x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 42 - AGOLA free pages

  • 123001 words
  • 126000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
Layla ta wuce part ɗin Hajiya, ja baya tayi ganin Rayyan na kokarin fita, ya tsaya kallon ta da mamaki yace "Ke ya kike musu yawo da Baby?" tace "Ina gaishe da Hajiya zan koma ai" ya kai bakin sa kunnen ta ya mata whisper, murmushi kawai tayi taki kallon sa ta shige parlorn da sallama, Hajiya da ke zaune tace "Ashe tare kuke?" tace "Eh, Hajiya" bayan sun gaisa ganin yadda take son Babyn Hajiya tace "Toh Allah baki ke ma Layla" murmushi kawai tayi daga haka ta mike, ta wuce sashin Mummy, ta shiga da sallama, duk suka dago suna kallon ta da mamaki, ta sake baki tana kallon Maman ta ta karasa wajan ta ta zauna gefen ta tace "Ashe zaki zo shine baki faɗa min ba?" Hajiya Fatima tace "Oh, ai naga ke kin faɗa min" taɓe baki tayi ganin su tare tasan yanzu kuma wani makircin zasu shuka, tana kallon Mummy tace "ina wuni" tace "Lafiya" daga haka bata sake ce mata komai ba, kuma har sannan Mummy idon ta akan Babyn, Mama na kallon Niswa dake selecting kayan fitan bikin ta tana nuna mu su tace "Niswa baki ga Yayar ki bace?" Layla tace "waya ce miki wannan tana da tarbiyya, ai haka nan take bata gaisuwa" Niswa ta tsaya kallon ta sai kuma ta cigaba da aikin gaban ta, Mummy ta mata wani mugun kallo ta kasan ido sai kuma tayi murmushi tace "Ni ban san me yake faruwa tsakanin Layla da Niswa ba haka nan suke na rasa gane kan su" Hajiya Fatima tace "Toh maganar gaskiya kuma anan ai karami ne zai bi babba, balle ma yanzu tana matar Yayan ta" Mummy tayi yar dariya tace "Naga alama dai so suke su bata zumunci mu na tun tula tula" Layla na ɗan jijiga Babyn hannun ta gudun kar yayi kuka dan taga ya farka a bacci, Rayyan ne ya fito a dakin sa, kallon yadda Laylan ke yi yace "Toh sannu Maman Babyn" tayi murmushi, shi kuma daga haka ya fita, Mama tace "Wai ɗan waye ne wannan?" tace "Babyn Leena ne fa" Mummy ta sake baki tana kallon ta tace "Wata Leenan kuma?" tace "Leenan dai da kuka sani" Mama tace "Ji wani kalar amsa da kike ba mutane, ki buda baki kiyi mana baya ni" tace "Toh yanzu dan Allah Leena nawa kuka sani a rayuwar ku? Toh Leenan gidan nan mana" Mama ta tsaya kallon ta haka Mummy ma, dan ita kam har taji wani abu ya tsaya mata a makoshi tace "yanzu naga har shiri kuka fara ko?" Hajiya Fatima tace "ban gane shiri suka fara ba?" Layla ta mike jin zai fara kuka Hajiya Fatima tace "Ke an kawo miki naki ɗin kin ne?" Layla da ta kama hanyar fita ta jiyo tana kallon Maman ta tace "Wani ɗinkin kuma Mama?" tace "Ashoben bikin Niswa ɗin mana, kin san jibi za'a fara event" Layla ta taɓe baki tace "Toh da zasu saka ni ne? Ni ban ma san komai game da bikin ba ma balle a bani ashoben" Hajiya Fatima tana kallon Mummy tace "Me yasa kuke ware Laylan? Ko dan basu shiri da Niswan ne?" Mummy tace "sai kace wasan yara? dan suna fada sai aki bata ashoben" tana kallon Layla tace "ga naki ashoben can a daki na zan bawa tela na, ya iya dinki cikin sauri" Layla tace "No ki bari zan bawa nawa telan" daga haka ta fita ba tare da ta sake jin me zasu ce ba, ran Niswa yayi mugun ɓaci dan taji haushin Mummy ba kadan ba, bayan