x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 52 - CUTARWA

  • 153001 words
  • 156000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 539

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
zama matar Muhammad, inyeee babyn ba" zolayar raihan ta yi yawa, sai da ya sakata murmushi tana rufe fuska.

Ya ce "Bari na tafi, ki je ki huta, ki ci abinci sosai da sosai" ta jinjina masa kai suka yi sallama.

Washegari da sassafe ƴan gagarawa suka isa kano, sai dai babu Iya, dan cewa tayi ba zata je ba.

Ranar juma'a tun sassafe, su Yaya maryam suka je kafin kaya, sai dai sun riƙe baki da ganin gidan ummi, gida ya haɗu sosai da sosai, ya ƙawatu kai da gani ka san an kashewa gidan kuɗi ba kaɗan ba.

Ba ƙaramin murna ummi ta yi ba, ganin an zo da Nana, ƴan gagarawa a gidan dr. Suka sauka, su mama kuma suna ɗaya gidan.

Bayan sallar juma'a, aka ɗaura auren Ummi da raihan, a kan sadaki naira dubu ɗari biyar.

An sha surutu shi ma a kan sadakin nan, mussaman ƴan gagarawa, har da cewa dr. Zai aurar da ummi ga ɗan yankan kai, tana bazawara ana wannan bushashasha haka a aurenta.

Manager yayi mamakin ganin wai raihan ne mijin da ummi za ta aura, dan ko da ya ga katin ma, bai kawo shi ne ba, dan Muhammad Muhammad Tahir aka saka a katin bikin.

Duk in da ummi ta yi, noor da Nana ne ke biye da ita, su ne ƙawayen nata, can gidan su raihan Hajiya ce take hidima da jama'ar da suke ta shiga suna fita.

Wani irin danƙareren leshi da raihan ya saya mata ta saka, ɗinkin doguwar riga, da mayafi, ba wani make up aka yi mata ba, komai dai-dai kalar fatarta.

Idan ba an gaya maka ba zaka ce mama ba ta da lafiya ba, ta sha kwalliya cikin atamfa ita ma, tayi kyau sosai da sosai.

Ƙarfe huɗu da rabi raihan ya aika motocin da zasu tafi da waɗanda zasu je walimar da za ayi.

Daga baya kuma motarsa ta je ɗaukar ummi, ta yi kyau sosai da sosai, cikin tausaywa da soyayya yake kallon ummi.
Ta shiga cikin motar da sallama, tuni ƙamshin turaren ta ya cika motar, ta sunkuyar da kanta ta ce "Ina wuni?"

"My wife, legally sealed you now belongs to me Salma" yayi maganar yana riƙe hannunta.

Tayi murmushi ta ce "Ka rabani da headmaster ko...

Ba ta gama ba, ya riƙe hannunta da ƙarfi ya ce "Ki sake maganar wani a gabana ki gani, da kin aure shi in ba sai ya gaji ya sakar mini ke ba, idan na din ga sintiri a gidan ki har uwar ɗakinki" ƙunshe baki tayi tana dariya, haryanzu gani take kamar ba ita ba, wai raihan za ta aura, abun da mamaki.

Babu mutane da yawa a wurin, an ci an sha sosai, sai dai duk da mayafi ne a jikin ummi irin na amare, daga sama har ƙasa, tana ta rufe jikinta, amma sai da raihan ya ji wani abu a ransa na kishi.

Ana ta hotuna, a nan ƴan gagarawa suka ga mariya, tsaf da ita kamar ba ita ta haifi ummi ba, tsaf da ita gashi ta yi kyau sosai da sosai, shekara sha takwas rabon da a haɗu.

Suka din ga gaisawa da facalolinta, ta kalli sa'adatu ta c "Ina Alhassan mai yi mini Albishir da mutuwar mijina?" Tayi tsuru-tsuru tana basar da zancen, dan ba su zaci ganinta a haka ba, sun ɗauka hauka take yi tuburan.

Ana ƙoƙarin yin hoto, noor na ta ture Sagir, wai ya koma kusa da raihan shi ne ɗan uwansu, su kuma su ne ƴan uwan ummi, a kusa da ita za su tsaya.

Zuwa sallar isha'i aka tashi daga wurin, noor da Nana suka shige motar Salim, noor ta ce "Bawan Allah dan Allah ka mayar da mu mukaɗai gida, kar ka ɗauki kowa, motar daɗi" kallonsu yake yi, har gara Nana akwai ƙauyanci a tare da ita, amma ya lura da noor, tun a wurin bikin tana da rawar kawai sosai da sosai.

Ya kalli noor ya ce "Ke bana son surutu, ke ki shiga bayan mota, ke kuma dawo gaba" yayi maganar yana nuna Nana.

