taji hankalin ta ya tashi tana kallon Rayyan da ko ajikin da tace "mun shiga uku" sai taga kamar daɗi ne ma yaji da Daddy ya gansu yace "Laifin me kika aikata da kika shiga uku?" Leena ta juya ta bar wajen ya bita da ido sai kuma yayi murmushi ya koma in da ya fito, bayan Leena ta koma ɗaki ta kwanta gaba daya sai yanzu abubuwan suka dinga ringing a kwakwalwan ta hawaye taji ya fara gangaro mata tasa hannu ta share yanzu ne abinda ya faru ya fara bata kunya ma daga karshe bacci ne ya ɗauke ta.
Bayan Leena ta dawo daga exams shirin tafiya makarantar Haddah ta fara bayan ta gama ta wuce sashin Hajiya ganin bata nan sai ta fito kawai ta wuce part ɗin su tayi wa Ammi sallama sannan ta tafi. Daddy na dawowa daga sallah Asr ya wuce ɗakin sa ɗaukan wayar sa yayi, ya yi dialing numbern Rayyan yana shiga Rayyan ya ɗaga kiran Daddy yace "kana ina?" Rayyan yace "ina ɗaki" Daddy yace "ina son ganin ka yanzu" Rayyan yayi jim sai kuma yace "Okay, gani zuwa" daga haka Daddy ya katse kiran ko minti biyar be yi ba sai ga Rayyan yana sallama a kofar ɗakin sa Daddy yace "come in" Rayyan ya shiga samun waje yayi a kasan carpet ya zauna yace "Daddy gani" Daddy yayi gyaran murya yace "Rayyan" Rayyan ya ɗan kalle sa sai kuma ya sauke kansa kasa Daddy yace "Rayyan, I won't keep an eye on you and Leena, so you can continue doing what you're doing! Wato a asibiti na kawar da kai na shine da daddare ka sake zuwa ko?" Rayyan yayi shiru kansa a kasa Daddy ya cigaba yace "Either you bring wife na maka aure Or I'll find one for you, myself" Sai sannan Rayyan ya ɗaga kai yana kallon sa Daddy ya gƴaɗa masa kai yace "Sure!" Rayyan yace "But Daddy ai na fada maka wanda nake so, kuma itama Ni take so, za'a iya fasa da wancan tunda Alhamdulillah ba wai an ɗaura auren bane" Daddy yayi dariyan manya yace "you're so funny, Rayyan. Sai a fasa ko? put yourself in Muhammad's shoes idan aka maka haka zaka ji dadin? Kuma ba yarinyar bace ta kawo sa? Idan har bata son sa ba zata kawo sa ba inason ka san da wannan" Rayyan yayi shiru Daddy ya cigaba "kuma Meyasa tun farko baka yi magana ba? Zan so ka da Leena saboda We all know who she is ta ɗauko halin mahaifiyar ta duk basu da hayaniya ga hankali da sanin ya kamata amma ba zanki bin adalci na baka ita na hana wannan ɗin ba" Rayyan ya kalle sa sai kuma yace "Daddy saboda Leena naki aure fah, If you recall, I mentioned to you a few years ago that I have someone.. amma ba za'a yarda a bani ita ba a lokacin nace maybe say tayi SSCE, so, ina planning ta gama exams ne sai nayi maganan" Daddy yayi shiru yana tunani tabbas a lokacin sai daya zargi cewa Leena ne amma daga baya daya ga ko shirya sun daina sai ya wasar da batun Daddy yace "Rayyan naga ka daina mata magana so shiyasa ka ga banyi magana ba amma Nima tunda nake son ka da Leena" yana son yace Mummy ce ta hana sa mata magana sai kuma yayi shiru baya son abunda zasu samu misunderstanding, yace "Rayyan na maka alkawari tunda naga yarinyar ma tana son ka idan har Muhammad ya janye toh tabbas kai zan aura wa Leena, ko kuma ita Leenan ne da bakin ta tace bata son Muhammad din, amma yanzu kayi hakuri kaje ka ci-gaba da addu'a Nima zan taya ka" Rayyan yace "in shaa Allah, thank you, sir." Daddy yace "Amma ka janye baya da ita bana son ganin abinda idanuwa na suka fara gani, saboda kaima kasan ba'a nema akan nema" Rayyan yace "zan ja baya in shaa Allah" daga haka ya masa sallama ya fita.a compound ya haɗu da Leena da ta shigo yanzu daga islamiyya tana kallon sa tace "Yaya naci mock ɗin mu so sunana yana cikin na ƴan yaye" gaba ɗaya hankalin sa na kan part ɗin su yace "Ma shaa Allah" tace "barin baka invitation card" ta ciro jakkan ta da niyyar dubawa yace "I'm in hurry, Leena. So, ki tura min ta Whatsapp" daga haka ya wuce ta bisa da kallon sai kuma ta wuce itama..
