x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 24 - CUTARWA

  • 69001 words
  • 72000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 538

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
rabu da mutanen nan lafiya, kowa ya ɗebo da zafi ai bakinsa, gobe ba ya ƙara ba".

Da labari ya iske idiris kuwa, masifa ya fara yi, yana baloƙoƙon shi fa ba ya son Hindu, ban da zalunci yarinyar da har haihuwa ta yi, tayaya za a ce wai ayi mata kaya kamar budurwa, saboda son zuciya.

Cikin tsananin fusata mahaifinsa ya ce "Rufe mini baki, ko na turmushe ka a wurin, mara mutunci, muna zaman zamanmu ka janyo mana masifa, ka sanya kowa a tashin hankali, kuma wallahi ko ka so, ko ka ƙi sai ka auri yarinyar nan, ka ƙarata can bayan auren" yayi masa ta tas ya tafi ya bar shi.

Magaji yayi murmushi ya ce "Allah sarki ummi, baiwar Allah yanzu idan na ce hakkinta ne ya fara bibiyarku, sai ace ƙarya ne a hayayyaƙo mini, da ka yi haƙuri da ummi, ka nema mata magani tsaf zata warke ku zauna lafiya, amma ka din ga muzanta ta, kana yamaɗiɗi da ita a kan larurar da ta same ta, har abokan ka suna ce maka angon ɗaɗɗoya saboda zunzurutun wulaƙanci da tozarci, ka saketa bayan ka gama azabtar da ita, saboda ka na taƙama da kai ɗan iska ne.
Kai ma gashi Allah ya tozarta ka, gara nata tarihi zai iya shafe shi, naka kuwa har gaban abada ba zai goge ba, kuma kaɗan ka gani, ba dai bariki ba sai ma ka auro wannan ɗin, zaka san ka yi asarar mace".
Duk wannan faɗan da magaji yake yi masa, bai iya cewa komai ba, saboda ya san ba shi da gaskiya, kuma yanzu yana cikin tashin hankali da tunanin menene mafita.

***
Ummi tana ta dakon zuwan kawu, tare da fatan Ubangiji Allah ya sanya ya samo in da mama take, gara ta tattara ta koma can wurinta, dan da ta san in da take da ta daɗe da barin gidan nan, ko bola take bi za ta din ga bin ta.

Sai da aka shafe kusan sati uku, sannan dr. Ya zo gida, bayan yayi kwana biyu ya ɗan nutsu ya huta, ummi ta same shi shikaɗai a falo, ta gaishe ta samu wuri ta zauna.

"Ummana, ya aka yi ne?"

"Dama ba wani abu bane kawu, dama tambayarka zan yi ko ka gano in da maman take?" Tayi maganar kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

Ya ɗan yi shiru yana nazarin ta, sannan ya ce "Akwai matsala ne?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Na san ba zaki faɗa ba dama, rabonki da yi mini wannan zancen an kwana biyu, na san a takure ki ke ummi, amma ki yi haƙuri, ina nan ina ta ƙoƙari a kai, ba yadda ban yi da Iya ba, ta ce mini ita ba ta sani ba.
Ƙanin babanmu da yayi masa walicci ma ya rasu, su ilyasu sun ce basu san sunan garin ba, su dai kawai an zo da mota an kai su, na san faɗa kawai suke yi, Iya ce ta hana su faɗa.
Amma ina nan ina ta bincike, ina da hotunanta biyu, da aka yi mana bayan bikin da na je gida, ina ta bincikawa, na samo sunan garin, ainihin yankin da take a garin ne ban sani ba, ana ta bincikawa ummi, ina sane ban manta ba, ki cigaba da addu'a da kula da karatunki, komai zai warware in sha Allah".

Ummi ta risuna ta ce "Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi".

Ya ce "Amin ummana, baki ce Allah ya yi mini albarka ba"

Rufe fuska ummi tayi tana murmushi.

