x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - AGOLA free pages

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
na cigaba da kokari ina ba zanyi Jss 3 ba ko?" yace "Eh ba zakiyi ba" tana kallon Ammi tace "Toh Ammi kinji ko? Kuma a school ɗin mu ko baka cika ba idan kana kokari su suke maka tsallake" Ammi tace "Haba, ai dole zata ma yi Leena fah kawai sawon kafa ne gare ta kuma fah haka aka mata tsallaken primary 6 yanzu kuma kuce zata kuma yi" Rayyan yace "Toh ai Anty what matters shine ace tana da kokarin balle Leena kuma sai dai ace Alhamdulillah" Daddy yace "bar yarinya tunda bata so karki cuce ta" Leena tace "Wallahi ya Rain ina so naga na gama secondary da sauri" Ammi tace "ke bana son Manyan ce" Sallama aka rafka a bakin Kofa Ammi ta tashi daga kujeran da take ta koma gefe ta zauna Hajiya ta shigo Ammi tace "Dan Allah Hajiya kiyi hakuri yanzu fah nake son shigowa na gaishe ki sai gashi kin shigo kuma" Hajiya tace "A'a, ke kuwa banda abun ki ai mune ya kamata mu shigo mu muki sannu da hanya da kuma ta'aziyya" Ammi na Murmushi ta gaishe ta ta amsa nan Hajiya ta mata kara mata ta'aziyya Hajiya na kallon Leena tace "ba shakka yau Kinga Ammin ki shine ba zaki kulani ba ko" Daddy yayi dariya yace "yanzu kar a shiga tsakanin ku mutun yaji kunya kuma" Leena tace "Dama fa ina jira ki gama magana da Ammi nane fa" Hajiya tace "kiyi ta kanki ke kika sani kuma" Leena ta fara dariya daga haka ta tashi ta fita Rayyan ma ya mike Ledan hannun sa ya mika ma Leena yace "Ki kaiwa Ammi" Ammi tace "Me haka kuma ya Rayyan" yace "Ammi naga yau kika dawo Toh yaushe kuma kikayi girki shine nace barin tsaya na siyan miki kawai" tace "Toh na gode, Allah an fana" yayi ma Daddy sallama sannan ya fita. Washe gari da safe bayan Ammi ta gama shirya Leena tasa mata abinci a lunch box ɗinta sai ta ɗago tana kallon Leena tace "Amma nikam Leena baki cin abinci ne da na tafi naga kina rame min?" "toh bayan kin tafi kin barni Kuma kinsan Mummy ba zata bani ba, Hajiya kuma kullum sai munyi faɗa sometimes I prefer na sha Golden morn, sometimes kuma ya Rain ke siyamin abu" Ammi ta karasa saka mata jakkan ta a baya tace "it's okay Leena, yi sauri ke tafi kafin su riga ki fita su fara mita" daga haka tayi wa Ammi bye ta wuce parking space tana zuwa ta gaishe da driver ya amsa mata da fara'a tana zaune sai gai su Nisreen sun fito suna zuwa suka shige motar. Nisreen na kallon abincin ta daya zuɓe a kasa tana ɗaga kai sai suka haɗa ido da Leena, Leena ta buɗe lunch box ɗinta ta raba abincin into 2 ta bar ɗayan akan desk ɗinta dayan kuma ta tashi ta karasa inda Nisreen take ta mika mata tace "take this, Nisreen"  Nisreen da hawaye ke zuba a fuskan ta ta wanke Leena da mari tace "shine kika zuɓar min da abinci na?" Kowa ya buɗe baki yana kallon Nisreen da mamaki wani teacher ne yazo wuce wa ya tsaya yana kallon su yace "Hey, girls, what's happening here" Nisreen tace "She poured my food on the ground" ta karasa maganar tana pointing ɗin Leena duk matan class ɗinsu suka buɗe baki suna kallon ta da mamaki teacher ɗin su ya