x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - AGOLA free pages

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
"Hajiya abincin fa yana kan wuta ne" Hajiya ta ɗauke kanta tace "toh naji ko?" Leena tana mamakin Hajiya ita da yanzu suka gama faɗa da Hajiya, Nisreen ta tashi ta fice Hajiya tace "munafuka sak halin uwar da gado munafurci ne ya shigo da ita" Hajiya taga hawaye na gangara a fuskan Leena tace "ke kuma me?" tace "Hajiya kin ga har test fa munyi kuma an bamu Assignment gashi kuma Mummy tace ba zan kara zuwa ba, kuma Nisreen tana jin daɗi dan nayi missing test, dama tun da can tana jin haushi na saboda Ni ke cin first position" Hajiya tace "kyale su na ɗayan nan kuwa sai kin ci" sallama akayi me aiki ta gaishe da Hajiya sannan ta ajiye kulolin da ke hannun ta tana fita sai ga Rayyan yayi sallama Hajiya ta amsa Leena dake kwance ta tashi ta zauna tana kallon sa bayan ya gaishe da Hajiya tace "kai kuma ya na ganka yau wani iri haka fa?" yana shafa kansa yace "bana ɗan jin daɗi ne" tace "Allah sauwake" yace "Amin" Leena tace "ya Rain, what's wrong with you?" yace "I'm okay Leena" ta tashi ta dawo kujeran da yake kai tace "Ya Rain kaga yau an bamu Assignment kuma munyi test ma" ta karasa maganar hawaye na zuba a idon ta He asked, "who told you Leena?" She replied "Nisreen just left here, I heard her telling Hajiya that we had a test and one teacher gave us an assignment" yayi shiru sai yace "it's Okay, gobe ki shirya da wuri Ni kuma idan na tashi break a office zan karasa school ɗinku zanje nayi magana a baki makeup test kinji?" ta gyaɗa kai tace "Thank you Ya Rain". Washe gari da kamar jiya Rayyan yayi ta knocking kofar su Leena yaji bata amsa yana cikin knocking sai ga Leena a bayan sa tana tahowa jira yayi har ta karaso gaishe sa tayi ya amsa yace "tare da Hajiya kika kwana?" gyada masa kai tayi yace toh "je ki shirya toh" ta kuma gyaɗa masa kai daga nan ya sauka ya wuce part din Hajiya. Bayan Leena ta shirya ta wuce parking space already su nisreen suna wajan Muryar mummy taji nan gaban ta ya fara duka uku uku zata ɓuya a bayan motar kawai suka haɗa ido da Mummy da sauri tace "Mummy good morning" mummy tace "wato baki jin magana ko, inaga sai na cire Miki kunne daya zaki fara fahimtar me nake nufi" kuka ta fara tana ba Mummyn hakuri, Mummy na tsaye tace da driver"Malam zaku iya tafiya ko?" Jiki na rawa ya shiga motar ya tada suka fita har sannan Leena bata daina kuka ba Muryan Rayyan suka ji akan su yace kizo nayi dropping dinki kafin na wuce aiki Leena ta fara share hawaye Mummy ta rike haɓa tace "Lallai Rayyan wuyan ka yakai yanka toh dan Allah ka kaita idan kai ka haife kanka" yace "Mummy, please have pity on her, she's just a little girl" Mummy tace "Ni zaka kalla kace bani da imaani, Rayyan?" yace "Mummy, please try to understand me" tace "toh ban yafe ba idan har ka kaita" daga haka ta wuce ciki he's just speechless kawai ya wuce ciki shi din ma Leena ta fara kuka, ba ta da wani Alternative banda ta tafi makarantar da kafa duk da makarantar nasu nada nisa ta karasa gate mai gadi yace "Leena ina zaki?" tace makaranta yace "anya zaki gane hanya?" ta gyaɗa masa kai hoping zata iya amma itama tasan ba lalle ta gane ba, tunda ta fita tafiya kawai take absent-minded
Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


_By Jiddatul-khayr_
~Book 1~
Chapter 3
Alhamdu Lillah
Leena tafiya take absent-minded,  Har rana ya gama fitowa Ita dai bata ga ta isa makarantar ba kuma bata gane hanyan da take bi ba. Daddy ne yayi shirin fita aiki ya ajiye briefcase dina a cikin mota sannan ya wuce part din Hajiya dan gaishe ta sallama yayi sannan ya shiga ya zauna nan kasan carpet Hajiya jin muryan sa yasa ta fito daga cikin yace "dazu ai na leko naji ki shiru Hajiya" tace "kila dana koma bacci ne" gaishe ta yayi ta amsa da fara'ar ta tana sa masa Albarka mikewa yayi zai fita tace "tafiya aiki za kayi yanzu!" yace "Eh zan leka office ɗin mu na nanne" tace "toh, sai ka dawo, daman wata magana ne" Daddy da har ya mike ya koma ya zauna yace "Inaji Hajiya" tace "A'a dai ka tafi sai ka dawo karna ɓata maka lokaci" yace "Toh Hajiya ince fi lafiya?" tana murmushi tace "Eh toh, klau ɗin dai za'a ce, daman akan Khadija ne amma ka bari sai ka dawo ɗin" yace "toh shikenan