x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 36 - AGOLA free pages

  • 105001 words
  • 108000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
"Ɗawainiya kuma Hajiya?" Hajiya tace "Hmm sakani na da Khadija ai Allah ya isa kawai zan ce mata, ji matar nan ta hana ana bakin girkin gidan kuma Ni da take zuba wa ma yanzu idan banje na roka ba baza a kawo min ba, Ni da ɗana? Idan ban haifa ba ina zata gansa balle ta san dadin sa, gashi yanzu duk ta juya min kan ɗana baya wani kula da mu kuma kwatakwata baya son laifin ta da zaran na fara Maganan ta sai kiga yana bata rai, kwatakwata baya son laifin ta fah" Ammi tace "Allah kyauta" Hajiya tace "Amin, shiyasa yanzu na daina baccin dare, toh ina ni ina bacci? ɗana na cikin ukuba? ga ɗan nata ma gaba daya bayi da nutsuwa yanzu, har yafi kyan gani kafin auren nasa, yanzu sai fafa take a gari 'yar ta zata aura ɗan Sarkin Katsina shine fa take ta ji da kan ta, ko gaishe ni yanzu ta daina" Ammi tana jinjin audacityn Mummy a ranta Hajiya tace "Ai Zanyi maganin ta ɗan wallahi ɗa na yafi ƙarfin ta, yanzu zan tashi tsaye da gaske duk abinda take takama da shi na kulle kulle Allah tona mata asiri idan ma wani abun take Allah karya shi, lokacin da shi Muhammadun zai dawo hayyacin sa in yaso ya sallama ta kowa ya huta" Ammi dai bata ce komai ba tana sauraron ta dai kawai. Sultan na kallon Sadeeq bayan ya haura zuwa dakin su na da, yace "Ina so muyi wata magana idan ba damuwa?" Sadeeq ya ɗan kalle sa sai kuma yace "Akan me?" Sultan yace "zaka ji ai if you're ready" Sadeeq ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda yake yi a wayan sa, Sultan ya wafce wayan yace "ya zanna maka magana ka maida Ni ɗan iska" Sadeeq dake kallon sa yace "Then, who knows?" Sultan ya dinga kallon sa ba ko kiftawa yace "thank you, then! ko ma me zaka ce Please i just need your attention" Sadeeq be sake kallon sa ba ya cigaba da danna wayan sa Sultan yace "Ina son sanin dalilin da yasa yanzu kuke samun matsala da Leena" Wani tsawan da Sadeeq ya daka ma Sultan ba shiri dan jin sunan da ya ambata yace "Enough!!!" Sultan har sai da abin ya basa tsoro yana kallon Sadeeq with shock, Sadeeq yayi calming kansa down ya mike yana kallon Sultan yace "This should be the first and last time you speak about my wife, Sultan" furta wife da yayi sai da yaji kasa ya mugun tsara masa da sauri ya dafe kan nasa da hannu bibbiyu, Sultan bai daina bin Sadeeq da kallon mamaki ba daga karshe ma tashi yayi ya bar masa dakin. Dakin da Leena take ciki yayi knocking Leena ta daga kanta tana kallon kofar jin ana knocking tasan da Mami ce da ta shigo jin har sannan ana knocking yasa ta sauka jiki a tsanyaye ta karasa jikin kofa taga ma ashe a bude yake ba key a jikin ta buɗe kofar tana kallon sa sai kuma ta masa baya ta gaishe shi ya amsa yana tambayar ta ko da akwai abun da take bukata tace "Babu komai" har sannan kallon ta yake da tausayi yace "Leena, don't hide, please" tace "wallahi Uncle Sultan babu komai" muryan Mami suka ji a bayan su tace "Ajiya kayi a dakin da zaka ɗauka?" ya