x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 48 - AGOLA free pages

  • 141001 words
  • 144000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
mu tafi" ta mike ta wuce gaban mirror tana jin fargaban haɗuwa da familyn Farouq. Mamaki ya kusan kashe ta bayan duk bayanan da tasa a nemo mata akan Layla, ta ɗauka Layla na bin maza amma sai duk ace mata ita Layla mostly tana raba dare a club amma tasan mutuncin ta, kuma dagaske tana dating manya dan suna spending mata da zaran sun fara neman ta kuma zata yar da su, hakan yasa Niswa tsanar kan ta akan laifin da ta aikata, yanzu kuma bata san ta yadda zata ɗauki revenge ba.


08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr

Young talented writers association (YOTA)


56......

Alhamdulillah! It's part two of Agola

A year later.....

Wani babban parlor ne da ke ɗauke da tsadaddun furnitures, kyau da tsaruwan parlorn sai ka ɗauka ba a Nigeria yake ba, Babban mata ce wanda ba zata haura 70 years ba ne zaune a wani laulatsan kujera tana tsanye da white glasses sai kuma hannun ta rike da wani littafin amma hankalin ta yana kan Tv, gefen ta wani Babban mutum ne wanda shima ba zai haura 82 years ba, sai wasu mazan da duk suke mid 50s ba, sai wasu mata biyu zaune da wasu mazan, sai kuma jikokin su da suke parlorn su ma, a hankali tsohuwar matar cike da ilimi ta mike tsaye tace "Do I need the details?" duk suka ɗaga kai suna kallon ta, daga haka ta juya ta wuce ɗaya daga cikin ɗakunan dake cikin parlorn, zuciyar ta na kuna. Tana sanye da black Abaya wanda ya sake fito da ainihin white skin ɗinta ta ɗaura black shade akan veil ɗin da tayi rolling, hannun ta na dama na rike da car key ɗin ta sannan da ɗan karamin hand bag ɗin ta ɗayan hannun na ta kuma tana rike da ɗanta mai shekara ɗaya, tayi kiɓa ba kamar yadda take a baya ba, wanda hakan ya sake fito da ainahin kyan ta, She's more famous now than before as she's, tana sauri su tafi mall kafin a fara ruwa dan taga garin da hadari, amma kwatakwata yaki yarda ta ɗauke sa, wai da kansa zai yi tafiya, daga karshe ya ƙwace a hannun ta ya fara tafiyan sa shi kaɗai tace "Okay Nawaf, Should I go and leave you?" sai kuma ya tsaya yana mata dariya, ɗan jim tayi tana kallon sa sai kuma take ganin kamar mahaifinsa ne ke mata dariya a wannan moment ɗin ta kawar da tunanin da sauri a ran ta, sannan ta ɗan duk ta ɗauke sa har sannan dariya yake mata, bayan ta karasa wajan motar ta ta buɗe front seat ta ajiye sa yace "Amma" tayi kissing ɗin sa tace "Yes darling" ta saka masa seat belt Sanna ta rufe ta zaga ɗayan site ɗin ta shiga, ta ciro wayan ta a jakka ta kunna masa cartoon ta mika masa sannan ta tada motar ta bar haraban wajan, bayan ta isa cikin mall ɗin tayi parking, ta ɗauki hand bag ɗin ta sannan ta zaga wajan sa ta buɗe masa yana murnar ta ciro sa, tsala mata ihu yayi wai ta sake sa da kansa zai yi tafiya, saboda gudun karya damu mutane da kuka yasa ta sauke sa, haka nan taji bata numfashi da kyau ga bugun zuciyar ta da ya karu, addu'a kawai ta fara tana bin Nawaf da yayi gaba kamar yasan wajan, "Leena! is that you?" yayi maganan cike da mamakin ganin ta, Cak ta tsaya dan san gaskata abinda kunnuwan ta ke sanar mata, ɗaga kai da zata yi kawai ta sauke idon ta cikin na sa, yana tsaye yayi folding hannayen sa yana mata murmushi, duk da kiɓan da ta kara hakan bai hana sa gane ta ba, Nawaf kamar ya san shi yayi wajan sa da gudu, shima bai yi wata wata ba ya duka ya ɗauke yaron sama yana masa murmushi, ya karasa har inda take tsaye still Nawaf na jikin ta a hankali tace "Muhammad" ya sakar mata