bata wani daɗe ba tace "zata tafi" Leena suka fito parlorn tare kamar zata yi kuka tace "Ammi bani wayan ki Anty jidda tasa min numbern ta" Ammi ta mika mata ta sa sannan tayi dialing ya shiga sai ta kashe, tana kallon Ammi tace "Ammi da zaki yarda ki bamu Leena da munji daɗi" Ammi kawai tayi murmushi, tayi kissing forehead ɗinta tace "zan yi missing ɗinki Leena Allah baki lafiya" tace "Amin ki gaishe min da Mami da Uncle ɗin na tace "wanne kenan?" tace "O'o ban son wannan arrogant ɗin" Jidda sai dariya take zata fita Ammi tace "Leena raka ta mana" Leena zata bi ta haka Ammi tace "bana ce Miki kina sa hijabi idan zaki na fita ba ta koma ɗakin ta ta ɗauko hijab har bakin gate ta raka ta Jiddah tace "ba zaki gaisa da Uncle ɗin ki ba" Leena tana karasa jikin motan suka haɗa ido da Sadeeq ta sauke idon ta kasa tana wasa da bakin hijab ɗinta sai kallon ta yake ko kiftawa be yi ba tace "Ina wuni" ya ɗauke kan sa ta kalli Jidda da ke bayan ta tana kallon su tana dariya ta sake mayar da dubanta kanshi ta murguɗa masa baki karaf a idon Sadeeq daya sake jiyowa da sauri ta juya ta koma baya tana kallon Jiddah ta mata bye bye ta shige gidan su Jidda zata buɗe motar taga Sadeeq na Murmushi ta taɓe baki sai kuma tace "toh Ya Sadeeq ka gane ta ko?" ya ɗaure fuska yace "ita wa ɗin?" daga haka bata sake ce masa komai ba ya taɗa motar suka tafi. Leena na komawa parlor Ammi tace "zo Leena" ta karasa ta zauna gefen Ammi tace"gani Ammi" Ammi tace "Aina kika san wannan kuma?" tace "lokacin da na ɓata ai sune suka ɗauke Ni a gidan su na kwana" Ammi with shock take kallon Leena tace "ban gane ba yaushe ne kika ɓata? Ai na kuma" Ammi ta jera ma Leena duk waɗan nan tambayoyin Leena ta fara "Lokacin da kika yi tafiya kika barni......" Ba abinda Leena ta mance bata faɗa ma Ammi ba, Ammi ta rungume Leena ta fara kuka. Wajajen karfe 3pm Rayyan yayi sallama Leena ta leko da gudu tana masa murmushi yace "Eh Lalle lafiya ta samu" tace "yanzu zamu tafi?" yace "go and wear your hijab" daga haka ta koma ciki sai gashi ta fito, tun da suka fito suka fara tafiya suna taɗi Leena na dariya yana bata labari ya gaji yayi shiru ta cigaba da basa Labari suna dariya tsintan kansu sukayi a street C Leena tace Laaaa ya Rain ga can gidan dana kwana ranan" kallon gidan yayi sai kuma yace "wai haka kike son yawo? Baki gaji bane?" Dariya take yi, kallon motar da tayi a parking a kofar gidan su Jiddah yasa take kallon ciki ganin kamar da mutum suna zuwa daidai wajan kawai taga Sadeeq ne kallon ta yake kuma be fasa ba har suka yi gaba be fasa kallon Rayyan da yake yi ba, Rayyan na kallon ta ya e "ke mu koma gida, ganan short code mubi ni na gaji" suna cikin tafiya yace "Leena" tace "Na'am" yace "Hope zakiyi jumping a school ɗin ba? Ba za kuyi jss3 and Ss3 ba ko?" tace "sai dai kama Ammi na magana wai ita nayi karama" yace "zan mata magana" duk sukayi shiru sai kuma yace "Leena" ta kalle sa tace "baka da Lafiya ne" sai ya girgiza kai ba wanda ya sake magana har suka isa gate din giɗan su Leena ta rike cikin ta tace "Ashh" yana kallon ta yace "what?" tace "ciki na" ta fara yarfe hannu ta ɗurku sa nan kasa ya ɗaga ta, har wani mota ya zo yayi parking a bayan su Amma shi bata motar ya ke ba, wani murɗa wan da cikin ta yayi bata san sanda ta kankame sa gamgam ba,nan yayi noticing blood daya gani a jikin hijab ɗinta yana kokarin gyara mata hijab ɗin still tana manne a jikin sa tana kuka aka buɗe gate ɗin za'a fito nan yayi ido hudu da Mummy da Aminiyar ta duk suka tsaya with shock suna kallon sa.
Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
_By Jiddatul-khayr writes
Chapter 10
He was shocked that his mother had slapped him. It wasn't like her to lash out physically, and he couldn't remember the last time she'd done it. That's because she loved him so much, and usually showed her displeasure in other ways. Leena ta kalli Rayyan Who looked utterly shocked, and then turned to his mother, Mummy tana nuna ta da yatsa, her eyes blazing with a mix of anger and disappoinment "Kalle ni da kyau Uwar sa ce Dan ubanki, this should be the first and last time I see you with my son, idan ba haka ba wannan fuskar taki da kuke ji dashi daga ke har uwar ta ki sai nayi damaging ɗinsa Shegiya, ki ɓace min daga gani na" Leena take fama da cramp ita da ko sanin menene ma abun bata yi ba ta juya jiki a tsanyaye zata shiga cikin gidan, Mummy tace "daga yau kuma kin bar makarantar da su Nisreen suke ciki, wannan ne yasa kike da guts ɗin yi komai kan ki tsaya" bata ko juyo ba ta buɗe gate ɗin gidan ta shige, Fatima Aminiyar Mummy tace "Ai tun farko ke kika yi sake gashi kina gani zaki kwashe bakin ciki" Mummy na kallon Rayyan tace "Look Rayyan! Daga yau duk ranan da ka sake ma Leena magana ko Uwar ta, toh Wallahi ban yafe maka ba" da sauri ya ɗaga kansa yana kallon ta,Her words cut deep, leaving him feeling deflated and defeated. but her statement somehow pierced his heart, making him feel chilled to the bone. The pain of her words was like a physical blow, and he could feel his emotions plummeting, Mummy ta ja hannun Aminiyar ta suka karasa inda motan ta yake Rayyan ya buɗe gate ɗin gidan ya shiga feeling somehow and Her words kept echoing in his mind Dakyar yake iya tafiya. Fatima tace "yau dai kin gasgata abin da nake faɗa Miki ko?" kalli yadda lokaci ɗaya ya gigice daga cewa baki yafe ba, toh wallahi saura ki sassauta masa ki bata mana aiki" Mummy tace "ki bari ku karasa gida za muyi waya kawai". Leena bata tsaya ko ina ba ɗakin ta ta wuce yanzu ciwon cikin da take ji ma duk ta neme shi ta rasa sheshshekan kuka ta fara ita ba maganar da Mummy tayi akan zata bar makarantar bane da muwanta, marin da Mummy tayi wa Ya Rain ne idan ta tuna sai ta fashe da kuka She cherished him so much, as a brother. a haka Mummy ta shigo ta same sa a compound ɗin kamar ba tafiya yake ba zunzurutun dakyar yake iya daga kafan sa, ta wuce sa ko ta kansa bata yi ba. Ammi da kwana biyu take fama da kanta gaba ɗaya ta rasa meke damun ta ta fito zata kitchen taji sheshshekan Leena ta karasa ɗakin da sauri tace "meya faru Leena?" Leena ta ɗaga kai tana kallon Ammin ta sai kuma tace "ciki na ne?" Ammi ta ɗurku sa ta ɗago ta nan taga har ta ɓata kayan ta. Rayyan tun daya shiga banda zazzaɓi da yaji ya rufe shi sai kuma sanyin da yake ji ga kuma maganganun Mummy da ke ta yawo a kwakwalwar sa, bayan wannan ba wani abu da yake ganewa kuma a duniyan, ya kwanta ya rufe da duvet Hawaye kawai ke zuba daga idon sa He hated that woman with passion yasan ita ta ɗaura Mummy akan wannan gurɓataccen shawaran, ya rufe ido yana kiran sunayen Allah. Daren ranan daga Leena har Rayyan ba wanda ya samu yayi baccin kirki, Rayyan damuwa ce ta rufe sa ga zazzaɓin da yake ji, Leena kuma ga ciwon ciki daya addabeta idan ta tuna Abunda ya faru duk sai taji ba da ɗi, idan ta tuna da sabon yanayin ta kuma addu'a take Allah yasa Rayyan be gani ba, idan ta tuna lokacin da yake kokarin gyara mata hijab sai ta kuma fashe da kuka tace kila ya gani ne. A week later, he still couldn't shake off the feeling of hurt. Leena ta fito rike da jakkan Haddan a hannun ta, yanzu har ta warware part ɗin Hajiya ta wuce ta shiga ciki da sallama ta shiga tana kallon Hajiya da take sallah zama tayi a kan cushion tana kallon Tv har Hajiya ta idar da sallah ta juyo tana kallon ta tace "Makarantar islamiyya zaki?" tace "Eh Hajiya, ina wuni" tace "Lafiya, dama ina neman ki ne" tace "Eh haka Ammi na ta faɗa min" Hajiya ta ninke