x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 38 - AGOLA free pages

  • 111001 words
  • 114000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
kanta jikin cushion ɗin, ya mike yace "barin bi bayan ta". A mugun ruɗe Hajiya ta dawo gida ita bata ma san mai ya kawo ta gidan ba, suna gama magana da Binta ta kama hanyar gida bata kai ga shiga part ɗin Daddy ba ta hango Rayyan da shigowan sa gidan kenan da saurin ta ta fara zuwa inda yake shi kuma ya zuba mata ido har ta karasa ya buɗe baki zai yi magana ta riga sa "Rayyan ka taimake mu, yarinyar nan rai a hannun Allah ita da abinda zata haifa, yanzu sunce aiki CS yake ko me? Toh shi za'a mata, ga miji ya sake ta kuma ba wanda zai sa mata hannu" with totally speechless Rayyan ke kallon ta haka mamaki karara written all over his face Hajiya tace "Ji kuma wani wulakanci ina maka magana zaka zuba min idanu kana kallo na, ko kaima ka koma kamar ubanka da uwarka ta shanye ne?" Sai sannan yayi gathering courage dinsa yace "No Hajiya ban fahimci me kike nufi bane?" Hajiya ta kama hannu sa ta fara ja, yana shiga Mota ya jata a mugun speed bayan Hajiya ta fada masa asibitin da suke, Hajiya sai ihu take masa ya rage gudun da yake amma ina baya ko sauraran ta sabar yadda zuciyarsa ke bugawa. Mai aikin Mummy da gudu ta shiga parlorn tana "Hajiya!" Mummy da yaranta mata dake breakfast a dinning ta daga kai tana kallon ta tace "ke wata irin mara hankali ce" Niswa ta ja dogon tsaki tace "Ni wai Meyasa kike abu kamar dabbace" tayi kasa da murya tace "kiyi hakuri Hajiya dama labari ne na kawo muku" Mummy ta ajiye spoon ɗin hannun ta tace "Ina jinki" yarinyar tana murmushi tace "Dama jiya da Daddare dana je duba sauran abinci a kitchen ɗin waje naga mai gadi ya buɗe gate sai kuma ya koma bangaren Maman Ayaan can sai ga kanwar ta na Niger ɗin ta fito, ba'a dau lokaci ba sai ga itama da kanta ta fito sukayi gate naga sun Shigo da Leena kamar ta suma ne ma nake ga, dazu da safe kuma sai ga Hajiya ta shigo a ruɗe lokacin Ɗan ki ya shigo da motar sa da gudu tayi kansa tana cewa wai ya taimaka ita kuma Linan da abinda yake cikin ta zasu mutu, kuma wai mijin ya sake ta sannan.." Mummy ta katse ta da sauri ta fara dariya tace "Toh dama meya kaisa zama da gayyar tsiya? Je ki na gode, tabbas kina da dubu goma na wannan labarin mai daɗi" yarinyar ta fita tana Godiya Niswa tace "Oh'oh yanzu zamu ga yadda za suyi ai, kullum gadaran su wannan shegiyar kyaun nasu" har sannan Mummy na dariya Nisreen tace "amma nikam i feel bad for her, ba daɗi wallahi, Allah basu lafiya toh" Niswa wani kallo take mata Mummy kam buga mata baki tayi tace "Shegiya mai bakar aniya, da a baya niswa ce bata goyon baya na amma yanzu naga kece kike son ki daina" Nisreen ta mike tana rike da bakin ta tace "amma ai gaskiya na fada, sannan ba wanda zai so haka, atleast tunda bata auri Ya Rayyan ba ai shikenan sai ku hakura kuma haka nan" Mummy ta dauki mug ta wurge ta da gudu ta masa cup din ya faɗa kasa ya tarwase, Mummy ta dauki Wayan ta tashi kiran wani number. Ko gama parking mai kyau Rayyan me yi ba, da sauri ya sauka ya wuce ciki, sai sannan ya