juya yana kallon Mami sai kuma yayi murmushi yace "No, kawai ina tambayan ta ne idan da abun da take so sai tayi magana" Mami tace "Toh bar wajan , bana son ko da Sadeeq ne yasan tana nan" da sauri ya daga kansa ya kalli stairs sai kuma yayi kasa da murya yace "yana sama ai" Mami tace "wato bai bar min gida ba ko" Sultan na kallon Leena ta da sunkuyar da kai yace "Shikenan, zan sa Jiddah ta faɗa min duk abinda kike nema sai na kawo Miki" daga haka ya juya Mami na kallon Leena tace "Do you need anything?" Leena ta girgiza kai Mami tace "toh koma ciki" Leena ta juya ta koma dakin, zuwa yanzu har ta gaji da zaman ta a dakin ita kadai. Mami ta haura sama dakin su knocking tayi ta shiga kallon Sadeeq da ya rike kansa ta tsaya yi, ta shiga da niyyar suyi magana akan Leena amma ganin yanayin sa yasa tace "Sadeeq, Lafiya?" dakyar ya iya daga jajayen idon sa ya zuba mata tace "SubhanAllah kana lafiya? ta karasa maganar tana karasa inda yake zaune ta zauna tana facing dinsa yace "I'm Okay, Ma" Mami ta dinga kallon sa ya mike tsaya yace "I'm Okay, nace" daga haka ya fita, Mami ta bisa da kallo tunani fal a ranta. Bayan Mami ta koma dakin ta ta kira Jiddah tana dauka wa cike da damuwa tace "Jiddah nikam Yayan ku lafiya kuwa?" Jiddah tayi shiru sai kuma tace "wani abun kuma ya sake yi?" Mami tace "Not at all, naga kamar ba shi bane, kuma yadda kwana biyu yake reacting ya fara bani tsoro, duk shariyan da nake da shi amma ko a jikin sa shine na fara tunanin anya kalau kuwa" Jiddah ta sauke ajiyan zuciya tace "i doubt much, Mami, amma Ya Sultan yace za suyi magana yau, so ina jiran ya dawo ne naji me yace" Mami tace"toh shikenan, yanzu Sultan din ya bar nan, Nima zan sake magana da Sultan din" daga haka sukayi sallama. Yau Monday, Ammi ta tashi tana hada breakfast saboda Ayaan da zashi school taji Sallaman Hajiya ta fito daga kitchen ɗin tana amsa sallaman nata da mamaki Ammi ke kallon Hajiya bayan ta buɗe mata kofar parlorn tun kafin Ammi tayi magana Hajiya ta rika ta tace "dama zan ce Miki ne kar kiyi karin kumollo da Ni yau, saboda yanzu zan kama hanyar wani kauye" Ammi ta kalli garin da ko wayewa bai gama yi ba tace "toh Hajiya kuma haka zaki tafi baki ci komai ba, naga gari ko gama waye wa bai yi ba" Hajiya tace "da ba dan bana son kiyi asara bane da ko nan ba zan zo ba, saboda yanzu zani kauyen dan da ɗan nisa Zanje na karbo mana maganin nan ne wanda ake cewa kaikayi koma kan mashe ki ya, dan ba zan lamun ta ba, Inaji ina gani a raba Ni da ɗana gashi kemw yanzu ya yanke kafa da shigowa bangaren ki" tana kaiwa nan ta kara gaba, Ammi nason tambayar ta ko da kudi a hannun ta amma ina har Hajiya tayi bakin gate. Tun jiya da ya bar gidan Mami har zuwa yau baya ko iya fita sallah, sai dai yayi a cikin dakin nasa daga karshe ya fito parlorn gidan ya kwanta, tun jiya da ya ambaci kalmar my wife har sannan baya jin dadi ta shi yayi ya wuce kitchen yaga alamar ma ba tayi girki ba, ga wani yunwa da yake ji, dakin ta ya buɗe yaga alamar ma bata kwana anan ba, da sauri yaja baya sai kuma ya fara bin gidan