An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
CUTARWA!
P1
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
⚠️⚠️
*Ƙirƙirarren labari ne, duk abun da aka gani a ciki, yayi kamanceceniya da wani abu, na zahiri ko makamancin haka, arashi ne*
*Haƙƙin mallakata ne, ban yarda a juya mini shi ta kowacce irin siga ba, sai da izinina"
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH).
Gagarawa Jihar jigawa.
Kasancewar wata ya nausa, domin kuwa watan jumada ula, ya kai kwanaki ashirin da biyar, wanda yake dai-dai da watan Nuwambar shekarar miladiya.
Mislain ƙarfe biyu da rabi, dare ya tsala, duhu ya mamaye ko ina, baka jin sauti ko motsin komai, sai kukan ƙananan ƙwari, da sautin busassun ganyen bishiyu, da iska ke kaɗawa lokaci zuwa lokaci.
A dai-dai wannan lokacin da kusan galibi mutane ke kwasar bacci, ni kuma har a lokacin idon ta tamkar an soya, babu alamar bacci a tare da idanun nata, sakamakon bushewar zuciya da raɗaɗi da take ji.
Sai yau ta tabbatar da cewa, nutsuwar zuciya, da kwanciyar hankali, da ƙarancin tunani, suke haɗuwa su haifar da daddaɗan bacci, mai cike da annashuwa.
A hankali ta tashi daga kan katifar da take kwance, na nufi tagar ɗakin, ta buɗeta, wani sanyi ya daki fuskarta, ta kalli ƙaton tsakar gidan, da baka iya gane komai a cikin sa, saboda duhu.
Ta ɗaga kanta, ta kalli taurari, yadda suka yi wa sararin samaniya ado, ƙudura da iko na Ubangiji na riƙe da su a sama.
Tayi ajiyar zuciya, tare da kamanta rayuwarta da wannan baƙin daren, mai cike da duhu, da ban tsoro.
A lokacin da karin maganar bahaushe ya yi amsa amo, a tsakanin ƙabilar ta hausawa, na cewa dauɗar gora ciki ka sha ta, sai dai kash! Zamani ya zo mana da cigaba, ta hanyar nuna mana muhimmancin lafiyarmu.
Duk da cigaban da aka samu, hakan bai hana a tauye ta ba, a shayar da ita dauɗar gorar ta ƙarfin tsiya ba, wanda hakan yake CUTARWA! Domin kuwa ya zame mata tamkar guba, domin ya zama silar sanya mata ciwon da take ta fama da shi, ta rasa maganin sa, wanda tun yana ɓoye, sai da ya fito yayi tsiron da mutane suke yi mata tambari da shi.
Haka zalika, azancin hausawa na ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ya samu gindin zama a da yawa daga bakunan mata, sai dai ita a nata ganin, ciwon ƴa mace, na ta ne ita kaɗai. Wataƙila ko a cikin ta ta rayuwar ne Allah bai sa ta yi katari da waɗanda ciwon ƴa macen yake zama nasu ba.
Duk iya ƙoƙarin da ta yi wurin haɗiye yawun bakinta, ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi, wani irin zafi zuciyarta ke yi mata, wanda ya haddasa numfashina fita cikin huci.
A hankali ta furta "Me ya rage? Tun da duniya cike take da rikici, da tarin ƙalubale, kowa kansa kawai ya sani, kuma kuɗinka shi ne mutuncinka, tabbas! Tura ta kai bango, na ɗaura aniyar fito na fito da duk waɗanda suka cutar da ni. Tun da babu sani babu sabo, dole in fasa ƙwan da warinsa ka iya sanadiyyar tarwatsewar zumunci, idan ya so na gani, ko suma suna iya jure ɗaɗɗake dauɗar gorar a cikin su, kamar yadda suka yi mini, daga nan na ƙara gaba,, na basu wuri tare da gwagwarmayar nemawa kaina mafitar rayuwa.
*****
La'asar sakaliya, wata matashiyar mace ce da ba zata gaza shekaru sha takwas a duniya ba, zaune a ƙaton tsakar gida, tana ta ƙoƙarin tsince waken da zata daka, ta zuba a cikin miyar yauƙin da take yi, cinyarta wata yarinya ce ƴar kimanin shekaru uku da rabi a duniya a kwance, ta saka babban ɗan yatsanta a baki ta na sha, hannunta ɗaya kuma tana wasa da cibiyarta.
Idan ka kalli yarinyar sau ɗaya, sai ka sake kallonta, tare da son sanin daga wace ƙabilar wannan yarinyar take?.