"A'a ka barmu mu zauna a baya daukkanmu"

"To ku nemi wani"

Noor ta ce "A'a yi haƙuri, Nana ki koma gaban" suna tafe suna ta surutu ita da Nana.

Nana tana magana tana fulatanci, Noor ta ce "Nana, Allah ya sa nima na auri irin yaya raihan, mai kyau kamarsa"

Sai da Salim ya waiwaya ya kalli noor, ba ya tunanin ko fitsarin kwance ta daina take zancen wani miji.

Suka yi ta surutu, ko gajiya ba sa yi, har ya kai su gida.

Washegari aka yi wunin biki, da isha'i aka kawo motocin ɗaukar ummi, da mariya da yaya maryam da wasu daga ƴan uwan su, suka tafi da ummi gidan farida, domin yi mata sallama.

Yaya maryam ta din ga yi wa farida godiya, saboda riƙe ummi da ta yi, sai wani cika take tana batsewa, ta zata za ta gan su ƴan ƙauye, sai dai ta ga sun sha dressing, sun yi kyau, tayi mamakin ganin babar ummi, ta ɗauka ita ma baƙa ce wuluk, amma ta ganta da haske kuma shar da ita.

Dressing ɗin da aka yi wa ummi, ta din ga kallo, ita kanta a ƙasan zuciyarta ta san son zuciya ne ke sanya suke ce wa ummi mummuna, tana da baƙi ne dai kawai amma ba wani muni.

Dr. Ya yi wa ummi nasiha sosai da sosai, ummi ta yi masa godiya tare da neman yafiyarsa, ya ce shi ba ta yi masa komai na laifi ba.

Ƙarfe tara na dare, aka kai ummi gidan raihan, dr. Da kansa ya kaita a motarsa bayan yi mata nasihohi masu ratsa jiki, mutane sun yi santin gidan nan sosai da sosai, dr. Sai da ya cika ko ina, kitchen ɗin ta kuma su yaya maryam sun yi rawar gani, ga uban kayan turaren wuta duk an yi mata, komai nata sai masha Allah.

Dangin mami da ta din ga ce musu ba ta da gata, sun ɗauka ba za a zuba mata kayan kirki ba, su samu na gori, amma suka sha mamakin kayan da dr. Ya zuba mata.

Kowa ya watse, ummi idonta ko kuka ba ta yi ba, saboda ita a wurinta cigaba ta samu, ta bar wa farida gidanta, sai fatan Ubangiji Allah ya sassauta mata ƙalubalen gidan raihan.

Sai sha ɗaya ya shigo, daga shi sai Salim da wasu mutum uku, da take kyautata zaton ƴan uwansa ne, suma suka yi musu nasiha, tare da addu'a zaman lafiya, suka watse suka bar su.

Ya dawo ya tarar da ummi a zaune a in da ya bar ta, ya yi gyaran murya ya ce "Yaya" ta ɗago kai ta kalleshi yayi murmushi ya ce "Kin yi kyau fiye da kullum" ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Ya zauna a kusa da ita, ya miƙa mata hannunsa ya ce "Ɓalle mini" jikinta na rawa ta ɓalle masa maɓallan hannun rigarsa, ya cire babbar rigarsa, da ta cikin, ya shiga banɗaki yayi alwala, yayi mata umarnin yi ita ma.

Bayan sun yi salla raka'a biyu, raihan ya daɗe yana yi musu addu'a, bayan ya kammala kuma, ya din ga yi wa ummi nasiha.

"Salma, bayan gwagwarmaya daban-daban, Allah ya cika mini burina a kanki, ina da yaƙinin na kawo mace ta gari, kuma uwa ta gari ga ƴaƴana, ummi duk wani aure da nasa ƙalubale, amma in sha Allah, daga gareni babu ƙalubale, sai abun da ba a rasa ba, amma zaki yi haƙuri da wanda zaki fuskanta daga ƴan uwana, mu zama masu haƙuri da riƙe sirrin junanmu, kamar yadda na yi wa mama alƙawari, zan riƙe ki amana na kula da ke, in sha Allah zan yi iya yi na, Allah ya bamu zaman lafiya. Na san ba a za a rasa ɓacin rai a harkar auratayya ba, kin san halina wasu lokutan ina da zafi, amma ki zama mai yi mini uzuri, Ubangiji Allah ya bamu ikon kula da juna" ta amsa da Amin, ya tambayeta ko ta na da abun cewa ta ce masa a'a.

Duk yadda yayi da ita ta saki jiki ta ci abinci, ummi fafur taƙi, shi yayi ciye-ciyen sa.

Ita kuwa ummi wata irin fargaba da tsoro ne ya addabwa zuciyarta, abun da ya faru a aurenta na farko ne ya din ga ya dawo mata, tana ta fargaba da addu'ar kar ta sake cin karo da matsalar da ta faru a farko.