Hajiya sai na dawo" daga haka ya fice daga parlorn. Rayyan ya gama shirin fita aiki yaji alaman Mummyn sa itama na shirin fita yayi sauri ya koma ciki har sai da yaji fitan ta shima ya fito part ɗin su Leena ya tafi yayi ta knocking yaji shiru yayi magana still no any response, part ɗin Hajiya ya wuce yace "Leena fah?" Kallon sa take yi tace "Yau naga ta kaina, yarinyar dake zuwa makaranta shine zaka same ta yanzu?" ya girgiza kansa yace "bata tafi yau ba ai" Hajiya tace "haba" ta rike haɓa tace "Haka jiya fah Maihaifiyar ka ta hanata zuwa harda dukan tsiya, baka gani ba abun ba kƴan gani wallahi, toh ya zamu ce" ya juya zai fita Hajiya tace "Toh dai gaskiya bata shigo nan ba" haka nan yaji hankalin sa ya kasa kwanciya ya sake komawa part ɗin su Leena ya yi ta knocking still shiru ya murɗa handle ɗin ya buɗe bin parlorn yayi da kallo sannan yayi hanyar dakin ta yayi knocking kafin ya buɗe ya shiga ciki bai ganta ba har ya fita sai kuma ya koma ya duba toilet ma nan ma empty ya fita ya ja kofar ya koma part din Hajiya yace "Hajiya bata can part ɗin su fah" tace "toh kila fa tabi su nisreen can makarantar ne" ya girgiza kansa yace "A gaba na driver ya tafi da su" Hajiya tace "kila toh ko tana bacci" ficewa yayi daga dakin ta can bakin gate ya nufa yana ganin driver yace "wa da wa ka kai makarantar yau" yace "yau Niswa ne da Nisreen" yace "Leena fah?" yace "gaskiya tun dana kai su nisreen na dawo ban ma ganta ba" Mai gadi ne ya karaso yan washe baki yace "Ai Alhaji karami baka san me ba ta tafi makarantar ai tun ɗazu" Rayyan yace "ita da wa?" yace "tace min da kafa zata tafi" Rayyan yace "What!!! What the fuck! What were you thinking, leaving her to go by herself?" Tunawa yayi da fa Mai gadin ba turanci yake ji ba ya cika bakin sa da iska ya sake sannan ya dunkule hannun ya dake iska da shi, ba mai gadi ba hatta driver sai da suka tsora ta da yana yin sa yana kallon mai gadi yace "ta ina tabi?" yace "wallahi na hanata tafiya tace min zata gane hanya shine na buɗe mata kofar ta fita amma ta can karshen layi ta bi" ya karasa maganan yana nuni da hannun sa Rayyan be san sanda yaja tsaki ba direct makarantar su ya wuce class ɗin su ya tafi yayi taking permission daga class teacher yana son ganin Nisreen, Nisreen ta fito tana ganin sabon yanayin yayan nata, ba wasa a fuskar sa yace "ina Leena?" tace "Yaya bata zo makarantar yau ba ai" yace "ke, tambayar ki nake ko daga baya ta karaso" sai da ta tsorata da yadda ya karasa magana ta girgiza masa kai da sauri tace "wallahi bata karaso ba ka duba ajin mu ka gani" yace "idan wani abu ya samu Leena Nisreen kiyi kuka da kanki, ke kikayi causing everything da gaya mata anyi test bata nan" daga haka ya juya ya barta wajan a tsaye Nisreen ta fara share hawayen da ya gangaro mata. Ya koma motar sa sai zufa yake haɗawa ya rasa ta inda zai fara Toh ai mai gadi ya tabbatar masa ta fita a gida 'innalillahi wa'inna ilahi raji'un' yayi ta maimaitawa kiran Hajiya yayi a waya tana ɗaga wa tace "hello Riyan" yace "Hajiya Leena fah ta fita a gida akan zata makaranta da kafa inji mai gadi gashi na karaso makarantar dan naga ta iso amma bata karaso ba" Hajiya tace "Innalillahi ina take Rayyan?" yace "Hajiya makarantar tasu fa da nisa ta'ina Leena zata gane hanya fisabilillah, shi kuma habu wani irin hauka ne da yake damun sa har zai buɗe mata gate ashe be san aikin sa bama" cire wayar yayi daga kunnan sa bai jira cewar Hajiya ba ya kashe wayan kawai, hanyar komawa gida ya nufa hoping zai ganta a hanya amma still shiru ba lungun da bai shiga ba amma har yanzu yana karasa kofar gidan su mai gadi ya fito zai buɗe masa gate ya masa alama da A'a karya bude yazo kawai mai gadi ya karaso yace "gani Alhaji" Rayyan na kallon sa yace "ta dawo ne?" Kai ya girgiza masa yace "A'a wallahi" wani kallo Rayyan ya masa yace "Allah taimake ka kar ta dawo yanzu zaka je station kayi bayani" daga haka yaja motar da mugun speed ya bar layin, mai gadi iya tsorata ya tsorata addu'a ya fara yana rokon Allah bayyana Leena, toh ina ma zata je ai kila ma ta isa makarantar. Zazzaɓin da jiya yaji ya tafi shi yake jin yana shirin dawowa toh ko ya kira Daddy ne ya sanar masa da sauri ya girgiza kai dan idan ya tsanar da shi yanzu kuma aka same ta ya san iyayen nasa zasu iya samun matsala.