sallayan ta karaso cikin parlorn ta zauna tana kallon Leena tace "Lina dama tambayar ki zanyi" tace "Me kuma Hajiya?" tace "Naga kaff gidan nan Riyan ya fi shiri da ke, shine nace zan tambaye ki wai meya ke damun sa ne? yace miki akwai Abunda yake damun sa ne? Kai ta girgiza wa Hajiya dan ita yanzu rabon da ta gansa tun ranan da Wannan abun ya faru "Hajiya tace "toh ke kuma baki tambaye sa me yake damun sa ba ne Lina? Ko ke baki ga yadda ya rame bane?" Leena tace "toh ai Ni bamu haduwa yanzu" Hajiya tace "ko da yake ke yarinya ce ba sanin komai zaki yi ba" Leena na kallon Hajiya tace "barin tafi dan na fara latti" daga haka ta fita a hanya tayi clashing da Rayyan wanda ko kallon ta be yi ba ta tsaya tana kallon yadda ya koma tace "Ya Rain!" Ko jiyowa be yi ba balle tasa ran zai mata magana daga haka ta yi wucewar ta jiki a sanyayye. Rayyan ya shiga parlorn Hajiya da sallama ta amsa masa yana shiga ya samu 3 seater ya kwanta ya lumshe ido Hajiya tayi tagumi tana kallon sa ita duk yana yin Rayyan na kwana biyun nan na mugun damun ta, wannan sauyin nasa ta rasa daga ina ne, tana kallon sa tace "Riyan ya buɗe ido yana kallon ta" tace "Dan Allah nikam ka faɗa min Abunda yake damun ka? Ni wallahi yanzu kuma damuwan nan naka shine damuwa, dubi duk yadda ka zab ge ka rame lokaci guda" Rayyan da ya gaji da surutun ta ya mike ya zauna tana kallon sa tace "baka ce komai ba fah" yace "ba abinda ya ke damina, bari na koma can dama na shigo ne na gaishe ki" ta tashi tace "yi kwanciyar ka nasan halin ka yanzu zaka ce surutu name ya dame ka" daga haka ta tsuke fuskar shi kuma ya koma ya kwanta. Leena na taho wa daga makaranta wata mota ce tayi parking gaban ta har sai da ta tsorata ganin gaban motar tayi taga Sultan na driving Sadeeq na gefen sa ta washe baki ta karasa wajan tace "Laaa, Uncle it's you?" yana mata dariya ya mika mata hannu su tafa har ta ɗaga sai kuma ta tuna da maganar Ammin ta sai ta sauke hannun tana murmushi tace "ina wuni, ina Anty jidda?" yace "Lafiya kau, ai Anty jidda na fushi da ke" tace "Wallahi Ammi nane bata barni nazo mata ba beside bani da lafiya ma, ai ta sani" yace "it's Okayy, little girl" ɗan lekan Sadeeq tayi ta, shi da ko sau ɗaya bai kalle inda take ba, tama Sultan alama da ya taɓa shi tana kunshe dariyar ta shi kam gaba ɗaya Leena dariya take bashi ya taɓa Sadeeq yace "Ana maka magana Sadeeq" Leena ta zaro ido tana rufe bakin ta da hannun ta sai kuma tace "Hey! Uncle, good evening" be ko ɗago ba balle tasa ran ze amsa mata ta harare sa tace "Nikam Uncle Sultan, baya jin magana ne shi?" Sultan ya fashe da dariya ya ɗago kan sa for the first time Leena ta bar wajan da sauri yana ma Sultan wani kallo yace "dalla Malam zaka ja motar ne ko ka tsaya kana yake wa yarinyar cikin ka haƙora" Sultan yaja motar yana dariyar. Rayyan ya shigo parlorn su kamar tafiyar ma Dakyar ya keyi Niswa ta kalli ƴaƴan nata cike da tausayin sa tace "Ya Rayyan na dafo maka shayi ne?" ya kalle ta sai ya girgiza mata kai sai ya cigaba da tafiya Mummy da ke dinning tana kallon sa cike da tausaya wa tace "ka ci abinci ne Rayyan?" ya kalle ta yace "sai anjima zan ci" tace "kalli karfe nawa? Magrib da ake shirin kira kace sai anjima" yayi shiru sai kuma yace "zanci" daga haka ya wuce ɗakin sa tayi shiru tana tunanin anya bata yi wa ɗan nata zafi da yawa ba but tasan no matter what tasan zai wuce. Da daddare Daddy yayi sallama a Kofar parlorn Hajiya ta amsa masa ya shiga ciki bayan sun gaisa ya mika mata Ledan hannun sa yace "Hajiya ga kayan ciki na gani nace barin tahi Miki da shi" ta karba tana Godiya ta cire takeaway tace "Allah sarki Riyan dama shike siyamin kusan kullum" sai kuma ta mayar da duban ta gun Daddy tace "Muhammadu nikam ba zaku tambaye yaron nan me yake damun sa ba, lokacin daya ya zabtare ya rame kamar ba shi ba, yanzu ko ɗan maganan da daa yake yi yanzu duk ya daina" yace "Hajiya har ɗakin sa na shiga na tambaye sa amma yace min