x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 51 - AGOLA free pages

  • 150001 words
  • 153000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
gaishe ta, daga masa hannu tayi ta mike tsaye tace "wato Malik zaka iya zaɓan abun da bana so kace lalle shi kake so?" Malik ya fahimci Abbah kenan ya mata maganan, haka nan yasa ya saukar da kansa Umma ta cigaba "ina maka magana zaka min shiru? Har nice zaka bijirewa magana ta? Tun da na nuna maka bana son yarinyar nan ka nuna kai kuma nan kake son ta, Uban me take da shi da sauran matan ba su da shi" yadda take magana da karfi yasa a hankali yace "kiyi hakuri Umma" tace "idan har mata kake so zan shiga gari na nemo maka wacca ta fita da komai" ya ɗaga tsaya yana kallon ta, toh ita ina ta santa da har zata nemo masa wacca ta fita ɗin? A hankali yace "Umma dan Allah akwai abin da ta miki ne? Naga tun kafin kisan ita wacece kika tsane ta, balle kiji nayi maganar ta sai nan da nan ran ki ya ɓaci" tace "Okay, dan ban isa da kai bane yasa kake tuhuma na?" Daga haka ta wuce ciki da sauri ya bita dan duk duniya baya jin akwai wani abu da zai iya ɓata wa Mahaifiyar sa rai ya hakura. Da Daddare Mummy na zaune gefen Daddy shi kuma yana dinner, duk da ba wani sake mata yake ba amma hakan baya sa ya tauye mata hakkin ta, bayan ya gama cin abincin a hankali tace "Yallabai ina da wata magana" ya zuba mata ido alamar yana jin ta" a hankali tace "dama wata magana ce naga yana yawa a unguwar nan, kuma shine nace ya kamata na sanar da kai duk da ban san ya zaka ɗauki maganar ba amma kuma nima ba wai na san da hakan ba ne sai kwanan nan da magana ya fara yawo shine na sa ido dan gasgatar wa, kuma naga hakan ne" yace "Bar wannan baya nan, ina son kallon news, just go straight to the point" tace "Okay, regarding wanda ke zuwa wajan Leena ne, kaga yadda ake magana kuwa? fin shekara kenan, idan ma auren ta zai yi gwara kawai ya fito da wannan zuwan na sa, kasan yarinya karama ace da zauranci bai yi ba" Daddy ko uffan bai ce mata ba ta dinga kallon sa ganin yadda ko amsa ta bai yi ba, but deep down him yasan gaskiya take faɗa, atleast ya basa chance tunda shima witness ne almost a year yake ganin sa. Leena har tayi shirin kwanciya taji karar message duk tunanin ta Muhammad ne daya sako ta gaba kwana biyun nan, hakan yasa bata kula wayar bama har sai da zata kwanta ta jawo wayan dan ganin content ɗin sai kuma taga Malik ne, har sannan baya iya kiran ta sai dai ya tura mata da message bayan ta gama karanta message ɗin nasa ta ja tsaki sai kuma ta ɗauki wayan ta shiga typing masa idan har ba zai iya kiranta ko kuma fuskantar ta ba toh kada ya sake neman ta, bayan ta tura kamar da minti 2 sai ga kiran sa, ta dinga hararan wayar kamar wanda wayan ne ya mata laifi. Tun da gari ya waye Mummy ta shirya da wuri ko breakfast bata jira ba balle ta haɗawa Daddy breakfast duk da kwanan ɗakin ta ne, ta fita har sannan 'yan gidan basu gama tashi ba dan babu kowa compound ɗin, bayan ta fita a daidai gidan kawar ta Hajiya Fatima tayi parking, Hajiya Fatima da ta fito daga dakin ta zata