Ya ɗora da cewa "Kwanaki an ce mini ɗan uwan mamanki ya zo ganinki, Iya taƙi gaya masa in da ki ke, ta ci mutuncin sa ya tafi. Amma dai in sha Allah ina nan ina ƙoƙari a kai".

"To kawu na gode"

Ta tashi ta nufi ɗakinta, tana sake jinjina ƙiyayyar da Iya take yi wa mahaifiyarta da ƴan uwanta.

Kasancewar maryam gaba take da ummi dama, dan haka ta riga ummi candy, tun kan ta yi candy aka kawo kuɗin aurenta, dan haka an yi candy babu daɗewa bikin ya tinkaro.

Maryam ba ta tsaya saurarar ummi ba, ta sayi anko ta bawa ummi duk kyauta, sai dai da ƙyar farida ta bar ummi ta je rana ɗaya bikin, shi ma da ta je kasa sakewa tayi, dan wareta ƴan makarantar ma suka din ga yi, dan haka nan da nan ta koma gida ta bar wurin.

Satin Maryam biyu a gidanta, mijin ya tafi da ita can wurin aikinsa, kasancewar soja ne babba.

***
Kwanci tashi asarar mai rai, iyayen hindu suka din ga tatsar su Iya kuɗi, har sai da ta yi watanni shida cif a gida, sannan aka ɗaura auren Idris da hindu, saboda babanta dagewa yayi a kan sai an kai kuɗin aure da duk wani abu na al'ada da ake yi.

Tare da cigaba da yi musu barazanar cewa, zasu dawo musu da ƴar su.

Abun kunya dai da ake gudu, ya riga ya gama watsuwa a cikin gagarawa, na abun kunyar da jikan Iya ya tabka.

Gidan da ummi ta zauna, aka sake kama haya, kansancewar ba kowa a ciki, aka ƙara gyara gidan, aka kai hindu da jaririyarta.

Ko kallo hindu ba ta ishi idris ba, haka ita ma ba ta kansa ta bi ba, ta cigaba da sabgoginta da ƴar ta, sai dai cikin dare yarinyar nan ta tashi, ta din ga tsala ihu kamar za ta shiɗe.

A fusace ya tashi ya ce "Dalla malama ki ɗauki ƴar ki saka tayi shiru, ta cika wa mutane kunne da kukan banza".

"To kai mai zai hana ka saka tayi shirun, na ga kaima ƴar ka ce"

"Ƴar gaba da fatihar? Kar ki sake haɗani da ita".

"Ko ƴar gaba da meye uban waye yayi cikinta, ai ba ita tayi kanta ba, ka ga wallahi ka ce zaka takura mini, ko ka ɗaga mini hankali sai na koma gida na gaya musu. Kai ba ma ka da kunya, ni ka ke gayawa ƴar gaba da fatiha ce, uban waye ya lalata ni?".

"Iyayenki dai suka ja miki, da ba aurenki zan yi ba, suka hana ni".

Hindu ta yi shewa ta ce "To uban wa ye zai baka auren ƴa? Kana ɗan iska?"

"Eh ina ɗan iskan amma ai gashi an liƙa mini ke"

"Oho kai ka sani dai"

Ta dubi ƴar da ke ta tsala ihu ta ce "Ke hajara tsohuwar banza, ubanki ya ce ki yi masa shiru, ƴar gaba da fatiha"

Idiris ya ce "Tsohuwar banza, kakata ki ke zagi kenan?"

"Eh to, idan ka tsargu hakan ne" haka suka din ga faɗa kamar kaji, a tsakiyar daren nan maƙwabta na jin su.

Abdul ne yayi sallama a kitchen, ummi na girki, suna ta tilawar Alqur'ani ita da noor.
Raino ummi take yi wa noor da kulawa, bacci ne kawai yake raba su, baccin ma wataran a ɗakinta take yi.
Tun kan noor ta shiga makaranta, ta iya azkar da karatun Alqur'ani, dan ba ta yi pre nursery ba, kai tsaye nursery 1 aka kaita, saboda ta har rubutu ta fara iyawa.

