x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 13 - AGOLA free pages

  • 36001 words
  • 39000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
ce" daidai nan driver yayi parking Leena ta buɗe ta sauka Zahra ma ta sauka Leena na kallon sa tace "Mungode" daga haka suka kama hanyar shiga school. Zahra irin yaran nan ne wanda suka taso a Ghetto area, sai dai ita tana da tarbiyya kuma ga ilimi shiyasa wani ya dauki nawin karatun ta ganin kokarin ta, ɗan karamin gida suke rayuwa a ciki wanda kana gani kasan suna fama ne da kansu, da kafin Leena ta koma makarantar da take da sassafe take fita saboda da kafa take tafiya kuma sai takai wajan hour daya da rabi, amma haduwa da Leena sai kawai take shigowa anguwan su wanda bata fin 20minutes a hanya zata karaso, sai su tafi a motar gidan su Leena ko kuma Ammi ta basu kuɗin taxi. Bayan sun karasa bakin hall Leena tace "ai banso da kika biye ta ba Zahra" Zahra tace "Dalla shirun da kike yi ne yasa suka raina ki, dama ina da jin haushin uwar ta amma yanzu na sauke akan ƴarta, baki ga da taga da gaske nake sai ta sassauta murya wai enough". Bayan sun karasa gida Nisreen ta fice a motar cikin zuciya ko rufe kofar motar bata yi ba, ta karasa cikin gidan kamar zata tashi sama hoping ta samu Mummy unfortunately bata nan. Da yamma Ammi tana dakin Hajiya ta kai mata tuwon semovita da miyan shuwaka da tace Ammi ta girka mata Hajiya tana ta godiya tace "Ai ke baki gaji tsiya ba, Nagode Hauwa, Allah sa abinda kike min ƴaƴanki su miki fiye da shi" Ammi na Murmushi tace "Amin Hajiya" Hajiya tace "Allah kuma ya tabbatar mana da Alkhairi akan wannan yaron da yake son Leena Baban su yace min kaff cikin Habuja wannan unguwar da yaron suke yace min sunfi kuɗi, ina mata fatan taje can ta huta da abinda wancar matar take mata amma sai naga kamar Leena bata so" Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba bayan murmushi da take yi sai can tace "toh Hajiya barin tafi" daga haka ta fito, a compound ɗin taji Mummy nama Driver ihu kamar ɗanta tace "toh wallahi daga yau idan ka kuskura ka sake daukar Agolan nan a motar nan a bakin aikin ka" Ammi ta taɓe baki ta wuce abinta, tana shiga taga Leena, Leena dake kan dinning tana cin Abinci ta gaishe da Ammi Ammi ta amsa tace "ke kuma yau me ya haɗa ki da Mummy?" Leena tace "Bayan mari na da tayi min da safe ban san komai ba" tace "toh naga tana hana driver ɗaukan ki ne" dai sannan tace "Ohh, wai fa ɗazu dan ya dauke mu zai kaimu makaranta shine Nisreen ta fara masifa ina ga shine ta fada mata" Ammi tace "Duk abinda zai faru kiyi kamar baki gani ba kinji?" Leena ta gƴada kai kawai. Da Daddare Mummy tayi hadaddiyar abinci ya sha nama ga kuma yoghurt me sanyi sai fruits da kanta ta ɗauka ta wuce part ɗin Hajiya ta shiga da sallama Hajiya da ta idar da sallar Magrib tana lazimin ta karasa cikin parlorn tana kallon Mummy da mamaki Mummy da fara'ar ta ta sauka akan kujeran ta zauna kasa tana gaishe da Hajiya, Hajiya ta amsa duk mamaki ya cika ta Mummy tace "ga abinci da kaina na girka Miki wannan kuma fruits ne" Hajiya tace "Ayyah toh na gode kwarai" Mummy ta tashi tana murmushi tace "sai da safe Hajiya" daga