murmushi sai kuma yace "Long time? is this your Baby?" ya jera mata tambayoyin while kuma yana wasa da Nawaf tace "Eh, Alhamdulillah" yace "Oops.. I heard that you're divorced, very sorry" ita dai zuwa yanzu ta fara gajjiya da shi ta ɗan kalle sa taga ita yake kallo a takaice tace "Alhamdulillah" sai kuma taji tayi sounding somehow tace "Me ya kawo ka Kaduna?" wayan sa ya fito da shi a aljihun sa yana mika mata yace "Please I need your contacts, ina son muyi magana, please kar ki ce min no Leena, saboda abun da ya faru, i need to explain myself" wafce wayan na sa akayi duk suka juya suna kallon ta, ita tun suna cikin mall ɗin jin ya ambaci 'Leena' hankalin ta ya tashi har ta biyo sa a baya bai sani ba, tun bayan bikin su taji labarin Leena har ta gaji daga wajan sa har wajan su  Nawaal, strictly Muhammad yace "Bani waya na?" ya kare maganar yana haɗe rai, Leena ta sa hannu ta karɓi ɗan ta ba tare da ta sake kallon wani daga cikin su ba, zai kwace wayan matan sa ta ja baya da sauri tace "sai dai ka kashe ni" ya ɗan bi Leena da sauri wanda yake mata magana taki tsaya wa yace "your Instagram handle, please" bata san ya akayi ba kawai tsintar kan ta tayi da ce masa "Leena Abbah (Mighty pen)" ta ɗan dakata sai kuma ta karasa cikin mall ɗin, bayan ta gama tsiyayya taje biyan kudi cashier tace "An biya miki already, Ma" ta sake baki tana kallon ta tace "Ai baku san kayan nawa na ɗeba ba?" tace "just go Ma" a hankali tace "thank you" daga haka ta fita tana mamakin Muhammad, dan har sannan motar da ya taɓa bata take hawa. Bayan tayi parking ta sauka idon ta na kan mutanen gidan da suka taru ta kalli motar da Hajiya take ta furta Alhamdulillah, nan take ta gane Bugatti La voiture ne ta sake kallon su, Hajiya ta daga kai tana kallon Mummy dake dan gefe da su tace "Khadija Kinga abun arziki daya samu 'yar uwar ki ko? Wajan shekara nawa tana fama da motar yara yau kuwa Allah ya sa ta samu nata, duk sofrice ya mana" Ayaan ya fara dariya yace "Surprise ake cewa Hajiya" tace "Eh ɗin" Mummy ta kalli Ammi dake jikin Daddy ta rufe bakin ta da hannayen ta biyu har sannan bata gama fita a mamaki ba, sai kuma ta ɗaga kai ta kalli Daddy da ko sau ɗaya bai kalle ta ba, ta juya fuuu ta wuce hawaye taji suna neman taruwa a idon ta, Hajiya ta taɓe baki tace "Allah ya kyauta" tana kallon Ammi tace "Toh Hauwa, Allah ya sanya Alkhairi ya sa a tsufar lafiya" daga haka ta juya ta wuce, sai sannan Daddy ya jawo Ammi jikin sa yace "What is it? beyi miki bane a canza?" ta ɗan kalli compound ɗin sai kuma ta rungume sa, kawai samun kanta da kuka tayi, nan da nan Daddy ya birkice yana bata hakuri, Mummy bayan shigan ta ɗakin jikin windown ta ta wuce ta ɗaga curtains tana kallon su, duk wannan reactions din Ammi akan idon ta ya faru, ta sake curtains ɗin ta duka nan wajan hawaye na bin kuncin ta dan yau wajan wata biyar kenan bata gane wa Daddy. Farouq ya ajiye spoon ɗin hannun sa yana kallon ta ganin yadda tayi, yace "Niswa baki ce komai ba? Ko ba zaki je bane?" ta girgiza masa kai da sauri tace "A'a, Zanje mana, just that kai na ne yake ciwo Shiyasa nayi shiru" ya mike tsaye yace "Make sure kin sha magana, Allah ya sauwake" daga haka ya bar dinning ɗin, Niswa ta rintse ido, ita ba rashin son zuwa gidan bane bata so, yadda daga Mummyn sa har Na'ila babu mai sake mata fuska ne abun ke kwana mata rai, duk yanzu tsakanin ta da Farouq da sauki sai dai har sannan akwai rashin yarda a tsakanin su, ko da yaushe sai taga yana son bincika wayan ta musamman idan yaga ta kwanta hakan ne ma yasa ta cire passcode ɗin wayan, yayi ta bincike idan yaga