suka samu Malik da wasu few friends din sa, ya karasa ya gaishe su, Mummy ta dinga kallon sa haka sauran friends din na ta ma, bayan sun shiga motar, motar su Hajiya yayi gaba wanda Mummy ke ciki, motar su Hajiya Amina kuma na biye da su, Hajiya Amina tace "Kambala'i! Amma wallahi ansha da Khadija" duk suka kwashe da dariya, Hajiya Amina tace "Ni fa wallahi dana ga mutumin nan ko wuka za'a samin a wuya ba zan yarda bashi da kuɗi ba, kalli yadda skin ɗin sa ke shinning" wata friend ɗin Mummy tace "ku gayawa Khadija gaskiya, ta ajiye makaman hannun ta kawai, dan wallahi wannan halin nata wata rana zai kai ta ya baro ta" a haka dai har suka karasa gida akayi dropping ɗin su. Hajiya ta sauka ta wuce cikin gidan, Mummy tun da ta sauka bata ko kalli Hajiya ba ta wuce sashin ta kamar zata tashi sama, tana shiga ta kafa kiran Rayyan a waya. Bayan fitan su Mummy Leena ta yaye veil ɗin kanta tana bin parlorn da kallo, dan tun suna cikin mota yadda Mummy ke magana yasa take Allah Allah a kaita ta kalli me Mummy ke magana akai, still Leena ta tsaya kamar statue tana bin parlorn da kallo, bata taɓa shiga shock haka ba a rayuwar ta, buɗe kofar akayi ta ɗaga kai tana kallon sa, murmushi ɗauke a fuskan sa. Dakyar Rayyan ya samu yayi parking motar sa a kofar gidan su, da sauri ya shige gidan saboda yadda Mummy ta ɗaga masa hankali da kira akan tana neman sa, yana shiga parlorn ya ganta tsaye hakan yasa zuciyarsa kusan bugawa yadda yagan ta yasan something is bad yace "Mummy is everything alright?" ya karasa maganar hankalin sa tashi, Mummy tana kallon sa tace "Rayyan kace min wanda zai auri Leena ba shi da kuɗi kuma har iyayen sa ma basu da hali?" Rayyan ya sauke ajiyan zuciya dan ba kadan zuciyan sa ya tsinke ba, ya zauna yana kallon mahaifiyar ta sa yace "Sure! Hakane maganar" ta matsa tsawa tace "Karya kake? Har Ni zaka ma karya Rayyan?" yace "Wallahi ba karya nake miki ba Mummy" tace "Shine naga gidan da aka kaita har yafi gidan mijin ta na da kyau? Su da suke da gidajen man fetur ma kenan?" Rayyan yana kallon Mummy da mamaki a hankali yace "A'a wannan ba gidan sa bane, ɗaya daga cikin gidajen Daddy ne ya basu su zauna a ciki" Mummy ta dafe kirjin ta tana gwalo ido tace "Gidan Daddyn ku ne wannan wai? Furnitures ɗin kuma fah?" Yace "Gidan Daddy wanda aka gama renovating sannan furnitures kuma ban sani ba" Tace "Bansan Daddyn ku bashi da tunani ba sai yau, yanzu sai ya dauki gida ya ba wata Agola? Gashi da yara?" Calmly Rayyan yace "Me aciki Mummy? Duk ai muna da wajan zama na rufin asiri sannan ita kadai ce wanda ta auri wanda bayi da shi shine Daddy ya tausaya mata, kuma yace zai samar masa aiki ai ba wani abun bane Mummy" Mummy ta ja dogon tsaki tace "Dan Allah ka bar min gida" daga haka ta wuce dakin ta kamar wacca zata hadiye zuciya ta mutu dan bakin ciki, ta dauki wayan ta zata kira Hajiya Fatima sai sannan ta tuna ashe ko inviting ɗin ta bata yi ba bayan ita ta bata kuɗin da ta kaiwa Malamin dan ya sa Leena ta so Malik, cilli tayi da wayan ta zauna