masa wa Leena tace "welcome on board, little sister" Leena na Murmushi ta shiga Jidda ma ta shiga ta kulle kofar. Leena ta faɗa kan sofa tana kallon Jidda tace "amma Anty Jidda Quarters ɗin ku ya min kyau" Jiddah tayi murmushi tace "kuma ba ruwan kowa da kowa, sai kayi shekara ma baku hadu da neighbors ɗinka ba sai may be da safe idan za'a fita aiki" Leena tace "One thing da yasa nake son unguwar mu kenan" Jidda tace "Toh tashi ki shiga ciki mana idan ma abinci zaki fara ci ko wanka duk wanda kike so sai kiyi" Leena tace "I'm gonna take a bath first, tunda lokacin Asr yayi sai nayi sallah" jidda tace"Okay" ta nunawa Leena ban ɗakin sannan ta fito ta cigaba da cika wasu files da take dubawa. Yana zuwa a sallahn Asr ya wuce part ɗin Hajiya da sallama ya shiga ba kowa a parlorn dan haka ya zauna kan kujera yana danna wayan sa, Ayaan ne ya shigo parlorn yana kuka Rayyan ya ajiye wayan hannun sa yana kallon yaron yana masa murmushi ya mika masa hannun Ayaan ya rike hannun Rayyan, Rayyan ya ɗaga sa ya ɗaura sa a cinyan sa yana masa wasa har Ayaan yayi shiru ya koma dariya a haka Hajiya tafi to ta same su Rayyan ya gaishe ta ta amsa tana kallon Ayaan tace "kila yanzu fah saboda rashin ƴar uwan sa ne yake ta kuka kasan ya fi sabawa da ita fiƴe da uwar ma" Rayyan sai kallon Hajiya yake yi yace "ina ita Leenan ta tafi?" tace "Habuja mana, baka sani ba ne" yace "Me taje yi acan? Yaushe? Kuma ita da waye?" Hajiya tace "A'a ya zaka jera min tambayoyi kamar ɗan jarida, idan nace yanzu baku kula junan ku, sai ku karya ta ni, amma ya za'ayi ace baka san da tafiyan nata ba" Rayyan yayi shiru ya cigaba da wasa da Ayaan Hajiya tace "ita kaɗai mana ta tafi, toh wa suke da su a garin Kadunan da zasu raka ta, ai ba a mota kuma ta tafi ba balle ace muna jin tsoron kada ayi kidinafin ɗin ta" sai sannan ya kalli Hajiya yace "ita kaɗai kuma? Toh wa ta sani acan da zata tafi? Ba kwanan nan zasu fara Waec ba?" Hajiya tace "kasan wannan Abunda take yi mana, na magana a cikin mutane shine a Habuja aka ai ko mata da katin gayyata shine fa ta tafi" yayi shiru be ce komai ba Hajiya ta kuma cewa "kasan wanan Sadeeq da jidda duk a Abujan suke aiki yanzu toh tare da su zata zauna, danma su suka roke Daddyn ku har ya yarda" sai sannan Rayyan ya ɗaga kai yana kallon ta kawai ji yayi baida interest da jin labarin yace "Hajiya kuma ita Ammi ta yarda? How , please? Bata san cewa Leena har yanzu yarinya bace?" ya karasa maganar so pissed off ya ajiye Ayaan ya tashi ya fita Hajiya ta sake baki ta bisa da kallo tace "iyyeee" ta rike haɓa, kawai da ta fashe da dariya ita reaction ɗinsa ne ya bata dariya toh ji yadda ya wani ɓata rai kamar ita takai Leena Habujan. Da yamma Leena na kwance akan 3 seater tana duba abubuwan da zata yi performing gobe, Jidda dake zaune a kasan carpet tana danna wayan ta tace "ke Leena kin san dazu muna tare da mutumin ki" Leena ta ajiye wayan a gefen ta tace "wa kenan?" Jidda ta harare ta tace "Ya Sadeeq mana" Leena ta ya mutsa fuska tace "yanzu yana ina?" tace "ya tafi can inda yake aiki 6pm ma jirgin su zai tashi zai koma Kaduna" Leena tace "Better wallahi, ni dama bana son haduwa da shi" Jiddah tace "Ni kuma naso ku haɗu wallahi" ta karasa maganar tana dariya Leena bata ce komai ba Jidda tace "Leena kinsan me? I planned to attend your poetry performance tomorrow, but I won't be able to because we have a