tuna ashe shi be san inda take ba dan ya bar Hajiya a baya ganin anty Binta yasa yayi wajan da sauri ya tambaye ta nan ta nuna masa inda suke, ko Ammi bai lura ba ya banka ɗa kofar dakin da take ciki ya karasa har inda take, ya fita ya farawa Nurses ɗin wajan ihuu kamar zai dake su, wani doctor ne ya karasa inda yake ya fara masa magana a hankali Rayyan yace "Ba za'a duba condition dinta ba lalle sai ansa hannu idan ta mutu kuma fah?" daga haka wasu daga cikin Nurses suka yi kansa sannin cewa shima likita ne kuma yakan zo asibitin, rigar aiki yasa ajikin sa da kansa ya kaita dakin da zasu mata aiki, tare da taimakon wasu likitoci suka mata aiki. Malik tunda ya koma gida ya kasa samun nutsuwa haka nan yaji damuwar Leena ya tsaya masa arai ya rasa yadda zai yi, har ya tafi makarantar da yake koyarwa amma hankalin sa na kan ta, daga karshe ya bar makarantar ya kama hanyar gidan su Leena, bayan yayi parking mashin ɗin sa ya sauka gatekeeper ya leko jin anyi parking machine nan da nan ya tuna Mutumin jiya ne a ransa ko yace ikon Allah, to ko dan uwan Leenan ne?


Idan na samu more reaction zaku iya samun update da Daddare.


Jiddatul-khayr✍🏼
08110615256
*AGOLA

Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION

Chapter 44




______Bayan ya karasa suka gaisa Malik yace "Dan Allah ina son sani wani hali Leena take ciki?" Baba mai gadi yace "Ai tun jiya da Daddaren suka tafi asibiti so har sannan ba su dawo ba" Malik ya dinga kallon sa sai kuma yace "Toh Allah bata lafiya" jiki a sanyaye ya koma gida dan ji yayi ba zai iya koyarwa a yadda yake ji ba".  Sultan tunda ya shiga parlorn yake kallon Mami data yi shiru tana kallon waje daya ta daga kai tana kallon Sultan tace "Naje ba kowa a gidan nasu, ina kuma suka tafi? yarinyar nan ace haihuwa ya taso mata ya zata yi?" Sultan ya karasa cikin parlorn ya zauna inda Jiddah ke zaune ya zauna yace "Mami kiyi hakuri nasa ana min tracking din sa, so! Everything will be Okay, by Allah grace" Mami ta sauke ajiyan zuciya tace "Allah yasa a dace toh" yace "Amin".. "Alhamdulillah" Rayyan ya furta ganin sun gama aiki successfully, ya duka ya dauki Babyn yana kallo sa, sai kuma ya kalli Leena, bai taɓa aiki ma wani ba yaji tausayin sa har cikin ransa kamar yau da yayi wa Leena aiki, dan har sai da ya zubda hawaye ganin yadda take wahala, har sannan yana rike da Babyn a hannun sa, sauran Nurses matan kuma suka gama dressing ɗin ta, Rayyan ya duka a gabanta ya sakar mata murmushi yace "Sorry lil sis, Allah baki lafiya?" Kallon Babyn hannun nasa kawai take yi ba tare da ta basa amsa ba ganin haka ya ajiye mata Baby a jikin ta nan da nan yaga hawaye ya fara sauka a idon ta da sauri ya daga Babyn yana kallon ta yace "Be strong please, ke fah jaruma ce" bata ce masa komai ba, bayan wata Nurse mace ta mata allura, ta rufe idon ta Rayyan ya gyara mata kwanciyar ta sannan ya mike, buɗe kofar yayi kana ganin Ammi sai ka tausaya mata yadda ta koma, duk suka daga kai jin an buɗe kofar dakin ganin Rayyan rike da Babyn yasa duk suka yo kansa, Rayyan ya mika wa Ammi, Ammi bata karbi Babyn ba tace "Leenan fah Rayyan?" yace "Ta samu