da kallo, toh ina take? rasa me basa amsa yasa ya kurawa waje daya ido kamar yana son gano wani abu, can ya fita da sauri ya buɗe motar sa ya shiga. Jin yadda kafafun ta suka kara kumbura, bata da aiki sai danna waya tana tambayar ko normal ne kumburin ta dan yanzu kam kamar balloon ya koma, ji tayi yayi tsami sosai ta mike ta kalli agogo da ke nuni da karfe 2:05pm tasan is hardly Mami ta dawo a wannan lokacin ta mike ta ajiye wayar ta akan dressing mirror sannan ta fita da niyyar wasa kafa a nan parlorn ta haɗu da housegirl ɗin Mami ta gaishe ta Leena ta amsa daga haka ta fita compound ɗin sai taji kamar ta wuce gidan su kawai dan tayi missing Ammi sosai, ta fara tafiya a hankali tana zaga gida amma gaba ɗaya hankalin ta baya tattare da ita jin wani yunwa yasa ta koma ciki mai aiki Mami tace "Har kin gama wasa ƙafan?" Leena na murmushi tace "No, yunwa nake ji" tace "Ayyah" daga haka Leena ta barta a parlorn ta wuce dinning area tayi serving kanta ta fara cin abincin a hankali jin an buɗe kofar yasa ta ɗaga kanta da sauri ta kalli wanda zai shigo kallon sa tayi kamar yadda shima yake kallon ta da sauri ta sauke kanta kasa ji tayi kamar taje tayi hugging ɗin sa so tight, she really miss her husband, nan da nan tajii hawaye ya cika idon ta shi kuma ya haura sama kamar wanda ya tuna abu ya sauko yana kallon mai aiki yace "Mami ta dawo?" ta girgiza kai tace "No, sir" har sannan Leena na zaune tayi nisa a tunanin memories ɗin su na baya, jin muryan sa ne ya doki dodon kunnen ta "ke! tashi mu tafi" Leena ta ɗaga kai tana kallon sa ya kuma mata tsawa yace "baki ji ne?" ta girgiza masa kai ya tamke fuska yace "kar ki bari na sake repeating kai na" Leena tace "Mami bata nan ka bari idan ta dawo Please" bata karasa rufe bakin ta ba ya sauke mata wani mari har sai da mai aikin ta gudu dakin ta ɗan tsoro yace "get up, jhoor" Leena ta mike tsaye ya kama hannun ta ya fara janta gudun karya ji mata ciwo yasa ta hakura kawai ta fara bin sa a baya, amma sai dai kuka ta dinga sha kamar ba gobe, tana ji tana gani bayan yasa ta a mota yaja a mugun speed suka bar layi.
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION


Chapter 42

Bayan yayi parking a kofar gidan yaji sabon damuwan sa ya ninku fiye da na da, tsanar ta, da na gidan ya ninku, a tsawa ce ya fara magana "who told you to go to Mami's house and stay there? Are you crazy?" Leena bata ɗago ba sai ma sheshshekan kukan da take yi, ji yake idan be yi harming dinta ba ba zai taɓa jin dadin rayuwar sa ba Strictly yace "I went to Mami's house because I want peace and quiet, not to share a roof with you. Shiyasa na bar nan, and you just show up there?" Leena ta girgiza masa kai yayi unlocking car door din, ta kai hannu zata buɗe ta sauka yace "kika sake kika sa ke taka gidan Mami zaki sha mamaki na" sai sannan ta ɗaga kai tana kallon sa hawaye na sauka kan kunci ta tace "A'a, it's Mami who came and took me, zan ce mata A'a ne?" Wallahi kallo yake mata yace "Shut up! Don't ever dare go to her house again, Get out" Leena ta buɗe kofar ta sauka a