Baƙa ce sosai, mai ƙiba, tana da ɗan goshi, sai dai yalwataccen gashin girarta ya rage fitowar goshin nata, tana da manyan idanuwa farare, sai dai ƙwayar idonta brown ce, maimakon baƙa, bakinta ɗan cukul, sai dai laɓɓanta jawur, tamkar an saka mata jambaki. Babban abun da zai baka mamaki, bai wuce yadda take da dogon gashi ba, baƙi wuluk, mai tsayin gaske, ba curkukuɗaɗɗe irin na baƙaƙen fata ba, tamkar gashin larabawa, kalba aka yi mata guda biyu, amma ta saukko har cikinta, hancinta ba shi da wani tsawon kirki, saboda kumatu ya shanye su.
"Wai Mariya ba zaki ajiye wannan gunsumemeiyar yarinyar ki mayar da hankali ki kammala aikin nan ba. Kawai kin ɗauki ƴa kin narka a cinya ƴa ba kaɗan ba ko nauyi ba kya ji? Na ga dai ba nono za ki bata ba"
Mariya a ranta ta ce 'Ban da abun iya, ta yaya saniya za ta gaza da ƙahonta?'
A zahiri kuwa cewa ta yi "Yanzu zan kammala iya"
"To ki ajiyeta ta shiga cikin yara tayi wasa mana, wannan uwar matan ta zauna a cinya, kema ki haihu ki yi mata ƙani, kin naɗe kin ƙi haihuwa, kiyi ƙoƙari dai ki haifo wani, ko Allah ya sa a samu mai ɗan dama-dama, wannan ƴa muninta yayi yawa, Ko da yake can danginku ta kwaso wannan baƙin da muni, barebari ai haka ku ke baƙi kamar zunubin mutanen farko"
Mariya ta sunkuyar da kai tayi shiru, ta na jin zafin maganganun nan, amma ba yadda ta iya, haka ta ƙaƙalo murmushin dole, ta ce "Hajiya iya kenan, jikar nan taki mamaki zata baki, idan ta tashi kawo miki siriki, mai maiƙo za ta kawo, wanda zai kai ki makka".
Iya ta furzar da goron bakinta ta ce "Da wannan baƙin da munin? Maza na rububin farar mace, wa zai kwashi kayan muni, ai ko wannan idon nata, ya isa hanata auruwa, ido abun tsoro kamar ragowar maita, sai ido furi-furi kamar bururrun gawayi"
Sake kwanciya yarinyar ta yi a jikin uwarta, tare da kawar da kanta gefe.
Mariya ta shafa kanta ta ce "Ummina, ki tashi in haɗa abinci, kar yayyenki su dawo ban gama girki ba, ki tashi ki je ki yi wasa da su Auwwalu"
Noƙe kafaɗa yarinyar tayi, tana tura ɗan mitsitsin bakinta, ta sake gyara zama ta mayar da hannunta baki.
Sallamar da aka yi ne, ya sanya su haɗa baki wurin amsawa.
Sai dai ba ƙaramar razana ta yi ba, da jin muryar mai sallamar, dan sai da tayi wani zillo ta tashi zaune, wani ɗan matashin saurayi ne, hannunsa riƙe da wata ƴar jaka.
Iya ta ce "Ahh, idris ka dawo?"
"Eh, an gama abinci ne?"
"Ina fa, tana nan tana laƙai-laƙai tana fama da wannan jibgegiyar yarinyar, ita ba nono za ta sha ba, sai iskanci da taɓara dan sangarta".
Ya kalli yarinyar ya ce "Ummi, zo mu je na sai miki biscuits, ki bari anty ta gama mana girki"
Maƙale hannunta tayi, tana zazzaro ƴan idanunta, da tsoro ya bayyana ƙarara a cikin su.
"Ummina, dan Allah ki bi yaya idris, in kammala aikin nan"
Hawaye ya cika mata ido, tana kwantar da kanta a jikin mahaifiyarta.
Ya miƙa hannu zai ɗauke ta, ta fashe da kuka mai kama da na shagwaɓa, amma a zahiri na tsoro ne.
"Kai dalla ƙyale mata ƴar ta, dan ta samu za a ɗauke ta, ji iskancin da take, ita shagwaɓar ma ba kyau take yi mata ba, aba ba kyan gani kamar turotso".
Ta ƙarfin tsiya ya saka hannu, ya ɗauketa, tana ta kuka, mariya kuwa cikin kara da kawaici, ta tashi tana cewa "rigimammiya sam ba kya girma".
Ya fita da ita a kafaɗarsa, bai tsaya a ko ina ba, sai wani sashi na gidan, a ƙofar wani ɗaki da ba kowa a sashin, yanayin wurin zai nuna maka wurin ɗakin ƴan maza ne.
Ya buɗe ɗakin ya shiga da ita, yana zuwa ya dungurar da ita a tsakar ɗakin.
"Rufe mini baki, ko na shaƙe ki, ki mutu" cikin sheshsheƙa take ƙoƙarin danne kukan nata, gaba ɗaya ta burkice cikin matsanancin tashin hankali.
