x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - CUTARWA

  • 45001 words
  • 48000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 495

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
yawu ya haɗiye, yana ƙare wa ummi kallo, duk baƙin fatar nan ta ta fatar tana da ɗaukar ido.

A wurin yayi yinƙurin sake afka mata, sai dai ba ta sauya zani ba, duk da ta samu sassauci, na ciwon saboda yanzu sau biyu take sauya wando a rana, kamar yadda Na'ima ta gaya mata.

Amma duk da haka tana wannan ƙarin mara daɗi, duk da jikinta baya wari yanzu, saboda ta samu sabulun wanka.

Zura masa ido kawai tayi, saboda a galabaice take da ciwo

Wata mummunar ashar yayi mata, yana zubar da yawu, ya ɗagota ya din ga kifa mata mari.

Kukan ma ba ya iya fita, saboda azaba da masifar idiris, da yake abu kamar dabba ba ɗan adam ba.

Ya din ga tsine mata albarka, da ita da iyayenta, dan har Iya sai da ya zaga.

Ƙarshe ma ya danƙara mata saki a wurin.

Ƙafarta ko takalmi babu, ta gyara suturar jikinta ta fice daga gidan a haka, ta tafi gida ga hannunta ɗaya kamar ba a jikinta yake ba, saboda takata yayi a hannun.

Iya da ke iza wuta ta miƙe tana faɗin "Ke lafiya?"

Kan ummi ta yi magana, jiri ya ɗebe ta ta faɗi ƙasa.

Da sauri Iya ta ƙarasa kanta ta ce "Ke, menene wai?".

"Iya zan mutu, yaya idris zai kashe ni, dan Allah kar ki mayar da ni, ya ce ya sake ni" tayi maganar cikin gunjin kuka.

Ta taɓa jikin ummi ta ji zafi, ga fuskarta shaidar yatsun Idris kwance a fuskar ta har idonta yayi taruwar jini.

"Lallaɓa ki tashi ki shiga ɗaki ki zauna, daga yin aure ba a kashe shi ba, bari dai ya zo mu ji me ki ka yi masa" Iya ta tashi ta fita.

Kuka ummi ta din ga yi, tana jin dama ta mutu ta huta, idan aka mayar da ita gidan idris ta san sai ya kashe ta.

Da ƙyar Hashim ya nemo idris, aka nemo babansu, domin jin menene yake faruwa.

Sai dai daga mugun kallon da yake yi wa ummi, ka san babu Allah a ransa.

Babu zato babu tsammani sai ga kawu yahaya ya dira a gidan, kuma bai tsaya ko ina ba sai sashin Iya.

Sai dai babu walwala ko fara'a a tare da shi, suka gaisa da Iya da ɗan uwansa, da su Hashim. Sannan ya kalli Iya ya ce "Iya dan me za a aurar da ummi, ba tare da na sani ba? Sai shekaranjiya magaji yake gaya mini?"

"Saboda kai ne ubanta? Uban waye ma ya ganka balle ya gaya maka, tangarɗa aka samu da wadda zai aura, na saka aka yi da ita dan rufuwar asirinmu".

Ummi da baccin wahala ya ɗauka, kamar a mafarki ta ji muryar kawu yahaya, miƙa hannu ta fara yi ta ce "Kawu"

Cikin azama ya nufi ummi ya ce "Na'am mamana"

"Dan Allah ka kai ni wurin mama, idan na koma gidan Idris kashe ni zai yi" ganin tana ƙoƙarin tashi ta kasa, ya sanya ya ɗago ummi.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya faɗa a razane.

Fuskar ummi ya gani a kumbure suntum, ga hannunta ɗaya ma ya kumbura ba ta iya motsa shi sosai.

"Meyafaru haka?"

"Dukana yake yi kawu, dan Allah kar ka bani a nan wallahi mutuwa zan yi, idan baka san in da mama take ba, ko gidan marayu ka kai ni, ko idan akwai makarantar almajirai ka kai ni, zan mutu wallahi " tayi maganar tana wani irin gigitaccen kuka.

"Kar ku ce mini shi yayi mata wannan dukan?"

Iya ta ce "Ka ga Yahaya, ba abu ne na tashin hankali ba, abun da muke shirin sasantawa kenan, kai me take yi maka ne?"