hankali, ita ji kawai take ya mata duk abinda yake da niyya kawai ta huta ta gaji da wannan sauyin nasa tana kuka ta karasa cikin gidan. Mami bayan ta dawo daga aiki ta samu mai aikin ta na kallo a parlorn, ta gaishe da Mami, Mami ta amsa daga haka ta wuce dakin ta bayan ta wasa ruwa ta fito still housegirl dinta na parlorn Mami tace "Leena taci abincin kuwa?" tace "Eh dazu ta fara ci amma bata ci da yawa ba sai.." Mami bata jira ta karasa maganar ba kawai ta katse ta, so take taji tace mata 'Eh ko A'a' daga haka ta wuce dinning ta gama haɗawa Leena abincin a tray ta dauka ta wuce dakin Jiddah ta buɗe kofar ta shiga bata ga Leena a dakin ba, bin dakin tayi da kallo ganin wayan ta na kan dressing mirror sai ta ɗauka ko tana toilet ne kawai ta ajiye abincin ta fita, dinning ɗin ta wuce ta fara lunch ɗin ta, bayan ta gama ta mike zata dakin Leena sai taji sallamar Sultan nan ta tsaya har ya karasa cikin parlorn ya gaida ita, ta amsa masa tace "ina zuwa" mai aikin ta tabar parlorn ganin Sultan, bayan Mami ta koma dakin taga still Leena bata nan kuma yadda ta ajiye abincin da alama ko taɓa shi ba'ayi ba tace "Leena!" tana kallon kofar toilet din shiru taji instead of da idan ta kira ta zata yi gyaran murya ta nuna alamar dai tana toilet, Mami ta kuma cewa "Leena!" still shiru nan da nan taji bugun zuciyan ta ya tsananta ta karasa jikin kofar toilet din tayi knocking bata ji alamar da mutum ba kawai ta buɗe taga ba kowa da sauri ta fito a dakin Sultan ya bita da kallo tana kwalawa mai aikin ta kira ta sauri ta fito tace "gani Mami" Mami tace "ina Leena, ta fita ne?" a hankali tace "Ɗazu ta fito wai kafar ta yayi tsami bayan ta gama zaga gidan nan shine taje ta fara cin abincin wai yunwa take ji.." Mami ta katse ta tace "tambayar ki nake ta fita ne?" tace "Eh, Ya Sadeeq ne ya ɗauke ta suka tafi" Mami tace "Sadeeq kuma?" tace "Eh shine, dan har ta fara kuka amma ya jata suka tafi" Mami ta juya tana kallon Sultan da shima ya zama speechless sannan ta mayar da kallon ta ga mai aikin ta tace "kamar karfe nawa kenan suka fi ta?" tace "ai basu wani daɗe ba kika zo" Mami tace "shikenan koma ciki, Nagode" Mami ta karasa cikin parlorn ta zauna tana kallon Sultan da shima abun ya basa mamaki Mami tace "Amma nikam Sultan, anya ɗan uwan ka lafiyar sa kuwa?" Sultan yace "I doubt much Mami, mun zauna fah da shi akan ta, baki ga reaction ɗinsa ba, kuma kwana biyu gaba ɗaya abin nasa ya fara bani tsoro duba da yadda shima ya tare miki a gida" Mami tace "Ni yanzu tsoro na kar yaje yayi ta marin ta ne, kasan yarinyar ba magana take yi ba, kuma kamar naga wayan ta a daki" Sultan yace "ki kira shi kawai ya dawo da ita shine magana ko kuma ki masa warning in har zai cigaba da musguna mata ne kawai ta dawo gidan ki da zama" Mami ta girgiza kai tace "Anya Sadeeq baya fama da depression?" Sultan yace "Depression kuma Mami?" Mami tace "Eh mana" Sultan yace "Ga Jiddah ma da wai ko ya fara shaye shaye ne nace ba Sadeeq ba kam"  Mami ta mike tace "akwai wani abokin Baban ku, yanzu Babban ne a wannan fannin gaskiya zan