kasan dakin tana jin wani baƙin ciki. Leena na kallon Malik da wani expression tace "Tell me, gidan nan kuma fah?" Ya sauke ajiyan zuciya dan bai san Daddy bai sanar da ita ba, a hankali yace "I thought Daddy ya sanar da kee, yace mu zauna anan kafin har Allah ya hore min, so da ban so karɓan offern ba but ba yadda za'a yi nama Daddy garda ma" Leena ta share hawayen fuskan ta tace "Allah sarki Daddy, Allah saka masa" a hankali yace "Amin". Sadeeq kamar zai yi hauka duk ya burkice musu, Sultan yace "Mistake da kake yi a rayuwa sai kace ba komai zaka yi magana akai ba, kuma hakan bayi bane" Mami tace "Wallahi ban so da Leena táyi aure ba, amma yadda naga idan wai ba'a yi mishi magana ba shi ba zai iya buɗe baki yace wani abu ba shiyasa na zuba masa ido" Jiddah tace "And to be sincere maganar karɓan Nawaf kamar za'a shiga hakkin ta" duk maganar da akeyi Sadeeq bai kalle su ba, daga karshe ma mike wa yayi ya wuce sama ya bar su. Bayan kwana biyu, Mummy na zaune gefen Daddy da ke breakfast tana ta jan sa da hira, maganar da yayi ne ta karshe ya tsaya mata a rai, ta dake tace "Amma Daddyn yara bangane haka za'a bar mijin Leena ba?" Daddy daya gama breakfast din sa ya mike yace "Eh, ai Kinga idan har an kyale sa haka nan bamu kyauta ba tunda muna da hanyar sauya masa wajan aiki, dama tuni mun gama magana da Rayyan akan samar masa wani aikin" Mummy ta dake tace "Ai kam hakan yayi Alhaji" daga haka ya mata sallama ya fita. Tun fitan Daddy, Mummy ta dinga kiran Rayyan a waya baya ɗaga wa sai gashi can ya kira ta back ta ɗauka tace "Ina ta kira kana ina ne wai?" Yace "Mummy a asibiti muka kwana Layla ce ta haihu" to his surprise sai ji yayi tace "Okay, dama ina son na sanar da kai ne babu ruwan ka akan neman ma mijin Layla aiki" yayi shiru har sai da tace "Baka ji nane wai?" Yace "Ina ji, but Mummy mai hakan zai yi, naga taimako ne kuma ai dan Leena da Ammi zamu yi hakan" Mummy tayi masa wani tsawa "Har zan kawo magana kana jayayya da Ni Rayyan? Toh wallahi ban yafe maka ba idan har baka cire bakin ka a maganar nan ba" Rayyan yayi shiru yace "Idan kuma Daddy ya saka ni fah Mummy? Please kiyi hakuri ki janye bakin da kika min" kit ta katse kiran, Rayyan ya cire wayan a kunnen sa yana kallon screen ɗin, tunani iri da kala ne ke yawo masa a kai. Leena na zaune akan cabinet tana kallon Malik dake wanke waste plate a sink sai dariya take masa, ya juya yana kallon yadda take dariya sai kuma ya juya ya cigaba da wanke plates ɗin yace "Oho, Ni dai all what I knw na fiki iya wa" ta masa hararan wasa tace "A hakan? Chap sannu ko" ya wanke last plate Sannan ya fara clearing wajan ta sauka zata taya sa yace "Nace miki bana son kina sa mun hannu a duty na, ki bari idan naki ya zo ba zan taimaka miki ba" tace "Hutu na" tare suka fito a kitchen ɗin yace "Kiyi sauri ki shirya kar muyi yamma" tace "Alright" daga haka ta wuce dakin ta, shi kuma ya koma kitchen ya dauko food basket da suka jera da warmers a ciki ya kai bakin kofa ya ajiye sannan ya wuce cikin na sa