Cikin fitsara da rashin kunya ya ce "Haba Iya, kin san ni ba son ta nake yi ba, yarinya da take saura ce, ai kin san komai aka liƙa mini ita, ga sanyi ya kasheta ban da wari da ɗoyi ba abun da take yi, an liƙa mini na kwashi masifa gaskiya ba zan iya ba, jikinta kamar an buɗe masai, nima ba iya zama zan yi da ita ba".

Tsit suka yi, babu wanda ya zaci fitowar wannan maganar daga bakinsa, baƙin ciki da takaici ya rufe Hashim.

"Madalla, ka iya rubutu ai ko?" Ya jinjina kai.

Kawu yahaya ya ciro takarda da biro ya ce "Sakar mini ƴa ta"

Iya ta fara "A'a Yahaya, ai dauɗar gora ciki ka sha ta "

"Ba wata dauɗa iya, koma menene ya samu ummi laifinki ne, kina me sanyi yayi mata wannan kamun? Da dauɗar gorar ciki ke shan ta, shi ya kasa rufa mata asiri ya nema mata magani, ya tona mata asiri haka, shi mai ya hana ya sha dauɗar gorar?, laifin waye idan ba naki ba, ya saki ummi, da ita zan tafi, abun da yayi kansa ya yi wa, ƴar shekara sha uku aure wata ɗaya ya rabu, In sha Allah ba zata wulaƙanta ba, na yi imani da Allah balarabe ba zai bari iyalinmu su wulaƙanta bayan bamu ba" yayi maganar ƙasan zuciyarsa yana jinjina girman hukuncin da ya yanke, dan ya san da badaƙala idan ya je da ummi gidansa.


(Ina godiya da tarin comments da ake yi a kan litattafan bright pens, cutarwa, munafukin miji, yi wa kai, masu ƙorafi a kan littafin cutarwa, ayi haƙuri da yadda labarin yazo, ina ganin sharhi da ƙorafe-ƙorafe ina godiya sosai 🙏)


Ayshercool
08081012143
    

                                  *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)


P13

Iya ta ce "A'a Yahaya, kar mu yi haka da kai, wannan abu ne na cikin gida da yakamata a sasanta shi, wannan ai sai asirinmu ya tonu, duniya ta zage mu"

"Iya zagi na nawa kuma? Kalli jikin yarinyar nan fa, baiwar ubansa ce ita? A gabanki a gaban ubansa yake aibata ta yake cewa baya son ta, baya ƙaunarta, wallahi dole ya saketa, zan je da ummi ta cigaba da karatunta".

"Gaskiya ban lamunta ba yahaya, ba zaka ɓata zumunci ba da abun da na ƙulla dan ƙarfafa zumunci ba".

Hashim da bai yi niyyar sanya baki ba, sai da ya ga abun na iya yaƙi ci ya ƙi cinyewa ya ce "Iya wane zumunci kuma banda wanda aka ɓata?"

"Rufe mini baki dan ubanka, ai duk kai ne munafikin da ka kunno kowacce wuta, ban yadda a tafi da ummi ko ina ba, ko auren ya mutu, muna nan a bar mini ita".

Yahaya ya kalli Iya ido cikin ido ya ce "Wallahi iya idan ki ka hana ni tafiya da ummi, zan ɗebowa idiris hukumar kare hakkin ɗan Adam, su bi mata hakkinta, kuma idan suka tashi, har ke ba zasu bari ba, da duk mutanen gidan nan, na farko ga child abuse, by forced marriage, kun mata auren dole da ƙanan shekaru, ga dukanta da ci mata mutunci, deformation of character ɓata mata suna, ta hanyar yaɗa larurar da take fama da ita a cikin mutane, wanda duk ya zo kunnena tun kan na zo nan na samu lanari, kuma mariya ma zata iya shigowa cikin lamarin nan, ƙwace mata ƴa babu dalili da ki ka yi, dan dai suma ba su san ƴancin su bane, da sun haɗa ki da hukuma, da sai kin basu ƴar su".

Saminu ya ce "A'a yaya yahaya, ba za ayi haka ba"

Cikin rikicewa Iya ta ce "Yahaya ni zaka kai ƙara hukuma ka saka a rufe ni?"

