x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 35 - AGOLA free pages

  • 102001 words
  • 105000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
Jiddah ta girgiza kai ta e "kar mu fara haka dake, wallahi akwai Leena, i can see, toh me amfanin boyewar?" Leena da har hawaye ya fara cika idon ta tana kokarin mayar da shi baya tace "Babu fah" Jiddah ta zuba mata ido tace "ki daina kallon na a matsayin kanwar Ya Sadeeq, ki kalle ni a matsayin Aunt ɗin ki na da" Leena bata san sanda ta fashe da kuka ba Jiddah ta barta tayi me isar ta sannan tayi shiru duk yadda Jiddah taso Leena ta fada mata haka nan taki cewa komai daga karshe ta hakura a haka ta koma gida bayan Sultan ya zo ya ɗauke ta. Mami ta fito daga dakin ta around 8pm taga har sannan Sadeeq na gidan tace "kai Malama Ko ka manta kana da iyali ne zaka tare min a gida tun ɗazu" a takaice yace "Na sani" Mami tace "Amma kasan awannan stage ɗin ne ba'a son ana barin ta ita kadai?" Sadeeq bai tanka mata ba ya wuce dinning Mami tace "toh Karka sake kara min ko minti biyu ne a gida" daga haka ta wuce dakin ta, Sadeeq ji yayi ya tsane ta with passion ko hada roof daya da ita baya so. Mami tayi shiru tafi minti biyu a haka, har sai da Jiddah ta ciri wayan a kunnen ta, ta ɗauka wayan ya yanke ne, ganin yana reading yasa ta fahimci bata kashe ba, Jiddah tace "Mami" Mami tace "Uhm, wato shi yasa ya wuni min a gida? Ni zai zuba wa kasa a ido daga basa yarinya sai ya fara wulakanta ta, Har ya isa?" Jiddah tace "kawai ki sa masa ido zaki gani da kan ki ma" daga haka sukayi sallama. Rayyan da ke kwance kan 3 seater gaba ɗaya yaji duniyar ma ta masa zafi shi sai yanzu ne ma yake kara tsanar Layla kuma yake jin haushin abinda mahaifiyar sa ta masa, tun karfe 8pm ya dawo gida amma yanzu wajan 12am ne bata gida, dan bata ma san ya dawo ba, wato ma siyasa ta kira sa da yake a asibiti zai kwana shiyasa tayi fitar ta, yana ta tunani iri da kala yaji alamar tana buɗe kofar parlorn bayan ta shiga cikin parlorn ta kunna wutan nan nan da nan haske ya garwaye parlorn kallon Rayyan da tayi kwance yasa ta tsaka ihu sai kuma ta toshe bakin ta da sauri jikin ta ya fara bari ta buɗi baki tace "ba.ba.. kace zaka.. kwa kwana a asibiti.. ba" Rayyan tun da ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa be sake bari yaga direction ɗin ta ba, da kyar ta iya ɗaurewa ta shiga dakin ta bata ma san ta ina zata fara ba, gashi wani ɗan iskan kaya ne a jikin ta balle tace daga unguwa take, zama tayi a bakin gado tana ta tunani iri da kala. Yau tunda safe Sadeeq ya bar gidan Leena tana fatan kar ya dawo gidan irin na jiya sai dare, bayan ta gama aikin ta ta koma parlorn ta fara rubutun ta dan kawai ta ɗaukewa kanta damuwar da take ciki, ringing ɗin da wayan ta ya fara ne yasa ta mike taje ta ɗauka ganin Zahra yasa ɗaga kiran, Zahra tace "ina kofar gidan ki" Leena ta kashe wayan ta fita dan shigowa da Zahran. Asma wani kallo take ma Layla tace "Ni wallahi ban san yaushe kika zama haka ba, kamar ba Laylan da na sani ba, har yaushe zaki bari namiji ya ke baki