meeting" Leena frowned tace "Haba Anty Jidda ya kike son nayi cupping bayan ba ki nan?" Jidda ta harare ta tace "A Kaduna da kike zuwa kina yi naga tare muke zuwa" Leena tace "but Kaduna fa daban nan ma daban" tace "kisa a ranki duk ɗaya ne and perform well, Amma harga Allah natso nayi attending but ba yanda na iya ne" Leena tayi shiru tana kallon ta da shagwaba. Da daddare Leena da har ta kwanta da wuri saboda tana son ta samu enough bacci kar da safe ta tsaya bacci ta makkara zuwa can, gashi waje ne da zaiyi containing manyan mutane from different state, wayan ta ne ya fara ringing ta buɗe ido tana kallon wayan sai kuma ta jawo ganin Ammi ne ke kira tayi picking takai kunne Ammi ta ce "Har kin kwanta?" Leena tace "Eh Ammi" Ammi tace "Dama Ayaan ke kuka zaiyi magana da ke" tun kafin Ammi ta rufe baki Ayaan ya karɓa wayan yana "Anty aina" jidda na murmushi tace "baka yi bacci ba?" ya "gƴada mata kai kaman tana kallon sa ta ce "toh je ka kwanta, zan kira ka da safe ko" yace "good night, bye" daga haka ta kashe watan baki ɗaya ta kwanta. Da safe bayan Leena ta tashi tayi sallah ta idar da azkar ɗinta sannan ta jawo wayan ta ta kunna tayi dialing numbern Ammi, bayan ta ɗauka suka gaisa da haɗa ta da Ayaan saboda zai tafi makaranta suna gama wayan ta ajiye wayan nata akan gadon, Jidda ta shigo ɗakin tana murmushi suka gaisa, bayan sun gaisa Jidda na kallon ta tace "da me zakiyi breakfast Leena?" Leena tayi dariya tace "kai Anty jidda sai kace Ni ba kuwa ce" ta harare tace "dallah ko zaki buɗe baki kiyi magana ko kiga abinda zan Miki" Leena na Murmushi tace "anything, muje na taya ki ma" tare suka gama breakfast, program ɗin Leena 10:am za'a fara ita kuma Jidda tana da wani abu da zata karasa a office 9 zata tafi meeting ɗin nasu zai fara 10am. Jidda na kallon Leena tace "je ki fara shirya wa nima barin shirya though zan riga ki fita amma ina so naga wankan ki, Leena ta wuce ciki har Jiddah ta gama ta fito parlor Leena bata fito ba ganin agogo tayi hakan yasa ta karasa bakin kofar ɗakin tayi knocking Leena tace "abuɗe yake" Jiddah ta tsaya kallon ta from head to toe tace "Ma shaa Allah, kin yi kyau a maroon Abayan nan kamar wata bakarabiya" Leena na Murmushi tace "thank youu" Jidda tace "da fah makeup zan Miki amma sai naga hakan ma zaki fi kyau, kar a ɗauka makeup ɗinne ya kara Miki kyau" Ita dai bata ce mata komai ba Jidda tace "toh yanzu zaki tafi ko sai ɗan anjima" Leena ta kalli agogo dake nuni da pass 9am tace "zan bari sai 10am kawai zan fita Jiddah tace "ina ne ma venue ɗin" Leena ta buɗe watan ta tana kallo tace "transcorp Hilton, Abujs" Jidda na gƴada kai tace "iyyee, manya" ta karasa tana murmushi daga haka sukayi sallama Jidda ta fita ta bar Leena da take ta rehearsal ɗin poetry performance ɗin ta. Goma nayi bolt ɗinta ya iso ta fita ta kulle ma jidda gida ta shiga bolt ɗin a daidai bakin Transcorp Hilton Abuja ya sauke ta tun daga bakin gate ɗin take ganin tsaruwan wajan Ma shaa Allah ta furta Manyan motoci ne na gani na faɗa ke parke a layin wasu kuma ta jikin gate ɗin Hilton ɗin wasu kuma a ciki akayi parking Babban banner dake bakin gate ɗin ta kalla wanda yake ɗauke da wannan rubutun *Event Name:* "Abuja Economic and Cultural Summit" (AECS)
*Event Type:* Annual economic and cultural summit featuring keynote speakers, panel discussions, and performances.
*Venue:* Transcorp Hilton Abuja.