Sai dai noor masifaffiya ce, ba ta taɓuwa a wurin yayyenta, dan baki ne da ita sosai da sosai.
Ba ta jin maganar farida, kamar yadda take jin maganar ummi, fitsara da rashin kunya kuwa ba a magana, ummi da Abdul kawai take ɗagawa ƙafa, ƴar mitsitsiya da ita ga azabar taurin kai, ummi ce kawai take iya sarrafa ta yadda take so, dan haka ba wani shiga shirgin noor suke yi ba, tayi maka rashin kunya ka jibgeta ba za ta yi kuka ba.
Ummi tayi ta mata faɗa, dan ita kanta tana mamakin rashin kunyar noor.

"Yaya ummi" Abdul ya kira sunanta.

Cikin haɗa baki ita da noor suka ce "Na'am yaya Abdul"

Abdul ya tsuke fuska ya ce "Da ke nake?" Ta girgiza masa kai tana ɗan murguɗa baki.

Ummi ta kalli Abdul ta ce "Yaya Abdul yaya ake ciki? Ka dubo mini"

Ya miƙo mata envelope ya ce "Eh to, congratulations you got nine credits including maths and English, i know you can do it ai"

A take ummi tayi sujjadar godiya ga Allah, noor ma ta durƙusa tayi, ummi ta ɗago tana Alhamdilillah.

Noor ta ce "Wai menene? Me aka yi?"

Abdul ya ce "Yaya ummi ta ci jarrabawa, dan haka ita ma very soon zata shiga jami'a"

Tsalle noor ta din ga yi tana ihu, ba tare da ta san ma menene cikakken bayanin ba.

Kausar ta shigo kitchen ɗin tana tambayar lafiya.

Noor ta ce "Yaya ummi ta ci jarrabawa, za ta shiga jami'a".

Tsaki kausar ta yi ta ce "Shi ne kuma ki ke yi mana ihu?"

"Eh ɗin, yeeee yaya ummi ta ci jarrabawa " tayi maganar tana tsalle ta fita daga kitchen ɗin.

Kausar ta yi tsaki ta fice, Abdul ya ce "Yaya Ummi, kina zaune an haifi mai tare miki faɗa"

Ummi ta ce "Ni mamana saliha ce, amma mama ƙarama ta fiye tsiwa" suka yi dariya, ummi na sake godewa Allah a kan wannan gagarumar nasara da ta samu.

Takanas saboda ummi dr. Ya dawo gari, saboda shirye-shiryen nema mata admission, Abdul yana level 2 a BUK yana karantar Agric.

"Dr. Wai ya na ganka a gida a tsakiyar sati haka? Kuma na ga baka daɗe da tafiya ba".

"Abdul yayi mini magana a kan waec ɗin ummi, ina son in ƙarasa mata abubuwan da yakamata kar ayi mini ba dai-dai ba".

"Shi ne ba zaka wakilta wani ba, sai ka dawo da kanka?"

"Ki na da damuwa da hakan ne?".

Haushi ne yakamata tayi masa banza, duk iya ƙoƙarin ta a kan cire hankalinsa daga kan ummi, ta kasa nasara ɗari bisa ɗari.

Ta sake kallonsa ta ce "Wai ni dr. Zuwa yaushe zan cigaba da jerawa da ummi a gidan nan, intee tana gama secondary, nake son a aurar da ita, yaron ya matsa, ita kuma tana nan shirin tafiya jami'a ma take yi, gaskiya ina son privacy a gidana, ba zan cigaba da jerawa da gandamemiyar budurwa ba".

"Intee ke ki ka takura a karɓi kuɗin aurenta, ba dole na yi muku ba, ni kuma a ƙyale mini ƴa tayi karatu. Guda nawa ummin take da ki ke wani zancen gandamemiyar budurwa, yanzu fa za ta shiga jami'ar".

"To wai ina uwarta, a mayar da ita wurinta mana".

A fusace ya ce "Wai a kan ki ummin nan take ne?".