"Ba ƙararki zan kai ba, ƙarar wannan sakaran zan kai, idan kuma na kai ƙararsa su hukuma zurfafa bincike zasu yi, ina gaya miki abun da hakan ka iya haifarwa ne, kai kuma ɗauki takarda da biro, ka sakar mini ƴa, ko daƙiƙancin naka bai bari, ka iya rubutun ba?"

Cikin kumbura baki ya ɗauki takarda da biron, ya rubutawa ummi saki biyu.

Kawu yahaya ya karɓa, ya kalli ummi ya ce "Tashi in tayaki ki haɗo kayanki mu tafi"

Magaji ya ce "Bari na tayata" a hankali ta ce "Ai kayan suna can gidan, sai kuma kayana da ke ɗakin itace"

Kawu Yahaya da kansa ya tashi, ya je ɗakin itacen, ya ɗaukko vivar kayan ummi, sai dai ya ga tsummokara ne kawai, dan haka ya ce ba za su tafi da su ba.

Iya ta din ga harar ummi, amma ummi tayi kamar bata gani ba, magaji ya kawo kayan ummi.

Jama'ar gida suka taru, suna kallon ummi za ga tafi birnin kanon dabo gidan kawu yahaya, wasu na tausaya mata, wasu kuma na yi mata murna.

"Yahaya" Iya ta kira sunansa.

Ya amsa mata, ta ce "Ka yi mini alƙawarin ba za ka kai ummi wurin mariya ba, dan idan haka ta faru, abun da zai biyo baya ba zai yi mana daɗi ba".

"Abu ɗaya na sani, na ɗauki ummi tsakani da Allah dan inganta rayuwarta, ni ban san a in da mahaifiyar ta take ba, amma akwai lokacin da lallai dole a nemi dangin mahaifiyar ummi, ta gansu, dan babu in da shari'a ta ce a yanke alaƙa tsakanin uwa da ɗan ta, ko da kuwa kafura ce, abun da yake tsakanin ki da mahaifiyar ta daban, kuma bai kamata ya shafi ummi ba" Iya tayi muƙus, dan ba ta son yi wa kanta sagegeduwar ɗan abun duniyar da yake bata.

Sosai kawu yahaya ya yi wa ƴan uwansa ta tas, a kan abubuwan da suka faru a kan ummi, kasancewar shi ne babba suna girmama shi, duk da kaf ɗin su sun riga shi yin aure, dam su ba karatun boko suka yi ba, wasun su ma shakara sha tara suka yi aure, amma suna girmama shi sosai mussaman da yana da abun duniya.

Magaji ne ya riƙo ummi, sai layi take saboda yunwa da kuma rashin lafiya.

Magaji ya ce "Ummi shikenan sai tafiya, in Allah ya yarda wahala ta ƙare, sai jin daɗi da kwanciyar hankali, ki kula da kanki, ki yi karatu da kyau".

Ummi ta ce "To yaya, kai ne ka gaya wa kawu halin da nake ciki?"

"Eh ummi, aron waya na samu, na kira shi, idan ba haka ba, bani da wata mafita da zan taimake ki".

Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah ya sa kar iya tayi ta yi maka faɗa, dan Allah idan ka ga yaya na'ima ta zo ka gaya mata bana nan, ba zan iya zuwa yi wa mama sallama ba, jikina ba ƙwari ba zan so ta ganni a haka ba"

Ya ce "To shikenan, in sha Allah"

"To zaka din ga zuwa kanon muna gaisawa?"

Yayi murmushi ya ce "Zan din ga zuwa, ai kema zaki din ga zuwa muna gaisawa ko?"

Ta yi saurin girgiza masa kai ta ce "In Allah ya yarda ni da gagarwa har abada, ba zan sake zuwa ba, dan Allah idan ka samu labarin in da mama take, ka gaya mini"

Sak yayi jikinsa yayi sanyi yana kallon ummi, jin abun da ta faɗa, sai dai bai kamata ya ga laifinta ba, an azabtar da ita azabtarwa mai munin da dan ta faɗi hakan, ba ta yi laifi ba.
Kawu yahaya ya tsaya suna magana da kawu Ilyasu da sagir, wanda yanzu suka zo riski zasu tafi.

Kawai Idris ya tsinci kansa da dawowa, dan ya tabbattar da gaske tafiya za ayi da ummin? Ko kuwa ba gaske bane ba?.