Ya fita daga ɗakin, ya dawo da wasu kaya a hannunsa, ya ce "Ƙaraso" yayi maganar yana yi mata nuni da hannunsa.

Ta tashi tana sinnewa ta ƙarasa, ya ɗaga mata wata doguwar rigar bacci, ja mai kyau, nasa kayan ma jajaye, ya ce "Ungo naki"

Jikinta na rawa ta karɓa, wani irin girma da kwarjini ta ga raihan ɗin yayi mata.

"Ki saka naki, bari na baki wuri" yayi maganar yana ɗaukar nasa kayan, ya fice daga ɗakin.

Ta lura raihan yana son jar kala, ta din ga jujjuya rigar, a ranta ta ce "Taɓ ni zan saka wannan rigar kamar a turai, ba kunya kuma in kalle shi?' ta zubawa rigar ido, sam ba ta ji za ta iya sakawa ba, haka ya dawo ya tarar da ita, shi har ya saka nasa, kallo ɗaya tayi masa ta kawar da kanta, ya cika tasa rigar shirt ɗin cif, an rubuta i love you, a gaban rigar sai wandon ta ja 3quater.

"Ya baki canza ba?" Yayi tambayar yana kallon ta. Tayi shiru ba ta ce komai ba.

Ya ƙarasa gabanta ya ce "I understand, bari na taimaka miki" yayi maganar yana janyo mayafinta.

"A'a dan Allah, yi haƙuri" tayi maganar kamar ta yi kuka. "Oya ki canza ina jiranki, dare yana yi" Ya juya ya sake ficewa, bayan wasu mintuna ya dawo, ta saka rigar amma ta yafa mayafin kayanta.

A ransa ya ce 'Lallai aurenki na fari mijinki yayi fama da taurin kai' rigar iya gwiwar ta, tayi kyau sosai, bai takura mata sai ta sauke mayafin ba, ya kama hannunta suka bar ɗakin.

Suka ratsa falo suka shiga wani ɗakin daban, an yi wa ɗakin ado na musamman, duk da a cikin fargaba take, ɗakin ya yi mata kyau sosai, ya yi wa komai adon jar kala.

"Sai ka ce ɗakin amaryar indiya" tayi maganar a hankali.

Yayi dariya ya ce "Duk wani abu na soyayya ummi, ba sai a wurin wasu ba, mu ma zamu iya idan har bai saɓawa addininmu ba, bai burge ki ba?"

Ta ce "Yayi kyau sosai" ya yi murmushi, suka ƙarasa gaban gadon ya zaunar da ita, ya tashi ya kashe fitilar ya dawo da plate ya zauna a kusa da ita ya ce "Ki na buƙatar isasshen abinci sweetheart, ba zan bari ki kwana da yunwa ba, na kashe fitilar tun da kunyata ki ke ji, dan Allah ki ci"

Sai a lokacin ummi ta tuna aurenta na fari, ko fara Idris bai shigo mata da ita ba, yau kuwa kazar da ta gani a ƙalla ta kai biyar, ban da kayan marmari da lemuka.

A hankali yake lallaɓata yana ba ta a baki, kai ka ce wani babban mutum ne mai shekaru.

Duk da ba da yawa ta ci ba, ta ji daɗin hakan, dan dama tana jin yunwa, hira ya ɗan din ga yi mata, kan ya bata damar ta kwanta.

Sai dai ummi tamkar zuciyarta ta tsaga ƙirjinta, ta faso saboda tsananin tsoro da fargaba, da zunzurutun tashin hankali, duk da kulawar da ƙoƙarin kwantar mata da hankalin da yake yi. Shi har mamaki ta bashi, kamar wadda ba ta taɓa aure ba.

Raihan ya nuna mata banbancin ilimi, da zunzurutun jahilci, banbancin dattaku da tarin wauta, banbancin wayewa da kuma ƙauyanci.

Komai na shi cikin nutsuwa da aji yake gudanarwa, ba kamar yadda Idris ya yinƙurin haike mata, tamkar wani jaki ko mahaukaci ba.

Ya nuna mata ita mutum ce, mai ɗauke da zuciya mai rauni a ƙirjinta, da ke buƙatar tausasawa da kuma kulawa tare da tarin soyayya, ba abar wulaƙantawa da cin mutunci ba.

Yau ta san meye aure, ba auren Idris ba, dan auren Idris ta bar shi a matsayin wata ƙaddara da dole sai ta faru da ita.

Raihan ɗin da take yi wa kallon auren sa abun kunya, haka tana kallo ta zama cikakkiyar mallakinsa.