Layla ta koma part ɗin su Leena, Ammi ta zuba mata abinci tace "Laa, Ammi na koshi" Ammi ta karbi ɗan da ke son yin kuka tace "Ni dai na ajiye miki sai dai kiki ci, kuma ke da Rayyan" tayi murmushi ta buɗe tsadaddun warmers ɗin ta fara serving kanta, Ammi kuma ta wuce ciki rike da Babyn a hannun ta ta mika wa Leena tace "Feed him, naga ya na son yin kuka". Har kusan yamma Layla na sashin Ammi har hakan ya ba Hajiya mamaki, bayan tafiyarsu su ne Ammi tana kallon Leena da ke game a wayan ta tace "Leena tashi kije dakin Daddyn ku ki kai masa Babyn" Leena ta tsaya tana kallon Ammi sai kuma a hankali tace "toh" ta dauki hijab dinta ta saka sannan ta karbi Baby da ke hannun Ammi, a compound ta haɗu da Hajiya da zata part din Daddyn itama hannun ta rike da kasko da laida tana kallon Leena tace "Ina zaki?" a hankali tace "Ammi tace na kai ma Daddy Babyn ya gani" Hajiya tace "Koma sashin ku abinki" sai kuma tace "ki kai masa ɗin" Leena ta karasa ita kuma ta daka ta ta zuwan ta. Leena tayi sallama a hankali ba tare da tayi knocking ba Ayaan dake kwance kan kujera yana kallon cartoon a wayan Daddy ya mike da gudu tun kan Daddy ya bada izini har ya isa bakin kofar yana cewa "Daddy, it's my Addah" ya buɗe mata, ta sakar masa murmushi ya masa mata yana cewa "Addah ki ban Babyn" ya karasa maganar yana mika mata hannu tace "Naji zan baka" ta karasa cikin parlorn kanta a kasa Daddy ya dinga kallon ta har ta zauna sai sannan ta daga kai ta kalle sa da sauri ya ɗauke kansa yana kallon wani wajan tace "Daddy ina wuni" yace "Lafiya Leena" ta karasa gaban sa ta duka tana mika masa Babyn ya karba idon sa akan Babyn yace "Ya jikin kuma?" tace "Da sauki yanzu" yace "Allah ya raya mana bisa sunna" tayi shiru tana wasa da fingers dinta, Daddy bai taɓa jin kunya irin na wannan lokacin ba, dan ma ya kasa hada ido da ita, Hajiya ta shigo kanta tsaye, Daddy ya mika wa Leena Babyn, ta karba ta mike tace "sai an jima" nan ma kasa amsa mata yayi bayan ta fita Hajiya tace "Allah sarki, Uwar ta kam mai hakuri ce, irin su kadan ne a duniya, Allah shiga lamarin ta da ƴarta" Daddy be iya cewa komai ba, ta ajiye kaskon hannun ta ta fara zuba hayakin a ciki, sai kuma tace "toh sai ka taso kazo kayi na wankan" yace "Hajiya ki bani maganin zan yi anjima" ta masa wani kallo tace "Saboda matar ka ta samu damar hana ka?" daga haka ya mike. Leena na komawa part din su ta sami wayan ta na ringing ta ajiye Babyn a gadon sa kafin ta karasa har ya yanke, ta ɗauka tana kallon missed call ɗin Malik, tsaki tayi dan yanzu kuma abun nasa ya koma takura. Bayan sun koma gida, toilet ya wuce yayi wanka sai da ya gama sannan yayi amfani da maganin da Hajiya ta basa da be yi believing ba amma ganin da gaske aka raba Leena da mijin ta hakan ya basa tsoro, dama kuma kiran da Hajiya ta masa kenan dan ta basa magani, ya dauki lokaci sannan ya fito, samun Layla yayi har ta gama gyara dakin tasa turaren wuta sakar masa murmushi tayi ta ajiye abin hannun ta akan dressing mirror tace "bari na daura mana dinner" yace "ki bari zamu fita mu ci" ta tsaya kallon sa yace "Sure, we're going out on a date, ko baki so ne?" tace "Ina so kai, abinda ban samu ba tun a waje" yayi murmushi jin yadda tayi