bacci itama, amma zata zauna a asibiti for 7days" Ammi tace "Jikin nata fah" yace "Alhamdulillah" Hajiya tasa hannu ta karbi ɗan tana kallon sa, Anty Binta ma ɗan take kallo a hankali ta furta "Ma Shaa Allah" tana kallon hadaddan kayan Babyn da Rayyan yasa wata Nurse ta saya, dan babu wani kayan haihuwa da suka zo da shi asibiti. Ganin wayan sa na ringing ya daga da sauri yace "Luxurious accommodation kuma?" ya kalli Mami sai kuma yace "Alright, thank you" daga haka ya katse kiran  kafin yayi magana Mami ta riga sa tace "A can Sadeeq ɗin su ke ko?" Kai kawai ya gyaɗa mata tace "Toh shi a wani rashin hankali zai dauki mata da tsohon ciki ya kaita can" daga haka ta ɗauki keyn motar ta, Sultan ya kalle ta sai kuma yace "Mami ki bari Zanje da kaina, no need ki tafi kina bukatar hutu" wani kallo ta masa tace "kana tunanin zai ji maganar ka ne har ya biyo ka gida?" daga haka tayi kofa Jiddah ta mike yace "Ki zauna dear, kina bukatar hutu" ya sakar mata murmushi ka mayar masa daga haka ya bi bayan Mami da sauri, ya samu har ta shiga motar ta yace "Barin kaimu Mami" ta fita ta zaga zuwa dayan side ɗin motar ya tada motar sai kuma ya dauki wayar sa ya kira mutanan da suke basa info yana daga wa Sultan yace "ina son genuine details pls" daga haka ya katse kiran sai da suka yi tafiya mai nisa sosai sannan suka isa Luxurious accommodation, bayan yayi parking a compound ɗin ya Ciro wayan sa yana duba detail da aka turo masa just of recently, sannan suka kama shiga hanyar reception. Wani matsakaicin gidan ne mai dauke da ɗa karamin ciki da parlor sai kuma wani dan karamin dakin a gefe, gaka ganin gidan kasan kawai wadatar zuci gare su, dan basu da komai wanda zai nuna suna da hali, gaba ɗaya sun yi depending akan ɗan su ɗaya tilo, wanda shima inda yake aiki albashin nasa bai wuce dubu ishirin ba, rayuwar su suke cikin kwanciyar hankali da kaunar juna, dan basu da wata damuwa sun gama sallame lamarukan su ga Ubangijin, wata Dattijiwa ce dake kwashe abinci a tsakar gidan dan ko kitchen babu gare su, bayan ta gama kwashe abinci ta ɗauka ta kai nan parlorn, na mai gidan ta kuma ta shigar da shi dakin dake cikin parlorn ta sake komawa cikin ɗan karamin compound ɗin na su, dakin dake gefe ta karasa tana cewa "Wai ko baka da Lafiya ne Malik?" Malik dake kwance a kan dan karamar gadon sa ya mike zaune yace "Umma lafiya ta fah" ta daga labulen dake makale a kofar tana kallon sa tace "Naga kabar wajan aikin naka da wuri kuma har sannan baka sa komai a cikin ka ba, ga dukkan alama kana cikin wata damuwa" ya mike ya fito daga dakin yana kallon Umman nasa yace "A'a Umma, kawai dai bana ɗan jin daɗi ne" Umma ta harare sa tace "Ko dai kun samu matsala ne da surkar tawa" bai kuma ce mata komai ba yana biya da ita har ta shimfida tabarma a nan compound ɗin bayan ya zauna ta ajiye masa kwanan abincin a gaban sa, tana kallon sa tace "Menene damuwar ka?" yayi shiru kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "ina wannan yarinyar da nace miki mutane suna cewa muna kama?" Nan da nan Umma ta hada rai saboda tun day one daya bata labarin Leena taji ta tsane ta har cikin ran