zancen ya dosa, ta ce wa noor "Rakata ku yi cefanen, sai ayi girki kowa ya ci"
Iya na kallonsu ba ta kula su ba.
Kusan mintuna talatin, ummi ta tayar da salla, ta ji sallamar su noor, sun dawo, sai dai suna shigowa ba daɗewa Idris ma yayi sallama, kuma bai yi wata-wata ba, ya hau yarinyar ta sa da duka.
Ihu take yi tana neman taimako, ummi ta yanke sallar ta fito da sauri, ya saka itace yana ta jingar yarinyar, har bakinta ya fara kumfa.
Ummi ta hankaɗe shi, ta riƙo ta, bai san wacece ba, ya kuma kawo itacen yana ƙoƙarin janye yarinyar, a fusace ummi ta tsinka masa mari, da ya sanya shi ɗaga ido ya ga wacece.
"Jahilin ina ne kai? Azzalumi mara imani, ƴar ta ka ma baka ƙyale ba, dabban ina ne kai idris?"
Ayshercool
08081012143
*CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
37
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Alhamdilillah ala kulli halin, ina amfani da wannan damar, wurin isar da ɗimbin godiyata ga ƴan uwana marubuta, tarin masoya makaranta, da sauran al'ummar da suka yi mini ta'aziyyar rashin kakata, ina fatan Ubangiji Allah ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya, ya kuma bar zumunci, yayi mana jagora a rayuwa baki daya, Allah ya sanya kaburburan magabatanmu ya zama dausayi daga aljanna, idan tamu ta zo ya sanya mu cika da imani*
37
A razane yake kallon ummi daga sama zuwa ƙasa, iya kuma ta miƙe tsaye da sakakken baki ta kasa magana.
Ummi ta durƙusa ta ɗago yarinyar da take zubar da wani irin yawu daga bakinta, saboda wahalar duka.
Noor kuwa na gefe tana tsuma, duk da basu saba ba, tare suka yo cefane, har noor ta bata shawarar su sayo taliya sai tafi sauri, tun da ummi ba ta gaya musu me zasu sayo ba.
Suna tafe a hanyar ta kalli noor ta ce mata "Ya sunanki?"
"Sunana mariyatul kibɗiya, ana ce mini noor"
"Masha Allah, sunanki me daɗi"
Noor ta ce "To ke ya sunanki?"
"Wai hajara, sunan kakata aka saka mini, ni kuwa na ce wallahi bana so, na canza suna ake ce mini Nana"
"To meyasa ba kya so, ba kakarku ba ce? Au kamar sunan iya ne ai ko?"
Nana ta ce "Eh mana, baki ga yadda ta tsane ni ba, ni ma kuwa na tsaneta, yauwwa idan kuɗin yayi ragowa muka sayi kifi, ba za ta ce komai ba?"
Noor ta ce "Ai idan ma kifin ki ka saya da duka kuɗin babu abun da za ta ce miki, yaya ummi fa babu ruwanta"
Nana ta ce "Na gani, kin san wani abu, wallahi ta burgeni, ga muryarta mai daɗi, a nutse take komai, sau ɗaya na taɓa ganinta sun zo da kawu yahaya, ƴar sa ce?"
Noor ta ce "Ke, ni ma fa ƴar sa ce, iya duk kakarmu ce kenan? To ya aka yi ban sanki ba"
Noor ta ce "Ni ba kakata ba ce ba, kakana ta haifa dan haka babu abun da ya yi mini zafi da ita"
Wani yaro suka haɗu da shi a hanya ya ce "Nana, ana ta nemanki a gida, wallahi ki je gida baba yana nemanki"
"Ba zani ɗin ba, in je a jibgi jaka, gidan iya zan je, tayi baƙi za a dafa abinci, sai na ci na dare zan dawo gida"
Mamaki ya kama noor, jin amsar da ta bayar, da aka ce babanta yana nemanta.
Sai dai sun shiga sashin iya sun yi sallama babu jimawa, Nana ta fara ɗaukko kwanukan da zasu yi amfani da su su yi girkin, Idris yayi sallama da itacensa a hannu, ya fara jibgar Nana.