buɗe baki zai yi magana sai One of the students said "Uncle, Nisreen is lying. She fell down with food in her hand, and it spilled on the ground" ya juya yana kallon Nisreen da mamaki Basma said, 'And uncle, you know what? Leena was just trying to help Nisreen. She divided her food into two and gave her half, but Nisreen just slapped her and said it was Leena who poured her food" wata tace "this is bad Nisreen" Uncle scolded Nisreen, saying, 'You're lying. What you did was wrong. The food spilled from your hand, not because someone poured it. You should stop behaving like this, okay?" daga haka ya fice a class ɗin Nisreen started crying Leena ta juya tana kallon Basma, All the students started shouting, 'Nisreen, stop lying! Nisreen, stop hating your sister! Nisreen, you're bad!" Leena ta haɗa hannayen biyu tana rokon su tace, it's okay, please stop shouting at my sister. She's good enough." Nisreen ta maso daf da Leena tana kallon cikin idon ta tace "I hate you, Leena" daga haka ta fice ta bar class ɗinsu Basma na kallon Leena tace "Toh me na damuwa?" Leena ta girgiza kanta kawai ta koma kan desk ɗinta ta zuba abincin ta fara ci, can sai ga Nisreen da Niswa sun shigo class ɗin tare Leena kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta Basma tace "Look at her, she called her sister, and she wants to cause trouble" daga haka Basma ta fice da gudu taje kiran teacher ɗin ɗazu Niswa tace "ke Leena uwar me ta Miki zaki kai karanta wajan malamin ku har kisa ƴan ajin ku su fara mata waka" Leena ko ɗago kai bata yi ba cin abincin ta take hankali kwance wata tace "Sister ba haka abun ya faru ba, sistern kice bata da gaskiya at all so don't just judge her" ta harari yarinyar ta mayar da dubanta kan Leena tace "ke dan uwar ki ba zaki kulani ba ina Miki magana kina jina" Leena tace "Excuse me, please. If you're not comfortable speaking English, I'd like to clarify that we're in a school setting, where English is preferred. At home, I can communicate with you in Hausa, but here, let's try to use English, okay? Ƴan ajin suka kwashe da dariya Suna ihu Niswa tace "bura uba!! Har Ni zakiwa rashin kunya?" ta daga hannun ta wanke Leena da mari daidai lokacin da Uncle ɗin yake shigowa class ɗin tare da Basma, zane niswa yayi sannan yayi warning Nisreen, Niswa taci alwashin sai ta rama dukan da aka mata akan Leena da kuma rashin kunya da ta mata har tasa ana mata dariya,


Hey, sis! Please hint the star at the corner.

_By Jiddatul-khayr writes
Chapter 7

Unfortunately Daddy ne yazo ɗaukan su hakan yasa Niswa ta hakura da abin da tayi niyyar yiwa Leena but taci Alwashin sai ta dake ta ko a gida ne, Daddy na parking duk suka sauka kowa ya wuce part ɗin su, Da yamma Leena ta fito a part ɗin Hajiya tana sanye da uniform ɗin Haddan su a jikin ta Hajiya ta fito tace "Ikon Allah, toh fita kikayi?" Leena tace "Hajiya gani fah a bakin kofar ɗakin ki, takalmi nake sawa, kin san yana da wahalan shiga ne" Hajiya ta fito tana mika mata takeaway ɗin hannun ta Leena ta karɓa tana washe baki tace "Laalaa dukka dambun