kitchen ta tsaya kallon Mummy da mamaki sai kuma ta kalli agogo tace "Lafiya?" Mummy na murmushi ta karasa cikin parlorn tace "wallahi kalau, magana fa zamu yi dan ba ta waya bace yasa na zo kafin lokacin office yayi" Mama ta dawo tsakin parlorn tana kwalawa Ayrah kira, bata ɗau lokaci ba ta fito, Mama tace "Je ki karasa breakfast ɗin kar kiyi latti tunda lectures ɗin safe gare ki" ta amsa da toh ta gaishe da Mummy sannan ta wuce kitchen, Mummy ta dawo kusa da Mama tace "Kina ji, wani ne yake zuwa wajan Leena yau kusan shekara gudu, idan kin gansa zaki ɗauka balarabe ne ko kuma ɗan gidan shugaban kasa tsabar yadda yake ji da kansa, Ni kuma nasa a min bincike akan sa ashe ɗan gidan talakawa ne, da naso nace Malamin ya raba ta da shi amma ganin ance min ga yanayin sa shine nace kar ayi komai a kansa sai ma son da za'a kara musu suji suna son juna kamar za su mutu idan ba ɗaya" Mama ta dinga kallon ta da mamaki tace "Amma ke ya akayi kika san ɗan talakawa ne?" tayi dariya tace "Harisu na sa yayi min bincike, ashe wai haka yake yaudarar 'yan mata saboda kyan sa while gidan su ko karen gidan mu ba zamu sa a wannan gidan ba, Ni har kama da Leenan ma naga yake yi" Mama tayi murmushi tace "Toh ba damuwa, zan sanar da shi kawai ayi auren na su ko? Amma zaki sha kudi" tana murmushi tace "kudi ba matsala bace" sai kuma ta ɗaura "Da fa Hajiya Amina cewa tayi kawai na sa Rayyan ya aure ta har na masa magana sai kuwa naga wannan mutumin" Mama ta dinga kallon ta ba ko kiftawa tsabar mamaki, da har ranta bata ji zata kai sunan Leena gun Malami ba amma yanzu lamarin Mummy ya fara bata tsoro, wato 'yar ta ko haihuwa bata yi ba za'a fara Maganan mata kishiya, ganin Mama ta faɗa duniyar tunani yasa da sauri Mummy realizing me ta gama faɗa har sai da shock ya ɗan bayyana a fuskar ta sai kuma tayi murmushi tace "kinsan da fir nace ban yarda ba amma sai ta nuna min cewa wata uku kawai za suyi ya sake ta shikenan" Mama na mata wani kallo tace "a tunanin ki kin isa ki sa ya sake ta ne a wata uku? Kuma kinsan dama yana son ta, a kaddara ace ciki ya shiga ki bar ganin biyayyar da Rayyan yake miki wallahi saf zai rufe ido ya gwada miki cewa ba zai rabu da ita ba" Mummy tayi yake tace "Allah ma ya kiyaye na hada jini da ita" sai kuma ta mike tana kallon agogo tace "Kinga barin wuce office kar na makkara". Daddy yayi shiru yana sauraron Rayyan, sai kuma ya gyara zama yace "amma da kuka yi magana mai ya ce maka?" yace "ya gwada min yana son ta da aure ne kuma ita ma da na mata magana tana son sa Shiyasa naga zaman nata haka bai kamata ba" Daddy yace "But planing ɗina fa ta koma makaranta ne Rayyan, ace duk yara na mata sun yi karatu banda ita?" Rayyan yace "Daddy aure baya hana karatu, kawai taje tayi a gidan sa idan yaso mu sai mu cigaba da ɗaukan nawin ta" Daddy yace "Okay, zan yi magana da ita Sirbajo sannan kuma kace wa yaron ina son ganin sa" ya gyaɗa kai yace "Da na so ta koma gidan mijin ta ne wallahi, amma Sadeeq ɗin nan ɗan rai nin hankali ne, dama tun farko ba magana muke ba sai da ɗan uwan sa, Daddy can you imagine mun