Ya bankaɗa gefen wata katifa, ya ɗaukko almakashi, ya durƙusa a gabanta ya ce "Kin gaya wa mamanki ko?" Ta girgiza masa kai, hawaye na zuba daga idonta, ga ƙoƙarin haɗiye kuka da take yi tamkar zata shiɗe.
"Kin faɗa ko baki faɗa ba?" Ta sake girgiza masa kai cikin razani.
"Duk ranar da ki ka faɗa, sai na gutsutstsura namanki da almakashin nan, na zuba a leda na kaiwa karen namadi, ya cinye ki, kuma sai na saka ki a murhun da babarki take girki, ai kin taɓa ƙonewa kin san zafin wuta"
Ba ta iya cewa komai, sai bin sa da ido, hawaye na zuba daga idonta.
Ya ajiye almakashin, ya janyo ta, ya fara ƙoƙarin cire ƴar doguwar rigar jikinta.
Sake fashewa ta yi da kuka, har da ɗan ƙara sauti, aikuwa ya zare mata ido, ya shaƙeta ya ɗaukko almakashin, ya saita tsinin a maƙoshinta, jikinta na rawa ta yi gum da bakinta.
Kamar yadda ya saba ɗaukkota yayi mata, haka yau ma idris yayi mata, sai da ya gama abun da Allah ya nufe shi da yi, sannan ya ƙyale ta, sai dai bai taɓa gangancin ƙetara ta ba.
Ya cigaba da yi mata kashedi, tare da firgita ta, a kan idan ta faɗa, sai ya sakata a murhu ya babbaketa.
Ya bar ta a nan zaune, ya kintsa, sannan ya zo ya ja hannunta, da ƙarfi sai da ta ji zafi, amma ba damar yin kuka, tana tsoron kar ya babbakata a wuta ko ya yankata da almakshi.
A wulaƙance, ya tafi da ita kanti, ya saya mata biscuit ɗin naira ashirin, da alewar naira biyar, ya sake fizgo hannunta ya nufo gidan da ita, sai tankaɗata yake yi yana masifar tayi sauri.
"Ba zaki yi sauri ba, sai wani jagwab-jagwab ki ke, kamar tsohuwar talo-talo" tafiyar sa da tata ba ɗaya ba, mussman ita da ke da jiki, haka ya ja ta sai daf da zasu shiga gidan, ya sake jaddada mata, kar ta gaya wa kowa abun da yayi mata. Ya saɓata a kafaɗarsa ya shiga da ita gidan.
"Anty mariya, ga rigimammiyar ƴar ki nan, uwar kuka, ta karɓe mini biskit, amma har muka dawo kuka take, saboda shegiyar ƙyuya".
"Ohh, Ummi Allah ya shirya mini ke, an girma amma ke ba kya girma, kamar ba ƴan mata ba" gaba ɗaya ummi hankalinta baya jikinta, a tsorace take sosai da sosai, sai dai kasancewar ita kan ta mariyar yarinya ce, shekarunta sha takwas, a zaton ta kawai rigima ce, kasancewar ummi, yarinya mai azabar ƙyuya da miskilanci.
A nan tsakar gida ta yasar da biskit ɗin, ta je ta rirriƙe mahaifiyarta, ana daf da sallar magariba, mahaifin ummi ya dawo, ya ɗauke ta yana juyi da ita a tsakar gida, yana faɗin "Ummi, waye ya taɓa ni ƴa ɗaya tilo, na ga kamar kin sha kuka? Ko dai kin daketa ne?" Yayi maganar yana kallon mariya.
"A'a wallahi, ƙyuya ce kawai, ba zata yi wasa a cikin yara ba, ta maƙalƙaleni, dan idris ya ɗauke ta take kuka".
"Ki daina ƙyuyar nan dan Allah, na zo miki da alewa daga kasuwa, da yalo ai kina ci ko?".
But iya ta fito daga ɗakin ta, "Balarabe wannan ƴar ka sunkuta ka ke shillawa sama, sai ƙirjinka yayi ciwo tukuna ko?"
Yayi murmushi ya ce "Iya guda nawa ummin take"
"Ajiyeta dan Allah, duk a haka ku ke sangarta ta, tayi ta taɓara tana iskanci, ƴa sai ka ce teba" cikin jin nauyin mahaifiyar sa, ya ajiye ummi, yana murmushin yaƙe.
"Ina alewa da yalon da na ji ka ce ka zo da su? Bani nan a rabawa sauran yaran gidan, ai ba ita kaɗai ce ƴa ba, nan idirs yanzu ya fita da ita ya kaso mata uban kuɗi, amma kai sai ka zo da abu ka hana sauran yaran? Saboda ka haifi gwal?"