sounding. Niswa tace "Wallahi Mummy idan baki tashi tsaye da gaske ba sai Layla ta saki kuka" Mummy tace "Naga alama kam Niswa, wallahi da na san haka ne da tun farko ban cusa masa ita ba" Niswa ta taɓe baki tace "Gashi kuwa yanzu kamar ya fara son ta, dan na gani a idon sa" Mummy tayi tagumi Niswa ta cigaba tace "Dan wulakanci wai ta haɗa kai da su Leena?" Mummy tace "gashi uwar ta har sannan bata bari na nayi magana da malamin nan, ko da munje a waje take bari na balle na kai masa Sunan Laylan" Niswa tayi dariya tace "Hajiya Mama ba daga nan ba". Da Daddare bayan Ammi ta gama gyara dakin ta, tasa turaren wuta, tana kan kunna mosquito coil taji an buɗe kofar dakin duk zaton ta Ayaan ne yasa bata juyo ba amma Kamshin da ya dake hancin ta ne, the smell that she is obsessed with, kafin ta kai ga juyawa ya rungume ta ta baya, tayi shiru tana tunanin yaushe rabon ta da shi, a hankali yace "I'm sorry wife, nasan ban kyauta ba" Ammi tace "wani abun ya faru ne?" ya juyo da ita yana facing dinta yace "Your silence is killing me, Dan Allah kice duk abinda kin san zaki huce, dear" Ammi ta girgiza masa kai tace "It's Okay" yace "I'm sorry, I'm so sorry, please! Kin san haka kawai ba zanyi ignoring dinki ba" Ammi bata ce koma ba ta janye jikin ta ta cigaba da kunna coil ɗin ta ajiye a spot din sa ta mike taga har sannan kallon ta yake yi yace "amma kin san you're my all time favorite, kimin uzuri mana" tace "Bakomai wallahi" yace "Wallahi na kasa hada ido da Leena nasan zata yi tunanin dan bani bane mahaifinta ko?" ya karasa jikin gadon ya zauna yana bin Ammi da kallo dan yayi missing ɗinta ba kadan ba, yadda take magana da shi, yadda take basa shawara, yadda take kwantar masa da hankali, uwa uba ga safta da iya girki, a hankali Ammi tace "A'a akan me zata dauka? Ai a baya baka rage ta da komai ba, so kar kayi tunanin haka" Daddy ya jingina kansa da gadon yana kallon sama. Washe gari bayan ta gama shirya Ayaan har driver ya kai sa, haka nan Daddy wai sai dai da kanta zata yi feeding dinsa, ta kalli parlorn da sauri sai kuma ta tura masa plate ɗin abinci gaban sa tace "idan 'yarka ta ganmu fa, kar ka manta ka zama kaka fa" ya buɗe hannun sa alamar ina ruwan sa yace "Ai zata koya ne daga gare mu, itama sai take ma mijin ta" Ammi tayi yar dariya ta mike ganin da gaske yaki breakfast ga kuma Binta da Leena dake zaune a Parlorn, bayan ya gama breakfast yace ta raka sa, tana rike da briefcase dinsa ta raka sa har jikin motar sa, sai tsokar ta yake yi duk da taki biye masa amma tana murmushi, tunda Mummy ta fito idon ta akan su, har ta gagara controlling kanta, bayan Daddy yayi hugging Ammi zai shiga motar sa, ganin haka yasa Mummy sake jakkan hannun ta duk juyawa suka yi, ganinta yasa suka ɗauke kai ba wanda ya kara bi ta kanta, barin ma Daddy da yake jin tsanar ta a ran shi. gaba daya a wajan aiki Mummy ta kasa samun nutsuwa, sai faɗa take da sauran ma'aikatan wajan daga karshe ma gida kawai ta dawo dan ta kasa sukuni, kuma tayi ta kiran aminiyarta amma baya shiga. A haka Mummy tayi rayuwa kwana biyun nan a gidan Daddy bata da wani peace of mind, sai ma baccin da bata iya yi da daddare, ga baki sun fara taruwa saboda bikin Niswa da ake shirin yi.