haka ta fita, Hajiya ta rike haba tana mamakin Mummy, toh wani makircin take son haɗawa? tun da ta shigo ɗa safe ta gaishe ta tace anya? Toh ga yanzu ma. Leena na zaune tana koyawa Ayaan karatu wayan ta yayi ringing ta duba taga Uncle Sultan ne tayi picking yace "ki fito ina kofar gida" tace "toh" tana kashewa ta tashi tana kallon Ammi dake can tana karatun Alkur'ani tace "Ammi uncle Sultan ne ya kirani yana waje wai na ɗan fito" kai kawai Ammi ta gyaɗa mata, ta kama hannun Ayaan suka fita tare, tana fita taga Sultan ke driving gefen sa kuma Sadeeq ta karasa inda Suke ta gaishe sa ya amsa mata da fara'a, yace "iyyee, our young celebrity, yanzu ganin ki ma sai an yanka ticket" tana dariya tace "Kai Uncle Sultan" ta kalli Sadeeq da ko kallon ta sau ɗaya be yi ba tace "Ina wuni, Uncle sadeeq" yayi banza da ita, Sultan ya ɗan kalle sa sai kuma ya buɗe motar ya sauka, yana wasa da Ayaan, ya buɗe back seat ya fito da wani Leda yace "inji Mami" ta karɓa tana Godiya yace "tace ai yanzu kin daina zuwa" tana murmushi tace "wallahi exams ne shiyasa" yace "it's Okayy, ki gaida Ammi" tace "toh" ta saci kallon Sadeeq taga har sannan wayan sa yake danna wa, daga haka suka wuce cikin gidan...

[5/28, 7:39 PM] Jiddatulkhayr writes: *AGOLA (Behind the palace walls)*




15.......
Sai da safe tama Ammi tun kafin Daddy ya shigo ta wuce ɗakin ta, karatu ta fara sai ga kiran ya shigo wayan ta gani tayi kamar tasan numbern ta ɗauka ta kai kunne sai tayi shiru, wanda ya kira ta ɗinma shiru yayi, sai sannan tace "Assalamu Alaikum, yace "Uhm Wa'alaikumus salaam" muryan sadeeq taji sai da ta kusan fashewa da dariya wato shi ya kira ta amma yayi magana shine ba zaiyi ba well, tace "ina wuni" yace "Lafiya! Ya studies?" tace "Alhamdulillah" yace "Hope you're doing well and getting the best out of it" tace "Sure, In shaa Allah!" Sai kuma duk sukayi shiru ji tayi kawai yace "you looks so pale, what's wrong with you?" tace "I look so pale ? How did you know! you didn't even look at me!" Sadeeq take kwance sai da ya buɗe ido ya tashi ya zauna yana mamakin jin amsar da ta bashi bai san sanda yayi murmushi ba har Leena na juyo sa, yace "it's Okayy, tho" tace "i think exams stress ne" daga haka yace "good night, sweet dreams" Leena tace "thank you" daga haka ya katse kira tana mamakin shi toh yaushe ya zama haka, daga haka ta kashe wayan ta tayi addu'a kawai ta kwanta. Washe gari ko da tayi sallahn asuba ta karasa kitchen ta ɗaura breakfast saboda exams ɗinta na safe ne tana cikin yi Ammi ta shigo kitchen ɗin Leena ta gaishe ta Ammi tace "da Safe zaku fita kenan?" Leena tace "Eh, shiyasa ai ko bacci ban koma ba" Ammi tace "barin je na shirya Ayaan sai ku ajiye sa sannan ku wuce" tace "toh" daga haka Ammi ta fita a kitchen ɗin Leena kuma ta cigaba da soya doyan da take yi tana gamawa ta ta fito da breakfast ɗin kan dinning ta kira Ayaan suka yi breakfast tare sai ga Ammi ta fito da lunch box ɗin Ayaan a hannun ta tana mika wa Leena, Sallaman Zahra suka ji Ammi tace "shigo mana Zahra" ta karasa cikin parlorn tana gaida Ammi, Ammi ta amsa mata tana tambayar ta ya exams Leena ta ɗauki plate ta zuba mata doyan da ta