Please kar a manta ayi min Voting..
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
21.........
Leena na shiga sashin su bata ga Ammi a parlor ba ta wuce ɗakin ta ganin bata nan ta fito kenan taga Ammi na fitowa daga kitchen da gudu taje ta rungume ta Ammi tace "Alhamdulillah, saka mako yayi kyau kenan?" Leena na dariya tace "Eh Ammi" sai sannan ta sake ta ta buɗe jakkan ta ta ciro list of students ɗin da Za'a yaye da invitation card tana mika mata bayan Ammi ta gama karanta wa tace "Saura sati Daya kenan ya rage, toh ki kaiwa Daddyn ku ki nuna masa" Leena tayi jim tana tunani sai tace "Toh" Ammi tace "idan kin basa kije da kanki ki faɗawa Hajiya" Leena tace "In shaa Allah" dauko wayan ta tayi a ɗaki kafin ta kai masa sai da tayi snapping ta turawa ya Raina kafin ta tafi, tana fara sallama sai ga Daddy ya fito yana son ya fara shirin zuwa masallacin dan an kusan kiran Magrib Leena ta sauke kai kasa da sauri sannan ta gaishe shi ya amsa mata da fara'a yace "ya studies kuma?' tace "Alhamdulillah, dama na kawo maka ne IVn da islamiyyan mu suka ba mu" ya karɓa dukka biyu ya ɗan gani sai kuma yace "Ma shaa Allah, Bari idan na dawo anjima zan duba yanzu ba ganewa zanyi ba" tace "Toh shikenan" Leena ta wuce ɗakin Hajiya a bakin kofa tayi sallama sannan ta shiga ta samu Hajiya na cin dambu ta gaida Hajiya, Hajiya ta amsa Leena na kallon cikin kwanon tace "Hajiya shine kika samu dambu yau kika manta da Ni?" Hajiya tace "ji jaraba, toh ba shi akayi yau a gidan bane" Leena ta girgiza kanta ta zauna kan kujera tace "tun yaushe Mummy ta hana Masu aiki kawo mana abinci ko zuwa side ɗin mu ai ta hana su, shine Ammi kawai ta fara yi mana tace dama haka take so saboda taste ɗin baya mata daɗi" Hajiya ta rike haɓa tace "wai dama tun wancan cass ɗin da Daddyn ku ya shiga dama bata bari sun ci-gaba ba?" Leena tace "Eh fah, shine Ammi tace wa Daddy ba komai kawai zata na yin nata daban" Hajiya tace "Toh dama me Ammin ki zata yi da abincin gidan nan da kamar har yanzu su ke koya, abincin kullum ba daɗi idan kin ga naci abinci nayi nak toh na uwarki ce" ta karasa maganar tana mika ma Leena warmern dambu Leena ta karɓa tana washe baki tace "sai nayi sallah zan ci" ta ajiye a gefe sai kuma tace "Hajiya dama na zo ne na faɗa Miki sati me zuwa saukan mu" Hajiya tace "kinci jarabawar kenan?" Leena ta gƴaɗa kai Hajiya ta rangaɗa buɗa tace "yanzu ƴar nan kin Haddace izu sittin a kai?" Leena reaction din Hajiya kaɗai abun dariya ne ta fara dariya tace "Eh mana Hajiya" Hajiya tace "Chap gaskiya ko nawa Muhammad ya bada sadaki be faɗi ba dan yayi dacen mace" ambata Muhammad da Hajiya tayi ya sa gaban Leena ya faɗi ita har ta manta da wani Muhammad sai yanzu ma take tuna kalan missed calls ɗinsa da take gani gashi bata kira sa back ba tayi tagumi tana tunanai Hajiya tace "ke kuma Lafiya?" sai Sannan Leena ta kalle ta jin anan kiran sallah ta tashi ta wuce ban ɗakin Hajiya dake ciki Hajiya ta fara masifa "Ai kin san na tsana ana shigan min ban ɗaki, ke ba wanke wa mutun kika