ta, ganin shirun da tayi yasa yace "Umma!" ta kalle sa sai kuma tace "Me?" yayi shiru yana kallon ta sai kuma yace "naga kin bata rai ne" tace "kawai dai kai na ne ya fara ciwo amma ba komai" yace "Toh Allah sauwake" daga haka ya fara cin abincin gaban sa ba tare da ya sake ce mata komai ba. Knocking suke a hankali ya daga kansa yana kallon kofar da ake ta knocking for almost 5 minutes kenan tunanin ko ma'aikatan hotel ɗin ne yasa ya mike a hankali dan gaba ɗaya wani zazzaɓi yake ji da kyar ya karasa jikin kofar ya buɗe with shock yake kallon su Mami, Mami ta karasa buɗe kofar ta shiga cikin dakin Sultan na biye da ita bin dakin tayi da kallo tace "Toh ina Leena?" Sadeeq ya durkusa nan kasa ya kifa kansa da bango duk suka bi shi da kallo, Mami tace "tambayar ka fa nake yi" Sultan ya durkusa a inda yake yace "Brother!" ga mamakin sa hawaye yaga Sadeeq yake yi ya juya yana kallon Mami ya mata alama da kuka fa Sadeeq yake yi, Mami ta karasa wajan da sauri ta daga kan Sadeeq tana kallon hawayen dake sauka a kuncin sa, tace "Sadeeq!" ya lumshe idon sa sai kuma ya faɗa jikin Mami yana zubda hawaye Mami hankalin ta yayi mummunan tashi tace "Menene? Ka buda baki kamin bayani mana" a hankali kamar me raɗa yace "Mami can you imagine na sake Leena" Mami bata san sanda ta zabura ta mike ba tana kallon sa Sultan ya duka inda yake zaune yace "can you here yourself, please? Kasan me kake cewa kuwa?" Har sannan Mami tana kallon sa with shock yace "Ban san what comes over me ba, nasan kawai idan na sake ta zan samu nutsuwa, ban san wani hali zata shiga yanzu ba" kawai ya fashe wa Mami da kuka kamar yaro karami ya kama kafafun ta, Mami na girgiza kai tace "Sadeeq kasan kuwa me kake cewa?" Ya daga kai a karo na farko yace "Mami na sani, amma believe me bansan me ta min ba na tsane ta, ban san me tamin ba na sake ta, i can still remembered her last words" Mami tayi ta maimaita innalillahi wa'inna ilahi raji'un' she's very disappointed on him kuma har sannan ta gagara kwakwaran motsi, Mami tace "ina Leenan take yanzu?" yace "ban san inda ta tafi ba, nasan tana rokana akan na taimaka mata" Mami ta rasa me zata yi ta kamaimai. Hajiya ta dinga masifa ganin har sun wuni a asibiti amma Daddy ko lekan su be yi ba, wato ma ko a jikin sa tunda ba 'yar sa bace, Rayyan ne ya shiga dakin da aka mayar da Leena after tayi 5hours acan duk kuma suna dakin, kuma har sannan Leena na bacci, Rayyan ne yayi sallama duk suka amsa masa bayan ya shiga ya gaida su, Sannan ya ajiye sayyayan abubuwan da yasan zasu buka ta, Ammi tace "Mun gode da ɗawainiya Rayyan, Allah Ubangijin ya maka Albarka" yayi murmushi yace "Haba Ammi, ai Leena kanwa ta ce, so, mention not" Hajiya tace "ai mun gode Allah da baka yi hali irin na uwar ka ba" Rayyan be kuma cewa komai ba Leena ne ta farka tana bin su da ido tana hada ido da Rayyan ya sake mata murmushi ta ɗauke kanta Hajiya ta mike ta karasa wajan ta tana mata sannu, Anty Binta ma haka Ammi kuma ganin Hajiya yasa ta kasa magana amma tana kallon 'yar nata da cike da tausayawa, Rayyan yace "make damun ki yanzu?" ta ce "ciki na" yace "Sorry zai daina" Leena na