x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 30 - AGOLA free pages

  • 87001 words
  • 90000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
sanda ta sake zuwa Miki karki kuskura ki sake mata fuska? Anty Mairamah tace "wani sake fuska kar ma ki buɗe mata kofa, ki faɗawa mijin naki idan ita ce karma ta shiga, dan mutanan nan basu da imaani" wayan ta ne ya fara ringing da sauri ta kwace wayan a hannun Ayaan ganin Sadeeq ne ta mike sai kuma tayi realizing reaction dinta ta ɗan kalle su sai ta koma ta zauna Anty Binta tace "Ni wai yaushe Leena kika zama mara kunya ne?" Anty Mairamah tace "tashi ki shiga ki amsa wayan mijin ki" Leena tace "Ba fah shi bane" daga haka ta wuce cikin dakin ta. Sadeeq dake kwance a parlorn gidan su duk tsokanar da Sultan ke masa be tanka sa ba, ya kuma kiran Leena a karo na biyu tana dauka ya mike ya haura sama wayan kare a kunnan sa after few minutes sai kuma ya sake sauka ya wuce kofa. Bayan ya isa kofar gidan su Leena ya shiga har cikin gidan ya gaida Daddy, sannan ya wuce bayan yayi sallama da Ammi ya wuce ɗakin Hajiya, Leena ta rike Ammi sai kuma ta fara kuka Ammi tace "bana son iskanci, sake Ni kar mijin ki yayi ta jiran ki" sai kuma ta turo baki Anty Binta tace "Toh Leena Allah bada zaman lafiya mu ma jibi zamu koma" Leena tayi hugging ɗinsu tana jin kamar su cigaba da zama da Ammi, Anty Mairamah tace "zamu yi waya, Allah yasa ma kina yin abubuwan da nake faɗa Miki" ta saci kallon Ammi daga haka ta wuce ta fita ba tare da ta sake kallon Anty Mairamah ba, dakin Hajiya ta wuce, ta mata sallama sai kuma ta tsaya Hajiya tace "Lafiya kuma?" tace"Hajiya baki da abun daɗi ne?" Hajiya tace "A'a nikam babu komai" Leena tace "toh barin sha ruwa" Hajiya tace "ke da zaki gida yanzu" Leena ta karasa jikin fridge ɗin Hajiya ta buɗe tana ganin Nono da fita ta ɗauke ta karasa cikin parlorn tana dariya tace "Ni dai na dauke wannan" Hajiya ta sake baki tana kallon ta tace "ai kwana biyu da baki nan na huta, amma daga zuwan ki dan abun da ya rage min kin ɗauke, bayan mijjn ki ya loda miki" Leena tayi dariya daga haka ta wuce, tana buɗe gate taga yana tsaye yana jiran ta fito, tun da ta fito har ta karasa jikin motar idon sa na kanta, har ta karasa sai sannan yace "Baby, do you know how much I miss you?" da sauri ta juya tana kallon layin na su ganin babu kowa tace "dan Allah ka bari kar wani ya zo" yayi kissing forehead ɗinta sannan ya buɗe mata kofar front seat ta shiga, a kofar gidan Mami yayi parking, duk suka sauka bayan sun shiga yaune rana ta farko da taji tana jin nawin mutanan gidan Jiddah tayi hugging ɗin ta tace "Aunt Leena" Leena ta gaishe ta, Sultan ma na dariya yace "Aunt amarya" duk ta gashe su, ta karasa ta zauna gefen Mami amma a kasa, sannan ta gaishe ta Mami tace "tashi ki zauna, bana son wani surkuntaka, I'm still the same Mami from years back, please still see me as that Mami, Okay?" Leena ta gyada mata kai. Har dare suka kai a gidan Mami, duk babu wanda ya nuna wa Leena yanzu da baya ba ɗaya take ba, kamar ma yanzu sun fi son ta than a