iya ba sai dai ki ɓata ki bar mutun da gƴara" duk mitan Hajiya sai da Leena tayi kamar bata ji ta ba ta shige abinta. Bayan Ammi ta idar da Sallah taja wayan ta tana kallon numbern daya kira ta dialing back tayi ba'a ɗaga ba sai ga numbern ya sake kiran ta back immediately Ammi ta ɗaga ta kai kunne daga ɗayan bangaren aka ce "Assalamu alaikum, Ammin." Ammi jin haka yasa ta amsa tace "Sorry ka kira ina sallah ne, shiyasa ban ɗaga ba" yace "Sure, sai dana kira nace kila awajan ku kun shiga sallah ne, I'm sorry" tace "bakomai, amma ban fahimci wanene ba" yayi shiru sai kuma yace "Muhammad ne, Ammi." Ammi tace "Muhammad kuma?" yace "Eh, your son-in-law from Abuja" sai sannan Ammi ta gane tace "Ayyah, Allah sarki ya kuke?" yace "Alhamdulillah" sai yayi shiru Ammi ta fahimci akwai Magana a bakin sa tace "Ina jin ka? Feel free and talk" yace "Ammi dama i just want to confirm.." sai yayi shiru ta fahimci kunya yake ji tace "kayi magana mana" yace "kwana biyu ne idan na kira Leena bata ɗauka so last Wayan mu tace min kanta na ciwo so bansan ko lafiya bane naga shirun yayi yawa ne kuma bansan gun wanda zanyi confirming ba" Ammi tace "Everything is alright! So Karka damu, kawai kwana biyun ne bata zama saboda kasan exams ɗin biyu take gana WAEC sai kuma na islamiyya" yace "Sure! Kawai ne I'm so disturbed ne da jin shirun kuma ba daɗi ban kira nayi confirming ba tunda ina da numbern ki, amma ba wai na kira ne dan nace bata picking call ɗina ba" Ammi tace "na fahimce ka Karka damu" yace "Okay, Ma. Thank you" Ammi tace "The pleasure is mine, indeed" daga haka ya katse kiran Ammi tayi shiru for almost 5 minutes ita kaɗai tasa wannan ta kunce tasa wancan. Bayan Leena ta idar da Sallah kulan dambun ta ta ɗauka ta juye a plate din Hajiya ta koma cikin parlorn ta zauna tana ci Rayyan yayi sallama ta ɗaga kai tana kallon sa yace "baza ki amsa ba?" tace "Wa'alaikumus salaam, ina wuni" yace "Lafiya our little Hafiza" gani tayi har ya ɗan chanza mata compare yadda yake a asibiti ya zauna yana ganin yadda take cin dambun da hannu tace "Yaya ka duba ka gani?" yace "Uhm nagani har nayi replying ɗin ki back, tho Ni ba za'a sanmin dambun bane?" ta kai bakin ta tace "toh ai a gidan ku akayi Nima Hajiya ne ta bani" ta kare maganar tana mika masa plate ɗin ya girgiza kai yace "sai dai idan ke zaki bani hannu na ba kyau" tayi shiru tana tunani tace "toh ai ba spoon anan" yace "Eh dama da hannun zaki bani" ta ɗeba ta kai masa bakin ya karɓa sai da hada da yatsan ta da sauri ta cire akan idon Hajiya da ta fito ta ɗauke kai ta fara masifa ita kaɗai Rayyan ya kalle ta Leena kuma ta cigaba da cin abincin ta Hajiya ta karasa cikin parlorn tace "Ni dai gaskiya zaki daina shigo min ɗaki tunda komai kika ɗauka ba zaki mayar wajan sa ba" Leena ta turo baki taki kallon ta Hajiya taci gaba "Haka jiya bani da niyyar fita da yamma kika sa na raka ki asibiti wajan Rayyan zaki kai masa abinci kika ce muna zuwa zaki bani kaza amma har yanzu shiru kin mayar da Ni ban san me nake yi ba" Leena