Sojojin dake bakin gate ta gaisar da su dayan na mata wani kallo yace "Do you have a gate pass?" ta girgiza masa kai tace "I don't have one. I'm here to perform a poem. I'm from kaduna, state" sojan yace "Let me see your invitation card" ta ciro wayan ta a jakkan hannun ta ta buɗe ta ciro IV card ɗin da aka buga da hoton ta ajikin ta mika masa yana kallo ya gƴada kai dayan sojan ya kalli IV card ɗin ya mika mata wayan yace "No wonder I saw your face so familiar! I just saw your picture on the banner inside the hall" suka buɗe mata gate ta shiga kowa da take kallo a wajan ba kananun mutane ne bane basu kudi ne na gaske ta gagara shiga ball ɗin ta kira numbern da suka yi inviting ɗinta kamar da 5 minutes sai ga wani mutum ya fito yana mata sannu da zuwa yace "Bismillah mu shiga" to her surprise tana shiga ball ɗin she was greeted by a massive banner with her picture, name, and details about her upcoming performance. The banner read: 'Leena, 18 yrs, from Kaduna state, Performing 'Voices of the Future' at the Abuja Economic and Cultural Summit'. Kawai taji wani honored bata san sanda ta rufe ido ta buɗe ba kowa kallon ta yake a hall ɗin ita dai gaban ta kawai take kallo take bin Mutumin daya shigo da ita wani kujera ya nuna mata wanda taga sunan ta a manne a jikin kujeran da lakanin special guest, ta zauna kai tana ganin kayan alatu da aka tara mata. Event nata gudana wajan da awa daya da rabi aka kira ta kan stage sunan Allah ta fara kira a ranta saboda duk taron da take zuwa tayi performing bai kai wannan da komai ba ta haura kan stage da Bismillah ta daidaita tsayuwar ta ta gama addu'o'in da zata yi a ranta sannan ta ɗauki mic a natse ta fara magana wanda yasa hall ɗin yayi tsit gidajen rediyo da BBC da duk wani kafafen sada labarai suka yi kanta suna ɗaukan ta, tayi delivered a powerful poetry performance on 'Voices of the Future,' captivating the audience of governors, business leaders, and dignitaries with her words on Nigeria's potential and the aspirations of its people. Hall ɗin kafa ya ɗau sautin tafukan hannaye kawai cos Leena tayi magana cike da kwarewa kuma a tsare, ta kusan karasa Last stanza ɗin idon ta ya faɗa cikin na shi sai da taji gaban ta ya faɗi ta ɗauke kai ta karasa tace "Thank you" ta sauka zata karasa gun zaman ta, aka dinga karɓan Acc details ɗin ta. Ana gama program wasu kafafen sada zumunci suka yi caa akan Leena ana mata video manyan mutane suka dinga cewa a musu hoto da Leena, ta tsaya kenan za'a mata hoto da kaduna's Governor yana proud ai daga state ɗin sa take Leena ta hango sa daga nesa yana taho wa ta ɗauke kanta tana ci gaba da pictures ɗin da Za'a fara mata da president taji an ja hannun ta juyawa tayi da sauri tana kallon sa tace "What is the meaning of this Yaya sadeeq?" be ko kalle ta ba shi de ya ci-gaba da jan ta suna tafiya, ganin zata iya calling attention din mutane yasa ta hakura ta biye masa take binsa amma tayi tayi ta kwace hannun ta a nashi ta gagara har suka isa inda yayi parking motar sa ya buɗe front seat ya jefa ta ciki ya kulle sannan ya xaga ya shiga driver seat ya tada motar tace "Meye hakan ina zaka kai Ni?" wani kallo ya juya ya wasa mata sai da ta tsorata taja bakin ta tayi shiru, addu'a kawai take gani wani irin tukin da yake yi kamar irin yana so su mutu wani waje da ba kowa ya tsaya ya juya yana kallon ta ya mata tsawa hakan yasa ta fara hawaye yace "So kike ki buɗe ido tun kina karamar ki ko?" Ta girgiza masa kai yace "shut up, kin wani tsaya kina hotuna da mutane ke har kin san kizo Abuja performing while kin san maza sun fi yawa a ciki, da ace taron mata ne akwai wanda zai Miki magana?" Leena da zuciyar ta yake bugawa ga wani tsoron sa daya dira mata yasa da sauri ta girgiza masa kai tace "I'm sorry na daina daga yau" kallon ta yake baya ko kiftawa...
