x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - AGOLA free pages

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
"kaji ka da wata maganar kuma" tayi tsuka Leena tace "ya Rain I begged her before she gave me one meat, and she even insulted me" Rayyan yana murmushi yace "it's Okay" Hajiya tace "inma gulma ta kukayi toh da ubanku kukayi ba ni ba, Atoh danni na haife sa gwara ku sani" Leena ta tashi tayi wucewar ta Rayyan yace "Haba Hajiya taya za muyi gulman ki, barin tafi dama na shigo na gaishe ki ne" tace "toh dan Albarka, da daddare dai karka manta ka zo min da nama irin wannan din" yace "in shaa Allah". Leena ta kusan isa part dinsu sai ga Nisreen tazo da gudu ta wanke ta da mari Leena ta tsaya cak tana kallon tace "What did I do to deserve a slap from you?" tace "Ban sani ba" kafin ta karasa rufe bakin ta Rayyan ya sauke mata mari yace "Nisreen ban hana ki mugunta ba, me ma tayi miki da zaki mare ta?" Kawai Nisreen ta fashe da kuka tace "Yaya Rayyan, I'm your biological sister, so why do you love Leena more than me" ya jata zuwa jikin shi yace "I love you equally, and you're both my sister, okay?, toh me ta Miki da zaki mare ta?" tace "an yaga min assignment dina ne kuma nasan itace And she's not your sister, she's just a Agola" tsawa ya daka mata, Leena ta daga kafadan ta tace "Do what suits you, okay? As Agola, I know I'm better than you in every aspect, so Alhamdulillah!" ta juya ta fara tafiyan ka tsaita Ba nisreen ba har Rayyan sai da yayi mamakin ta ya kama hannun Nisreen ya jata zuwa part din su yana mata magana akan su daina ma Leena abubuwan da suke mata har suka isa kofar parlorn suna shiga suka ga Mummy na parlorn tana aiki a system Nisreen ganin Mummy a parlorn yasa take matsar kallo Rayyan ya fake idon Mummy yace "ki sake kice na mara ki kiga" yace "Mummy sannu da aiki" ta ɗaga kanta ta mishi kallo daya tace "thank you" sai kuma ta ajiye aikin da take yi a gefe tana kallon Nisreen tace "ke! Kinje kin same ta ɗin?" ta gyaɗa mata kai kawai Mummy tace "bana son shashan ci ki buɗe baki kimin bayani ko dai kin zama jaka ne kika bari Leena ta dake ki?" tace "A'a ai ina zuwa na mare ta" Rayyan yace "Mummy me ta mata kuma?" tace "Assignment din Nisreen ta yaga" yace "ya akayi kuka sani?" tace "toh waye mate din Nisreen din a gidan nan?" Yace "toh ai naga ko nan part din bata shigowa" tace "toh ai ga fuska ta Sai kazo ka rama mata, mara kunya" Rayyan yaja bakin sa yayi shiru sai ga Niswa ta fito a kitchen tace "Big bro baka san yarinyar nan bane, sai ta ringa abu cikin katsaita da gadara gata da rashin kunya" Rayyan ko daga kansa yaga Niswa baiyi ba balle tasan yasan da ita a wajan, Niswa tace "ko fa a school ne sai kaga kowa ya fi tson Leena akan Nisreen, harda teachers dinmu Gashi dai aji daya suke amma kowa Leena" sai sannan Rayyan ya daga kansa for the first time ya kalle ta yace "ashe kenan bata da rashin kunya tunda She's the favorite of everyone" Yana kai wa nan ya tashi ya fice a parlorn Mummy ta bishi da kallo tace "anya ba lashe min zuciyan ɗa suka yi ba?" Niswa tace "Hmm mummy ga alama,. Da daddare Rayyan ya shigo gidan da leda guda uku a hannun sa direct part din Hajiya ya wuce ya shiga parlorn da Sallah, Hajiya sauraron labarai ta dauke muryan TV tana kallon sa tana yake hakora ya mika mata daya daga cikin laidan daya shigo da shi yace Hajiya ga sakon ki washe haƙora tayi ta karɓa tana cewa "Ayyah riyan, Allah saka maka ya baka mace ta gari da ƴaƴa masu Albarka kamar ka" yace "Amin Hajiya" He's starring all around the parlor as if there's something he wants to see, can ya curo wayan sa ya fara danne danne can dai ya kalli Hajiya yace "Hajiya ina Leena?" tace ai bata shigo ba" yace "Ai na dauka anan zata kwana" tace "kasan ƴar nan kuwa Ni fah tsoro ma take bani idan tana wasu abubuwan wallahi, ɗazu fah tana shigowa taga Uwarku kawai tayi juyawan