x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 47 - AGOLA free pages

  • 138001 words
  • 141000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
kallon sa tace "daga ta faɗa gaskiya? to kabar min auta ta sarara dan Allah" Daddyn su yace "Toh ai autar na ki ma na kusan cewa tabar min gida, ina duk mate ɗin ta suna aure amma kullum sai kiyi ta saka mata cewa ita karama ce" Na'ila ta kalli Daddy tace "I'm just 23 fah, Daddy" sallamar gatekeeper suka jiyo daga parlorn Daddy kaɗai ya amsa yace "Alhaji wasu mutane biyu ne wai suna neman ka ko kuma Alhaji karami" Daddy yace "waye su?" yace "wallahi ban san su ba, amma suna dai sanye da kalar kayan da masu aiki a banki suke sakawa" yace "It's Okay, kace su shigo compound ɗin gani fitowa" daga haka ya juya zuwa isar da sakon sa, Daddyn Farouq ya mike yana goge bakin sa yace "barin duba ko su waye ne" daga haka ya wuce, da mamaki shimfiɗa a fuskar sa ya karasa wajan su, bayan sun gaisa suka ciro IDcard ɗin su suka nuna masa tare da kuma mishi bayanin meya kawo su, with shock yake kallon su sai kuma ya daure yace "Sure, ɗa nane hope ba matsala?" suka mika masu envelope ɗin hannun su suka ce idan ba damuwa ka isar mana da sakon nan zuwa gare sa, ya karɓa suka masa godiya daga haka suka juya suka fita, haka nan yaji hankalin shi ya tashi sai kuma ya juya ya koma parlorn na sa, briefly ya musu bayanin me ya kawo su, Farouq yaji hankalin shi ya tashi, yana mika ma Farouq envelope ɗin Mummy ta kwace da sauri ta buɗe tana karanta contents ɗin ciki, ta sauri ta ɗaga kai tana kallon Farouq, wanda Daddyn ma kallon nasa yake yi, Na'ila tace "Sammaci kuma daga court? amma ko sun fara hauka ne? Ko dai ba nan zasu kawo ba?" Farouq ya fara jin zufa na karyo masa strictly Daddy ke kallon sa yace "Umar karya kace min baka san akan menene ba, dan baka nuna wani shock da jin maganar ba, so what is it?" ya girgiza ma Daddy kai ba tare da yace komai ba, yana mamakin dama Niswa tasan gidan su ne ko kuma tracking ɗin sa akayi.
Bayan kwana biyu, Daddy ya fito yana tsaye a compound yana waya sai ga Rayyan da ya sako Niswa a gaba sun fito daga part din Mummy suna tahowa inda Daddy yake tsaye, bayan sun kara sa duk suka shiga motar bayan Rayyan ya data motar yana kallon Niswa dake bayan motar yace "Saura idan anje ki tsaya kina rufe baki kiki bayani ko yace ba haka bane kiyi shiru, dan wallahi tun a wajan zan fara dukan ki kamar jaka" bata ce komai ba haka Daddy ma.

Lemme see 60 reaction🤭

Hauwa Jibrin Sulaiman
Jiddatul-khayr__ 08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr


Young talented writers association (YOTA)