Marin da ummi ta yi masa ba a kan sa hankalinsa yake ba, face shaiɗan da ya shiga ƙawata masa ummi, hijjabi ne a jikin na roba, dan haka ya kwanta a jikinta, gaba ɗaya tamkar ƙibarta ta koma ƙirjinta, haka da ta juya baya ma, kamar an aunata an dasa mata ƙugunta.
"Ke yanzu lalacewar taki har ta kai haka ummi, Idris ɗin ki ka mara?"
Duk da jikin ummi tsuma yake da tashin hankali da tsoro, dan ko a mafarki ita kanta ba ta taɓa zaton aikata abu makamancin haka ba.
Amma ta ji zuciyarta ta bushe, ta ce "Iya yaushe zaki bari kanmu ya haɗu a matsayin iyalanki ne? Kalli fa dukan da yake yi mata? Mutum ba dabba ba"
Cikin ƙwarin gwiwa, da son ɓoye halin da ya faɗa ya aro jarumta ya ce "Ni zaki mara? Kin san abun da ta yi ne?"
"Ina ruwana da abun da tayi maka? Barewa za ta yi gudu ɗanta yayi rarrafe ne? Abun mamakin daga haɗuwata da yarinyar yau, har ta fara faɗar irin damuwar da take ciki, look at her, just an innocent kid like me before"
Tayi maganar cikin matuƙar rauni, hawaye na zuba daga idonta, tana share wa yarinyar hawayenta da wannan yawun, da daƙalƙallen hijjabin da yake wuyan yarinyar, sautin kukan na ta ma ya kasa fita sai sheshsheƙa, santaleleliyar yarinya kai da ganinta ka san fara ce, azabar datti da rashin kula duk ya dafar da ita.
Bilhakki ummi ta rungumeta tana kuka, wanda kukan na ta yana da alaƙa da tuna irin baƙar rayuwar da ta yi a baya.
Iya kuwa ba ta taɓa zaton ummi ta yi kilewar da zata iya gaura wa Idiris mari har haka ba.
Hashim ne yayi sallama tare da matarsa, ya ji labarin ummi ta zo, ya ce bari ya zo tare da matarsa su gaisa, dan ba su taɓa haɗuwa ba.
Amma ya tarar da mutane cirko-cirko, ga Idiris a gefe yana ta huci, ummi a durƙushe da yarinya tana kuka.
Ya kalli mutanen ya ce "Lafiya kuwa? Meyafaru ne?"
"Ai magaji ba lafiya ba, ƴar daba ta zo mana gida, ashe bayan lalacewa a birnin ina ga ko dai shaye-shaye ko daba ta fara, wai ace ummi ta ɗaga hannu ta zabge Idris da mari"
Saroro yayi ya ce "Wane irin mari kuma ana zaune ƙalau?"
Iya ta ce"Au to ƙarya zan yi maka, ba gata nan a zaune ba?"
Hashim ya ƙarasa gaban su ummi, ya ce "Ummi meyafaru ne?" Ummi ta kasa magana sai kuka.
Ya ce "Nana meyafaru?"
Cikin kuka yarinyar ta ce "Ƙawata na raka tasha, na tayata sayar da abinci, da ta gama ta bani na ci, shi ne babanmu ya biyoni yana dukana da itace" tayi maganar tana kuka.
Magaji ya ce "Tabbas abun da ya baka tausayi, watarana zai iya baka tsoro, Allah ya kyauta, kuma wannan tsayuwar da ku ka yi duk ba mafita ba ce ba, dan Allah kowa ya watse " haka sai hashim ya sallami kowa.
Suka gaisa da matarsa da ummi, ummi cikin kuka take yi wa hashim ƙorafin abun da yake faruwa a familynsu, na muzanta wanda wata ƙaddara ta same shi, ko kuma a ɗorawa mutum tsana babu dalili.