pressure?" Layla tayi shiru, Asma taja tsaki tace "ba dole ya raina ki ba, shakkar sa karara a fuskan ki, ai samun waje yayi, kin gama submitting masa kanki har ya fahimci kina mugun son sa" Layla ta numfashi tace "Ba zaki fahimce ni bane Amsa, Ni yanzu ya Zanyi wallahi tun jiya da daddare har yau da ya fita ko cikan ki be cemin ba, bana son wannan shirun nasa atleast ai ko faɗa ne ya min na samu salama" Asma tace "Kina da kayan takaici wallahi, toh sai kiyi ta zama a gida kamar me takaba? Iskanci ma guri ya samu" buɗe kofar da akayi yasa suka daga kai suna kallon sa, kamar ba Rayyan ba, har tsakiyan parlorn ya karasa yana kallon Asma with serious face yace "Look! Bana son sake ganin ko da shadow ɗin ki ne a gidan nan, Get out!" ta mike tsaye ta sake baki tana kallon sa za tayi magana Layla ta rike ta daga haka Rayyan ya wuce ciki, Asma ta ƙwace hannun ta a na Layla tace "So, dama haka kike zaune da wannan? Wallahi kinji kunya" she grabbed her bag Layla tace "Haba Asma" tana kallon cikin idon ta tayi wani murmushi tace "Baki ji me yace bane? Zan yi magana kuma kika hanani, so what exactly do you want me to do?" Layla tayi shiru so speechless, Asma tace "Kin gama down grading kan ki Layla, ban sa yaushe kika canza ba, Allah ya kiyaye namiji ya dinga controlling dina this way kuma na tsaya kallon sa" daga haka ta fita Layla ta zauna kan kujera tayi tagumi. Tun daya shiga street ɗinsu yake jin ɓacin ran shi yana tsanan ta, a daidai gate yayi parking motar dan baya jin zai iya shiga da motar ganin abu kawai zai dauka, bayan yayi parking ya sauka ya shiga cikin gidan, dakin sa ya wuce direct. Leena da ke kwance a dakin ta tun bayan tafiyan Zahra bata sake yarda ta fito ba, sai yunwan da ya kaɗa mata hankali yasa ta mike, har ta kama handle ɗin kofar zata buɗe taji shigowan Sadeeq yasa ta fasa budewa tana tsaye jikin kofar har taji shigan sa dakin sa. Ya dauki duk dakardun da zai yi amfani da su ya kai mota har zai tada mota sai ya tuna ya bar system ɗin akan gado kawai ya shiga gidan ba tare da ya kulle gate ba, jin fitar da sa yasa Leena fitowa ta wuce dinning area bata kai ga karasa zama ba sai gashi ya shiga parlorn, kallon ta da yayi ya sake jin wata tsanar ta har cikin ran shi, ya tamke fuska, kamar be san meye murmushi ba, Leena ta fara addu'a a ranta, ya karasa dinning Leena ta sauke kanta kasa yace "Who the hell are you da har zaki min amfani da cup ?" Leena ta kalli cup din da ke kan dinning ta san neman magana yake dan ita ba abinda ta taɓa, kai kawai ta girgiza masa hawaye har ya fara sintiri a fuskar ta, ya mata wani tsawan yace "Daga gidan ku ne kika zo da dinning ɗin?" jiki a tsanyaye ta sauka, mari ya kai mata yace "Ina Miki magana zaki min shiru?" Leena ta fashe da kuka tace "Dan Allah kai ba zaka tausaya min bane? Wannan wani irin rashin imaani ne?" wani marin zai sauke mata suka jiyo Ihuun Mami daga bayan su "Are you mad Sadeeq?" ta karasa dinning ɗin rai bace ta sauke masa wani wawan mari sai da ya dauki sekonni sannan ya daga jajayen idon sa ya zuba mata sake kai masa wani