Leena tun tana tafiya taga ta gagara gane hanyar makarantar ga zafin rana da ake yi sanin cewa ko ta tafi makarantar ma tayi mugun latti ta sake juyawa da niyyar zata koma gida ta sake bin wrong way, tun tana tafiya idan ta gaji da zauna idan ta huta sai ta tashi ta cigaba da tafiya haka take har ta fara ganin wasu ɗai ko kin motoci suna shiga unguwan da student a cikin motar hakan ya sa ta fahimci har wasu makarantun sun tashi wani Babban layi ta tsinci kanta a ciki da farko ta ɗauka layin su ne sai kuma taga ba nasu bane shima layin yayi tsit kamar layin su baka ganin kowa a waje kowa na gidajen sa yunwar da ta fara jine yasa ta je jikin wani gida ta zauna hawaye ya fara zuwa a idon ta gashi tayi mugun gajiya bata san ta ina zata fara neman gidan su ba kuka taji ya zo mata da sauri ta share hawayen ta zauna nan jikin wani gida ta cire school bag dinta cup din da ta zuba Golden morn ta ciro a cikin jakkan ta bude bottle water ta zuba ta dama sannan ta sha amma still bata ji ta koshi ba ita yanzu damuwar ta taga ta koma gida shine kawai ta jingina da wall din gidan kawai bacci ya ɗauke ta. Tunda Rayyan ya koma office bashi da wani rest of mind gashi ya rasa me zai aikata Hajiya ya kira a waya ta ɗaga yace "Hajiya ta dawo gidan kuwa?" tace "wani dawowa kuma Ni tun ɗazu da ka fada min hankali na ya tashi ba inda ban shiga ba a sashin su amma ban ganta ba ga su Niswa sun dawo daga makarantar amma ban da ita" ajiyar zuciya ya sauke Hajiya tace "ka ga nace ko zaka fada wa ubanka ne tunda shi babban mutun ne a garin nan ya kira polis ya sanar musu kaga sai a fara neman ta lungu da sakon cikin Kaduna" yayi shiru yana jinta tace "hello" yace "ina jinki Hajiya" taja tsaki tace "ka ga matsalata da kai kenan, sai ayi ta magana kana ji ba zaka ce komai ba" yace "toh Hajiya duk yanda kika ce ayi hakan kawai" bayan ya gama waya da Hajiya ya ɗaura kansa akan desk din office ɗin sa be san me taka meme idan zai ganta ba shi yanzu tunanin sa idan mahaifiyar yarinyar ta iso gari yau ya zasu ce mata?. Mai gadin ya buɗe musu gate din gidan fita su kayi acikin gidan da mugun speed sai kuma wanda ke tuka motar ya fara reversing motar da hankali ya dawo baya Sadeeq yana kallon Sultan yace kai kuma lafiya sai da ya tsaya sannan ya juya yana kallon inda Sultan din ke kallo, tsaki Sadeeq yaja Sultan yace "Look at how peacefully she's sleeping" Sadeeq responded, "what businesses do you have with her" Sultan yaja motar suka tafi. Hajiya ta kuma kiran Rayyan for, numerous times yana ɗaga wa tace "Riyan ka ganta" yace "No Hajiya, barin kuma fita nama rasa inda zan tafi neman ta ne" daga haka ya katse kiran ya cife a cikin asibitin na su, Hajiya taji hankalin ta ya fara tashi gashi uwar yarinyar na ganin girman ta, tsoron ta kar uwar Leena ta dawo yau toh suce mata me? kiran Daddy tayi a waya tace "Kana ina ne wai? Gashi mun kusan shiga bakin duniya, Ni yanzu idan uwar yarinyar nan ta dawo kasar nan me zamu ce mata?" Daddy yace "Hajiya me yake faruwa ne ban gane ba?" tace "Gaskiya toh idan ba wai wani abu kwakkwara kake ba toh ka dawo yanzu wallahi" Daddy yaji hankalin ya ya ɗan tashi dan Hajiya bata fiye masa wannan kira tace ya dawo gida ba. Har su Sultan suka dawo daga inda suka tafi Leena na nan wajan but this time around jin karan motar su yasa ta buɗe ido tana mutawa Sultan ya dawo daidai da inda take ya tsaya da mota yana kallon ta yace "Hey little girl" tace "Good afternoon, uncle" ta fada tana kokarin gyara