dakin, ba'a dau lokaci ba sai gata ta fito dama tayi wanka kaya kawai zata sa, shima ya fito, ta dauki keyn motar ta ta mika masa, ya girgiza mata kai yace "Kawai kiyi driving ɗin mu" daga haka yayi gaba ba tare da ya jira ta ba, itama fitan tayi ta bisa a baya, yana sa basket ɗin a bayan mota ta saka masa keyn a hannun sa tace "Wai mayasa kake min haka ne" murmushi yayi yace "I'm sorry, then", A hanya sai labari suke idanun sa na kan titin, Ita kuma sai kallon sa take yi, can ya ɗaga gira ɗaya yace "Yes na miki kyau ne?" 'yar dariya tayi tace "Let me confess, wallahi kayi kyau" yace "You too, You are so adorable and beautiful wollah" ta harare sa, ta dauki wayar ta tace ya ɗan jiyo, yana jiyo wa ta musu hoto sai Kuma ta tsaya kallon hoton tace "Ikon Allah" yace "What?" Tace "Wallahi muna kama, Ni sai yanzu na gani a hoton nan" yace "No, bamu kama, kin fini kyau fah" daidai yana parking a kofar gidan su, ta sauka shima ya sauka, yaune rana ta farko da zata fara haduwa da parents ɗin sa, ya dauki basket ɗin yana gaba tana biye da shi a baya har suka shiga cikin gidan da sallama, Umma da Abbah dake compound duk suka daga kai suka kalle su, Nan da nan murmushi fuskan Umma ya washe cos bata taɓa ɗauka kamar nasu haka yayi sosai ba, Abbah da ba wai yana da magana bane amma hakan sai da ya basa mamaki ya dinga kallon su har suka karasa kan tabarman da suke, A hankali Leena ta sake musu sallama, Abbah kaɗai ya amsa Malik ya ajiye basket ɗin a parlorn sannan ya fito ya zauna kan wani kujera, Leena ta gaida Abbah, ya amsa mata da fara'a, ta juya tana kallon Umma, da sauri Umma ta sauke idon ta daga na Leena tana avoiding eye contact da ita ta amsa mata gaisuwar ba yabo ba fallasa, Umma ta mike tace "Mu shiga ciki ko?" Leena ta mike, haka Malik ma duk suka bi bayan Umma. har Leena suka fito bayan Magrib zasu koma gida Umma taki yarda su haɗa ido wanda hakan yayi matukar ba Malik mamaki, sannan yayi mamakin sauyin Umma cikin sauri haka. A hanya Malik ya ɗan kalli Leena dake hamma yace "Ko zamu karasa gidan Ammi ne ta bamu ɗan mu yau" Leena ta ɗan kalle sa sai kuma tayi dariya tace "Ai Ammi ba lalle ta yarda ta bata Nawaf yanzu ba" yace "Ai rokon ta zamu yi" tace "Dan Allah ka bari ko nan da sati ne" yace "Deal?" Tace "Sure!" Ya tsaya a hanya yayi mata siyayyar kayan zaki sannan suka wuce gidan. Abbah na kallon Umma da ta buga uban tagumi yace "wallahi Ni gaskiya yau wannan al'amarin ya bani tsoro ba kaɗan ba" Umma tace "Wallahi tun ban ganta ba dama ban so ace tazo kusa da mu ba, amma gaskiya ban ɗauka har abun ya kai haka ba" Abbah yace "Gaskiya ina ga zai yi kyau ace mu san familyn ta" Umma ta masa wani kallo tace "ban gane ba?" Yayi shiru ba tare da ya ce mata komai ba
Tun farkon labarin na gina sa ne akan Malik da Leena, So! Muyi hakuri har zuwa karshen labarin, Nagode.
#jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Leena tayi parking a kofar gidan Rayyan, ta juya tana kallon Malik dake kallon ta tace "Idan ka gama kallon kyan nawa sai mu shiga ko?" ya Harare ta yace "Where's the beauty?" Tayi 'yar dariya tace "Abun da ya kawo ka kenan" ya ɗaga kira ɗaya sama yace "Sure" daga haka ya buɗe motar ya sauka itama ta sauka, bayan sun shiga suka samu Mama na zaune a Parlorn rike da jaririyar Layla, duk gaishe ta suka yi ta amsa musu da fara'a Leena tace "Anty Laylan fah?" Mama tace "Tana ciki" tana rufe baki sai ga Layla ta fito Rayyan na bayan ta, buɗe ido yayi ganin su, Layla ta karasa cikin parlorn tana cewa "Amarya waya ai ke ki fitowa?" Leena tayi dariya tace "Na zo ganin Leena" Layla da rashin fahimta tace "Bangane ba?" Leena na Murmushi tace "Toh ban manta deal ɗin mu ba, your first daughter is named Leena, and you’ll name her after me, just like we agreed" Rayyan ya fara dariya ganin how serious she is, Layla ma dariyan ta fara tace "Sannu da kokari" Mama tace "Ah toh idan har da agreement ba zan yarda na bi bayan rashin gaskiya ba" Leena ta gyada kai tace "Yauwa Mama" Layla tace "Amma haka muka yi?" Ta karasa maganar in funny tongue, Leena ta gyara zama tana kallon Mama tace "Mama kinga haka nan wai sai dai a sawa Nawaf Ya Rayyan, nace son kai ne, toh dole a sa ma 'yar ta na farko Leena shine ta mayar masa Nawaf, Ni kuma Leena nake so ta sa mata" Rayyan yana kallon su yana mamakin har haka suka saba though yasan daga Leena har Layla ba masu saurin sabo bane, Mama tace "Rayyan kana dai ji ko? Leena dai yanzu ta dage sai dai asa sunan ta" Murmushi yayi yace "It's Okay ai Mama, tunda har Layla ta mata Alkawari" Layla tace "Toh sai ki mata huɗu ban ta dauko kyan ki kawai" Mama ta mika wa Malik Babyn ta mike ta wuce ciki daga haka, yana kallon Babyn sannan ya ɗaga kai yana kallon Rayyan da draman su bai bari sun gaisa ba yace "Mun wuni lafiya?" Rayyan ya karasa wajan sa yace "Sorry ashe bamu gaisa ba" ya zauna suka gama gaisa wa, Leena ta daga kai tace "Daddy ina wuni" ya Harare ta yace "Daddy kuma Yau?" Tayi dariya tace "Ba gashi ka zama Baban Leena ba" abun ya basu dariya dukkan su, Layla tace "kin dai nace" tace "Eh naji, Kuma ana sake haifo mana namiji Malik za'a saka masa" Malik ya Kalle ta yaɗan buge ta da kafa ta fake idon Rayyan itama ta rama, bayan zasu tafi har waje Rayyan ya raka su daga nan kuma shima ya wuce dan ya leka office. Mama tace "Dama kun taɓa magana da ita kenan?" Layla tace "A wasa fah muka yi magana Mama, amma kinji ta ɗauka da gaske ne" Mama tace "Ni kuma hakan yayi min daidai, ko dan Khadija, nasan sai bakin ciki ya kusa kashe ta idan taji yarinya an sa mata Leena" Layla tace "Dama wallahi nayi niyyar idan sunan ta zai saka nace wallahi A'a, gwara ya sa Hajiya" Mama tace "Ki kyale ta, akwai ranan da zata yi kuka, kuma wallahi ko da wasa ba zan taɓa yarda ta tako waje na ba, Me kika mata da za'a ce yau wajan kwana uku da haihuwar ki amma taki leko wa, ace har kishiyar ta da surkuwar ta su zo amma banda ita?" Layla tace "Ah toh yanzu dai Mama zaki fara gane cewa Ammi da Hajiya basu da matsala itace dai bai bakin hali da hassada kuwa". Mama tace "ki kwantar