bayan ma, duk suna dinning suna dinner, Leena na kusa da Jidda, Opposite ɗinta kuma Sadeeq ne, bini bini sai ya daga kai ya kalle ta, ganin kamar she's not comfortable kuma kamar ta fi sipping drink din ya dauki nasa ya juye a cup din ta Mami tayi kamar bata gan sa ba, Jiddah ta daga kai sai suka haɗa ido da Sultan, ya Ciro Wayan sa yana kallo sai kuma yace "Ohh, who is she?" Zun zurutun dariya sai da Jiddah ta kware Mami tace "bana son shiririta fah Jiddah" daga haka ta mike ta wuce dakin ta Leena ta ɗan rikice ganin ta kware ta mike zata buɗe mata bottle water Sadeeq yayi saurin rike hannun ta yace "zauna" tace "Zan bata ruwa ne" kallon da yake mata yasa ta koma ta zauna, Jiddah ta sakaita dariyan ta tana kallon Sultan ta yayi kamar be san meke faruwa a wajan ba kamar ba shi yasa ta dariyan ba ya ɗan ware idon sa yana kallon ta yace "what?" ta Harare sa tace "Ban sani ba" yace "Ohh, Toh wacece ita?" Jiddah ta sake fashewa da wani dariyan ta mike tace "Wallahi Ya Sultan baka da kirki" daga haka ta wuce ciki, Sultan ya mike shima yana avoiding eye contact da Sadeeq, Sadeeq ya dawo kusa da Kujeran ta yace "ko ki ci ko nayi feeding din ki" gudun karya bata yasa ta fara ci dan ta ga kamar shi ba kunya gare sa ba. Bayan sun ma Mami sallama, ta haɗa ma Leena su turarurruka ta bata Leena tayi ta godiya, Jiddah ta raka su har compound tana kallon Sadeeq tace "Ya Sadeeq ka bari next tomorrow sai mu hada hanya" ko kallon ta be yi ba yana rike da hannun Leena suka fita. Fu'ad yana kallon abokin na sa da tausayi yace "Toh kai yanzu Rayyan ba yadda za kayi ka yi convincing Mummy akan maganar yarinyar" Rayyan ya sauke ajiyan zuciya yace "Fu'ad ba zaka taba gane wa bane, Mummy bata dauki maganar da sauki ba fa" Fu'ad yace "Wallahi dama kanwata Husna ka aura, kasan tana mugun son ka, kuma nasan zaka iya controlling dinta yadda kake so dan zata bika saboda tana son ka" Rayyan ya daga kansa yana kallon sama shi gaba daya yama rasa wani tunanin zai fara yi a wannan moment ɗin" ya sauke ajiyar zuciya, Fu'ad yace "sai hakuri fah Rayyan, wannan jarabawar ka ne, kayi addu'a Allah baka sa'an ci, kawai kayi biyayya wa mahaifiyar ka" Rayyan ya kalle sa yace "Ni yanzu tashin hankali na idan na tuna bikin wai in 2 weeks time ne" Fu'ad ya dinga kallon sa cike da tausaya masa. Ayrah dake kwance tana waya har pass 11pm sai ga Layla ta shigo, Ayrah tace da wanda take wayan "Excuse me, I'll call back" ta dinga kallon yayar ta ta da ta shigo tace "Amma anty Layla ya kamata kima kanki fada, idan mune muke wannan yawace yawacen ya kamata ki tsawatar mana amma ace ke ne kike yi" Laylan ta sake baki tana kallon ta har ta gama magana ta wanke ta da mari tace "How dare you talk to me like that! Do you think I'm your mate or something? This is the first and last time you'll speak to me like that. Make sure you know what you're saying before you approach me, I'm not your mate Ayrah, Okay?" Ayrah ta rike kuncin ta tana kallon ta ta bangaje ta ta wuce dakin ta.*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧



35.......