nawa ne? Nagode Hajiya na" Hajiya tace "Yayan ku ne ya tsiya mana" daga haka Hajiya ta wuce ciki abunta Leena na gama saka takalmin ta ta mike kawai taga Niswa tana ni fo ta, taki masa wa ta ci gaba da tsayuwa a wajan tayi kamar tana gyaran takeaway ɗin hannun ta ne, Niswa na karaso ta tace "Shegiya waye a gaba na yanzu?" Leena tayi kamar bata san da mutun a wajan ba ta wanke ta da mari sannan ta hankaɗe ta ta faɗi har takeaway ɗin ya zuɓe a kasa Hajiya ta fito da sauri tana cewa "Uwar ki ta Miki da zaki dake ta Niswa? Ni fah bana son bakin halin kun nan wallahi" Niswa tace "Ai Hajiya ita ta fara kuma Ni ba sa'ar ta bace da zata na min rashin kunya ina kyale ta" Hajiya tace "yanzu ke ɗin ba rashin kunya kika min ba idan haka ne na dake ki mana, uwar ku duk ta shafa muku mugun halin ta wallahi, riyan ne kaɗai yayo hali na da ke Allah na son sa, kuma duk bakin cikin ku akan Lina saboda kun san ta fi ku ne" Niswa ta haɗe rai, Leena ta tashi a kasa tana karkaɗe jikin ta Hajiya ta kalli dambun da ta bata duk ya wase a kasa ta buɗe baki tana bin dambun naman da kallo Leena tace "Do your worst, Niswa. Do whatever suits you. But let's be clear, you're not me, and I'm not you – God forbid. Whatever Allah blesses me with is yours to envy, not collect, kinji?" Niswa na kallon Hajiya tace "Hajiya Kinga tana min rashin kunya ko? Har sunana take kira ba Anty fah?" Hajiya tace "A'a Ni banga komai ba, sannan ai dole ta ɗena kiran ki Anty tunda kin zubar da girma" Niswa ta saya tana huci Leena ta harare ta, Niswa ta kuma hankaɗe ta har sai ta Leena taji ciwo jini ya fara zuba a hancin ta Hajiya tace "Lalle Niswa har Ni zan Miki magana ki kuma hankaɗe ta toh wallahi bari yayan na ku yazo, bar min gida ki wuce can inda kika fito dan ni bana son halin mugunta" Hajiya ta kalli Leena da jini har ya fara fita a hancin ta tace "Na shiga uku, kalli yadda kika fasa mata hanci" Niswa ta juya ta kalle ta sannan ta wuce kamar zata tashi sama, a hanya taci karo da Ya Rayyan amma ko ta kansa bata yi ba ta wuce sa ya ɗan tsaya yana kallon ta sai kuma ya juya zai karasa part ɗin Hajiya ya kuma haɗuwa da Leena da har fuskar ta yayi mugun ja ga hancin ta jini yana zuba ya tsaya yace "Leena" itama bata ko kalle sa ba ta wuce abun ta ya karasa yaga Hajiya tana share dambun naman da ya zuɓe a kasa yace "Sannu da aiki Hajiya" ta kalle sai sai kuma tace "sannu riyan" ta karasa kwashe wa ta kai waist bin ta zuba already har Rayyan ya shiga parlorn ta yana jira ta karaso danna wayar sa ta same sa yana yi ya ɗaga kai ya gaishe ta ta amsa sai kuma tace "Riyan kasan me?" yace "ina jin ki Hajiya" tace "Gaskiya ka jama kannan ka kunne dan sun sa yarinyar nan a gaba haka kawai fah Niswa ta karaso nan ko kunyan ta bata ji ba ta fara dukan ta har sai da taga ta fasa mata hanci sannan ta zubar mata da dambun da ka tsaya mana,  Ni abun da ya dame ni ma shine ko ta saya ta kwashe min Abunda ta zubar min A'a kawai tayi wucewar ta abunta" Rayyan ya kura ma Hajiya ido har ta karasa magana Hajiya ta kalle sa tace "Ji gantalelle, toh me kuma na kura min