kowa ya samu ƴancin yin hakan, sai yanzu ita kuma ta ce ba za a auro wata ba?"

Raihan ya ce "Abun kuma har da gori?"

"Eh an yi mata gorin, da ai ba ayi ba, siyama na nemanka wai ka je ta girka maka menene oho mata"

Yayi murmushi ya ce "Nifa yanzu abincin kowa ya daina yi mini daɗi sai na matata"

"Ka ga fitsararre, amma dai da namun ka ke ci ko? Wai wani matarka ka ga idan ba ka rage rawar kan nan ba a kak yarinyar nan, haka zaku yi ta faɗa da babarka"

Raihan ya miƙe ya ce "Ni kaina na sani, ina ƙoƙarin ragewa wallahi, amma hannun ummi akwai maggi ta iya girki sosai"

Hajiya Aisha kawai ta yi murmushi ta girgiza kai, tana sake jinjina wautar mami, a irin wannan stage ɗin, ba a saka pressure wurin cewa lallai sai an tanƙwara namiji, sai nasiha da rarrashi idan ma so take ta soke auren.

Da daddare mariya da kanta, ta gyara katifarta, ummi ta kwanta, ta kawo abun rufa ta lulluɓe ummin, sannan ta rungumeta.

Sai da ta tabattar da mariya tayi bacci, sannan ta tashi zaune ta kira wayar raihan.

Aikuwa a take ya ɗaga ya ce "Ina ki ka shiga ne? Tun safe nake kiran wayarki amma shiru"

Ummi ta ce "Albishirinka"

"Goro fari ƙal"

"Na haɗu da mama"

Yana kwance ya tashi tsaye, ya ce "Wace maman?"

"Mamana mahaifiya, ashe kawuna ya san in da take, wai dan kar in gudu in ƙi zama na yi karatu ya sanya ya ɓoye mini"

Adduoi na nuna godiya ga Allah ya din ga jerowa, yana hamdala can kuma ya ce "Congratulations to both of us ummi, dan wallahi da al'amarin nake kwana nake tashi, ina tunanin ta ina zamu fara nemanta, Alhamdilillah Ala mun gode wa Allah"

Tare suka din ga murna da raihan a waya, suka gama ta ajiye wayar, ta rungume maman tsam a jikinta, tana tuno irin rabuwa da suka yi, da irin so da ƙaunar da maman nata ta nuna mata.

Bacci suka yi sosai da sosai, babban abun da ya burge ummi, ya ƙara sanyata nutsuwa, duk da rashin lafiyar da maman take fama, tana yin salla, sai dai wasu lokutan akwai kura-kurai sosai a sallar ta ta, amma duk da haka tana kamantawa.

A washegari kawu ya ce zai koma Kano, nan da sati biyu zai dawo ya tafi da ummi.

Yaya maryam ta ce "Dr. Ka tafi da ita kuma, kusan shekara goma sha takwas, ba sa tare kuma ace nan da sati biyu za a zo a ɗauketa a tausaya mana dan Allah"

Dr. Ya ce "Eh ai ban gama maganar bane ba, abu na farko ummi tana aiki, in da take aikin kuma sun jin daɗin zama da ita, abu na gaba kuma an saka mata rana watanni huɗu, kun ga za ta yi shirye-shirye ita da mijinta, daga kano ace ya din ga zuwa maiduguri yayi masa nisa, duk da dole zai zo ya gaisheku"

Anty maryam ta yashe baki tana faɗin "Masha Allah, Alhamdilillah"

Malam ma ya din ga murmushi yana sanya albarka.

"To amma, akwai ɗan shirye-shiryenmu da muke yi wa yaranmu na aure, ai da an bar mana ita mun yi mata"

Dr. Ya ce "Nan da watanni biyu zuwa uku sai ta dawo nan, ku yi duk shirye-shiryen ku a tsanake"

Yaya ɗan lami ya ce "Amma ba za a ƙara mana ko wata ɗaya ko biyu ya zama nan da wata shida ba, mu gama shirinmu mu ma"

"A'a kar ka damu, in sha Allah babu wani abu da zai gagara, manyan mutane ne, idan muka ce a ƙara zasu ga bamu kyauta ba, hakan ma in sha Allah babu abun da zai gagara"

Suka kammala tattaunawa, suna ta yi wa kawu godiya, ya kama hanya ya koma kano.

Ummi taga gata da ƙauna, babu kyara, babu hantara babu cin zarafi, duk ba a rasa wanda sukan yi maganar cewa ummi ba ta kama da mariya, mariya ta fita kyau da haske, maryam ce ma a tsaye take faɗan kar wanda ya sake yi musu wannan zancen.

Ummi murmushi kawai tayi, dan da ta san abun da tayi going through, da wannan bai ɗaga mata hankali ba.

***
A ka yi bikon raihan da ƙyar ya koma kano, Alhaji sai tsokanarsa yake "ni zaka yi wa yaji ko? Zamu gauraya da kai ne".

Hajiya ta ce "Raihan ba a fushi da iyaye, nan gaba kar sake aikata abu makamancin haka"

Raihan ya ce "Hajiya ba fushi na yi ba, na tafi ne dan na je na samu nutsuwar zuciya, amma in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba"

Cikin tsananin fargaba ya tashi ya nufi sashin mami, ba addu'ar da bai karanta ba, saboda ya san dole ne zuwansa ya tarar da sabon ɓacin rai.

A bedroom ɗin ta ya tarar da ita a zaune, cikin ladabi ya durƙusa ya ce "Mami barka da gida"

Maimakon ta amsa sai ta ƙure shi da ido, da har sai da ya fara tsarguwa.

"Ai gara in ƙare maka kallo, in tabattar da ni na haifeka kuwa? Ba matar ubanka ce kuwa ta haifeka ba ko har ubanka? In haifi ɗa a cikina ya janyo mini zagi da cin mutunci, raihan kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ka sani sarai matar nan ba ƙaunata take yi ba, ka je ka sameta ka kai ƙara ta ta kira ni ta ci mini mutunci"

"Wallahi mami ba ƙararki na kai ba"

"Yi mini shiru tun kan na fasa maka baki, ka kyauta ba dai wannan mummunar yarinyar ba ce ba, ka je gaka nan gata, amma ka sani babu yawuna babu saka hannuna a aurenka raihan, kuma bayan ka aireta sai ka auri safiyya. Kuma ban lamunci ka yi mata kayan lefe ba, tun da bazawara ce, dubu ɗari biyar ɗin ta isa komai da komai"

Cikin damuwa raihan ke ƙoƙarin yin magana, amma ta dakatar da shi, tare da bashi umarnin ya bar mata ɗaki.

Kansa har wani sarawa yake yi, wai ita safiyyan nan dole sai ya aureta kamar wahayi? Baya son ta ba ya ƙaunarta amma an dage sai ya aureta, ga kuma wata magana, wai ba zai yi wa ummi kayan lefe ba, to iyayenta ne zasu saya mata sutura da kayan kwalliyar da za ta yi masa a gidansa? Kuma a wannan marrar nawa dubu ɗari biyar take, da har za ta isa ayi wa ummi kayan lefe, nauyin ai sai ya yi wa iyayenta yawa, shi
End Ads