haɗu a masallaci ina da niyyar masa magana ya ɗauke kai ya bar masallacin Shiyasa kawai na yanke shawarar tayi aure karma ta ɗauka yana da niyyar dawo da ita" Daddy yace "kayi abun da ya dace Rayyan, haka nake son ganin kana tsayawa a lamarin kannan ka, amma da na ɗauka ko kai ne zaka aure ta Shiyasa ban yi ma magana ba" Rayyan yayi murmushi yace "Daddy a barta da wannan sannan mu bita da addu'a tunda naga tana son sa" Daddy yace "it's true". Layla was totally shock da abin da Mama ta gama gaya mata tace "Mama wai matar nan ita a rayuwar ta bata so taga wani yana walwala ne? Ni yanzu uban me na tare mata take son ya auri Leena?" Har muryan ta ya fara breaking, Mama tace "Yanzu kam ai shikenan, sannan karma kisa abun a ranki balle ya dame ki" ta gyaɗa kai tace "Ba zan sa ba, in shaa Allah" sai kuma tace "Mama kin san Allah wannan Malik ɗin karya ake mata da aka ce bayi da kuɗi, ko kuma ba dai gidan su aka je ba, dan wallahi baki gan sa bane, ai da nake zuwa gidan ina ganin yana zuwa wajan Leena" Mama tace "Toh ai a gidan kike ganin sa, hakan ba shine zai nuna ainahin sa ba" Layla tayi wani murmushi tace "Toh Mama ki san abinda baki sani ba, Malik da kike gani ina following ɗin sa, dake yana following Leena so ya shigo min a suggestion Ni kuma na fara following ɗin sa a IG, Mama gayan nan bai yi kama da ɗan talakawa ba, beside kuma har kama suke da Leena" Mama tace "itama haka tace wai suna kama" Layla tace "Mama kiyi shiru da bakin ki, Ni fah da ban san Ammi ba sai nace ko Leena ba 'yar ta bace duba da yadda basu kama duk da Ammin ma kyakkyawa ce" Mama tace "kamar ya?" Layla tace "Ni fah ina zargin wannan kamar ɗan lekan asiri ne ko kuma nace da wata manufa, Shiyasa nace ki cire hannun ki a lamarin nan kuma dan Allah ko da wasa kar ki sanar mata" Mama tayi shiru tana mamakin maganganun Layla a haka dai suka rabu.


Jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧


Wattpad @Jiddatulkhayr
Instagram @Jiddatulkhayr writes


Young talented writers association (YOTA)


Chapter 60


Tunda Layla ta zo she has been dragging her into conversations, and it seems like she wants to know something about Malik, Leena tayi murmushi jin me ta gama faɗa, Layla tace "I'm telling you, this isn't something to joke about, wallahi kawai just marry him, ban san ya yaran ku zasu zama ba, kila ace daga Saudi suke ma" Leena, who was tired of listening to her talk tace "Yanzu kam ai shikenan tunda har Abbahn sa ya samu Daddy" daga haka ta cigaba da sawa Nawaf kaya, dan ita gani tayi everything Layla does seems driven by jealousy, and ita kam ta daɗe da cire Rayyan a ran ta, tun kafin auren ta da Sadeeq, tana gama sa masa kaya tace "Je ka wajan Ammi" ya juya ya fita, ta kalli Layla da murmushi a fuskar ta tace "Bari na ɗan kwanta kai na na min ciwo" daga haka ta haura gado duk da ba wai bacci take ji ba kawai tana avoiding magana da Laylar ne, daga haka Layla ta mike ta bi bayan Nawaf tana kiran sa. Tun bayan tsayar da maganan bikin ta da Malik jikin ta ya gama tsanyi, ta rasa meke damun ta, Rayuwar ta da Sadeeq shi ke