Oops! Where am I even going to start, My lovely dearest? Well, Assalamu alaikum, mutanen arziki, I'm a bit busy today, so today's chapter will be shorter than usual, ayi hakuri da hakan, thank you.

Hauwa Jibrin Sulaiman
(Jiddatul-khayr)
*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr


Young talented writers association (YOTA)




Chapter 49&50



_________Ammi dake kallon Anty Jiddah da Farida tace "bari a tashe ta ai la'asar ma tayi" Anty Jiddah ta mike tana kallon Ammi tace "A'a kar a tashe ta Ammi, bari kawai mu tafi, kawai dai idan ta tashi ace Farida ce ta zo gaishe ta" Ammi tace "ba ayi haka ba kam, ace tun daga wani gari ta zo gaishe ta ace kuma bata ganta ba?" daga haka ta wuce ciki, Anty Jiddah ta koma ta zauna, Farida sai kallon Babyn take yi, ba'a dau lokaci ba sai ga Ammi ta fito Leena na biye da ita a baya, ta sake baki tana kallon Farida sai kuma ta karasa cikin parlorn tayi hugging ɗinta tace "Sister Farida yaushe a gari?" Farida tayi murmushi tace "Jiya na shigo da daddare nace barin zo ganin Baby" ta zauna, bayan sun gaisa basu dade ba suka ce za su tafi, Leena ta mike ta raka su har gate, da take dawowa taga sai kallon ta ake ana magana kasa-kasa dake gidan yanzu ya fara cika, duk da yadda taji wani iri amma sai ta ɗauke kanta tana kallon kasa har ta karasa part din su, Ammi tace "an kira ki" ta karɓi wayan da Ammi ke mika mata ta kalli kiran Malik ne, ta ajiye wayan ba tare da ta sake bin kan kiran ba, tunda suka fara event Leena ko da wasa ba ta taɓa fita ko da compound ɗin ba, saboda duk sanda ta fita indai ta haɗu da wani na Mummy toh sai sun jefa mata magana akan mutuwar auren ta hakan yasa ko bakin kofa bata yarda ta taka, kuma Hajiya bata damu da ta sa suna shiga cikin su ba, Niswa tayi bridal shower wanda kuɗin da aka barar bana wasa bane, hakan ya sake tabbatarwa mutane ba karamin mutum Niswa zata aura ba, yau tun da safe Niswa ta bar gidan su ta koma gidan Kanwar Mummy, gaba ɗaya gidan sai hada hada ake yi, hatta bangaren Hajiya a cike yake da cousins ɗin Daddy da yaran su da suma sukayi takanas dan halartar bikin. Mummy tayi dariya tace "Wallahi kaman kin sani, ina aurar da Niswa ai burina ya cika" Kawar ta Maryan tace "Toh ba zaki kai ma ita kishiyar taki gate pass ɗin bane? Karfa aje can ayi barin kuɗi Kinga idanun su bai kalla ba balle bakin ciki ya kama su" tayi dariya tace "Wallahi kin kawo shawara, ai kuwa da kai na zan shiga na ba su". Daddy ya shiga parlorn da sallama, Anty Binta ta amsa ta mike zata dakin Leena yace "kawo shi" daga haka ta mika masa Babyn ta wuce ciki, Ammi jin muryan sa yasa ta fito tana murmushi yace "Madam yunwa nake ji" Ammi ta karasa ta karbi Babyn tace "Muje ka ci" dinning suka karasa tare suna hirar su, bayan ya gama ya mike yace "I think sai dare kawai zanna shigowa gida cos naga gidan yanzu a cike ya ke" ta gyada masa kai tace "Hakan ma it's okay ai" Sallamar