Muryar noor ce ta katse shi, tun daga wajen ɗakin take ƙwala masa kira.

Ya ce "Na'am shalelena"

"Kalli littafina, uncle ya saka mini 10 over 10, assignment ɗin da anty ummi ta koya mini".

Ya ce "Wow masha Allah, congratulations baby".

"Thank you " ta faɗa cikin iyayi sannan ta ce "To nima tunda na ci jarrabawar, zan shiga University?"

Ya kwashe da dariya ya ce "From primary one to university?"

"Eh, ba anty ummi ma ta ci jarrabawa zata shiga university ba?"

Yayi dariya, ya biye mata ta gama shirmen ta, ta tafi, sannan ya kalli farida ya ce "Farida wai zuwa yaushe zaki daina planing ɗin nan, noor tayi girma yakamata ace kin sake haihuwa, 4yrs fa".

Farida ta yamutsa fuska ta ce "Nifa na gama haihuwa, yaushe Allah ya amfana guda huɗun".

"Amma da bani da yadda zan yi na riƙe ne, sai ki faɗi haka, Allah ya yassare mini yadda zan kula da yarana, meyasa zaki ce kin daina haihuwa?".

Ta miƙe tsaye ta ce "Ka auri ummi ta haifa maka!".

Wani irin damm ƙirjinsa yayi, ya bita da kallo, saboda munin maganar da ta faɗa.

Ya girgiza kai kawai, domin ba shi da abun da zai faɗa gaba ɗaya.

Iya ƙoƙari kawu yahaya ya yi wa ummi, a kan harkar makarantar ta, dan ma farida na ta yi mata mugunta a kan wasu abubuwan.
Yayi mata komai sai dai ɓangaren sutura ummi na fuskantar barazana, domin kuwa ummi ba ta da suturar kirki, duk da ma'abociyar hijjabai ce, su kansu hijjaban nata duk sun mutu su yi haske.

(Kowane ƙalubale ummi za ta fuskanta a jami'a? Bright pens na godiya sosai 🙏)

Whats app only please.
Ayshercool
08081012143
   *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P20

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

20

Ummi ganin al'amuran take yi kamar a mafarki, duk da tsanani da matsi, haɗi da ƙalubale daban-daban yau ga ta a makarantar jami'a, lallai lokaci yana sauri.

Hakazalika ta na ta shirye-shiryen haɗa saukarta ta biyu, domin kuwa bayan ta yi sauka ta cigaba da zuwa makaranta, ƴan ajinsu galibi duk sun yi aure, dama duk sun girme mata.

Wuri ɗaya ta samu ta zauna a ajin, jikin window ne in da take, hakan ya bata damar kallon shige da ficen ɗalibai, tsofaffi wanda sun kusa fita ma, da masu rawar kai wanda yanzu suka shigo jami'a.

Shigowar wani babban mutum ajin ne ya sanya ɗaliban ajin nutsuwa, tare da gaida mutumin.

Ya amsa musu, tare da gabatar da kansa a matsayin HOD ɗin su, ya nemi da kowanne daga cikin ɗaliban, ya tashi ya gabatar da sunansa da kuma garin da yake.

Haka nan gaban ummi ya faɗi, dan kuwa ba ta son mutane, da duk wani dalili da zai sanya a takurata da kallo.

Ɗalibai suka din ga gabatar da kansu ɗaya bayan ɗaya, kan azo kan ummi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, sai wata irin fargaba take yi.

Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye, fuskarta sanye da facemask, malamin yayi mata alama da ta sauke facemask ɗin.

Gabanta ya sake faɗuwa a karo na biyu, hannunta har rawa yake yi, ta sauke facemask ɗin tana jiran jin ƙanan magana kamar yadda ta saba, sai dai ba ta ji hakan ba.

Sai dai ta kasa magana, sai da ta ɗan sauke numfashi, sannan ta ce "My name is.... Sai dai ta kasa ƙarasawa, saboda yadda gaba ɗaliban suka juyo suna kallonta.