jakkan ta zipping yace "What are you doing here? And you look exhausted, is everything alright?" ta girgiza masa She replied to him "I can't find our house" His expression is one of surprise yace "how?" tace "i just don't" ya kalli Sadeeq dake danna wayar sa yayi kamar be ma san dasu a wajan ba ya sake maida kallon sa kanta yace "So, what brings you here" She replied "Uncle, I want to go back home, but I haven't seen our house and I'm tired, so I'm sitting here to rest" Sadeeq yace "malam na gaji da ajiye Ni anan da kayi fah" Sultan yace "ɗan rainin hankali ba gashi mun karaso gidan ba ai zaka iya sauka ka shiga" Leena na kallon Sultan tace "I don't like your brother" Sultan ya kwashe da dariya wani kallo Sadeeq ya watsa mata to his surprise yaga kallon idon sa take ba alamar tsoro Sultan yace "I'm coming" karasa shiga da motan cikin gidan yayi sannan yayi parking Sadeeq ko kallon sa be yi ba ya wuce cikin gidan abun sa Sultan ya karasa gate ya shigo da Leena "Uncle, can you take me home?" yace "Sure! a wani street gidan ku yake?" tace "I don't know" kallonta ya tsaya yi tace "do help me, please?" yace "how?" ta mai alama da bata sani ba itama, har cikin parlorn su ya kai ta yace "ki zauna ana, bari nayi lunch sai na kaiki school din naku a duba min address dinki" ta gyaɗa masa kai tace "Uncle What time is it?" yace "pass 3" ta rufe bakin ta da sauri tana gwala ido yace "What?" tace "Na bar gida before 8am fah" sadeeq ya fito a daki yana kallon Sultan da mamaki yace "Continue attending to the stranger" yayi wuce War sa kitchen, Sultan ya maida kallon sa gun Leena yace "Tell me how?" Leena ta fada masa everything ya tashi yana girgiza kai Sadeeq daya fito a kitchen yana jin su yace "What do you plan to do now" Sultan yace "I know I won't take her back home until tomorrow. That way, they'll notice she's missing, I'm not worried about her father taking action against the stepmother" Leen tace no please kamar zata yi kuka tace "Ya Rayyan zai damu, Hajiya ma Daddy too" dakyar sukayi convincing dinta zasu mayar da ita anjima. Sadeeq ya jona wayan shi a chargy ya fita, Sultan kuma tunda ya haura sama be sauko ba Leena ta gama cin abinci da aka bata taje ta cire wayan Sadeeq a chargy ta buɗe wayan ta shiga Camera ta ajiye akan kujera yadda bazai faɗi ba ta fara video. Hankalin daddy yayi mugun tashi daya gama jin maganganun da Hajiya ta fada masa yace "Hajiya meyasa tun jiya ba'a sanar dani abun da ake ciki ba" daga haka ya fice a parlorn ta kiran Rayyan yayi yana ɗaga wa yace "Rayyan ka dawo gida yanzu" yana katse kiran ya kira wani friend dinsa D.P.O. sadeeq bayan ya dawo ya wuce sama abun sa me yankawa Leena ba duk tunanin sa wayan sultan ne a hannun ta. Sallama akayi a bakin kofar parlorn Leena ta daga kai tana kallon budurwan da ta shigo, Leena tace "Sannu da zuwa" tana murmushi tace "thank you" daga haka ta wuce dakin dake cikin parlorn.
Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


_By Jiddatul-khayr_


~Book 1~
Chapter 4


Tana chanza kayan ta ta fito daga dakin ta wuce kitchen ta ɗebo abinci har ta fito Leena na jikin waya tana ta maganganun ta Jidda ta tsaya tana kallon ta saboda yarinya ta burge ta tace "Hey! Baby girl, zo mu ci abinci" girgiza mata kai tayi sannan tace "is this Your house?" Jidda tace "yes, it is" tace "toh Brother dinki ya bani abincin naci" jidda taji yarinyar tana burge ta kawai ta karaso cikin parlorn ta zauna a kujeran da ke kallon na Leena,
End Ads