Ya ce "Ummi, wannan abun da zan iya maganinsa, da tun a kan ki na yi, lamarin yafi ƙarfina, kuma har da sakacin iyayenmu, da son zuciya irin na iyayenmu. Ba irin nasihar da ban yi masa ba a kan kula da yarinyar nan ba, amma yaƙi. Ƙarewa ba ya kula da su da uwarsu, aka korota daga makaranta, uwar ta koma ɗora mata talla, aka tasamma lalata ta, idan ma an lalata tan ban sani ba, duk in da tayi sai tsangwama, na ce ya bani ƴar ya hanani, idan aka ɗora mata tallan sai ta sayar ta kashe kuɗin su yi ta rigima, abubuwan dai duk babu daɗin ji"
Ummi ta dafe kai, tare da faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" muddin ba a takawa wannan lamarin burki ba, ƴaƴa da yawa za su cigaba da shan wahala a gidan, idan har basu zo a yadda ake so ba.
Ummi ta bata kuɗi, ta sayo sabulu ta yi wanka, ta bata kuɗin omo ta ce idan ta je gida ta yi wanki, ta ce washegari ma kan su tafi, ta zo ta karɓi kuɗin abinci.
Nana ta din ga yi wa ummi godiya, ummi ta roƙi Hashim a kan dan Allah azo mata da Nana kano lokacin bikinta, yayi mata alƙawarin da yardar Allah za a taho da ita.
Faranti ɗaya suka ci abinci da ummi, da Nana, nana na ta basu labarin irin azabtarwar da ubanta mahaifi yake yi mata. Ummi a ranta ta ce "Mugunta idan kana yi, ba ka yi wa kanka ba, ai baka iya ba' ta rubuta wa Nana lambar wayarta, ta ce gashi nan ta ɓoye, idan tana buƙatar wani abu, ta saka wani ya kirata.
Iya ta din ga bugun cikin ummi, sai ta ji yadda suka haɗu da raihan, da kuma sana'arsa amma ummi ta ƙi gaya mata.
Sai dai da dare yayi, Nana ta ce a wurin Ummi za ta kwana, idan ta je gida babansu zai sake zaneta, buɗar bakin Iya sai cewa tayi ba zata kwana da ƙazanta a ɗakinta ba, sai dai ta tafi gidan ubanta ta kwana.
Cikin tsiwa Nana ta ce "Sai ka ce wata tsiyar ce a ɗakin, ba dan anty ummi ba nima ba zan ce zan kwana a ɗakin nan ba, kuma in sha Allah sai ɗakin nan yayi gobara, kin ƙone a cikin sa"
Iya ta ce "Laaa, ki gani a kan uwarki, tsinanniya"
Nana ta ce "Wanda yayi zagi a kasuwa ya san da wanda yake" Ummi kasa magana ta yi, jin mummunan alkaba'in da ƴar ƙaramar yarinyar da ba ta fi sa'ar noor ba, ko sha huɗu ba su cika ba, take ja wa iya.
"Oho, idan ma baki ƙone a ciki ba, ko dai ɗakin nan ya zama kabarinki, ko kina ji kina gani zaki barshi tun kina raye"
Noor ta ce "Taɓ girma ya faɗi"
Ummi ta ce "Shut up noor"
"Ai ban ce komai ni"
Ummi ta ce "Nana, iyan ki ke gaya wa haka?"
"Kina ji fa yadda take tsine mini, ni me na yi mata take ce mini ƙazanta? Ba fa yau ta fara yi mini ba, In sha Allah kina raye sai kin ga ƙazanta a jikinki kuma ba zaki iya gyarata ba" Nana ta yi maganar cikin ɗaga murya tana kuka.
Abun duniya ya ishi ummi, ta yi dana sanin zuwa gagarawa.
Idris kuwa marin da ummi tayi masa bai yi masa zafin da abun da ya bijiro masa yake damunsa a kanta ba.
Yana zuwa gida ya tarar da Hindu a zaune tana tankaɗe, ta saki nono tana shayar da yaro kamar akuya, duk sun zuɓe sun suɗe, ya ja uban tsaki ya shiga ɗaki yana zage-zage.
Sai da ya shiga ɗaki ya tsaya ya yi shiru, wai ummi ce ta mare shi a kan ƴar sa, ummin da ya din ga cin ubanta a baya, wai yau ita ce da ƙwarin gwiwar tsinka masa mari.