marin ta yi, ya rike kuncin sa kamar me raɗa yace "Mami! you just slapped me?" tace "So, you even have the gut of asking me, right?" yayi murmushi daga haka ya wuce ta fuu ya fita, Mami ta mayar da kallon ta gun Leena da har ta durgusa kasa, Mami mamakin Sadeeq ya cika ta, ta gagara yarda da abinda idanun ta suka nuna mata just now, wato da badan Allah yasa sun manta gate a buɗe ba ba lalle ta san me ke faruwa ba, ta karasa har inda Leena take durkushe ta ɗago ta tace "Daughter" har sannan hawaye na sauka idon ta Mami ta share mata hawayen tana rike da hannun ta suka koma parlorn, ita bata ma son ta tambaye ta Meya faru dan ita koma menene ai bai kamata ya daga hannu har ya dake ta ba, ai ko ba dan ita ba ko albarkacin cikin ta sai ya daga mata kafa. Bayan Mami ta zaunar da Leena tana kallon yadda ta lalace tace "Meyasa baki taɓa faɗa min ko Jiddah ba abinda Sadeeq ke miki kenan?" Leena na share hawayen daya ki tsaya mata tace "Mami a baya ba halin sa bane shiyasa" Mami tace "wuce ki dauko kayan ki, sai yasan darajar ki kafin ki dawo gidan nan" Leena bata so ba amma atleast tasan da wani abu ya taso ga Mami kusa. Mami dake zaune a dakin ta tana waya da Jiddah tace "Jiddah ba zan iya barin ta agidan ba, na dawo da ita gida na, ace matar ka tana da tsohon ciki har zaka iya daga hannu ka mare ta?" Jiddah tace "Hmm Nima da farko da Ya Sultan ya faɗa min Mami ban yarda ba, sai fah da naje naga yanayin ta tana cikin damuwa shi yasa ma na fara yarda duk da mun san ba halin sa bane" yadda Mami take boiling bata ma son tayi magana, da scene ɗin yayi flashing a idon ta sai taji duk duniya ba wanda ya taba mata munin abu kamar Sadeeq, tace "Ki kyale ni kawai Jiddah, ina son rest" daga haka ta katse kiran. Dakin da Jiddah take  kafin ta yi aure nan Mami ta buɗe ta shiga ta na kallon Leena dake kwance tace "Daughter, zaki iya cin jallof ɗin ko a girka miki wani abun? Leena da damuwar duniya ya mata yawa tace "zan iya ci Mami" daga haka ta fita ta kulle mata kofa, ba'a dau lokaci ba sai gata ta kuma buɗe dakin har kan gado Mami ta kai mata abinci zata dauka Mami tace "No, yi zaman ki anan" Leena ta ja kulan ta buɗe ta fara zuba wanda zata ci a plate. Har ta gama ci Mami bata bar dakin ba, ta mika mata ruwa ta karba ta sha tana kallon Mami tace "Thank you, Mami" Mami ta kama hannun ta tana kallon ta tace "Daughter bana son ki boye mini komai, ina son sanin everything" nan take Leena ta ji hawaye har sun soma zuba a idon ta. Jiddah da take kallon Sultan tace "Wallahi ni fah Ya Sultan gani nake Ya Sadeeq ya fara shan wani abu dan ba haka nan ba" Sultan yace "Bana tunanin Sadeeq zai iya fara shan wani abu ko da kuwa anan gaba ne, cos I knw who is Sadeeq, ba abinda ya fi tsana ma sama da shaye-shaye shiyasa ko flavors bai yarda da su ba" Jiddah tace "But still it's not normal" yace "Sure! it's not, shiyasa nake so nayi magana da shi". Hajiya Fatima tace "Toh uban me kike so na miki yanzu?" Layla ta share hawayen ta tace "Mama ko fah kula ni yanzu ya daina" Hajiya Fatima tace "Toh ai shikenan, Allah