x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 54 - AGOLA free pages

  • 159001 words
  • 162000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
ta bi ta da kallo, Nawaf dake jikin Ammi ya taso da sauri zai bi ta, ta girgiza masa kai tace "yanzu zan dawo ba fita zan yi ba" kuka zai sa mata Ammi tace "Toh ɗauke sa mana" ta ɗauke sa, tana fita ta hango sa zaune a kan wani plastic chair a car park, ta karasa wajan ya karɓe Nawaf, ta gaishe sa, instead ya amsa sai taji ya jefa mata tambaya "Me yasa ki kuka ɗazu?" ta ɗaga kai ta ɗan kalle sa sai kuma taga shima ita yake kallo, ta sauke kanta kasa tace "Babu komai" yayi shiru yana kallon ta da mamaki, ta ɗan daga kai ta kalli Irin kallon da yake mata yasa tace "Yaya ka yarda babu komai fa" ya ɗan mata tsawa yace "Babu komai shine zaki fito da gudu kina kuka?" a hankali tace "A'a" yace "Toh mene?" Ta ɗan kalli Nawaf dake hannun sa sai kuma tace "Baban Nawaf ne yazo" ta sauke ajiyar zuciya dan maganar idan ta tuna na kona mata rai, a hankali ta cigaba "wai idan har zan yi aure toh zai karbe Nawaf a waje na" Rayyan ya ɓata rai yace "Bangane ba? Ya karɓe sa kamar yaya?" Tace "Ya ce wai ko na hakura da auren saboda Nawaf sannan na koma gidan sa ko kuma nayi auren amma babu yadda za'ayi ya bar mini Nawaf dole zai karɓe sa" Rayyan da ransa ya gama ɓaci yace "Saboda shi ya haife ki da zai baki option cikin gadara, a condition ɗin da ya rabu da ke da ba dan Allah ya takaita ba da anything can happen to you, kuma tun da bai san da zai mayar da ke ba sai yanzu da yaji zaki yi aure? Ai na ma ya samu wannan livern ne?" Yayi shiru sabar yadda yake boiling inside, ya Kalle ta yace "Sorry banji opinion ɗin ki ba, kina son koma wa gidan na sa ne?" tayi shiru kamar mai nazari sai kuma ta girgiza masa kai tace "Just that ina tsoron ya raba ni da ɗa na ne" yace "Better, da kince kina son komawar ki gidan, dana wanwanke ki da mari, sannan kuma bashi da right ɗin karɓe miki ɗa, ko Islamically ne ba'a yarda ya karɓe sa ba har sai mijin da zai aure ki yace ba zai zauna gaban ki ba, which is hardly Malik yace haka, shi da Nawaf kuma sai nan da 18 years kamar yadda yake a shari'a so calm down ki cire komai a rai balle ya dame ki, ko da wasa yazo karɓan sa sai inda karfi na ya kare i promise you" taji hawaye ya gangaro mata ta share tace "Thank you Yaya" yace "Ammi ta sani?" Ta girgiza masa kai yace "Don't let her know, please" tace "Toh" ya mike yana mika mata Nawaf, dan ba karamin haushin Sadeeq yake ji ba, ta karɓe sa tace "Ka gaishe min da Anty Layla" kai kawai ya gƴaɗa mata daga haka ya wuce, ita ma ta mike ta wuce ciki. Niswa nata sheshshekan kukan, Mummy da tayi shiru tana sauraron ta can tace "Toh tunda shegiyar uwar sa ta nace sai anyi aure tunda shi baya so da sauki, kawai ki kwantar da hankalin ki" Niswa tace "Mummy baki ji me nace bane? Cewa nayi fa duk haukan da yayi ta yi baya son auren wallahi yanzu har kiran ta yake a waya da kan sa, da har hankali na ya fara kwanciya ganin yarinyar ma bata son sa, shima baya son ta amma yanzu kuma ya fara waya da ita, kuma baya yadda yayi receiving call ɗin ta a gaba na sai Kiga ya fita" Mummy tayi wani ashar ɗin