Babban abun da ya razana ummi, tare da ɗaga mata hankali bai wuce yadda raihan bai ce mata komai ba, hasali ma ya juya mata baya yayi shiru. Hakan ya ɗaga mata hankali, tare da tabattar mata da an samu matsala a wannan karon ma.

Ayshercool
08081012143



PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

                       *CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

38

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

38

Ƙirjin ummi ne ya cigaba da bugawa, tare da sallama cewa, a wannan karon ma an samu matsala, wataƙila shi ma raihan ya ci karo da matsalar ta, ta farko.

Ta zubawa bayansa ido, duk da ɗakin ba haske, sai dim light na kan side bed.

Ko wane hukunci zata karɓa a wannan karon a hannun raihan? Allah ne ya bar wa kansa sani.

A hankali ta ga ya motsa yayi miƙa, yana gode wa Allah, ya tashi tsam ya nufi toilet.

Duk Addu'ar da ta zo bakin ummi yi take, saboda ita sam ba ta ga al'amuran sun faru kamar yadda take karantawa ko sauraro a littatafan soyayya ba, a zaton ta tun da abun da take tsammani bai faru ba, an sake samun matsala, tun da babu wanda ya zaunar da ita a nasihar da aka yi mata, aka yi mata bayanin menene gundarin auren.

Tana tufaka da warwara, da adduo'i, ya buɗe ƙofar ya fito, ba ta iya ganin me yake yi daga in da take, amma ta ji alamar ya buɗe wardrobe ya rufe.

Bai ɗauki lokaci da yawa ba, ya kunna fitilar ɗakin, hakan ya sanya ta sake shigewa cikin bargo tana jiran irin hukuncin da zata karɓa a wannan karon.

A hankali ta ɗago kai jin shiru, ta ganshi a tsaye a kan ta, ƙugunsa ɗaure da towel jikinsa da sauran ruwan wanka, ya yi murmushi ya ce "Ya ki ke sake shigewa cikin bargo, taso mana" yayi maganar yana miƙa mata hannu yana murmushi.

Jin maganar sa ya saka ta ɗaga kai ta kalli fuskar sa, ta ga me za ta iya ganowa, amma ba ta ga komai na damuwa ba, ko ɓacin rai ba.

"My love, ba fa canza miki ni aka yi ba, naga kamar wani abu ki ke son ganewa, yaron nan ne dai ki ke cewa ba zaki auri ƙaninki ba"

Ta sunkuyar da kai cikin matsananciyar kunya.

Ya ce "Ok, let me help you" yayi maganar zai ɗaga bargon amma ta riƙe ta ce "Ka bani hijjabi"

"Ai nan babu hijjabi, sai dai na baki towel sai ki yafa mayafinki" haka kuwa aka yi, ta ɗaura towel, ta yafa mayafinta, ya rakata har toilet, ya dawo kan gadon ya sake gyarawa, sai dai abubuwa na ta kai komo a ransa, duk da bai san dawan garin ba, amma ya san akwai banbanci tsakanin budurwa da bazawara, to ita ummi mecece? Budurwa ko bazawara?.

Yana tsaka da wannan tunanin, ta fito ya tashi da sauri ya nufe ta yana jera mata sannu, kamar wadda ta yi hatsari, sai raɓe-raɓe take tana tafiya a hankali.

Ya rungumota jikinsa ya kai ta bakin gado, ya zaunar da ita, cikin dabara ya zare mayafin, ya shiga tsane mata dogon gashin ta da yake jiƙe da ruwa da shi.

"My love, gaskiya yakamata mu tambayi mama, anya asalinku ƴan Nigeria ne? Ni fa ban taɓa ganin bahaushiya mai irin gashin ki ba"

Ta ce "HOD ɗinmu ma haka ya ce, wai ƙwayar idona ba irin ta ƴan Nigeria ba ce"

"Shi kuma saboda sa ido, har ya zuba miki ido ya gano ƙwayar idonki ba irin ta ƴan Nigeria ba ce?"

Ta tura baki ta ce "To ai ana ganina ake ganewa ba baƙa ba ce"

Ya ce "Idan na tashi dole a nemo hand drier, saboda tsane gashin nan, kar yawan wanke shi ba a busar ba, ya din ga saka ki mura ko ciwon kai"

Ummi ta ce "Ai ban damu da yawan wanke shi ba ma, saboda wahalar bushewa, na yi ta fama, duk ya dame ni, sai ... Sai kuma ta yi shiru.

Ya kwashe da dariya ya ce "Yanzu kuma wanke kai ya ganki, ba dare ba rana daga ɗaya zuwa sau ba adadi a rana" yayi maganar yana dariya, ta ja bakinta ta yi masa shiru.

Yadda yake ta tattalin
End Ads