ba komai sai ya ajiye mata wayar shi duk a tunanin sa bata san da hakan ba while kallon sa take yi kuma taki gwada masa balle yace dan haka ne ta zama loyal, a hankali ta mike zuwa ɗakin ta ɗan saka kaya. Bayan tayi parking, Nawaf ya dinga tsala ihu saboda ganin Daddy da yayi a compound ɗin zaune ga kuma Ayaan shi ma zaune a gefen sa sai dai Daddy yayi nisa da karanta news da yake a wayan sa, Leena ta masa tsawa "toh ba zan buɗe ka ba" ta karasa ta buɗe sa ta cire seat belt ɗin, Daddy ya ɗaga kai yana kallon su da gudu Nawaf yayi kan Daddy, Daddy ya ɗaga sa yana dariya ya manna masa kiss a forehead ɗin sa yace "Welcome back, jikalle" shi dai dariya kawai yake, Daddy ya ɗauki slice ɗin kankanan gaban sa ya mika masa, Ayaan zai karbe sa ya kankame Daddy, Leena ta sa masu bada Flowers ruwa su kwashe mata kayan dake booth ɗin ta su kai mata ciki, sai kuma ta karasa wajan Daddy ta duka kan kafafun ta ta gaishe sa Daddy ya amsa, Nawaf ya fara kukan kar ta karɓe sa, ta harare sa tace "waya ce zan kula ka ma" Daddy yace "Eh anji dama ba ruwan mu da ke" ta fara dariya ta kalli sabuwar motar dake fake wanda sai ɗaukan ido yake tace "Daddy kayi amarya ne?" yace "na Ammi ne" ta buɗe ido tana rufe bakin ta da hannun sai kuma tayi cikin gidan da gudu, Ammi dake zaune parlorn tana waya Leena ta karasa da dugu taje ta rungume ta tace "Ammi, congratulationssss" Ammi na dariya tayi ending call ɗin tayi hugging 'yar ta back tace "Thank you Sweetheart" Leena ta rike baki tace  "Surprise Daddy ya miki?" ta gyada kai tace "I never expect this coming, wallahi" Leena tace "Kai Daddy ya burgeni, Allah kara masa buɗi" Ammi tace "Amin, ina Nawaf?" tace "Yana gun Daddy, kinsan ba zai damu da ni ba tun daya gan sa ai" wayan ta ne ya fara ringing, kallon Malik ne yasa ta ɗauka ta wuce ɗakin ta Ammi ta bita da kallo. Mummy na kallon Hajiya Amina tace "wallahi yanzu ban san me zan yi ba, lamaruka na duk sun juya, ga kuma wannan shegiyar Layla ina ji da kyar bata gaya ma Rayyan komai ba, dan yanzu baya yarda ko ruwan gidan nan ya sha, ji nake kamar na ɗaura hannu aka nayi ta zunduma ihu, Daddyn su kuma wallahi darajar aure kawai nake ci amma shima yanzu duk ya fita har ka ta, baya son kula ni balle ya shigo har muyi hira irin na sakanin Mata da Miji" kawarta Amina ta sauke ajiyan zuciya tace "dole ki fara tackling issues ɗin nan kafin ki na ji kina gani zaki kwan ciki, firstly dole ki sa Rayyan ya kara aure ko dan saboda abu guda biyu, matar kuma ya zama na cewa Leena ce" Mummy ta dinga kallon ta sai kuma tace "Eh nima ina tunanin hakan, amma Meyasa sai Leena?" tayi 'yar dariya tace "dadi na dake saurin ruɗewa ga rashin forecasting, toh saboda idan har ya auri Leena kinga dole zaki ɓata tsakanin su, babu macan da za'a mata kishiya tace bata ji zafin ba, ki sa ya auri Leena ko saboda ki haɗa faɗa tsakanin su, na biyu kuma Kinga Layla zata ɗauki Ammi karamar mutum sannan a ruwan sanyi kin rama rashin kunyar da take miki" Mummy tace "Ba zan iya yarda Rayyan yayi rayuwar aure da Leena ba ne, ba zan iya ba" tace "Dama daga baya zaki sa ya tsake ta a karo na biyu, Kinga sai a fara irga mata aure, ba zaki bari auren yayi shekara ba, Kinga duk wanda ya zo da niyyar auren ta zai ji labarin auren ta na farko ana ranan ɗaura aure aka fasa, sannan bayan tayi aure kuma ba tayi shekara ba aka sake ta, auren ta na uku ma shima bai yi shekara ba aka sake ta toh Kinga za'a fara gudun auren ta, yadda tayi suna a media sai dai ta kare a can" Mummy ta numfasa tace "Inaga hakan zan yi, amma ya sauran kuma zan ɓullo musu? Ga Nisreen duk wanda yazo