soya ta ɗauki wani cup ta zuba mata tea sannan ta karasa cikin parlorn itama da ta ajiye a gaban ta tace "Nasan bakiyi breakfast ba toh kiyi kafin mu tafi" Zahra na Murmushi tace "ke Alhamdulillah a kosher nake" Leena ta harare ta tace "ashe yau ba zamu tafi exams ɗin ba kuwa"  bayan Zahra ta gama tana rike da hannun Ayaan Leena ta fito rike da jakkan sa suka ma Ammi sai sun dawo Ayan yace "Ammi karki manta ki dafa mana macaroni yau" Ammi na dariya tace "toh shikenan My Dad" yana dariyar suka fita a compound suka haɗu da Mummy ta zata tafi aiki Zahra ta ɗauke kai kamar bata ganta ba sai ma Leena da ta gaishe ta tayi banza da ita ta wuce su, ta shiga motar ta ta fice daga gidan suna karasa bakin gate driver da zuwan sa kenan daga kai Nisreen school yace "Leena ku shigo na kaiku kafin na shigar da motar cikin gida" godiya suka yi duk suka shiga. Bayan Leena ta dawo a makarantar tayi lunch sannan ta tafi sashen Hajiya tana shiga taga Niswa na zaune tana daddan na waya ta karasa ciki without saying 'Hey' to her tana kallon Hajiya ta gaishe ta Hajiya tace "Da safe naji ki shiru baki shigo ba sai Ammin ki take ce min wai ai kin tafi jarabawar" Leena tace "Eh shiyasa yanzu na shigo na gaishe ki" daga haka ta juya tace "toh sai anjima Hajiya". Ɗaukan wayan ta dake ringing tayi bayan ta ɗauka ta gaishe sa, suka jima suna hira wanda rabin sa shike magana ita sai dai ta amsa masa da "um ko uh'um" yace "Baby, are you listening to me? I need your attention, please!" Haka nan taji gaban ta ya faɗin tace "Ehh, i can hear you! yace "Good! Baby kin san me? My dad will be traveling to Egypt for a few weeks. I don't want to wait, so I'd like my dad to visit your parents and ask for your hand in marriage, for me, probably this coming weekend" Leena taji wani bugun zuciya ta gagara magana tayi shiru sai da yace "Baby?" tace"um" yace "kinji?" tace "Eh!" yace "so now, sai ki sanar da Ammi kinji?" tace "Toh" yace "barin barki haka, I'm heading to the gym now. Take care of yourself, my sweetheart. Bye" tace "In shaa Allah" ya katse kiran sai da Leena ta ɗauki some seconds kafin ta cire wayan a kunnen ta She's been frozen in place like a statue kiran sallahn Asr da akeyi yasa ta tashi duk jikin ta a sanyaye ita meyasa ma tun farko bata yi blocking dinsa ba ne, bayan ta idar da Sallah ta wuce ɗakin Ammi ganin bata nan ta wuce kitchen ta samu tana abincin dare wa Daddy, Ammi ta juya tana kallon ta ganin yanayin ta yasa tace "Leena lafiya?" ta girgiza kai Ammi tace "What's wrong?" tace "Wai Muhammad ne zai Turo this weekend" Ammi tace "Ma shaa Allah" Leena na kallon Ammi kamar zata yi kuka Ammi ta cigaba da aikin ta kamar bata san tana yi ba can ta juya tana kallon ta tace "Kinga tashi ki fice min anan tunda ba aiki zaki taya ni ba" Leena ta tashi ta fara tattara cikin kitchen ɗin, tana gama tattarewa ta koma ɗakin ta kiran Zahra tayi, Zahra na picking Leena tace "Zahra zaki iya zuwa gidan mu yanzu please?' Zahra tayi shiru sai kuma tace "Lafiya Leena?" Leena tace "Eh lafiya kawai magana nake so muyi" Zahra tace "kuma ba zai yu muyi ta waya bane?" Leena tace "ba zai yu ba gaskiya" Zahra tace "toh dai yanzu