Ummi na da murya mai matuƙar ɗaukar hankali, duk wanda bai santa ba, idan har tayi magana dole zai waiwaya domin ganin mai muryar.

Ko a islamiyya idan ana musaffa, Alla-Alla suke yi a zo kan ummi, saboda ta iya ƙira'a mai daɗin sauraro.

Ganin ta diririce saboda kallon da ake yi mata ne ya sanya malamin takowa zuwa gabanta, ta ko ƙara sunkuyar da kanta ƙasa, tare da wasa da yatsun hannunta a cikin hijjabinta.

"Kin manta sunan naki ne?" Ta girgiza masa kai.

Ya sake cewa "Ko ba turanci ne?" Nan ma ta sake girgiza masa kai.

"Oya ya sunanki?"

"Salma Muhammad Bashir"

Yayi murmushi ya ce "What a beautiful name, na ga duk a tsorace ki ke, but mark you, this is university idan malamai suka gane kina jin tsoron magana a public, za su yi ta takura miki da tambaya, ke kina jin tsoron amma ki ka zaɓi aikin jarida? Ai harkar jarida na masu baki ne. But you can do it when you overcome your fear"

Ta ɗago a hankali ta ce "Thank you sir"

"Ƴar wace ƙasar ce ke?"

"Jigawa" tayi maganar muryarta na ɗan rawa.

"Ƙasa fa"

Ta ce "Au Nigeria"

"Are you sure? Ko dai ta ɓarauniyar hanya ki ka shigo mana ƙasa? Kin yi kama da baƙaƙen larabawan Afrika"

Ummi a ranta ta ce 'Amma kuwa an cuci larabawa, ko kuma ni aka cuta, maybe ba'a yake yi mini'

Ƴan ajin kuwa dariya suka hau yi, ya ce "Kalar idonta da complexion ɗin ta, ba irin na ƴan Nigeria bane, dan haka zamu bincika idan baki da lasisin zama a Nigeria mu mayar da ke ƙasarku" yayi maganar cikin zolaya.

A dole ummi ta ƙaƙalo murmushi.

Ya ce "Yi zamanki, Allah ya yi albarka" kan ta zauna ta risuna ta ce "Na gode sosai Allah ya jiƙan magabata" ya ɗan ƙurawa ummi ido, yadda take amsa masa magana ma, kawai ya isa ka gane tana da tarbiyya sosai. Ya ce "Amin" sannan ya suce gaba.

Yayi musu nasiha sosai da sosai, a kan kula da ilimi da kuma tarbiyarsu, da ba su shawarar su riƙe addinansu, kar su lalace saboda kawai sun ga sun shiga jami'a.

Kowa harkarsa yake ba ruwan wani da wani, dan haka ummi ta ji daɗin hakan, da babu wanda ya matseta balle ya takura mata.

Baki har kunne ta koma gida tana murna, duk da tana zuwa gidan ta tarar da uban kwanukan wanke-wanke, da wankin kaya, kuma an cinye abinci tas, kuma ana jiran ta ɗora na dare.

Hijjabi kawai ta canza ta hau aiki, noor ta din ga bin ta, tana tambayarta "Anty, kin yi magana a gidan radiyon?"

Ummi ta ce "A'a mamana, sai an kwana biyu tukuna"

"To ta ina zaki din ga shiga radion kiyi magana?"

Sai dare yayi kin yi bacci, zan buɗe gurin batirin in shiga ta ciki.

Noor ta buɗe baki cikin mamaki, sannan ta ce "To zaki shiga da ni nima?"

"Sai kin ƙara girma sosai tukuna, noor ta dinga tsalle tana murna.

***

"Bilki, ki kira Bauchi ki gaya musu ba fa haka muka yi da su ba, ni fa ba bar musu ɗa na na yi ba, haba sun riƙe mini ɗa ko leƙo ni baya yi".

Ta kalleshi ta ce "Taɓ, ba ruwana
End Ads