sake zuwa mata, haka nan sai tayi ta kuka, but...She doesn't know what the future holds for her, Amma tana fatan Allah ya wuce lamarin ta, kuma she hopes that Malik will be a source of blessings in her life. Yau wajan sati guda kenan Umma bata kula Malik, duk yadda yaso ya bata hakuri bata basa wannan door ɗin, abin na damun sa but ya san ba zai iya rabuwa da Leena ba, saboda He is so much at peace with her. Kamar kullum yau ma, bayan ya gama shirin fita aiki ya karasa har parlorn, ita da Abbah su na zaune suna breakfast, wanda har Abbahn ma ta canza masa sai dai shi be gwaɗa mata ya fahimci hakan ba, Malik ya karasa ya zauna kan wani kujera dake parlorn yace "Umma, Abbah zan fita aiki" Abbah kaɗai yace "Toh Allah bada sa'a" ya juya yana kallon Umma yace "Umma zan fita aiki" sai sannan tace "Naji ai" sai duk jikin sa yayi sanyi yace "Dan Allah Umma kiyi hakuri" tace "kamin wani laifin ne?" Kai kawai ya girgiza mata, Abbah yace "tashi ka je Allah maka Albarka" ya amsa da Amin sannan ya kama hanyar fita amma gaba ɗaya sai yaji wani iri saboda Umma, bayan ya fita ya jiyo muryan Abbah, ya juya ganin Abbah ne yasa ya juya zuwa inda yake, Abbah ya dafa kafaɗar sa yace "Malik, Karka damu komai zai wuce, ina ji a jiki na auren nan akwai Alkhairi, kar kace zaka canza ra'ayin ka Saboda Mahaifiyar ka, ka tausaya wa yarinyar ko dan jarabawar aure da ya same ta kuma ka ga marainiya ce, Nasan mahaifiyar ka na hakan ne dan ka janye, amma da kanta zata sauko kar ka damu" Malik ya gyaɗa masa kai, Abbah yace "Allah maka Albarka" ya amsa da Amin daga haka ya kama hanya. Mummy tayi parking motar ta a farkon Layin unguwar na su, tana ta bin wajajen da kallon gƴama ta jingina kanta da jikin kujeran motar ganin wanda take jira bata hango ta ba, tsaki taja ganin tana bata mata lokacin, ɗaukan wayar tayi ta kira matan, yana fara ringing ta ɗaga tace "Hajiya gani fa a hanya yanzu haka ma ina hango motar ki" daga haka Mummy ta katse kiran ba'a dau lokaci ba sai ga matar, kwankwasa motar tayi, Mummy ta cire lock ta sauke windown tace "shigo" matar na murmushi ta buɗe ta shiga, Mummy taji numfashin ta na shirin ɗaukewa saboda yadda jikin matan ke tashi, Matan tace "Ina kwana Hajiya, Kinga na daɗe ko? Ta baya na bi saboda bana son aga ina shiga Mota ina fita a fara saka ido shi..." Mummy ta katse ta tace "Dan Allah yi sauri kiyi maganar da ya kawo ni" tace "Toh dai yanzu abun da ake ciki shine mahaifiyar sa bata son auren kuma tace sai dai bayan ran ta ne za'ayi auren" Mummy tace "Ita asali me dalilin ta na dake wa akan hakan?" tace "Toh bamu dai sani ba, amma ko jiya da na shiga gidan naji tana mita, kuma kamar ance yarinyar da zai aura suna da kuɗi kuma selebiriti ce, Inaga saboda haka ne" Mummy tace "amma kun gwada mata maganar?" tace "Chap, ai ki raba ni da ita, daga sa baki na ta kusan mari na sabar masifa" Mummy tace "Naji" ta buɗe Jakkan ta ta fito da dubu goma ta mika mata tace "sauka, sai na sake neman ki, ki cigaba da binciko min komai" matar ta fara Godiya tana washe baki a haka ta sauka tana mata