Umman mu bata gida kuma abinci dare zan ɗaura mana, idan har ba damuwa why not ki bari gobe da safe tunda bamu da exams sai na zo" Leena tace "it's Okay, Allah kaimu, thank you Zahra" daga haka ta kashe, Ammi ne ta shigo ɗakin nata ta zauna a bakin gadon ta tace "Ina jin ki?" tace "Ammi kina jin me?" Ammi ta harare ta tace "zaki min bayani ya kukayi ko zaki tsaya kina tambaya ta" tayi shiru sai kuma tace "wai Abban sa ne zai yi tafiya shine wai this coming weekend zai Turo" Ammi tace "sai kika ce masa me? tace "toh kawai nace masa" Ammi tace "saura ki nuna masa wani hali kuma" tace "Ammi Ni gaskiya bana so, I'm still teen, kuma ma ya zanyi da karatu na?" Ammi ta riko hannun ta tace "Leena" sai sannan ta ɗaga kai tana kallon Ammi, Ammi ta ɗaura da cewa "Leena ki dena tunanin nan Please, karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu, makaranta kuma ai za'ayi da shi zaki cigaba beside ai naga shima ba zai hana ki ba ganin yanayin sa, Leena buri na ki samu ki bar gidan nan ko dan saboda Mummy, yanzu ki kalla yadda kika shaku da Rayyan lokaci ɗaya ya daina Miki magana kuma ina da tabbacin saboda kar yace yana son ki ne ta raba ku, yanzu ko Ni Rayyan ya daina shigowa nan kamar yadda yake yi, Amma yanzu idan har kika samu kikayi aure Nima hankali na ze fi kwanciya kuma kin gwada mata Allah ke bayarwa ba mutun ba" Leena tayi shiru tana kallon one direction Ammi ta cigaba tace "Leena ki taimake Ni ki cika min wannan burina dan Allah" sai sannan Leena ta ɗaga kai tana kallon Ammi nan da nan jikin ta yayi sanyi ba zata iya cewa A'a ba saboda Ammi she's her everything tace "toh Ammi dan Allah ki daina damuwa" tace "ban damu ba Leena"  Leena tace "Ammi zanyi ne saboda faranta Miki" Ammi ta shafa kanta tace "Allah Miki Albarka, in shaa Allah ba zakiyi nadaman yi min biyayyan da kikayi ba" daga haka ta tashi ta fita. Bayan Daddy ya dawo daga sallahn Magrib Ammi na kallon sa tace "Nikam baka kuma ce min komai game da binciken da kasa a maka a kan wannan yaron ba?" yace "Oh wallahi aiki yawa yake min yanzu shiyasa" tace "Ayyah" yace "kinsan anyi min bin cike akan yaron nan, shaida me kyau ake gaya min, and abin mamaki kin san cewa yaron nan ɗan Minista ne?" Ammi ta zaro ido tace "Minista kuma?" Yace "Eh fah ɗan Arabi ne fah, Minister of petroleum resources ne fa" Ammi ta zara ido tana mamaki tace "toh kasan ɗazu yace ma Leena weekend ɗinne zai Turo iyayen sa?" yace "Haba? Toh Allah tabbatar mana da Alkhairi, Allah kaimu" tace "Amin ya Rabbi". Mummy ce ta shiga parlorn Hajiya da sallama a bakin ta Hajiya ta fito tana mamakin sauyawan Mummy na kwana biyun nan Hajiya ta karasa cikin parlorn tana kallon ta kallon ta Mummy tayi kasa da murya tace "Hajiya ina wuni" Hajiya tace "Mun wuni lafiya?" tace "Lafiya klau Hajiya" sai ta ajiye wa Hajiya kulan pepper chicken tace "gashi Hajiya ba yawa, tun ɗazu naso Miki amma ban samu dama ba, saboda na gaji" Hajiya ta karɓa tana "Godiya" Mummy ta tashi tace "toh sai da safe" Hajiya tace "mu kwana lafiya". Washe gari Thursday, Zahra ce ta shigo gidan a compound ta haɗu da Rayyan ta gaishe shi sannan ta wuce sallama tayi Ammi tace shigo mana Zahra, Zahra