"A'a Inna, ina sayo da su suma, gani na yi ita ce ƙarama, kuma yau kasuwar sai godiyar Allah, tun da ba ranar kasuwa ba ce ba, ɗan kaɗan ne na zo da su ba yawa" yayi maganar yana nuna mata ƴar ledar hannunsa.
Ta ƙaraso ta fizge ledar "To tun da ba ciniki, sai ƴar taka ta haƙura, kai dai balarabe kamar a kan ka, aka yi wahayin talauci, kullum kasuwa ba cigaba, kana kallon yadda ƴan uwanka suke ƙoƙari kowa da abun arzikin sa, kai kuwa ba ka ajiye komai ba, sai son mace da wannan mummunar yarinyar, daɗi aure ba zaka zage ka nemi arziki ba" shiru yayi ya sunkuyar da kansa, dan ba shi da abun cewa.
Mariya kuwa ta mayar da hankali wurin kwashe tuwo, roba-roba.
Malam Hashimu dodo, shi ne mijin iya, gidansu babban gida ne, da aka yi ittifaƙin babu gidan da ya kai su yawa.
Da yayi aure ya ja nasa ɓangaren a cikin gidan su. Kasancewar gidan babba ne sosai, dan kusan duk garin babu mai girman gidan.
Kowa ya san su, saboda galibi ƴan gidan manoma ne, sai masu taɓa kasuwanci, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado.
A hankali wasu suka din ga samun rufin asiri, suna watsewa daga gidan, malam hashimu yana sake shigar da wasu sassan nasa sashin.
Daga baya ya auri iya, bayan matarsa ta ladan noma wato salamatu. Malam Hashimu mutum ne mai hidimtawa iyali, a lokacin boko ba ta yawaita ba, sai karatun allo, dan haka da shi da ƴan uwansa suna da ilimin soro.
Bayan wani lokaci, salamtu ta mutu, ta bar yaranta huɗu, biyu mata biyu maza, iya ta cigaba da riƙon su, da nata ƴaƴan.
Sai dai iya macece me shegen son abun duniya, tamkar ta yi ƙwace, ga ta da iya fuska biyu, a waje ta nuna ta Allah ce, amma na cikin gidan, su suka san gashin da suke sha.
Ba ƴaƴan da aka bar mata ba, har facalolinta, da suke cikin gidan iya na azabtar da su, gwargwadon abun hannunka, da abun da ka ke bata, gwargwadon mutuncinka a idonta.
Aka aurar da ƴaƴan salamatu mata, ɗayan kuma Yahaya, ya ce shi karatun boko yake so. Iya tayi ta sukar abun, amma malam Hashimu da suke kira da baba ya bashi goyon ba.
Ƙaninsa kuma Ilyas, yana zaune a nan ƙauye, amma yana taɓa kasuwanci, nan da nan ya fara tara kuɗi, yayi wuf yayi aurensa, shima ya tare a cikin gidan.
Yaran iya su biyar, biyu mata Shafa da zaliha, uku maza, Sagir, Saminu, sai Bashir wato balarabe. Duk wanda yake da kuɗi shi ne nata, hatta a jikokinta bambanci take nunawa muraran, sagir ne babba shine baban Idris da kuma Hashim suna ce masa magaji, saboda sunan malam ne da shi.
Akwai tarin ƴaƴa da jikoki a gidan, bayan rasuwar iya ita ke tafiyar da gidan, saboda azabar faɗanta da iya masifa, hatta ƴan uwan malam tsoron ta suke ji, abun da ta dama shi ake sha.
Saboda balarabe ba shi da kuɗi, wato baban ummi, duk gidan shi ne samunsa ba mai yawa ba, dan dako yake yi a kasuwa da ƴan buge-buge dan haka samun nasa galibi sai damina idan yayi noma, hakan ya sanya duk wata ɗawainiyar gidan ta wahala, iya ta sa matarsa mariya ce ke yi, wadda asalinta ƴar Maiduguri ce babarbariya ce, sun zo garin biki suka haɗu, har Allah ya sa suka yi aure.
Tun da mariya tayi haihuwa ɗaya ta haifi, yarinyarta aka saka mata sunan mahaifiyarta, wanda yayi dai-dai da sunan uwar gidan malam, wato Salma ba ta sake haihuwa ba, tsawon shekaru uku kenan, iya ta ɗorawa yarinyar nan Ummi ƙahon zuƙa, da ba'a da cin mutunci, wai ta haifi wata halitta daban, da babu irinta a danginsu.
Ba ita ba har yaran gidan, da sauran mutanen gidan, na yawan kushe halittar ummi, tare da tsokanarta, gashi ayi ta tankata, saboda baƙinta, da kuma ƙibar ta, ga kuma kalar idonta, sai dai kuma mutane