I think you'd like this story: "AGOLA (Behind the palace walls)" by jiddatulkhayr on Wattpad https://www.wattpad.com/story/394027716?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=jiddatulkhayr
*AGOLA (Behind the palace walls)*
_By Jiddatul-khayr writes
Chapter 12
Thank you so much, my dear readers, for reading my book🫂🫧! I'm grateful to those who've added my novel to their reading list📖💕. May Allah bless you abundantly and provide for your needs, so you can keep enjoying my stories without any distractions (like running out of data 😊)! 🙏📚❤️
Gudun hauka yake kamar wanda ya ke son kashe su, ga shi Leena abinda ta tsana a rayuwar ta kenan hakan yasa ta tsorata matuka, a quarters ɗin su yayi parking kusa da block 1 yace "Get out" Leena jiki na bari ta buɗe kofar motar ta sauka ta karasa gidan da yake kallon inda yayi parking tayi knocking sau biyu sannan taji muryan wani yace "Who is it?" tace "It's Leena" wani saurayi ne ya karaso kofar ya buɗe yana kallon ta sai sannan ya matsa mata gefe yace "Come on through" ita duk tunanin ta may be wani ɗan uwan su Jidda ne ta fara shiga taji mutumin yace "thanks for coming to check on him. He's feeling a bit better now. The doctor even gave him an injection, and he's actually sleeping right now" sai sannan Leena ta ɗaga kai da sauri tana kallon sa sannan tabi cikin parlorn da kallo ganin ba na Jiddah bane za tayi magana taji yace " If you can wait for him, you're welcome to. I need to head back home for something important, so if he wakes up, please call me and I'll come back" ya karasa maganar yana mika mata hannu alamar ta basa wayan ta ya sa mata numbern sa da sauri tana girgiza masa kai tace "I'm so sorry, I think I'm mistaking. This isn't my sister's house. I think it's the next block" bata jira cewar sa ba ta buɗe kofar parlorn ta fita da sauri Mutumin ya tsaya kallon ta da mamaki and her face looks familiar to him, ko da ta fita bata ga motar sadeeq ba next block ta bi duk da taga mota kusa da shi amma still tana hoping shine tayi knocking Fortunately ashe gidan ne, Jidda tazo ta buɗe Leena na shiga ta fashe da kuka Jidda da take kan kallon Videon Leena da aka gama watsa wa a media tana murmushi ganin yadda Leena ke performing well shine taji anyi knocking kuma ta buɗe taga Leena to her surprise tho me ma yasa Leena kuka kuma tana tsaye bakin kofar har Leena ta karasa cikin parlorn sai kuma da sauri ta kulle kofar tabi Leena hankali tashe tace "Meya faru Leena? Kuma lafiya kuma?, ki daina kuka kimin bayani" Leena tana share hawayen ta tace "Amty Jidda, it's uncle sadeeq" Jidda tace "Uncle sadeeq? wani uncle sadeeq ɗin? Me yayi Miki toh?" Jidda na sheshshekan kuka tace "He went to where I was performing my poem and grabbed my hand, pulled me out of the hall, and forced me into his car. I didn't even get to say goodbye to the people who invited me, and the governor even wanted to take a picture with me, but he just dragged me away. He drove so fast, I was scared. I kept apologizing, but he wouldn't listen, just shouting at me. He brought me here and dropped me off" Jidda ta sake baki tana kallon Leena da mamaki Leena na sheshshekan saboda tsorata da tayi ta ci-gaba "I'm still shaken, Anty Jidda, I'm worried about how those people will feel, especially since I didn't even get to thank them or say goodbye" Jidda bata fasa kallon Leena ba sai kuma ta fashe da dariya Leena ta tsaya tana kallon ta sai kuma ta tashi ta wuce ɗakin da ta sauka aranta tana mamakin what was funny here, sai kuma taji haushin Jidda toilet ta wuce tayi Alwala sannan ta fito ta shinfiɗa sallaya, Jidda ita kadai ta ringa dariya a parlorn ta jawo wayan ta ta kira Sadeeq har ya katse be ɗauka ba ta kuma kira ya ɗauka a tsawa ce yace "Why are you calling me? Are you owing me? Stop calling me with this nonsense! It's all your fault for letting her go there alone to perform that so-called poem. Do you want her to be exposed to all those men? Can't you see most of the people there are males? What kind of aunt are you?" Duk maganganun nan be bata damar magana ba, tana ta kunshe dariyan da take ji yana gama magana ya kashe wayar sannan Jiddah ta fashe da dariya ita duk abinda taji a muryan sa tsantsan kishi ne bayan ga haka bata ga komai ba, tashi tayi ta koma ɗakin da Leena take ciki taga Leena ta idar da Sallah amma bata tashi akan dadduma ba ta zauna gefen ta ta kama hannayen ta tace "I'm sorry Leena! Ba wai dariya nake Miki ba, but to be sincere wallahi abinda na gane a cikin wannan lamarin Ya Sadeeq yana matukar kaunar ki Leena" da sauri Leena ta ɗaga kanta tana kallon Jidda, Jidda ta gyaɗa mata kai tace "Dagaske nake Leena, ko ƙaffara bazan yi ba Ya Sadeeq yana so ki, idan har ba haka bane ba yadda zaiyi wannan abun da yayi, na san Ya Sadeeq fiye da kowa bayi shiga harkan da be shafe shi ba, toh ki sani son da yake miki ne yasa ya Miki wannan Abunda yayi" har ta gama magana Jiddah girgiza mata kai take yi tace "Dan Allah ki daina faɗin haka Anty Jidda and I don't want to believe it" Jidda tayi dariya tace "ajuri zuwa rafi" Leena tace "in shaa Allah hakan ma bazai