Yau wajan kwana 10 kenan da zuwan Leena da mijin ta Sadeeq Abuja, har mamakin yadda suka yi sabo da juna suke yi su, Sadeeq ya sha cewa 'They were made for each other'. Farkawan Leena kenan daga bacci, ta buɗe ido tana kallon kyakkyawan fuskan mijin na ta, yace "Ki daina kallo na kafin kyau na ya kare" dariya ta fara saboda bata ɗauka ya farka ba tace "Ni Karka min sharri, Honey" ta janye jikin ta a nashi, shima tashi yayi yana addu'an tashi a bacci, ta kalli agogon dakin da ke nuni da karfe 6:30am da sauri ta kalle sa tace "Honey, mun makkara fah", bayan sun idar da Sallah su kayi Morning zikr ɗin su tace "Good morning, Lee's Honey" ya ja hancin ta yace "Morning baby" ta langwabar da kai tace "Kaga da ka barni na fara girki da sai yanzu na daura maka ko da light food ne, yanzu kafin ka je ka saya mana breakfast zaka makkara" yace "Oh, so kike ki fara girki ki wahalar min da kanki?" ya ja hancin ta yace "Maybe sai kin haifa min yara goma masu kama da ke sai ki fara" ta harare sa ta mike tana ninke Hijab ɗin ta tace "Yara goma sai kace wata inji" yayi dariya tace "at least da ka bari na fara kaga irin wannan rana sai kawai na mana breakfast fah" yace "sai mu sha tea da snacks ko?". Bayan Sadeeq ya gama breakfast har bakin motar ta raka sa ta mika masa briefcase dinsa sai kallon ta yake yi sannan ya karba tana waving ɗin sa har ya fita, ta koma cikin gida. Bayan Rayyan yayi parking kofar gidan su Layla, ya kira ta a waya, tana ɗauka yace "Kiyi sauri zan wuce office ne" daga haka ya katse kiran ba'a dau lokaci ba sai gata ta fito sai wani sheki skin ɗinta yake yi, front seat ta buɗe ta shiga tayi kasa da murya ta gaishe sa ya amsa, hannun sa ya kai wajan da kafafun ta yake ya ɗauki ladan wajan ya mika mata yace "Here is it" ta karba tana Godiya, sai kuma tace "Wai da gaske kake dama ba zaka yi attending any events ba?" yace "Meyasa kike son na ringa repeating kai na ne?" tace "Well, ɗan anjima zan tafi saloon, da yamma kuma, zamu fara event" yace "tun daga yanzu?" tace "Kai baby, yau fah saura 4 days shine tun daga yanzu" yace "Okay" duk maganan nan gaban motar dinsa yake kallo ita kuma ta zuba masa idanun ta, ya ɗan kalle ta yace "Toh zan tafi ko?" tace "Okay, take care of yourself for me, please" daga haka ta sauka tana waving dinsa, shi kuma yaja motar sa yayi gaba. Daidai wani eatry Leena tayi parking moton ta, ta sauka ta shiga ciki tayi ordern abinci tace a takeaway za'a zuba mata, bayan ta karba ta kama hanyar inda Sadeeq yake aiki, a daidai organization ɗin su tayi parking, tun daga bakin gate gatekeeper suka fara gaishe ta saboda sun san matar Sadeeq ne, tun da take haduwa da mutane kowa with respect ke gaishe ta har ta haura first floor, knocking office dinsa tayi yace "Who is it?" tayi shiru tana murmushi, ta sake knocking ya sake cewa "who is it?" taki magana , bayan ta sake knocking taji yaki amsa wa, ta dinga knocking Sadeeq yayi banza da ita, sanin ba zai amsa ba ta dinga dariya saboda komai na Sadeeq yana burgeta hankalin ta a kwance ta san 'yan mata ba ganin fuskan sa zasu yi ba, Ciro wayan ta tayi ta kira sa ya daga yace "Sweetheart, I miss