kyauta" Layla ta dinga kallon ta tace "Mama na kawo miki damuwa ta kice haka?" ta mike tsaye ta dauki jakkan ta zata fita Hajiya Fatima tace "Dawo ki zauna Layla" wani kallo take ma mahaifiyar ta ta sannan ta zauna amma taki kallon direction ɗin ta, Hajiya Fatima tace "Ko da yaushe na Miki magana akan sa sai ki nuna baki so, amma ai ke ma kin san sai da muka je wajan malamai aka rufe bakin sa yadda ba zai ma mahaifiyar sa musu ba" Layla ta katse ta tace "Toh yanzu Mama meya kawo wannan maganar kuma?" tace "Wai na tuna Miki baya ne, naga kin manta ne, shiyasa da zaran zan fara magana sai ki ce baki so ana masa asiri, gashi yanzu kina kuka wiwiwi saboda asirin ya karye, duk da cewa baki sani ba bayan auren ma ina biyan malalmai suna cusa mi shi son ki" Layla tace "Toh yanzu me za'ayi?" tace "Hakuri zaki yi na wani lokaci kadan, aiki za'a fara har sai Rayyan ya rabu da kowa a kanki" Sai sannan Layla ta fara murmushi tace "wallahi, can't wait! Ai dole ma nayi hakuri da shi".
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Hauwa Jibrin Sulaiman
Jiddatul-khayr ✍🏼


Young talented writers association

Chapter 41

_____Sadeeq tun safe yake gidan kuma Mummy ko ta kansa bata bi ba, harkan gaban ta kawai take yi ba tare da ta nuna tasan yana gidan ba ma dake yau Sunday ne bata da aiki, kuma ta hana Leena fitowa daga daki komai take bukata sai dai ta kai mata, Bayan ya dawo daga gym dakin su ya wuce ya watsa ruwa yasa simple jallabiya sannan ya sauko, Mami take dinning ita da mai aikin ta tana jera breakfast ɗin da ta haɗawa Leena a tray, ya karasa ya zauna yana kallon Mami yace "Good morning, Mami" Mami ta amsa masa ba tare da ta ko kalle sa ba, ta ɗauki tray din ta wuce dakin da Leena take ciki ya bita da kallo harta shige ta kulle sannan ya sauke ajiyan zuciya ya fara serving kansa. Leena data fito daga wanka ta ɗaga kai tana kallon Mami da ta shigo, ta dauki hijab ɗinta dake gefen gado ta sa a jikin ta, Mami ta shimfiɗa mata sallaya ta ajiye mata trayn breakfast din Leena tace "Mami Nagode" Mami tace "Bakomai, ki zauna ki samu kiyi breakfast" Leena tace "Toh Mami" daga haka ta fita ta kulle mata kofar, Leena ta zauna ta fara cin abincin a hankali, gaba ɗaya hankalin ta baya ma kan breakfast din her thoughts elsewhere. Tunda Mami ta buɗe kofar dakin ta fito idon Sadeeq ke kanta har ta karasa dinning ta dauki nata breakfast ta wuce dakin ta ko sau daya bata kalle sa ba, shima be damu ba saboda yasan kila tana fushi da shine akan Leena ne but he didn't mind, as long as Leena's name remained unspoken shikenan Is fine by him. Yana gama breakfast ya wuce dakin sa na sama. kallon wayan ta dake ringing a gefen bedside drawer ta yi ta mike a hankali ta karasa wajan ganin Ammi ke kira yasa ta ɗaga wayan ta zauna a kan gadon bayan sun gaisa Ammi tace "Leena an samu wacca zata zauna da ke ɗin ne ko nama Daddyn ku magana Binta ta zo ta zauna da ke? naga kin shiga watan haihuwar ki ne" Leena taji wani abu ya wuce mata a throat din ta dakyar ta buɗe baki tace "Ai yanzu ina gidan Mami ne ma da zama" Ammi