kallon anty Binta a hankali tace "Anty Binta ina son ganin Babyn" Anty Binta ta kalli Hajiya da har ta koma ta zauna ta karasa wajan ta tace "Hajiya bari a nuna mata abun da ta samu dan har sannan bata san me ta haifa ba" Hajiya ta rike haba tace "ikon Allah, wato yaran zamani ba kunya fa gare ku ba" Anty Binta bata bi takan Hajiya ba ta karbi ɗan ta kaima Leena da Rayyan ya gyara mata zaman ta, Leena ta dinga kallon fuskar yaron nan da nan ta fashe da kuka duk kallon ta suke Hajiya tace "ji wani iskanci kuma, kila saboda uban ɗan kika fara mana kuka halan" Rayyan yace "Ai dole ne Hajiya, gwara tayi kukan da ta rike abin zai fi damun ta" Hajiya ta juya a fusace ta fara balbale sa Leena a hankali ta kai hannu tana shafa fuskar dan, Hajiya ta sake baki tana kallon Leena Rayyan bai san sanda ya fashe da dariya ba ganin reaction din Hajiya, Leena ta turo baki ganin kallo da Hajiya ke mata, Anty Binta tace "toh karbi ɗan mana" Leena ta girgiza kai a hankali tace "ina tsoro". Jiddah da har bacci ya ɗauke ta tajiyo muryan su Mami a parlorn gidan, ta mike a hankali dan gaba ɗaya ba lafiya gare ta ba, ta sauka ta buɗe kofar sannan ta karasa cikin parlorn tana binsu da kallon a hankali tace "Ina Leenan?" Kana gadin su kasan duk hankalin su a tashe, kawai dai ga su nan ne, ta kalli Mami da ta jinginar da kanta tana kallon waje guda, Jiddah ta kalli Sultan tace "What is exactly happening here?" In briefly Sultan ya mata bayanin komai with shock take kallon Sadeeq tace "Ya Sadeeq!" bai ko kalle ta ba" tace "Mami ina Leenan toh?" Mami tace "ina muka sani Jiddah, ko baki ji ance a daren ta bar gidan ba" Jiddah ta mike tace "inaa, wannan ba yin kan sa bane" Mami tayi murmushin takaici tace "Ai da Leena nan ta zo akan ta je wani wajan, yanzu ta ya zamu fara hada ido da ahalin ta" Jiddah tace "ina zuwa" daga haka ta wuce daki ta dauki hijab ɗinta ta fito, Mami tace "ina zaki?" tace "zan je gidan nasu ne, ya kamata ace munyi confirming" kafin Mami tace wani abu har Jiddah ta fita. Sai da ta isa kofar gidan su Leena sannan ta tsaya ta fara tunanin me zata ce musu, dakyar tayi gathering courage tayi knocking gate ɗin Baba mai gadi yazo ya buɗe mata gate ta gaishe shi sannan ta wuce sashin su Leena ta dinga Sallama sai taji shiru ta wuce part ɗin Hajiya duk da yadda zuciyar ta ke bugawa amma bata damu ba, dan tasan Hajiya ba lalle su wanye kalau ba, tana isa ta samu part ɗin nata a kulle kawai tayi bakin gate tana kallon mai gadi tace "Dan Allah Baba ko kasan inda mutanen gidan suke?, ina nufin Hajiya da mahaifiyar Leena" yace "Oh Ayyah ai tun juya da daddare suka kwana a asibiti saboda Leenan kamar nakuda take yi" wani irin bugawa zuciyan Jiddah yayi taji kamar ba zata iya tsayuwa ba tace "Nakuda kuma Baba?" yace "Eh" daga haka ta fita da sauri taci karo da Binta da ta dawo gida zata haɗa musu dinner, Binta ta ɗan bata rai Jiddah bata damu da hakan ba ta gaishe ta bayan sun gaisa tace "yanzu nake jin wai Leena na asibiti" atakaice "Eh" Jiddah tace "Ya jikin nata?" tace "Alhamdulillah, Allah yasa an mata aiki cikin aminci, ta haifi dan ta namiji" Jiddah taji garin na
End Ads