Hannun hashim ya gani a cikin na ummi, ya riƙota sun tsaya suna magana, wani zazzafan abu mai raɗaɗin gaske, tamkar sukar kibiya, ya soki ƙirjinsa.

Taɓe baki yayi tare da jan tsaki, hashim suka ƙarasa gaban motar, ummi ta shiga ta zauna tana kallon hashim da ƙofar gidan da nan ne tushenta, amma azabar cikinsa ko zamanin bayi sai haka.

Yaran gidan har da mata, da maƙwabta sun yi dandazo suna kallon tafiyar ummi.

Kawu yahaya suka gama magana, ya shiga ya kunna motar Ummi ta sauke idanuwanta masu kama da na mage a cikin na Idris, idanun da suka kumbura saboda duka ɗaya yayi taruwar jini a cikin sa, wani irin kallo take yi masa mai kama da na ka saurari dawowata, zaka girbe abun da ka shuka.

Hanyar kano suka kama, suna tafe kawu yahaya yana yi wa ummi nasiha tare da rarrashin ta.

Ya kalli ummi ya ce "Idan mun je, kar ki kuskura ki gaya wa wani kin taɓa aure, kin ji ko?"

Ummi ta jinjina masa kai alamar to.

Suna tafe tana amai, kasancewar baya son su yi dare a hanya, ya sanya ya tsaya ya saya mata ruwan gishiri da suga, da kuma maganin zazzaɓi, suka cigaba da tafiya, ya tanbayeta ko za ta ci wani abun ne? Duk da yunwar da take ji, cikinta babu daɗi, dan haka ta ce masa ba ta buƙatar cin komai.

Tsayawa yayi ya saya mata kankana, ya ce ta sha, kaɗan ta ci ta kashingiɗa, tana tuna wulaƙanci da cin zarafin da idiris yayi mata, da yadda ya tona mata asiri a gaban mutane.

Ko da suka isa kano, wani asibiti ya fara wuce wa da ummi, aka yi mata teses, sannan aka rubuta mata magunguna, har za su tafi, kawu yahaya ya cewa ummi, ta yi wa likitan bayanin ɗaya matsalar ta ta.

Sai dai ummi ta sunkuyar da kai, ta kasa magana saboda tsananin kunya da ganin kamar tozarci ne bayanin wannan matsalar ta ta ga wani.

Ganin taƙi magana, ya sanya likitan tura su wurin wata nurse, tun da mace ce, za ta fi iya sakin jiki tayi mata bayani.

Sai dai ba ta sauya zani ba, nan ma ummi kasa magana ta yi.

Nurse ɗin ta kalli kawu yahaya ta ce "Yallaɓai me yake damunta ne? Ta ƙi magana".

Ya ce "Kina ji ƴa ta ce wannan, a ƙauye take hannun mahaifiyarmu, aka yi mata aure na je na tarar da matsala mijin ya ce ba ta da lafiya, sanyi yayi mata yawa, auren ma dai ya mutu"

Nurse ɗin ta kalli ummi sannan ta kalle shi ta ce "Bawan Allah kai gaka wayayye, ya zaka bari a yi wa wannan yarinyar ƙarama aure a yanzu, kalli fuskarta ma kamar shaidar duka, ni wannan yarinyar ai ba ta fi in saka zani in goye ta ba".

Ganin za ta fara yi masa faɗa, saboda yadda ta ɗau zafi, ya sanya ya yi mata bayanin komai.

Jikinta duk yayi sanyi, tana jinjina lamarin, gaba ɗaya tausayin ummi ya kamata, wannan ƴar ƙaramar yarinyar ita ce aka yi wa aure, har ya mutu.

Ta kalli ummi ta ce "Gaya mini menene yake damunki a wurin?" Ummi ta sunkuyar da kai tare da jin ta a takure.

Ta kalli kawu yahaya ta ce "Ɗan bamu wuri" ba musu ya fita waje.

Ta haɗe rai ta kalli ummi ta ce "Ke dan gidanku ki gaya mini nan asibiti ne, idan baki warke ba haka zaki yi ta aure yana mutuwa, saboda wannan matsalar".

Ummi murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ƙaiƙayi yake yi mini".

"Tun yaushe?"

"An daɗe"

"Ya aka yi aka daɗe, wasa ki ke da wurin?"

Ummi ta girgiza kai alamar a'a.