da hankalin ki wallahi sai na sata kuka, kuka zan sata bana wasa ba, mu zuba Ni da ita muga wa zai ci riba. Bayan Rayyan ya koma aiki, ganin Malik da yayi sai da jikin sa yayi sanyi, bai san wani irin zuciya ne da mahaifiyar sa ba amma yana addu'an Allah yasa ta janye bakin da ta masa, at least yaga soyayyar Leena a idon sa, and it seems suna zaman su lafiya without any issue. Washe gari da safe Leena na doing the dishes Malik kuma yana soya yam and egg suna aiki ne amma gaba ɗaya hira suke cike da nishaɗi, ya zo zai kwashe last suyan man gyaɗan yayi tsalle da sauri ya ja baya Leena ta ajiye Cup ɗin hannun ta ta juya ta kalle sa ganin har ya ja baya ta fara dariya tace "Allah bamu hakuri yanzu ɗan wannan ne yasa har zaka ja baya?" ya Harare ta yace "Who told you that? I just want to protect you" Leena ta fashe da dariya ta karasa wajan sa ta karɓe serving spoon ɗin tace "Barin kwashe kaje ka shirya it's almost 8" yace "Alright, wifey" daga haka ya wuce ɗakin sa, bayan sunyi breakfast Leena ta raka sa har waje sannan ta koma cikin gidan. Mummy bayan ta isa gidan Rayyan da yaran ta mata biyu ba tare da tayi sallama ba kawai ta buɗe kofar parlorn ta shiga su Niswa na bin ta a baya, Mama dake zaune ga Baby a gefen ta sai Layla duk suka ɗaga kai suna kallon su, Mummy tayi yake tace "Aminiyata" Mama fuskan ta a kame a takaice tace "Sannu" Mummy ta karasa parlorn ta zauna, Layla da Baby su gashe ta ta amsa musu, su Niswan ma gaishe da Mama suka yi, Niswa na kallon Layla a hankali tace "Ina wuni" tace "Lafiya kalau" Mama na kallon Baby tace "Baby tashi ki mika wa Mummy Leenan" Nisreen ta kalli Mummy da sauri, Mummy kuwa gwalo ido tayi tace "Bangane ba ko dai banji me kika ce bane?" Layla ta ɗauke kanta da sauri dan wani dariya ne ya taho mata tasan da gangan Mama tace haka, Mama ta kara maimaita kanta tace "Cewa nayi ta miko miki Leena" Baby dake mika mata Babyn Mama tace "A'a rike tukun nan" ta mayar da kallon ta kan Mama tace "A wani dalilin za'a sa mata Leena? Wato ke Layla har kin koro kan mu shine zaki sa ana ce mata Leena kuma kin san ba lalle nayi na'am da hakan ba" Mama tayi saurin cewa "Na'am da hakan ma kuma kamar yaya? Naga wanda ta haifa 'yar tace sunan da take so a sa mata kenan" Mummy da ranta yayi mugun ɓaci tana magana ne out of control tace "Idan ita haifi 'yar amma ina jika ta ne ko? Sannan ina da iko da uban 'yar ko?" Mama da dama tana cike da ita tace "And so what idan kina da iko da ɗan ki? Yau wajan kwana nawa da haihuwar ta amma sai yau zaki kwashe kafa ki zo, ce miki aka yi yanzun muna bukatar ki ne?" Mummy ta miƙe tace "Naga nan ɗin gidan ɗa nane ko? Kuma sai yadda naso zan yi da shi, sannan baki da ikon zama a ciki Ni kuma ko shekara zan yi bai isa yace na bar masa gida ba" Mama tayi wani murmushi tace "Toh Bismillah zaki iya sa shi ya kore mu ai" Mummy zata kara magana Niswa ta rike ta tace "Please Mummy hakan bai dace ba, calm down please" Mummy ta kwace hannun ta daga haka ta wuce ta fita ba tare da ta sake kallon wani a