ta shine har yanzu bata kuma dawowa ba" Rayyan ya mike yace "sai da safe" Hajiya tace "Allah tashe mu lafiya" yana fita Hajiya tace ji gantalelle ina masa maga kawai zai sa kai ya barni kamar mahaukaciya ai halin ka daya da Linan ai sai suyi ta abu kamar daga gidan sarauta suka fito idan ka kalle su kuma sai suyi yare suna zagin ka, ɗaukar kazanta tayi ta wuce daki. Rayyan be tsaya ko ina ba sai part din su Leena ya gwaɗa burɗa handle parlorn yaji a kulle yayi knocking sau uku ba'a amsa mishi ba sai ya ɗanyi magana yace "Leena it's me, zo ki buɗe" to his surprise tace "I'm coming" after some minutes tazo ta buɗe masa kiran tace "good evening" yace "Why not to stay with Hajiya tonight instead of sleeping here alone Leena?" tace "ya Rain kasan bana son Gori ba, right? So I prefer to stay here rather than go there" Rayyan ya tsaya kallon ta shi mamakin maganganun Leena na basa mamaki gata yarinya amma kamar wacca ake sa mata magana a baki, ga zuciya ga rashin tsoro yace "Okay, gashi" ya karasa maganan yana mika mata ledan hannun sa ta karba tana washe baki at same time tana leka cikin laidan tace "Wow, it's chicken, thank you Ya Rain" yace 'Rayyan not Rain" tayi dariya tana gyada masa kai yace "okay, good night" tace "bye" taja kofar ta kulle". Washe gari Rayyan yana zuwa a masallaci ya wuce part din Hajiya bayan ya gaishe ta ya wuce part din su Leena knocking yayi har sai da ya tabbatar ta tashi sannan ya tafi, Leena ta shiga toilet tayi brush sannan ta wasa ruwa tana fitowa ta shimfida sallaya tayi sallah tana idar wa tayi morning azkar yadda Ammin ta takoya mata, sannan ta tashi ta sa uniform ta haɗa cornflakes tasha ta dauki wani cup mai murfi ta zuba Golden morn, madara da sigar a cup din sannan ta rufe tasa a cikin jakkan ta, ta dau bottle water daya shima tasa a cikin jakkan before 7am har ta gama shirya wa ta fita taja kofar parlorn su ta wuce part din Hajiya ta gaishe ta sannan ta fito tayi car park gudun karsu shirya su tafi su barta Daddy ne ya buɗe gate din ya shigo Leena na kallon sa ta fara masa murmushi shima murmushi yake mata saboda Daddy yana kaunan ganin yara masu kokari shi ko nawa ne idan har yaro zaiyi karatu toh bazai ji kyashin kashe masa ko last card dinsa ba ga Leena kuma so gifted shiyasa yake son yarinyar da gudu taje jikin sa tana gaishe sa ya amsa da fara'a ya rike hannun ta suna hira har suka karasa part din Daddy ya bude kofan suka shiga tare ya nuna mata kan cushion yace ta zauna Ita kuwa sai basa labarin school take tayi Rayyan yayi sallama ya shiga parlorn ya gaishe da Daddy, Leena na kallon sa tace "Good morning ya Rain" Abba yayi murmushi Rayyan yace "trust you had a night rest?" ta gyaɗa masa kai sai ga Mummy ta Nisreen da Niswa sun shigo parlorn suma, Ganin Leena da Mummy tayi ta sake baki tana kallon ta sannan ta daka mata tsawa
Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧

_By Jiddatul-khayr_

~Book 1~
Chapter 2
Alhamdu Lillah
Tace "Uban waya baki livern shigowa nan" Camly Daddy yace "da ita kike yi ko dani?" ta juya tana kallon sa tace "Wai kai meyasa baka son ana mata faɗa ne, tana Agola har zata shigo part din mai gidan" Rayyan ya ɗaga kai for the first time yana kallon Mummyn nashi Daddy yace "Look! Da safen nan karki soma Khadija, Please I beg you" sum sum Leena ta sauka akan kujeran Rayyan ya mata alama da ta koma ta zauna ta ɗauke kai kamar bata gansa ba, Daddy yace "Leena go back" tace "Daddy na bar Assignment dina a cikin gida ne" bata jira cewar sa ba tayi tafiyar ta, parking space ta wuce ta share hawaye daya gangaro mata, Daddy yace "This is rubbish, Khadija. What have you been doing? This is nonsense! tsanar da kike ma yarinyar nan bansan daga ina kika koyo ba, Is this behavior driven by jealousy? wannan jahilci ne, dan banga ta inda ake wannan abun ba, kishi da yarinya how Please?" yayi tsaki yace "ya kamata ki chanza