neman ta sai ya gudu daga baya, ga Niswa dangin miji sun sako ta gaba, gashi har yanzu ko ɓari bata taɓa yi ba" ta kare maganar tana tagumi, tace "ki kwantar da hankalin ki, komai zai dawo daidai kwanan nan". Jin karan notifications da suke shigo wayan ta yasa tace "Hey, Darling! barin yi replying messages na baka wayan ko?" kuka zai fara mata tace "Haba Nawaf, baka son Small Daddy ya kai ka kallon horse ne" sai ya sake mata yana dariya, tayi kissing ɗin sa tace "Amma loves you" bayan ta gaba replying messages ɗin Whatsapp sai ta shiga Instagram duk da dai ita ba ta replying mutane dan sai ta iya receiving more than 200new messages per day, Message ɗin Muhammad ne ya shigo last ta tsaya kallo dan one time ta gane shi saboda picture ɗin sa dake DP ta dinga kallon kamar ba zata kula sa ba sai kawai ta shiga page ɗin sa a hankali tayi typing 'waalaikumus Salaam' tayi replying din sa back duk da tarin messages ɗin da ya mata, tana turawa sai kuma ta kashe datan ta dan bata san meyasa tayi replying ɗin sa ba. Tunda suka shiga compound ɗin zuciyar ta ke bugawa, bayan Farouq yayi parking ya juya yana kallon mood ɗinta hannun ta ya kamo ta kalle sa ya sakar mata murmushi yace "be you, please" ta gyaɗa masa kai daga haka duk suka sauka, Farouq ya tsaya amsa call hakan yasa Niswa shiga parlorn da sallama, ba kowa sai Na'ila dake kwance akan cushion tana dannan wayan ta ko sau ɗaya bata ɗago ba balle ta amsa sallamar ko ta gaishe da matar Yayan ta, har Niswa ta karasa cikin parlorn ta zauna bata ɗago ba, Farouq ya shiga da sallama, ta janye wayan daga fuskar ta ta mike tsaye tace "Hey, Brother!" fuskar sa babu yabo ba fallasa yace "kun gaisa?" ta ɗan kalli side ɗin Niswa sannan ta taɓe baki tace "Sure" daga haka ta kama hanyar stairs, Niswa scene ɗin ta da Layla ne kawai ya fado mata exactly yadda ta taɓa yi wa Layla da ta zo gidan su, amma ita Layla bata ɗaukan raini, ita kuma bata isa tace zata ma Na'ila ba, hawaye taji ya cika mata ido ta fara kokarin mayar da shi, ba'a ɗau lokaci ba sai ga Mummy sauko wa bayan ta shiga parlorn tana kallon Farouq da yake danna wayan sa tace "baka san ɗaki na bane da ba zaka haura ba sai ka sa na sauko?" yayi murmushi yace "Toh ai bani kaɗai bane ga Niswa ma" ta taɓe baki Niswa ta gaishe ta a takaice ta amsa, Daddy ne ya shigo parlorn yana kallon su yace "Ashe yau baki muke da su a gidan" Farouq yace "Allah Daddy idan baka daina kiran mu da baki ba zamu tare maka a gida" Daddy yayi dariya, Mummy ta taɓe baki daga haka ta mike ta wuce sama abun ta, Niswa ta zame akan kujera tace "Daddy ina wuni" yace "Lafiya kalau, ya wajan su Baban ki?" tace "Lafiyan su klau" yace "Da fatan ba wani matsala ko?" ta gyada masa kai tace "Babu" yace "Toh Masha Allah" daga haka ya wuce ɗakin sa, Farouq yabi Mummy a baya, ji tayi an buɗe bata kofa ta tsaya kallon sa har ya karasa ciki yace "Mummy me yasa kike haka ne dan Allah?" tace "Nayi ɗin, sai ka dake ni idan abun bai maka daɗi ba" yace "Haba mana, abu almost a year amma kullum abu ɗaya" tace "Muddun kace ba zaka kara aure ba toh wallahi ba zata taɓa samun fukata ba" Farouq ya tsaya kallon ta sai kuma yace "It's Okay, idan nayi nisa da gida shikenan 70ai" daga haka ya juya ya sauka kasa, Niswa har sannan ita kadai ce zaune yana kallon ta yace "tashi mu tafi" ba musu ta miƙe tabi bayan sa. Hoton ta dake screen wallpaper ɗin sa yake Kallo, ya rintse idon sa saboda zafin da zuciyar sa ke masa, a hankali ya buɗe su ya cigaba da kallon hoton yana jin ba zai iya cigaba da harming kan sa ba, ba shiri ya mike tsaye dan neman wani Alternative.