ido da kayi?" Yace "Hajiya kika ce ita ta fasa mata hanci?" Hajiya tace "toh na maka karyan dana saba" yace "kiyi hakuri ba haka nake nufi ba" daga haka ya mike. Leena na shiga parlorn ta haɗu da Ammi, Ammi tace "lafiya Leena? Me ya same ki? Kuma ya baki tafi Haddan ba?" Leena ta wuce ɗakin ta, ta ajiye hijab ɗinta da har ya ɓaci a kan gado sannan ta wuce toilet Ammi ganin ta shiga ɗakin ta yasa ta tashi ta bi ta har cikin toilet ɗin ta taya ta wanke fuskan ta, mata wanka gaba ɗaya tayi sannan ta kama hannun ta suka fito tana kallon ƴarta da tausayi tace "sune suka ji miki ciwo ko?" Leena tace "Eh Ammi, saboda abinda ya faru ɗazu a school shine yanzu ta dake ni, Hajiya na mata magana amma ta share ta ma" Ammi ta rungume ta tana tausayin ƴar nata tace "Toh bayan a school ɗinma naga ba laifin ki bane ai" kana ganin fuskan Ammi kasan ranta a bace yake Leena tace "Ammi dama kene kike hanani rama abinda suke mun, toh yanzu kam zan fara ramawa saboda hakan ne yasa kullum suke cin zali na" ta karasa maganan tana me fashewa da kuka Ammi ta fara lallashin ta Sallama Rayyan yayi a bakin kofar na su Ammi ta sake ta sannan ta koma parlorn tana me amsa masa sallama sai daya shiga kuma ya fara jin kunyan Ammi yama rasa mema zai ce mata sai yace "Am dama Ammi ina so naga Leena ne" Ammi ta koma ɗaki ta kira Leena har yanzu kana ganin fuskan ta kasan ran Ammi a bace Leena na fitowa Ammi ta wuce ɗakin Leena ta ɗauki uniform ɗin nata ta wuce laundry dan wanke mata, yana kallon Leena yace "Leena tell me everything nasan baki min karya me ya haɗa ki ke dasu Niswa" ta fara narrating masa tun abinda ya faru daga school har zuwa yanzu kana ganin sa kasan ransa yayi mugun ɓaci ya tashi without saying anything to her ya fice a ɗakin part ɗinsu ya wuce Luckily Mummy bata nan ɗakin sa ya wuce ya ɗauko belt ya wuce ɗakin su Niswa yanda ya buɗe kofar da karfi yasa duk suka juya suna kallon sa Niswa tayi saurin cewa "Yaya wallahi karya take maka" wani kallo ya wurga mata key yasa ma kofar yadda ba zasu iya guduwa ba ya zane Niswa yadda ransa ya ke so tana ta ihu tana basa hakuri Nisreen kam ta tsorata iya tsorata sai kuka take ya juya yana kallon ta yace "wato harda ke ko?" ta girgiza masa kai tana basa hakuri yace "kina karama kina munafurci ba" zuba mata belt guda uku yayi yace "sa'an ki ɗaya ke karama ce but next time ki gwada zaki sha mamaki na" kuka take tayi yace kuna jina duk suka gyaɗa masa kai yace "wallahi daga yau ko kallon Banza kuka sake ma Leena wallahi sai na muku abinda ya fi haka" daga haka ya buɗe kofar ya fita ya barshi suna ta kuka zai fita daga gidan yaga gatekeeper na buɗe gate yasan Mummy ce zata shigo da mota da sauri ya buya a bayan ɗakin mai gadi har ta shigo da motar tayi parking yana ji masu gadi na gaishe ta Amma ta share su tayi wucewar ta sannan Rayyan ya sauke ajiyan zuciya ya fito a inda ya ɓuya ya karasa gate ya musu sannu da aiki sannan ya wuce masallacin unguwar yana jira lokacin Magrib ta karasa tunanin yadda yau zasu kaya da Mummy ne kawai yake yi da sauri ya cire wayar sa yasa a DND