"To ya aka yi yake ƙaiƙayi, kafin ayi miki auren ya fara ko bayan an yi mikk auren?"

"Kafin ayi mini ne?"

Nurse ɗin ta numfasa ta ce "Sau nawa ki ke canza wando a rana?"

Ummi ta kalleta ta ce "Kan ayi mini?"

Auren ne ba zata iya faɗa ba, tana jin nauyin haka.

Ta ce "Eh, kan ayi auren"

"Wandona ɗaya ne, idan na wanke sai na saka"

Tayi ƙuri da ido tana kallon ummi, da ta ji ta ce wando ɗaya.

"Yaya ki ke tsarki?"

Amsar da ta bawa nurse ɗin ta girgiza ta, dan ciwon sanyin ummi, yana da alaƙa da rashin iya tsarki, da tsugunawa a banɗaki barkatai, da kuma rashin kyakywar kulawa na uwa da wurin bai samu ba.

Ta dubi ummi ta ce "Daga yanzu, wando sau uku zaki din ga canzawa a rana, kuma idan ki ka yi bayan gida, sai kin fara wanke wurin fitsarinki, sannan ki wanke wurin bayan gida, ba haɗe tsarkinsu.
Kar ki kuskura ki yi fitsari kina ɗigar da ruwan tsarkin, ki mayar da wando jikin ki, ko ki saka jiƙaƙƙen wando, ki samu ɗan tsumma mai kyau, ki din ga wankewa kina ajiyewa a banɗakin da ki ke, idan kin yi tsarki, ko kin yi wanka, ki din ga tsane wurin kan ki saka wando.
Idan fitsari ya kama ki a wani wuri daban ba gida ba, ki yi fitsarin a tsaye, idan kin gama sai ki wanke ƙafarki, da jikinki, ki daina shiga banɗaki barkatai" ta din ga yi wa ummi bayanin yadda za ta din ga kula da tsabtar wurin, dan babu wanda ya taɓa zaunar da ita yayi mata wannan bayanin.

"Kin fara al'ada ne?"

Ummi ta ce "A'a"

Nurse ɗin ta a aika ummi ta kira kawu yahaya, ta ce masa "Yallaɓai gaskiya sanyi ya yi mata yawa, kuma na lura rashin tsabta da kula ne ya haddasa mata hakan, dan haka dole ku kula, tun da yanzu ka ce ta dawo hannunka. Ku dawo ranar lahadi akwai gynea doctor ɗin da yake zama, sai ka kawota ta ganshi.
Na so ace da mace ku ka zo, sai ta fi fahimtar bayanina, amma kai ɗin ba ta ɓaci ba, ai uba ne kai. A yanzu, abu na farko a sama mata isasshen wanduna, a ƙalla shida zuwa dozen. Sai kuma a sama mata flask mussaman na ruwan zafi, na ta ne ta din ga kama ruwa da ruwan ɗumi.
Banda tsarki da sabulu, a samo mata ganyen magarya, a tafasa shi  ta din ga kama ruwa da shi.
Kuma ka san shi ciwo ne mai naci, dan haka a kula sosai, sai kuma ku nemi kanumfari, tafarnuwa ba mai yawa ba, da namijin goro, a jiƙa su a robar ruwa mai murfi, ta din ga tsiyaya tana sha, ta yawaita amfani da kanumfarin nan.
Sai kuma a samo saiwar zogale a din ga tafasa mata da jar kanwa, ta yi amfani da ko guda ɗaya kafin ku zo ku ga likitan, zata samu sauƙi in sha Allah. Wannan na ɗan gaya muku ne dabarunmu na cikin gida na gargajiya, kafin Allah ya sa ku zo ganin likitan".

Ya ce "To shikenan, na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da alkhairi"

Ummi ta bi bayansa suka fito, suna tafe a hanya yana jaddada da mata ta riƙe abubuwan da aka gaya mata, ummi kuwa gaba ɗaya jikinta sanyi yayi, wata irin kunyarsa ta rufe ta.

Shi kansa yayi mamaki da nurse ɗin ta ce masa ummi ta ce wando ɗaya ne da ita.

"Ummi"

Ta amsa da"Na'am"

"Ki kwantar da hankalinki, magnunnan nan zan saya miki zuwa gobe in Allah ya kaimu, har kayan da zaki yi
End Ads