Mummy suka jiyo, Mummy bata yarda an bata izini ba ta kusa kanta wani irin jiri ne taji yana neman ɗeban ta har wani dishi dishi take gani, dan bata yi expecting ganin Daddy ba, Daddy yayi ma Ammi sallama daga haka ya fita ba tare da ya bi takan Mummy ba, da kyar ta iya daurewa ta zauna akan cushion ɗin tana faking murmushi, cos yanzu har ta fara manta da wani bakin cikin da Daddy ya fara kunsa mata ba sai yanzu da ta shigo kuma taji damuwar ta ya dawo sabo, Ammi ta katse mata tunanin ta da cewa "Mun wuni lafiya ya taro?" tayi murmushi tace "Alhamdulillah, dama na kawo muku kati ne nace kar kuce ba'a fada muku ba" Ammi ta karbi gate pass ɗin data ke mika mata tana kallon tace "Allah ya sanya Alkhairi" idon ta nakan jaririn da Ammi ta ajiye a gadon sa tace "ina Leenan?" Ammi ta kwalawa Leena kira bayan Leena ta fito fuskar ta ba yabo ba fallasa tace "Ina wuni" Mummy tace "Lafiya Leena" sai kuma ta buga uban tagumi tace "Oh Ni Khadija yanzu fisabilillah yarinya karama Kamar Leenan nan ace an maida ta bazawara? ai shi yasa sometimes auren wurin nan babu alkhairi kwatakwata tattare da shi" Leena ta mike ba tare da ta amsa mata ba Ammi kuma kallon ta kawai ta tsaya yi da mamaki, Mummy tayi saurin cewa "Amma Leena kema baki tsaya kinyi tunani bane kika aure sa? Ko dai gudun kar ace an fasa auren ki yasa kika amince da auren sa? Ashe dai gidan su basu gaji arziki ba" kamar daga sama sai ga Anty Binta ta fito tace "Toh idan Allah ya kaddari abu babu bai canza ta, ko da kuwa suna son junan su kamar su cinye ne tunda aure tsakanin su ya kare ai shikenan dole su rabu" Mummy ta tabe baki tace "Ai wata sa'in naci ne ke jawo hakan" ta mike zata fita sai ga Layla na shigowa da sallama a bakin ta Mummy ta tsaya kallon ta sai kuma tayi yake sau daya Layla ta kalli Mummy tace "Ina wuni" Mummy tayi banza da ita ta fita ba tare da ta sake kallon su ba, Layla ta gaishe da Ammi da Anty Binta daga haka ta wuce dakin Leena, Anty Binta tace "wallahi munafurci ne ya kawo ta nan" Ammi ta mike ba tare da ta ce komai ba Anty Binta tace "Ammi wallahi duk ke kike kyale matar nan" Ammi ta ajiye katin hannun ta akan Centre table Anty Binta ta ɗauka tana kallon tace "Allah ya kiyaye wanin mu ya halarci wajan taron nan" Ammi bata ce mata komai ba ta wuce dakin ta", Layla tayi hamma, Leena tace "Toh ki hau gadon mana kamar bacci kike ji fah" tace "Wallahi baccin ne ma, dan jiya ban samu nayi ba gashi yau an hanani saboda tsinanniyar auren nan" taja tsuka ta kwanta akan sallaya, ita dai Leena bata ce mata komai ba. wata cousin ɗin Daddy tana kallon Hajiya tace "Hajiya ya naga baki fara shiryawa ba naji ance da wuri za'a je wajan event ɗin dan naji wai kamar motoci ma sun fara zuwa" Hajiya tace "Toh ni kuma tsofe tsofe da Ni zan kama hanya wai da sunan event? A'a ba dai Ni ba kam" tace "Toh ai Hajiya naga kin je na Rayyan ma balle wannan da kamu ne" Hajiya tace "Toh ba
End Ads