Hindu ba ta kula shi ba, ya hau zage-zage yana ci mata mutunci da ita da Nana.
Da abun ya isheta ta ce "Kaga ni fa ban yi maka komai ba, ba zaka din ga zagina ba, Nana kuma ka je can ka nemeta, ni ma ban san gidan uban da ta tafi ba, dan haka ba zaka huce a kaina ba"
"Ai koma menene ke ki ka ja, a can gidan Iya na sameta, ta ja mini mari shegiya watsatsiya"
Hindu ta ce "kai ne babban watstste da ka kawota duniya, kuma ko waye ya mareka, Allah ya saka masa da alkhairi" suka din ga faɗa, ba ganin mutuncin juna, balle kima.
Nana kuwa da ta je gidan, idiris ya kuma yinƙurawa zai daketa, ta fita da gudu, ba ta kwana a gidan ba.
Dama dr. Yana garin, cikin gari ya tafi ya samu hotel ya kwana, da niyyar washegari ya mayar da ummi maiduguri sannan ya koma kano, a ganinsa haka shi ne ƙa'ida duk da abun da ya faru a baya, yakamata ace da kansa ya kai ummi gagarawa su kai musu katin aurenta.
Da sassafe ummi da noor suka shirya, sai ga Nana da farar safiyar nan, dan a gidan iya tayi sallar safiya kamar yadda take cewa.
Ummi ta yi ta mata nasihar ba a salla da safe, ta ce "Ai ba a gidanmu na kwana ba, babanmu ne zai sake dukana na gudu na tafi ƙasan teburin wani mai tireda, na kwana"
Ummi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" tabbas idan ba a tsaya a kan yarinyar nan ba, to zata gagari kowa.
Har ƙasan zuciyarta ummi take jin damuwa a kan Nana, kyakywar bafulatanar yarinya kamarta ɗaya sak da mahaifiyarta, amma ba kula.
Tana kallon iya tana kallonta, amma ko kallo iya ba ta isheta ba.
Ummi ta dafa musu tea har da madara, ga bredi da ƙwai, duk da cin mutunci da Iya tayi musu, bai hanata cin abincin da ummin ta sayo da kuɗinta ba.
Gidan babu wanda bai san zancen marin nan ba, aka din ga surutu a kai.
Allah ya taimaki ummi, da wuri kawu ya zo, dan kuwa tuni kawu Ilyasu ya kira shi ya sanar da shi abun da ya faru.
Sai da Iya tayi ta faɗe-faɗen maganganu, tare da gaya masa ƙarya da gaskiya, amma ya basar da zancen, dan shi yanzu abun da ya dame shi, yadda zai samu sauran kuɗi, ya cika ya ƙarawa ummi kujeru.
Suna tafe a hanya, yake bata labarin gidanta da raihan ya kai shi, ummi ta ce "Kawu kar ka wahalar da kan ka, ka yi abun da Allah ya yassare maka kawai"
Ya ce "Haka ne, amma dai duk da haka dolena ne na fitar da ke kunya"
"Na gode sosai kawu, ubangiji Allah ya ƙara arziki"
Ya amsa mata da "Amin"
Aka jima ya ce "Ummina, meya haɗaki da idris har ki ka mare shi? Na dai ji zancen ne amma ban yadda ba"
Ummi ta sunkuyar da kai ta ce "Wallahi kawu ban yi tsammanin hakan za ta faru ba, ƙoƙarin ceton yarinyar nake yi, abun ya taɓa mini zuciya sosai da sosai, amma na yi dana sani sosai wallahi"
Dr. Ya jinjina kai ya ce "Na fahimce ki ummi, amma ki kula sosai".
"In sha Allah, amma kawu shikenan kowane family suna zamansu gwanin sha'awa, mu kuma shikenan idan ka zo ba a yadda ake so ba, sai a tsangwame ka, yarinyar nan zuciyarta a bushe take fa, za ta iya lalacewa" tayi maganar idonta na tara hawaye, dan sosai take jin abun a ranta.