tace "Yanzu wani abun suka masa dan ya so ta, tunda sun nace kika ce, toh ga irin ta nan zan yi abu kince baki so" Niswa tace "Mummy dana masa magana cewa yayi at least yanzu zai auri wacca zata ba wa 'ya'yan sa tarbiyya" Mummy tayi shiru, Niswa ta sake fashewa da kuka tace "Mummy duk wallahi Layla ce ta cuce ni, tun farko dama bata min ba, bata bin ba kwatakwata kika na ce Mummy" Mummy tace "bari na gama da project ɗin shegiyar nan Leena, idan na gama dole Rayyan yayi aure ko na tsine masa, sannan idan Farouq ɗin ba zai iya zama da ke ba kawai ya sake ki" Niswa tayi shiru tana jin mahaifiyar ta, jin motsin kamar ya dawo tace "Mummy sai da safe, i think ya dawo" daga haka ta kashe kiran, Mummy ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza wa, can tayi wani murmushi da kuma takaicin kawo Layla cikin ahalin ta. Har Leena zata kwanta haka nan taji ba zata iya bacci ba tare da ta kira sa ba kamar yadda Zahra ta faɗa mata, hakan yasa ta ɗauki wayan ta tayi dialing numbern sa har ya katse bai ɗauka ba, ta sake kira for the second time, har zai katse sannan ya daga, a hankali tace "Shi ne ba zaka kira Ni ba? At least abun da ya faru tambaya ta ya kamata kayi ba wai shiru ba" tana kare maganar ta fashe da kuka, Malik dake gidan wani Friend dinsa dan yadda aka dan taru a gidan na su, har ya kwanta amma gaba ɗaya tunanin sa baya jikin sai sai ga kiran ta. Bai san sanda ya mike zaune da sauri ba yace "SubhanAllah! Kuka kuma Leena, dan Allah kiyi hakuri kiyi shiru" ta cigaba da kukan ta daga karshe ta katse kiran, a ruɗe Malik ya mike dan bai taɓa ɗauka abun zai dame ta har haka ba, ba tare da ya jira abokin na sa ya shigo ba ya ɗauki makullin motar sa sannan ya fita da ɗan saurin sa. Leena ta gama shan kukan ta, ta kalli wayan na ta, ganin har sannan bai kira ba kawai ta dauki wayar ta shiga typing masa "No need ka cigaba da sani kuka, i think dama ba so na kake yi ba, Nima offer ɗin Ya Rayyan na karɓa not that wai dan ina son ka" tayi shiru tana tunanin tura masa hakan shine daidai, ta kai hannun ta zata yi pressing sent kawai taga kiran sa kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ba tare da tace komai ba kawai taji yace "Ina compound Leena, ki fito ki same ni please" tayi shiru har sannan idon ta na kan message ɗin da zata tura masa, dake wayan na speaker, da sauri ta clearing abin da tayi typing, a hankali ta mike ta ɗauki hijab ɗinta, kallon agogo tayi taga pass 11pm, ta wuce ba kowa a parlorn dan Ammi tuni ta kwanta da jikan ta, ta buɗe kofar parlorn a hankali, ta hango sa zaune, ta karasa car park tana jin hawaye na taruwa a idon ta, ya mike yana kallon ta har ta karaso, yayi kasa da murya yace "I'm very sorry, wifey" Leena ta rufe fuskar ta tana kokarin tsayar da kukan ta, Malik duk ya rikice haka nan yake jin Leena kamar wani sassan jikin sa, ya rike hannun ta yana lekan fuskan ta yace "I'm sorry Leena, na san nayi laifi" tace "Ko ka tsaya kaji menene amma sai ka share Ni" yace "Ai ban isa ba, I'm sorry dan Allah" ta gyada masa kai tace "Ya shirye shirye yasu Umma?" Jikin Malik yayi sanyi to the core, a hankali yace "Lafiya kalau, Wifey" ta sauke idon ta kasa sai yau ta