sai yanzu ma ta tuna ashe tama Hajiya Alkawarin kaza ta fara dariya Rayyan yace "wani iri kike so Hajiya a biya ki kayan ki?" Tace "Ni dai ko wani iri amma nafi son ban karus" Rayyan yace "toh ai Ni zaki sa na tsaya miki ba ita ba saboda ai bata aiki ita ina zata samu kuɗi" Hajiya tace "ba saurayin ta ɗan Minista ba ne Nasan ko yana turo mata" nan da Nan mood ɗin Rayyan ya canza and Leena can see it Dan haka dama ta gama cin dambu ta kai ma Hajiya kwanon ta kitchen ta wuce sashin su Hajiya na kallon Rayyan da ya jinjina da kansa tace "ka gani dai da idon ka ta gama ci taje ta ajiye min a kitchen" a hankali yace "toh Hajiya ina masu aiki kisa su wanke mana" tace "kai yanzu ka taɓa gani na bawa masu aiki sun wanke min kwanuka? Ai ko sun yi sai na sake wanke wa?" Yayi shiru be ce mata komai ba tace "yanzu kuma kaza ta ta dawo hannun ka" ya mike yace "barin je masallaci daga nan sai na biya na tsiyo Miki" daga haka ya fita. Leena na shiga parlorn ta ga Ammi na zaune ranta a ɓace nan da Nan Leena taji gaban ta ya tsinke Ammi na mata wani kallo tace "Leena, when was the last time you spoke to Muhammad?" Leena jin tambayar tayi har tsakiyar kanta kamar wacca aka cakkawa mashi tayi shiru tana kallon Ammi Ammi shouted at her "what nonsense is this? I'm talking to you, and you're looking at me like that? Ke kurma ce ban sani ba?" Leena taji kuka ya zo mata bata san sanda ta fashe da shi ba tace "Ammi, I think it's been 3 days now" Ammi tayi Wani murmushi tace "well done Leena, You must move on from him since you have Rayyan now, right?" Leena da ke share hawayen ta ta ɗaga kai da sauri tana kallon Ammi jin abinda ta ce da sauri ta girgiza kai tace "wallahi ba haka bane" Ammi tace "haka ne mana, 3 day da kika ce min ba lokacin bane kika zan cook ɗin Rayyan ba? ba lokacin bane? Shiyasa baki da time ɗin Muhammad balle ki ɗauki kiran sa, lokacin da Rayyan yake share ki ina har idan Muhammad be kira ba hankalin ki tashi yake yi kin dinga duba waya amma lokaci ɗaya ki canza ki bar bawan Allah da shiga damuwa, its okay, Leena" Leena na girgiza kai tace "Please don't misinterpret me, Ammi. Wallahi thats not the reason, ba haka bane" Ammi tace "Leena, I think I'll set boundaries between you and Rayyan" da sauri Leena ta ɗurku sa ta rike kafafun Ammi tace "Ammi dan Allah kiyi hakuri, kar kiyi min haka" Ammi with shock take kallon Leena tace "Tabbas ya tabbata zargi na, kije ki tattara kayan ki zaki koma Niger, ba zaki ci-gaba da zama da Ni anan ba, kije duk wahalan da zaki sha ko zasu baki ke kika sani, Leena. Kije idan har Muhammad yaga zai iya auren ki toh a ɗaura auren sai yaje ya dauko ki, idan kuma zaɓi da kika ma kanki ne fine ai yanzu kin girma zaki iya zabar ma kanki abin da ya dace da ke" ta kwace kafan ta tayi hanyar ɗakin ta Leena ta fashe da masanan cin kuka bata taɓa shiga tashin hankali irin na yanzu ba, tabi Ammi ta bata hakuri ma ta gagara sai da tayi kukan ta me isar ta har hawaye ya kafe mata sannan tayi kokarin tashi dan niyar yin Sallahn isha'i.