ba komai, nayi nayi ya faɗa min sai daga karshe yace min Stress ne, wani irin stress ne da har zai kwantar da shi a asibiti" Hajiya tace "Toh kuma ba maganar auren nan na sa bane?" yace "ina ga shi da uwar sa ne, dan naga bata damu ba, da ace bata san da abinda ke damun sa ba da bata kyale shi haka nan ba zata ta damina in tambaye sa inji menene" Hajiya tace "Allah kyauta, Nima nayi masa magana amma yace min babu". Washe gari Leena ta gama shirin school tun da wuri tayi sallama da Ammi ta karasa parking space sai ga Rayyan ya fito shima zai shiga motar sa Leena ta ringa kallon sa har ya karaso ya buɗe motar sa ya shiga zai rufe ta karasa da sauri ta rike kofar motar tace "Ya Rain, ba kalle ta ba kuma be ja kofar ya rufe ba yana jiran ta ta sake masa sannan ya rufe tace "Ya Rain na maka laifi ne?" Still bai ko kalli inda take ba tace "Na daina damun ka daga yau In shaa Allah, amma idan laifi na maka kayi hakuri" daga haka ta sake masa kofar motar sai sannan ya juya ya kalle ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya ja kofar ya kulle ya jinki da kansa sai after some minutes Sannan ya tada motar ya fita, Leena ta koma ta shiga Mota duk jikin ta yayi sanyi ta rasa me ta masa duk ya canza mata kwana biyun nan. Haka Rayuwa ta cigaba a gidan Alhaji Muhammad tare da matan sa biyu da yaran sa 4 a cikin shekara 5 da suka wuce, Ammi ta haifa ɗanta na miji wanda ake kiran sa da Ayan, haka Rayuwa ta cigaba sakanin Leena da Rayyan har yanzu ta saba da rashin mata magana da baya yi mata, itama ta daina kula sa har Hajiya tayi noticing hakan sannan tama dukkan su magana amma duk sunce ba komai, sakanin gidan Mami da su Leena kuma yanzu sun zama kamar ƴan uwa dan idan Leena tayi hutu gidan take zuwa tayi hutu Jidda kuma takan taimake ta akan mindset ɗin ta dan yanzu kusan duk kasan ansan da Leena, sai da Mummy tayi tasan yadda aka raba Leena da ƴaƴan ta a makarantar, hakan kuma ya zama mata Alkhairi dan makarantar ne da taimakon Jiddah ta sanu a duniya........
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Chapter 11
Hey readers! Follow me @jiddatulkhyar on Wattpad to stay updated on my writing journey!
Don't forget to add "Agola (Behind the palace walls)" to your reading list so you can stay up to date on the story and get notified about new chapters! 📖💕 Thanks for reading!
After the flight landed at Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, she emerged from the aircraft and made her way down the jetway, walking slowly, her eyes scanning the surroundings. Then, she turned her face, and I caught a glimpse of her features - it was who? Kyakkyawar budurwa wacca ba zata wuce 18 year ba amma sai ka ɗauka she's 20, saboda yadda jikin ta yake, ba siririya ba sannan bata da kiɓa sosai, fara ce sannan kuma tana da tsawo, kana ganin skin ɗinta yadda yake glowing kasan ba karamin jin daɗi take ba, tana sanye da Black Abaya hannun ta rike da hand bag ɗin ta, it was Leena. As she walked towards the baggage claim, she grabbed a cart to collect her luggage, her eyes scanning the carousel for her suitcase. As she scanned the crowd, someone called out 'Leena!' She turned with a bright smile, and her eyes lit up when she saw Jidda. With a burst of enthusiasm, she rushed into a warm hug, squeezing her tight.
tace "Nayi missing ɗinki irin sosai ɗin nan" Jidda na dariya ta nunawa driver jakkan Leena ya ɗauka. Bayan sun ɗau hanyar gidan Jiddah, Leena sai bin cikin garin Abuja take da kallo jin wayan ta na ringing yasa ta ciro wayan da sauri a cikin jakka ganin Ammi ne yasa ta ɗauka da sauri ta kai kunne tace "Ammiii!" tana murmushi bayan sun gaisa Ammi ke tambayar ta ta isa ne, Leena tace "yanzu Anty Jidda ta ɗauke ni bamu ma karasa gidan nata ba" daga haka suka yi sallama ta mayar da wayan ta cikin jakka, a NNPC Quarters dake Area 11, Garki, Abuja. Anan suka sauka jidda ta sallame me bolt Suka shiga cikin quarters ɗin jidda ta buɗe ɗakin ta ta