yarda suna kama yadda yake kallonta sai gani tayi kamar idon ta ne banne a fuskar sa, ta zauna shima ya zauna, basu daɗe sosai suna magana ba ya mike yace "Barin tafi dare nayi ki samu ki kwanta dan gobe babu baccin safe" tayi murmushi daga haka suka yi sallama. Tunda sassafe sai ga kawayen Mummy sun cika gidan, sai murna take kamar nata auren 'yar zata yi, tana kallon Hajiya Amina tace "Karfe nawa mai makeup ɗin zata zo ne?" Wata kawar ta tayi dariya tace "Wato Khadija baki canzawa yadda na sanki haka nan kike" duk suka kwashe da dariya Hajiya Amina tace "Wallahi sai kace anan ake bikin ina ji ko ita uwar Amaryan bata yi wannan gayyar ba" duk suka kwashe da dariya, Mummy ta mike tace "Ina zuwa" daga haka tayi part ɗin Daddy zata shiga sai ga Hajiya tana fitowa, ta masa mata da sauri har ta karasa fita tana dariya kana kallon ta kasan tana cikin farin ciki tace "Hajiya ina kwana, ya shirye shiryen bikin?" A takaice Hajiya tace "Lafiya" daga haka ta barta tsaye, ta shiga parlorn Daddy ta same sa na breakfast ta zauna gefen sa ta sake gaishe sa bayan ya amsa tace "Ka ga dear har an fara taruwa kuma atleast ya kamata ace ayi abinci saboda jama'a duk da karfe 2pm ne daura auren" Daddy yace "Toh ai ba za'a yi taro ba, haka Hauwa tace" Mummy tace "Amma dai gaskiya wannan ba yi bane, toh nikam har 'yan office ɗin mu sun fara taruwa ace za'ayi abun alkhairi kuma sai a hana inviting mutane, A'a hakan ba yi bane" Calmly Daddy yace "Toh me kike so yanzu?" Tace "wai zaka kawo kuɗi ne aje kasuwa tun yanzu a siyo kayan da za'a yi girki kafin lokacin daura auren" Daddy yace "Okay, kamar nawa zai isa?" Tace "1500k ma Is okay zan yi managing" yace "Okay then, zan miki transfer" ta mike tace "Allah kara buɗi" daga haka ta fita, dakin su Leena ta wuce ta shiga sannan tayi sallama, Ammi dake zaune parlorn suna magana da wata kawarta ta ɗaga kai tana kallon Mummy wanda sun yi wata ma basu haɗu ba, bayan ta zauna Ammi tace "Ina kwana, Maman Rayyan" Mummy na murmushi tace "Lafiya, ashe Abu fa har ya zo, kuma haka nan sai kice ba taro, ai na aka taɓa haka" Ammi tace "Aure bana farko ba? A'a ba sai an daura ma kowa nawi ba kawai su bi su da addu'a Shikenan" Mummy tace "A'a dai yanzu Daddyn su ya bada kuɗi, So, yanzu za'a je kasuwa, duk wanda zai zo ki barsa dan Allah, ai abun murna ne, so abinci kuma ba matsala bane a gidan nan, kuɗin kayan miya kuma Daddyn su ya bayar" Ammi tayi shiru sai kuma tace "Toh shikenan, Mun gode, sannu da kokari" Mummy tace "Me kuma na godiya" daga haka ta fita. Rayyan yayi parking motar sa a parking space na gidan, Layla ta sauka da kyar dan yanzu tafiyar ma wahala yake mata, Rayyan yace "Barin wuce part ɗin Daddy" ta gyaɗa masa kai daga haka ta wuce part ɗin Mummy, da sallama ta shiga taga Mummy da few friends din Mama sun ci uban gayu sai shewa suke yi, Layla ta karasa cikin Parlorn ta gaishe da Mummy, Mummy ta amsa da fara'ar ta tace "Ya nawin jikin kuma?" Layla tace "Alhamdulillah" ta gaida sauran Mamas ɗin na ta, wata tace "Wannan ba 'yar Fatima bace?" Mummy na dariya tace "Itace, ai kin san ɗa na take aure" Layla ta girgiza kai dan ta san makirci ne ya kawo su, daga haka ta mike ta wuce