Qur'an ya ɗauko ya fara karantawa. Mummy da ta gama cika tayi fam sai trying numbern Rayyan take baya tafiya ta kuma kallon ƴaran nata mata tace "wallahi yau sai Rayyan ya zaɓa ko Ni Ko wannan matar, ina har nine Rayyan zai iya dukan ku akan yarinyar dana fi tsana duk duniya, tun dana gwada bana son yarinyar nan kuma shi ya fara son ta" sake dialing number din nasa tayi taga baya shiga ta fita a part ɗin tana huci ta wuce part ɗin Hajiya dan tasan yawanci idan baya dakin sa toh yana dakin Hajiya ne, ta shiga parlorn Hajiya da sallama Hajiya ta amsa tana mamakin yadda taga kalar Mummy, Mummy ta gaishe ta Hajiya ta amsa da fara'ar ta tace Hajiya na ɗauka Rayyan yana nan ne ko dai kin aike sa ne?" Hajiya tace "A'a dai baya nan dan tun ɗazu daya shigo nan kuma sai ya fita to be sake shigowa ba" daga haka tace "sai anjima to" ta tashi ta fice, shigan Mummy part din Hajiya Daddy ya dawo gidan ita kuma saboda ɓacin rai bata ma lura da motan sa a parking space ba, kawai ta wuce part ɗin su Leena ta ban kaɗe kofar parlorn ta tsaya nan bakin kofa Mummy dake kunna burner a parlorn ta ɗaga kai ta kalle ta Mummy tace "Ina Agolar ƴar ta ki take? Wato saboda sunyi faɗa shine ta haɗa karya da gaskiya ta faɗawa yayan su dan ta shiga tsakanin su kamar yadda kika shiga tsakani na da shi ko? to ki haja ma ƴarki kunne dan wallahi ba ita ba harke sai kinyi dana sanin shigowa gidan nan, sannan abu na biyu idan ma lashe min zuciyan ɗa kika yi toh kinyi kaɗan dan yanzu zan ɗau mataki" Sai sannan Ammi ta kalle ta a ranta tana ji wannan lokacin ba zata iya kyale Mummy ba saboda itama ranta ya ɓaci da yadda suka fasawa ƴarta hanci tace "Toh ai idan kin isa da naki ɗan ai naga ba sai kin zo nan kina ɗaɗɗaga jijiyoyin wuya ba tun a ɗaki zaki tanƙwara sa" Mummy tace "Lalle har Ni zaki mayarwa Magana" Mummy ta shige cikin parlorn da zuciya sai kuma tayi turus ganin Daddy a zaune a dining room yana kallonta Daddy yace "A'a karaso mana" ta juya zata fita yace "wai ke meyasa Khadija kwatakwata baki son peace, You don't want peace to reign, Why?" ta juya tayi wuce war ta ko ta kansa bata bi ba ita yanzu damuwar ta ta haɗu da Rayyan ne. Daddy ya juya yana kallon Ammi yace "Hauwa nasan ki da hakuri Please ki kara akan na da kin ji sirbajo na" Murmushi Ammi tayi bata ce komai ba, kiran Magrib da akeyi ne yasa Daddy wuce wa masallaci. Ko da aka idar da Sallah Daddy ya hango Rayyan da hannu ya masa alama da ya zo hakan yasa ya karasa yana tsosa kansa Daddy na kallon sa yace "yau kuma meya faru?" Yayi narrating duk abinda ya sani yace "Daddy idan kana ganin ba haka bane just ask Hajiya a gabanta akayi komai" yace "No wonder Banga Leena ba, it's okay" daga haka yace "tashi mu tafi" yace "Daddy zan saya ma Hajiya abu ne a can bakin hanya daga haka ya tashi ya fita sai yanzu yaji haushin rashin fita da mota da beyi ba amma yanzu ko gigin wasa yasan ba zai iya shiga gidan nan ba har sai Mummy ta huce, ciro wayar sa yayi a Aljihun sa zai kira wani abokin sa to his own surprised yaga missed calls ɗin mummy wajan 18 hamdala yayi da ya sa
End Ads