you" tace "Toh buɗe min" yace "Ina?" tace "Office ɗin ka mana" ya katse kiran ya je ya buɗe mata ya sake baki yana kallon ta sai kuma ya masa mata ta shiga yace "Kamar kin san ina missing dinki" ta ajiye abincin akan table din gaban sa tace "Na san baka ci abinci ba ko? To gashi" ya langwabar da kai yana kallon ta yace "Sure, baby" tace "toh barin koma gida" ya mike sai kuma yaga tarin aikin dake kan table din sa yace "Oops da ba dan aiki ya min yawa ba, da na bikin mun koma gida tare" tace "Just take your time, Honey" daga haka ta fita tana kara jin son mijin nata har bargon jikin ta. Nisreen ta shiga parlorn na su da sallama, ta ajiye ghana-must-go ɗin hannun ta tace "Mummy ga ɗinkin nan" Mummy tace "Na Mother Eve din fah, Ya samu ya gama?" Nisreen tace "yana ciki" duk ta juye su nan kan kujera ta fara sorting nata out, Mummy ta dauki wani gown din dinner ɗinta tana kallo, Nisreen ta juya tana kallon Niswa da ko sau daya bata kalle su ba balle tayi magana akan nata dinkunan tace "Anty Niswa ba zaki duba na ki kayan ki gani ba?" Niswa taja tsaki Mummy ta sake baki tana kallon ta tace "Niswa bana son neman magana fah" daga haka Niswa ta mike ta wuce ɗakin su, Mummy ta bita da kallo, Nisreen tace "bari zan cire nata sai na kai mata" Mummy ta dauki nata tace "Ki kyale ta" daga haka ta wuce dakin ta da nata kayan a hannu, bayan Nisreen tabi Niswa daki da kayan tace "Ga naki kayan" sai sannan Niswa ta kalle ta tace "Toh ni nace a dinka min?" Nisreen tace "ashoben bikin Yaya ne fa? Niswa taja tsaki tace "Da kun san yadda na tsana Laylan nan wallahi ba wanda zai ce zai na min magana akan ta" Nisreen tace "ki daina fada haka kin san Mummy da Yaya ba zasuji dadi ba" Niswa tace "Dalla min shiru ke me kika tsani? Toh uban waya ce miki Yayan ma yana son ta ne? Wai fah akan ta har Mummy tabi bayan cin mutuncin da ta min wallahi idan naga dama sai na fadawa Daddy duk abinda ke faruwa a gidan nan inya so duk abunda zai faru ya faru, kowa ya huta shikenan ai" Nisree ta rufe bakin ta da hannun biyu tana kallon Niswa. Anyi decor cikin gidan nasu da balloons gurin har ya gaji da kyau tsabar yadda aka tsara sa ga wani babban banner dake rubuce da Layla's henna party, ga kuma friends dinta ta sukayi anko, Layla sai sheki ta keyi cikin shigar ta me kyau. Leena tana zaune a comfort zone ɗinta da ke cikin parlorn ta, a edge din parlon tayi creating wani waje ta gyara tayi arranging duk wani stuff da zata buka ta na creative writing ɗinta, ga kuma ɗan karamin bookshelf a gefe, ta mayar da hankalin ta kan rubutun poem da zata yi performing a wani organization, like kamar advertising zata musu, ji tayi an dafa ta ta baya a zabure ta mike tana kwala ihu da sauri Sadeeq ya rungume ta duk ya rike ce yace "I'm Sorry, baby" sai sannan tayi shiru tana maida numfashi leka fuskan ta yayi yace "Sorry, ban san zaki tsorata har haka ba" tace "ban fa ji shigowar ka bane, kuma ka zo da motar ka kuma?" yace "naga ai kinyi nisa cikin imagination world ɗinki, shiyasa ma baki ji shigowa ta ba" sai kuma ya fara dariya yace"ashe babyn tawa matsoraciya ce" ta zauna tana kallon sa, sai kuma ta mika