Is like kun fara loosing interest ko?🥹


Jiddatul-khayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧



Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Young talented writers association (YOTA)


Chapter 57

Ta fito tana sanye da blue Abaya, kallon Nawaf dake kwance jikin Ammi tayi tace "Nawaf, I'm going to see uncle, do you want to come with me?" da sauri ya tashi a jikin Ammi yana kallon Leena yace "Yes Amma!" ya karasa wajan ta da gudu, tana dariya ta rike hannunsa, tana kallon Ammi tace "Ammi sai na shigo" tace "Okay" daga haka suka fita tana rike da hannun Nawaf tun basu karasa compound ɗin ba Nawaf ya cire hannun sa a nata ganin Abban sa da yayi da gudu ya tafi wajan sa, shima da tun fitowar su idon sa na kan su, fuskar sa ɗauke da murmushi ya karasa ya daga Nawaf sama yana dariya shima Nawaf ɗin dariya yake yi, bayan Leena ta karasa ta taɓe baki tace "toh ko na koma ne tunda naga kamar wajan Nawaf ka zo?" ya ɗan tsakaita dariyar sa yace "Sorry, Madam" ta wuce ta zauna kan dadduman da aka shimfiɗa masa ta fara danna wayan ta, Malik ya juya ya bi bayan ta yace "wallahi Abaya ba karamin kyau yake miki ba, idan nayi kuɗi dole kayan sakawan kanwa ta ya koma Abaya" ta ɗanyi
End Ads