part ɗin Ammi. Ammi tace "ki shiga tana ciki, taki breakfast ma ki mata magana kila ta ji naki" Layla na Murmushi ta mike ta wuce dakin da Leena ke ciki ta same ta kwance, Layla tace "Me zan gani haka?" Leena ta mike ta zauna tana murmushi tace "Ai da baki fito ba tunda kin yi nawi" tayi dariya tace "Ni na isa kin zuwa ne, ai sai Rayyan ya kullace Ni" murmushi kawai Leena tayi, Layla tace "Yana gan ki wani iri?" Tace "Ba zaki gane bane, wallahi gaba ɗaya a tsorace nake kamar a fasa auren haka nake ji, ga wata irin bugawan da zuciya ta yake yi kamar wani abu na shirin faruwa" Layla ta riko hannun ta ganin yadda take magana in breaking heart tongue tace "Ki daina haka Leena, addu'a kawai zaki yi, in shaa Allah duk abin da zai faru Alkhairi ne" a haka ta dinga kwantar mata da hankali. Bayan an gama abinci Mummy da kanta ta sa na Ammi idan tayi baki, ta kaiwa Hajiya, haka nan Hajiya taji abincin bai kwanta mata a rai ba, dan yadda Mummy ke behaving ya ba Hajiya shakku. Niswa ta gaida friends din Maman ta sannan ta wuce dakin Mummy ta zauna kan gado tana kokarin cire charger a jakkan ta sai ga Mummy ta buɗe dakin ta shiga, Niswa ta ɗaga kai tana kallon ta, Mummy tace "Me yasa zaki zo Niswa?" Niswa tace "Kawai dai Mummy, sannan ai at least Leena zata ji daɗi" Mummy ta taɓe baki tace "Bana so kina shiga mutane da wannan raman na ki ne wallahi" Niswa bata ce komai ba Mummy tayi saurin cewa "Zan so ki zauna har dare ki ga gidan da za'a kai Leena, ke ko gidan iyayen sa ba zaki iya minti ɗaya a cikin gidan ba, Kinga nashi gidan sai a hankali" Niswa na kallon Maman na ta tace "Mummy ina ba ke kika yi forcing auren ba ko?" Mummy ta hayyako mata "Nayi forcing kamar yaya? Dama can na san yaron ne?" Niswa ta bata hakuri, Mummy zata koma parlorn Niswa ma ta mike tace "I'm begging you Mummy, kar kiyi wani abu da zaki shiga hakkin wani" Mummy ta sake baki tana kallon ta sai kuma ta wuce ba tare da ta ce mata uffan ba, Niswan ma bangaren su Leena ta wuce, bayan ta gaishe da Ammi ta wuce dakin Leenan ta samu Layla da Zahra suna cikin ɗakin, tayi gaisuwa in jam'i Leena da Zahra kaɗai suka amsa ita kuma bata ko yarda ta kalli side ɗin Layla ba, tace "Leena ya shirye shirye?" Leena tayi murmushi kawai. Har sannan Mummy na mamakin rashin ganin Hajiya Fatima da bata yi ba. Kamar karfe 12:30pm Rayyan yayi sallama a kofar dakin su Leena, Ammi tace ya shiga amma yace A'a kawai a mika masa takardar gwajin, ba'a dau lokaci ba sai ga Layla ta fito ta mika masa yana karɓa ya juya saboda gudun kar ya ɓata lokaci. Ana idar da sallahr jumu'a aka daura auren Leena Abbah da Malik Areej, ko Leena ba zata nunawa Mummy murnan da tayi da auren nan ba. Leena na zaune duk jikin ta yayi mugun sanyi sai ga kiran Malik, ta rintse ido sannan tayi picking call ɗin na sa, da accent ɗin sa na larabci yace "Am I free to call you my wife?" Leena tayi shiru a hankali tace "Um" yace "May Allah bless our marriage with everlasting love until death parts us" a hankali tace "Amin ya Rabbi" ta sauke wayan ta katse kiran. Bayan an gama mata nasiha Mummy da ta sha makeup da few friends ɗinta tace ita zata kai ta hakan yasa Ammi bata sake cewa komai ba..