kira asibitin su su mana booking appointment gobe muje su duba sa" Sultan yace "Toh Allah yasa a dace" Mami ta amsa da Amin ta wuce dakin ta da tunani iri da kala ita yanzu damuwar ta kar 'yan gidan su Leena suji meke faruwa da ita dan bata ji zata iya haɗa ido da su ba. Bayan Leena ta gama shan kukan ta me isar ta yunwa da ta fara ji yasa ta mike ta wuce kitchen gani tayi ashe ranan ko wanke wanke bata yi ba Mami ta tafi da ita sai da ta gyara gidan kafin ta daura kirki,  bayan ta gama ta ci wanda zata iya ci sannan ta wuce dakin ta tunawa da tayi babu wayan ta da yanzu ya rage mata kadaici kawai taje ta dauki wani littafin ta ta fara rubuce-rubuce dan yanzu rubuta is a therapeutic to her, jin wani bakon yanayi a tattare da ita yasa ta ajiye littafin ba tare da ta shirya ba. Layla ta fito a toilet da sauri tayi kan wayan ta dake ringing, bayan ta daga tayi sallama tana amsa gaisuwar sa, tayi shiru tana sauraron sa bayan ya gama mata bayanin da zai yi ta fashe da dariya tace "Great job, amma ka daina kira na idan ina bukatar information zan kira ka da kai na" daga haka ta katse kiran tana wani dariyan mugunta. Ammi dake ma Daddy magana ko daga kai bai yi ba aikin gaban sa kawai yake yi, tayi shiru tana kallon sa tace "tun dazu ina magana baka ce min komai ba?" Sai sannan ya daga kai yace "baki ganin abu nake yi ne, ko ke baki da hankali ne baki san ya kamata ba?" Ammi ta dinga kallon sa ba ko kiftawa kawai ta miƙe, ya bita da ido har ta fita, yanzu ta fara gane me Hajiya take nufi, dan gaba ɗaya ya canza mata ba kamar da ba, duk sanda take magana da shi baya bata attention yanzu har ya kai ga part dinta ma baya son zuwa ko da ranan girkin ta ne, tana shiga parlorn ta taga Binta zaune da alamar dai yanzu ta sauka Ammi tace "yaushe kika shigo?" tace "yanzun nan! ai dana ga bakowa nace kila kina sashin Hajiya ne" Ammi ta zauna tace "A'a Hajiya ta tafi kauye, Ayaan na islamiyya ai" sai sannan Aunty Binta ta gaida Ammi bayan sun gaisa tace"ya kuma Leenan da jiki?" Ammi ta e "Alhamdulillah" Binta tace "yau zan je gidan nata ko?" Ammi tace "toh ai yanzu din ma ta koma gidan Maman sa da zama Inaga kawai zakiyi zaman kine anan kila idan ta haihu ta dawo gida sai ki kula da ita anan" Anty Binta tace "Ayyah, ai dangin sa suna son ta wallahi" daga haka ta mike tace "Ammi barin yi la'asar kafin a kira Magrib" daga haka ta wuce ciki, Ammi tayi tagumi tana tunani. Niswa tace "Mummy Ni na fison wannan design ɗin" Mummy tace "A'a wannan bai kai wancan kuɗi ba" Nisreen tace "Chap aljihun Daddy zai girgiza yau kam" Mummy ta mata wani kallo tace "Naga yama Agola ma balle 'ƴar sa, ai dolen sa ne wannan" wata kawar Mummy Hajiya Maryam tace "Ah toh, kaya expensive one za'ayi selecting sai dai kudin sa ya kare tass, familyn manyan mutane ne fa zata shiga" Mummy tace "Ah toh" daga haka suka cigaba da zaga gurin suna selecting furnitures ɗin da Za'a kai ta da shi, babu kaya da suka tsayawa Niswa mai arha har bayan magrib suna wajan kuma tun safe suka bar gidan. Hajiya ta shigo gidan futufutu gaba ɗaya a
End Ads