Rayyan yayi sallama ɗakin Hajiya ya shiga ya mika mata yace "yanzu dai zaki daina magana tunda an kawo Miki" tace "ai dama alkawari tayi min ba da banayi magana ba" ya mike yace "toh sai da safe" tace "zauna za muyi magana" ya zauna yana kallon ta ta ajiye kazan ta a gefe tace "yanzu kuma me yasa kuka fara shiri bayan shekarun nan kamar masu aljanu" kallon Hajiya yake yi sai kuma yace "tun da ɗin ma ba wai da son raina na daina mata magana ba" tace "Toh amma ai yanzu sai da zata yi aure ku tsira wannan sabon rayuwan Rayyan? Kai fa Babba ne idan Ita Linan yarinya ce? Ko baka san hakan ba kyau bane zaka ce min" yayi shiru be ce mata komai ba sai kuma yana kallon ta yace "Toh Hajiya me yasa zaku ba wani ita bayan kinsan ina son ta" Hajiya ta sake baki tana kallon sa da mamaki tace "A'a ban sani ba, toh taya zan sani bayan baka faɗa min ba zan san abun da ke zuciyan ka ne?" Yayi shiru tace "kana ji na ko Rayyan, har ga Allah na so ka da Leena abaya amma daga baya dana ga ka daina mata Magana abin yayi ta damuna idan ba zaka manta ba har kiran ka nayi na maka magana akai amma ka mayar dani ƴar iska" Rayyan yayi shiru sai yanzu yake ganin illan hanasa magana da mummy tayi Hajiya tace "yanzu kuma kasan cewa haramun ne ka ce zaka neme ta bayan har an bata ma wani shi kuma ya bada sadakin ta" Rayyan be ce mata komai ba sai kallon one direction da ke yi ga kuma wani boiling da yake inside Hajiya ta gama maganganun ta wanda shi baya ma sauraron ta dan hankalin shi baya jikin shi sam ya kalli Hajiya yace "sai da safe" ya mike sannan ya fita.
Mummy da ta gama serving Daddy tayi kasa da murya tace "baka ce komai ba yallabai" yace "yanzu an daina yayi zuwa wani gari siyyaya kawai order za kuyi a kawo muku" ta kashe murya tace "Haba Alhaji, siyayyan bikin ƴarta ne fa! Kuma ta roke ni, taya zan ce mata A'a, da safe zamu shiga Kano da yamma mu dawo dan da Flight zamu dawo" Daddy na mamaki hali irin na Khadija sai in tana bukatar abu ne kawai take zama very calm yace "it's Okay, Allah tsare hanya" tace "Amin, Nagode dear". Leena tun lokacin da tayi idar da sallahn isha'i bata tashi akan sallayan ba tana nan wajan damuwa ya mata yawa tasa wannan ta sa wancan wani lokaci taji hawaye yana sauka kan kunci ta ta share a haka take har pass 10pm wayan ta ne yake ta ringing ta ta tashi tana kallon wayan sai kuma ta karasa ta ɗauka amma kafin tayi receiving call ɗin ya katse