dan ɗa na kowa ne kuma baki san me gobe zata haifar ba" Mummy na kallon sa cikin ido tace "wato nice jahilan kenan ko?" Daddy yace "I didn't say that, but you're acting like it" Rayyan ne ya tashi zai fita sai Nisreen da Niswa suma suka mike Daddy yace "Sorry girls, school zaku tafi ko?" suka tsaya suka gaishe sa ya amsa sannan suka fita yana kallon Mummyn dake boiling ta ciki yace "Bari na ɗan kwanta sai 9am nake son na tashi" be jira cewar ta ba ya wuce ciki abin sa, Mummy tayi like 3 mins sannan itama ta fita direct parking space ta wuce ta hango driver daga nesa yana taho, ta samu Nisreen da Niswa har sun shige motan ita kuma Leena na tsaye a waje dama haka take bata yarda ta shiga har sai driver yazo dan ko ta shiga ma faɗa zasu fara ko da gangan su bata mata uniform, Leena tunda ta hango Mummy na doso su hankalin ta yayi mugun tashi Mummy na karaso su ta ɗauke Leena da mari Nisreen ta kwashe da dariya dama kofar motar a buɗe take Mummy tace "shegiya ki wuce ciki, yau zanga uban da zai tsaya Miki, wannan ai ba uwarki bace ta tsiya motar ko? to babu ke babu zuwa makaranta a cikin ta" Leena tana tsaye a wajen ko motsa wa ba tayi ba balle ka fahimci ita aka mara Mummy ta daka mata tsawa tace "Dan ubanki har ina magana zaki shareni, wuyanki ai yakai yanka da kina makarantar da ƴaƴan mai gidan suke ba dole ki ga kina daidai da kowa ba, to daga yau kin bar zuwa makarantar, wuce min ki bani guri" Leena tace "Dan Allah Mummy kiyi hakuri amma karki hanani zuwa makaranta" Mummy ta kuma sauke mata wata marin Leena ta rike kuncin ta ta fara tafiya Mummy ko amsa gaisuwar driver da ya karaso wajan ba tayi ba ta wuce ciki inda zai kaita part dinta, driver a ranshi yake jinjina irin mugunta na Mummyn, Leena ta kusa karasa part dinsu taci karo da Rayyan daya fito daga part din Hajiya kallon Leena yake da take tafiya absent-minded da wani mugun ja da fuskanta yayi ga shatin hannu baro baro ya bayyana a fuskar ta ga kuma jaa da idon ta yayi yasa gaba ɗaya attention dinsa ya koma kanta kallon har zata wuce sa bata ma ankara da shi ba yasa ya riko hannun ta sannan ta ɗaga kai da sauri ta kalle sa yace "What's wrong, Leena? Is everything Okay? Tell me please?" Gaba daya hankalin sa ya tashi sai sannan hawaye ya soma zuba daga idon ta ta kwace hannun ta acikin nashi ta girgiza masa kai sannan ta wuce da gudu yana kallon ta ya gagara motsa wa jin mai gadi yana buɗe gate yayi hanzari wuce car park tun kan ya karasa har driver already ya riga da ya fita" nan ya tsaya har ran sa bai son abunda maman sa take ai katawa ba, part din su Leena ya koma ya kama handle din kofar yaji ta a kulle yayi knocking yace "Leena kizo ki buɗe min, Please" Leena dake kwance kan sofa tana kuka kamar ba zata tashi ba amma jin yana rokon ta yasa taje ta buɗe masa tana budewa taja baya ta tsaya tana kallon kasa bata son yaga tana kuka ne, kallon ta yake sannan ya shiga parlorn ya kulle kofan ya ɗurku sa kan kneel ɗinsa yana kallon ta yace me yasa baki tafi makarantar ba? kai kawai ta girgiza masa yace "Tell me? Mummy ce ta hanaki tafiya ko?" tayi shiru starring at one place yace "Leena you keep mute" hawayen suka fara sintiri a fuskar fiye da yadda dazu suke zuba tace "Please, ya Rain karka bari mummy ta cire Ni a school dan Allah" sai sannan ta fashe da kuka ya jawo ta jikin sa while patting her back yace "it's okay Leena, ki daina kukan nan" He doesn't know what to say, exactly, he's just lost for words kawai ya mike ya buɗe kofar ya fita Leena ta danne kofar sannan ta koma kan sofa tana sheshsheka. Sai around 10am ta farko dakin ta ta wuce ta cire uniform dinta a ran ta kuma tana addu'an Allah kawo Ammin ta yau, yunwa ta fara ji ta dauka jotting book dinta ta fice daga part din su ta kulle kofa ta wuce part din Hajiya dake gyara foot mat din gaban kofar parlorn ta ta daga kai tana kallon Leena da mamaki, Hajiya tace "ke