Ba lalle wannan chaptern ya ma kowa daɗi ba, but muyi accepting yadda hakan ya zo mana, thank you.

#Jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Young talented writers association (YOTA)


Chapter 64

Hajiya na jin wai Mummy ce zata kai Amarya da sauri ta mike, dakin ta ta wuce ta ɗauki Laffayan ta ta ɗaura, lokacin har wata friend ɗin Ammi da Mummy suna rike da ita, Mummy ganin Hajiya ta tunkaro su taji ranta yayi bala'in ɓaci, Ammi kuwa ganin Hajiya yasa hankalin ta ya kwanta. Mummy sai murmushi take a cikin motar, Drivern da ya ke driving ɗin su nai ya fara shiga Malali, layin manya gidaje, Mummy sai bin wajen take da kallo tana Allah, Allah su bar unguwar, kawai taga motar su ya parka a wani Babban gida, Mummy ta sake baki tace "Ha'a driver, ya zaka parka mu anan tun bamu karasa gidan amaryan ba?" Yace "Hajiya nan ne gidan na ta" Mummy ta sake kallon gidan sannan tace "A'a dai kayi ɓatan hanya, kalli wannan gida da uban kyau kace shine gidan?" Hajiya tace "Bangane me kike nufi ba Hadiza?" Mummy ta fara zufa, dan bata son da fara imagining wannan wai shine gidan Leena ba, ai gwara ta zauna gidan Sadeeq yau dubu, Driver ɗin ya juya bayan sa ya kalli sauran motar da suka raka su a bayan sa hakan ya sake tabbatar da cewa gidan ne, har sannan Hajiya bata daina kallon Mummy ta mamaki ba, duk suka sauka, Leena da kanta ke duke Hajiya ta sauko da ita, Kawayen Mummy da suke baya ma suka sassauko, kawayen Mummy sai bin gidan suke da kallo dan suma abun ya basu mamaki amma ba halin magana saboda Hajiya da ke wajan, bayan sun shiga gidan Mummy ji tayi kamar numfashin ta zai ɗauke sabar yadda gidan ya gaji da kyau ga furnitures masu tsadan gaskiya. Bayan sun ajiye amarya a Parlorn ta Hajiya ta kalle Mummy da kawayen ta da suke bin cikin parlorn da kallo tace "Zamu iya tafiya, tunda ba wai yarinya bace ko kuma auren ta na farko bane sai mu tafi ko?" Ta saka musu ido ta yadda ba wanda zai iya wani abu a cikin su. Wata kawar Mummy tayi karfin halin cewa "Kuma nan ne gidan na ta? To ina miji kuma?" Hajiya ta mata wani kallo tace "Yana kofar gidan, jira yake mu bar masa gida ya shigo ai" ta ja bakin ta tayi shiru Mummy ta goge zufan fuskanta tace "Amma abun da mamaki, yaron fa kowa ya san gidan su kuma ba wai aiki a babban waje yake yi ba amma kalli gidan da ya kama? Ko dai da wani abu da bamu sani bane?" Hajiya tace "Ni kam ko da wani abu ne a zuciyar ki da bamu sani bane Hadiza?" Hajiya Amina ta buga kafar Mummy da sauri, Mummy tace yake tace "Inaa, kawai dai ina taya ta murna ne" Hajiya tace "Muje" duk suka mike har sannan ba su gaji da kallon gidan ba, a compound
End Ads