kirari, Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta buɗe motar ta yatsar da miyau, tana tada motar ta bar unguwar. Niswa dake kitchen tana girki tana waya da Farouq sai dariya take, knocking taji ake yi a kofar parlorn hakan yasa tace "ana knocking kofa dear, barin je na duba, sai ka dawo bye" bata jira cewar sa ba daga haka ta yanke kiran ta goge hannun ta da towel ta fita zuwa parlorn, sai da numfashin ta ya kusan ɗauke wa ganin Mummy ce da Na'ila, muryan Mummy ya dawo da ita daga tunanin data faɗa, "Toh ba zaki bamu hanya bane ko ta kanki zamu shige?" Fuskar Mummy a tamke ta kare maganar, Niswa ta masa mata da sauri tana kirkiran murmushi tace "Sannu da zuwa, Mummy" Mummy bata amsa mata ba ta wuce cikin parlorn Na'ila na biye da ita a baya, Niswa ta rufe kofar duk jikin ta yayi sanyi ta karasa parlorn ta zauna tace "Sanni da zuwa Mummy, Ina wuni" Mummy tace "Fine, ina Umar ɗin?" tace "Baya gida sai dai anything yanzu zai dawo" ta juya ta kalli Na'ila dake danna waya kamar bata san da zaman ta a wajan ba, a hankali tace "Sannun Sister Na'ila" ta ɗan yatsina fuska tace "Ohh" Niswa ta sauke kanta kasa sai kuma ta mike ta wuce kitchen bata ɓa ta lokaci ba ta dawo parlorn rike da tray ta cika musu da snacks, ta duka ta ajiye a gaban Mummy, Mummy tace "Ni kam banda ci da kwanciya banga wani aikin da kike ba? Yanzu fah wajan shekara guda kenan" Niswa da rashin fahimta ta kalle ta sai kuma bata ce komai ba, Sallamar Farouq suka jiyo, tun da ya shiga ya tsaya daga bakin kofar yana kallon su da mamaki, Mummy ta mike ganin sa tace "dan an maka magana ranan shine ka ɗauke kafa a gida ko? Yau wajan satin ka nawa baka taka ko da kofar gida ba? Toh nazo faɗa maka ko zaka mutu ne sai dai ka mutu a cikin satin nan mahaifinka zai kai goron tambayar ka gidan su Fatima-Zahra" with shock yake kallon Mummy, Niswa taji hawaye ya cika idon ta ta sauke kanta kasa ba tare da ta bari wani yayi noticing ba, Farouq yace "Please Mummy kar ki.." ta katse sa, "Idan har ba zaka karbi zaɓi na bane sai ka fada min, yarinyar nan ba wanda bai san ta so wanta ba, yarinya mai hankali da kamala, ga tarbiyya, idan har zaka iya zama da wata macen karya kace ba zaka iya zama da ita ba, ko kana so ko baka so next month bikin ka, kuma ina son ka tanadar da wajan da zaka ajiye ta kuma kasan mahaifiyar ta ba karfi gare ta ba dan haka kayan kitchen kawai zasu yi sai ka fara siyan furnitures, period na gama magana" tana kallon Na'ila dake taunan chewing gum tace "Kee! Tatso mu tafi" daga haka ta fita fuuu, Farouq dakyar ya iya bin su da kallo sai kuma ya mayar da kallon sa ga Niswa da har sannan take duke a kasa, ya fuzar da isakan bakin sa sannan ya karasa dinning ya zauna yayi tagumi. Ta kalli Malik sai kuma tayi murmushi tace "wai me yasa kake damun kan ka ne? Kana da good future tunda har kayi karatu, wata rana sai ka sha mamakin yadda Allah zai mayar da kai, kuma ina jin a jiki na zaka samu sauyin wajan aiki very soon" yayi murmushi yace "Ina dai jin wani iri ne, You don't deserve someone like me, poor me, kawai dai ina da tsaurin ido ne da har
End Ads