tace "shine kuma ba zaki faɗa min ba" Leena tace "Ammi kiyi hakuri kawai dai bana jin dadi ne kwana biyun" Ammi tace "Allah ya sauwake ya raba lafiya" bayan sunyi sallama Leena taji saboda kuka ya zo mata haka ta dinga yi har ta gaji dan kanta tayi shiru, ta kwanta nan da nan bacci ya ɗauke ta. Niswa dake bin bayan Rayyan har suka shiga parlorn ba kowa a parlorn Niswa ta faɗa kan kujera tace "dan Allah Yaya kayi sauri ka dauko mu tafi kar su tashi" bai tanka ta ba ya wuce cikin dakin sa Layla ta shigo daga kai kayan ta laundry ta tsaya kallon Niswa dake zaune a kan kujera kallon kofar dakin Rayyan tayi ganin kofar kamar a buɗe yake yasa tayi ƙwafa Niswa ta ɗan kalle ta sai kuma tayi ƴar dariya tace "Anty amarya" Layla ko kaɗan bata sake kallon inda take ba ta karasa cikin parlorn ta dauki abun da zata ɗauka ta kama hanyar fita Niswa ta mike tace "kin yi abinci ne, Ni fah yunwa nake ji wallahi" daga haka ta kama hanyar kitchen Layla tace "Uban ki kika ajiye a gidan da zai da fah miki abinci" Niswa ta tsaya tace "ai ko ban ajiye ubana ba tunda kina gidan uban nawa dole ki dafa kuma zamu ci ko mutuwa zaki yi" Layla tayi wani murmushi tace "Zaki sha mamaki na Niswa, mark my words, you'll cry soon, By then, you'll realize you're nothing. I'm serious, take it as a bet, Layla ta fi karfin tunanin ki" Niswa tayi dariya tace "we shall see" daga haka ta wuce kitchen jin motsin Rayyan zai fito daga dakin sa yasa Layla barin wajan da sauri dan bata son haduwa da shi, bayan Rayyan ya karasa cikin parlorn yace "Niswa!" daga kitchen ɗin ta amsa yace "me kuma kike yi?" tayi ƴar dariya tace "yunwa fa nake ji, shine zan daura indomie" yace "Okay! Then, idan kin gama ki same ni kawai a Company" jin haka yasa ta ajiye pot ɗin hannun ta ta fito har yayi gaba ta dauki jakkan ta tana bin sa a baya. Mami da ta raka wata colleague dinta da ta zo mata ziyara bayan ta dawo tana shiga parlorn taga Sadeeq na sauka daga stairs ta sake baki tana kallon sa da mamaki har ya karasa cikin parlorn tace "Wait! Are you really even Okay?" Yayi shiru yana kallon ta meanwhile kuma yana zama a kan kujerar da ke kusa da shi Mami ta ɗan daga murya tace "Ba magana nake maka ba? ya zaka zo ka tare min a gida?" yace "I will leave " tace "Better" daga haka ta wuce dakin ta, tana mamakin hali irin na Sadeeq instead of ya bata hakuri shine zai ce mata haka ba, tayi ƙwafa tasan maganin sa zata kyale sa har sai yayi learning mistake din sa. Sultan ne yayi sallama Sadeeq ya daga kai yana kallon sa sai kuma ya mayar da kansa kan tvn da ke aiki, Sultan ya karasa har cikin parlorn yana kallon Sadeeq yace "kace kana gida, ashe zamu hadu anan ma da har ina cewa idan na tashi gidan Mami zan je maka" Sadeeq ya jinginar da kansa jikin cushion yace "Sure, ina nan, though anjima zan koma" Sultan ya mike yace "it's okay, Mami na nan" kai kawai Sadeeq ya gyada masa daga haka Sultan yayi dakin Mami da sallama a bakin sa. Ammi ta ajiye ma Hajiya warmern hannun ta, Hajiya tace "Nagode kwarai da ɗawainiya da ni da kike yi" Ammi tayi murmushi tace
End Ads