masa papern da tayi rubutu tace "Taya ni gani ka ga ko akwai Abunda zan kara" ya karba yana mamaki irin talent dinta yace "baby, everything is great" tace "gobe ina performing next tomorrow sai tafiya Kaduna ko?" Kai kawai ya gƴaɗa mata, daga haka ya wuce ciki, itama ta ajiye papern ta mike tabi bayan sa. Mummy da take tsaye akan Rayyan tace "Toh yanzu saura kamin Transfer din 1 mil ko?" ba shi ba hatta Niswa saida ta daga kai tana kallon Mummy sai kuma ta taɓe baki saboda karban kudin Mummy yanzu ya fara yawa, Rayyan yace "1 mil kuma Mummy?" tace "Eh mana, ko baka ji bane zaka kuma tambaya ta?" ya girgiza kai yace "me kuma za'ayi da wannan kudin?" tace "Okay, tambaya ta kake sai na baka amsa kafin ka bani kuɗin?" Niswa tana ta Allah, Allah karya sa Rayyan ya bada, Rayyan yace "Wai dama naji ko important abu ne saboda ba kudin yanzu a waje na" ta masa wani kallo yace "I'm telling you, Mummy, bani da kudi" ta mike tace "toh ai shikenan, dama Hajiya Fatima ne ke bukata wai zasu kara ma masu organizing mother's Eve" daga haka ta wuce ciki Niswa tayi kasa da murya tace "Yaya wallahi gwara da baka bada ba, dan Allah duk sanda Mummy zata ce ka bada kace baka da kudi, taya dan rainin hankali su kama wajan event kuma suce babu kudi" kallon ta kawai yake har ta kai aya daga haka ya mike ya fita. Jiddah ce take knocking a kofar gidan su Sadeeq, Leena dake jikin Sadeeq ta kalle sa tace "kamar fah knocking akeyi" be tanka ta ba ya ci-gaba da cika file da yake yi a wayan sa ta mayar da kanta kan chest ɗin sa sanin kuma ba zai ce wani abun ba, sake knocking akayi tace " Honey kamar fah knocking akeyi" ya ajiye wayan hannun sa ya dago da kanta yana kallon ta yace "akan ki ake knocking ɗin?" tace "How?" yayi kissing dinsa yace "then, sai kiyi kamar baki ji ba, koma waye ne ya koma ba zai ɓata min wannan precious moments din ba" ta kwanta abunta tayi kasa da murya tace "kasan anty Jidda tace idan ta samu lokacin zata zo min ne" yace "Who is she?" tayi dariya tace "haba mana" yace "Ohh toh uwar me Jiddahn zata Miki? tayi wucewar ta kawai, yanzu kila Sultan ya koma Kaduna ne" tace "Ya zo ne?" yace "Eh" tace "shine be zo mana ba" yace "Nine ban so ba" tayi shiru taga kamar akan ta har Sultan be yarda da shi ba can tace "Amma kamar they love each other ko?" yace "ki bar munafukai tun suna yara suke son juna, dalilin da yasa ya dawo gidan mu kenan, sai daga baya suka yi fada har ya kai daga baya Sultan ya fara neman wata zai aura ganin Jiddah taki sauransa amma da ta ga maganar zai yi karfi Jiddah ta fara masa hauka har sai daya janye maganar" tayi shiru tana tunani yace "maganar da nake faɗa miki bai wani daɗe ba" tace "Nima zan so ganin sun yi aure, cos sun dace kuma kana ganin su kasan suna son junan su" yace "Uhm" duk maganar da suke yi ba'a daina knocking kofar ba, wayan sa ya fara ringing ya kalli me kiran yace "Inaga Jiddahn ne dan itace ke kiran" Leena ta sauka a jikin sa tace "inje in buɗe?" ya harare ta yace "idan ita da wani katon ne kuma fah?" Leena tayi dariya tana kallon sa har ya fita, yana budewa kuwa yaga Jiddah, babu alamar wasa a fuskar sa ya amsa
End Ads