"Ummi, duk al'ummar da zata zauna cikin jahilci, dole a din ga samun irin wannan, bayan jahilci kuma har da son zuciya, sai dai fatan ke da nake saka ran Allah ya ɗaukaka, Allah ya sa ki zama silar gyaruwar komai" ta jinjina masa kai.
Haka kawu yahaya yayi ta ɗawainiya, dan bai koma kano ba sai cikin dare, kuɗinsa duk sun ƙare, a harkar bikin ummi, iya labulayen da zasu isa gidan ummin, sai da aka yi masa estimating kusan dubu ɗari biyar, ya dage baya son daga ɓangaren raihan ace sun ƙarasa wani abun.
Da safe yana zaune a falo, bayan ya karya yana waya, zai sayar da wani filinsa ya ƙara wa ummi kujeru, bayan ya gama wayar, Farida ta kalleshi ta ce "Wasu irin kujeru ne da sai ka sayar da filinka, ga ƴaƴa kana da su? Ba ka ce ka gama komai ba?"
Dr. Ya ce "Ke ina ruwanki? Ke ki ka saya mini filin? Falonta uku na riga na yi kujera set ɗaya, dole zan nemi yadda zan ƙara mata"
Waro ido tayi kamar za ta faɗi daga kan kujerar ta ce "Ban gane falo uku ba, ɗan wa za ta aura haka? Anya ka yi binciken sana'arsa kuwa?"
Dariya yayi, yana kallon yadda hassadar ta, ta kasa ɓuya ta fito fili, ya ce "Ai ummana, Allah ya gwangwaje ta da miji, ni na san sana'ar sa kuwa, sai fatan Allah ya sanya alkhairi"
Can maiduguri kuwa, noor ta sake sosai, tana hidimominta, gashi kasancewar mariya na son yara, kuma ta ji sunansu ɗaya, ya sanya noor da mariya jonewa, komai tare suke yi.
Raihan yana ta turawa da ummi kuɗi, a ciki ta yi wa noor ɗinkuna ita da Nana, da kayan fitar biki, shi ma raihan ya na ta samun gudunmuwar biki, duk da ba wani babban biki ya ɗaukko ba, amma ya kashe kuɗi sosai da sosai.
Ita kanta Ummi ta san ta gyaru, ta sha kulawa da gyara kala-kala daga wurin dangin mahaifiyarta.
Aka shiga satin biki, suka din ga shagulgulansu a maiduguri, har ummi ta gaji, daga wannan sai wancan, aka yi aka gama, ana gobe ɗaurin aure, ranar Alhamis, suka taho kano.
Sai dai dr. Ya aika Abdul, ya ce ya kai su tsohon gidansa, ya saka an gyara, a can za su zauna, su yi nasu taron bikin, saboda sanin halin farida.
A yammacin da suka zo, raihan ya zo, suka kuma gaisawa da su mama, kamar ya sace ummi, tana magana tana lumshe ido saboda azabar gajiya.
Ya ce "Madam, tun yanzu har kin gaji har haka?"
A ɗan raunane ta ce "Ba zaka gane ba MD, a gajiye nake sosai wallahi"
"Kar ki damu, akwai kulawa ta mussaman jibi in Allah ya kaimu da zan baki" tayi masa shiru.
"Babyna am talking fa" taƙi kula shi.
Ya sake cewa "Ina fatan da ki ka je gagarawan babu wata damuwa? Kuma ba ku haɗu da tsohon mijinki ba?"
Ta ce "To meya kawo wannan maganar kuma?"
"Saboda ina kishinki fiye da yadda ki ke tunani, duk da ɗan uwanki ne, ba zai sake saka ki a idonsa ba"
"Saboda me?"
"Saboda haka na ce" yayi maganar cikin isa, tare da tsareta da ido, sai da ta ɗan sha jinin jikinta. Ta tura baki ba tare da ta ce masa komai ba.
Ya ɗora da cewa "Gobe in Allah ya kaimu da wuri mai yi miki kwalliya za ta zo, duk in da huɗu tayi, ki kammala shirinki, zamu zo ɗaukar ki".