kuma me ya hanaki zuwa makarantar yau kuma?" Leena ta karasa bakin kofar shiga tana girgiza ma Hajiya kai Hajiya tace "Dadina dake ba buɗe baki zakiyi kima mutun magana ba" tasa kafan ta daya a ciki zata sa ɗayan Hajiya ta rike ta ta sake baki tana kallon fuskanta tace "Ke kuma Leena yaushe fuskan ki ya canza launi?" Leena ta girgiza kai bata ce komai ba Hajiya tace "ba zaki buɗe baki kiyi min magana ba?" Leena bata ce komai ba ta karasa cikin parlorn ta kwanta a cushion Hajiya ta sake biyo ta tace "kar dai wancan matan ne ta miki wannan abu ? Kuma ita ta hana ki zuwa makarantar ko?" Leena tace "Hajiya yunwa nake ji" Hajiya tace "ke bansan wacce iri yarinya bace ke, ayi ta tambayar ki abu kina ji kiki bada amsa, toh kinma kanki, kuma matan bata baki karin kumollo ɗin ba ko" ta wuce kitchen sai kuma ta fito tace "zaki sha shayi ne? Ko kuma da me kike so? tace "tea, bread, egg" tinawa tayi da naman ta na jiya sai kuma tayi shiru Hajiya tace toh ta wuce kitchen dan debo mata ruwan tea tana ta mita ita kaɗai tace "Anya kishiyar uwarkin nan zata ga Annabi? Mata kawai mugunta kamar kafiran farko? Bata da ɗigon imaani nake gani wallahi, mutun marainiya ma ace ana musguna masa, Ni fah gani nake harda haushin fuskan nan naki take ji wallahi ba ta ganki Ma shaa Allah ba, ƴaƴan nata kuwa hmm Allah kyauta dai" ta karasa tana mita ita kaɗai ta fito ta mika mata shayi da bread din hannun ta ,Leena ta tashi ta karɓa sai kuma tana kallon Hajiya tace "toh Hajiya baki sa egg ɗin ba" Hajiya tace "Ni fah wannan mugun halin naki ne bana so" Leena ta bata rai tace "Toh ai ban iya cin empty bread bane" Hajiya tace "wallahi Sa'a ɗaya kika ci dan Uwarki na wahala dani tana min komai shiyasa zan je na soya Miki". Tunda Rayyan ya koma dakin sa wani zazzaɓi ya fara ji gani yake ba zai iya tafiya aikin Bama gaɓa daya ya ma rasa meke masa dadi bai san ta ina zaima Mummyn sa magana ta fahimce sa akan Leena ba, yarinya ce karama toh me laifinta, for the 3rd time Mummy ta shigo ɗakin tana kallon sa taba sa tayi tace "Rayyan toh ko breakfast din ba za kayi ba? girgiza kansa yayi sannan ya tashi ya zauna yana facing dinta tace "toh ko zaka tafi aiki sai su duba ka" yace "it's just slight headache kuma na sha magani i'll be fine" daga haka ya koma ya kwanta tace "Allah kara sauki toh" ta tashi ta fita ta ja masa kofa. Da yamma Leena ta shirya cikin uniform ɗinta na islamiyya ta wuce part din Hajiya tace "Hajiya zan tafi islamiyya" Hajiya tace "toh adawo lafiya" Leena tace "toh ki bani chocolate" Hajiya ta sake baki tana kallon tace "Toh ai yayan naki riyan bai siyo ya kawo min ba balle ki tambaye Ni, kema ba ajiya kika banba" tace "toh Hajiya ki kira min Ammi na na gaishe ta" Hajiya tace "dauko wayan a cikin daki Allah sa dai yanzun a same ta" bayan Hajiya ta kira Ammi yanzun ma akashe take Leena ta juya ta fita duk jikinta yayi sanyi a bakin gate da gaida mai gadin ya amsa yana yake mata haƙora sai kuma can yace "Toh ke Leena baki gayawa Alhaji bane Hajiya karama ta hanaki zuwa boko?" Leena ta kalle sa sai kuma bata ce komai ba sai kuma ta kara kallon sa ta girgiza masa kai ya bude bata kofar fita tace "sai na dawo" yace "toh ƴar Albarka" tana tafiya tana ta bitan karatun ta har ta isa islamiyya. Da daddare Leena na kwance a kujeran Hajiya saiga Nisreen ta shigo da sallama Hajiya ta daga kanta ta mata kallo daya sai kuma ta mayar da kallon ta kan Leena tace "Leena tunda Uwarki bata da mugun hali wallahi zaki sha mamaki yadda rayuwan ki zai canza idan kika girma" Nisreen ta taɓe baki sai kuma tace "Hajiya baki san me ba, yau a school ba muka yi test, aka bamu Assignment, test din fa yayi daɗi kuma" Leena tayi kamar bata ji ta ba, Hajiya tace "Bana son munafurci dama can kina zuwa nan ne balle kimin taɗin makaranta" tace "kai Hajiya" Hajiya tace "yau din kuma uwar taki bazata bani abincin daren bane?" tace
End Ads