ta shigo ta gaishe da Ammi, Ammi ta amsa tace "kar dai akwai wani abu da zaku yi yau" Zahra na Murmushi tace "A'a Ammi, kawai nazo ne zamu ɗan yi karatu" Ammi tace "ki shiga tana ciki tana baccin asara" Zahra na Murmushi tace "toh" daga haka ta wuce dakin Leena, Zahra ta janye duvet ɗin da ke jikin ta Leena ta gyara kwanciyar ta, Zahra tace "ko na tafi ne? Sai sannan Leena ta buɗe ido ganin Zahra yasa ta jenye duvet ɗin jikin ta tace "Ashe kin zo?" Zahra tace "Ban sani ba" Leena ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskar ta ta fito da murmushi tana kallon Zahra sai kuma ta fashe da dariya tace "toh me hakan kuma?" Zahra ta koma ta zauna kan gadon ta tace "kar de baki yi breakfast ba ma?" Leena ta gƴada kai tace "Wallahi ban yi ba" daga haka Leena ta wuce taje ta ɗibo musu breakfast ta shigo da shi Zahra ta cire hijabin ta ta ninke Leena tace "sauko mu ci" Zahra tace "ke sai da nayi breakfast na fito" Leena ta harare ta sannan Zahra ta sauko bayan sun kama breakfast Zahra na kallon Leena tace "Leena kiran me kika min jiya?" Leena tace "Wallahi ina cikin damuwa kin san me" Zahra ta girgiza kai tace "Inaji" Leena tace "wallahi Muhammad ne wai zai turo, Ni kuma bana son yin aure yanzu Zahra, gashi Ammi tana son nayi, I'm so disturb, na rasa ya zanyi" Zahra tayi dariya me isar ta Leena tace "ke dalla me haka kuma?" Zahra tace "Ni wallahi na gama ɗauka wani abu ne shiyasa ko breakfast na kasa yi nace barin zo, jiya kuma haka nayi ta bin abun a rai" Leena tace "Dalla ni yanzu ki bar wannan a gefe idan kece a shoe ɗina ya zakiyi?" tace "well! Idan nice da farko wallahi zan yarda, toh me ma yasa bazan yarda ba? Ga mate ɗinmu daya muna gama paper za suyi, kuma ace Ammi naso toh meyasa ba zaki yarda ba" Leena tayi shiru tana kallon waje daya sai kuma tace "Amma ke baki gani nayi karama Zahra!" Zahra tayi dariya tace "Well, tho Allah kawo min wani yanzu kiga ko bazan yi ba" Leena tace "Amma fah Ni wallahi bana son sa, kuma na rasa sanin dalilin, kuma kar kice be damu da Ni ba, wallahi kullum sai ya kira" Zahra tace "toh idan zakayi hankali gwara kiyi, dan idan nice ba abinda zai sa nace A'a, kiga kalar rayuwan da kike yi a gidan nan, kwata kwata matan can bata kaunan ki" tare suka wuni sai can yamma Zahra ta tafi. Da Daddare Mummy ta karasa bangaren Hajiya ta shiga lokacin Leena kadai ke kwance a kan cushion Hajiya kuma tana ciki tana sallah Mummy tace "ke dalla tashi ki ba mutane waje" Leena da bacci ya fara daukar ta ta tashi tana kallon ta sai kuma tace "ina wuni Mummy" tace "Dan uwarki kika sake kallona saina tsole Miki ido" Leena ta sauke idon ta kasa ta ta fice a parlorn, Hajiya ta fito taga Mummy zaune a kasan carpet ta karasa cikin parlorn tana kallon ta Mummy tana murmushi tace "sannu Hajiya" Hajiya ta zauna tana tambayar ta ya aiki sai can tace "Hajiya dama wata magana nazo da shi" Hajiya a ranta tace da walaki sannan tace "Allah sa lafiya" Mummy tace "Eh lafiya dai" Hajiya tace "ina jinki toh" Mummy ta kashe murya tace "Hajiya dama nazo nan ne saboda wata magana kuma Nasan zaki fahimce Ni, sannan ki goya min baya kuma ke kaɗai ce zaki iya ma Baban su magana
End Ads