Chapter 55

According to the court's ruling, aligned with principles of Islamic law, Daddy's family was granted a favorable verdict. Daddy bai yarda an bar court ɗin ba ba tare da an ɗaure auren with the assurance of zata tare a week ɗin, tun a hanya da Niswa ta kifa kanta take kuka ta rasa gane what exactly take feeling, is it murna ko kuma akasin haka, daga Daddy har Rayyan ba wanda yace mata kala, dama Daddy har sannan magana baya shiga tsakanin su daga ta gaishe shi, a takaice zai amsa shikenan, bayan Rayyan yayi parking Daddy ya buɗe kofar motar ya sauka, Rayyan ma ya sauka ba tare da sun kula Niswa dake kuka a bayan motar ba, Rayyan ya fara bin Daddy a baya, bayan sun karasa har parlorn Daddy, Daddy ya zauna yana kallon sa yace "Weldon" murmushi kawai Rayyan yayi, Daddy yace "Hope yau zaka ɗauki matar ka ku bar min gida?" ya shafa kansa yana murmushi yace "Toh Shikenan, Daddy"  yace "Better" daga haka ya mike yace "let me have some rest" ya wuce ciki, shi kuma Rayyan ya mike ya fita zuwa part ɗin su, tun a hanya Hajiya ta kalle sa ta kwala masa kira kafin ya karasa shiga, jin muryan ta yasa ya juya zuwa wajan ta ya gaishe ta, ta amsa masa tace "Riyan ya kase ɗin kuma?" yace "Alhamdulillah, dan har an ɗaura musu aure" Hajiya tace "Ah toh, dan ba zai cuce mu ba" daga haka ta juya tana mita ita kaɗai. Bayan duk sun shiga parlorn sun zauna Daddyn Farouq shi ko a jikin sa dan abin da Daddy yayi shine ko wani abu na gari zai yi dan haka he don't care tun farko me ya kai Farouq ɗin ɓata musu yarinya, Mummy ce ta sauko daga stairs da saurin ta tana kallon su, ta kalli Farouq da yayi nisa cikin tunani ya jin gina da cushion haka nan Mummy taji hankalin ta bai kwanta ba, tace "What's the status of the case?" Daddy ya kalle ta yace "Alhamdulillah! Komai ya tafi daidai kamar yadda yake a shara'an ce" tace "I didn't get you" yace "Well! So, an ɗaura auren nasu, ai dama soyayya ce ta kai su ba? So court ta yanke hukunci dole ya aure ta?" Mummy ta samu waje ta zauna tsabar yadda taji kamar jiri ne ke shirin ɗibar ta tace "Kamar ya an aura masa ita?" yace "Kamar yadda kike tunani mana" tsumbul ta mike tsaye, har sannan kuma Farouq bai buɗe idon sa ba, amma yana jin duk conversation ɗin na su, tace "wallahi ba zaiyu ba, taya za'a aura masa wacca bata da tarbiyya" yace "Kamar yadda naki ɗan ma bayi da tarbiyya ba" Na'ila ta fito daga ɗakin ta tana kallon kamar abun a mafarki, Mummy tace "Toh wallahi sai ya tsake ta, dan banyi Na'am da ita a matsayin surkuwa ba" kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai ya fara tafiya sama yace "Idan kika kuskura kika kashe mata aure ki tabbatar naki auren kika kashe, kuma lokacin da kika basa go ahead ɗin ya fara nasa rayuwar a wani waje da nayi magana kice a other country ba haka akeyi ba ya malleki hankalin kan sa, he can build his own life, so, here's the result" daga haka ya shige ɗakin sa, Mummy ta koma ta zauna har sannan bata daina mamakin maganar da Daddy ya faɗa mata ba, wato saboda wannan bad bitch ɗin za'a ce auren ta zai mutu? Auren da yanzu take shekara na 34yrs a kanta shine lokaci ɗaya za'a datse mata, tayi wani murmushi ta miƙe zuwa sama, Na'ila ta kalli Yayan na ta daga haka ta koma ɗaki, Farouq ya san idan ta kuɗi ne su Daddy basu isa suyi winning ba just that Baban sa na supporting ne. Da yamma Rayyan ya shiga ya gaishe da Ammi, Ammi tace "Ashe an aura auren Niswan?" yace "Eh wallahi" Ammi tace "Toh Allah haɗa kan su ya basu zaman lafiya" yace "Amin, Ammi" daga haka ta mike zuwa ɗakin ta ba'a ɗau lokaci ba sai ga Layla ta fito rike da Nawaf kallo ɗaya ta masa ta turo baki ta zauna rike da Babyn yayi kasa da murya yace "Toh 'yar Ammi ko na tafi na barki anan ne?" tayi dariya tace "Oho" sai ga Leena ta fito rike da jakkan Layla, Rayyan yace "Ke Layla sai ki barta da ɗaukan Jakkan?" Layla tace "A'a ita fah ta ɗauka amma ban sata ba" yana kallon Leena da take gaishe sa yace "Ba an hana ki ɗaukan abu mai nawi ba?" ta kalli Jakkan sai kuma tayi dariya tace "yanzu ɗan wannan jakka ai ba nawi gare sa ba" yace "ke kika sani" Ammi ta fito da wani babban Nylo bag wanda ta cika cikin da abubuwa ta mika wa Layla, Layla na Murmushi ta girgiza kai tace "A'a wallahi Ammi" Ammi ta mata wani kallo ta ajiye laidan tace "idan yaso karki ɗauka" Rayyan yace "Idan bata so Ni kam ɗauka zan yi" duk suka yi dariya Ammi tace "Layla sai ki dage da azkar ɗin, sannan kar ki manta da abubuwan da na sanar da ke" tace "in shaa Allah, Ammi" daga haka Ammi ta wuce ciki, Rayyan zai karbi Nawaf Layla taki, daga karshe hakura yayi suka wuce ɗakin Hajiya Leena sai duk taji wani iri duk da ba magana suke ba amma ta fahimci Layla is so nice, bayan su gaishe da Hajiya, Rayyan yace "Hajiya dama sallama zamu miki yanzu zamu wuce gida" Hajiya tace "Aiho, Allah sarki!" Sai kuma ta kalli Leena ta kuma kalli Nawaf dake hannun Layla tace "Ok, Ashe har da Leenan zaka tafi ko? ko dai an baka ita ne?" Leena tana ma Hajiya wani kallo tace "Sai kuma haka kawai a basa ni?" Rayyan ya fara dariyan reaction din Leena, Layla kuma ba zaka gane me take ciki ba dan fuskan ta ba yabo ba fallasa, Hajiya tace "Toh na sani ne? naga ga ɗanki hannun Lailan sannan naga ga jakka a hannun ki" Leena ta mike tace "Wallahi tsufa ne" Rayyan ya dinga dariya duk suka fito ta raka su, zasu shiga part ɗin Mummy Leena ta ja baya ta tsaya Rayyan ya juya yana kallon ta yace "ya kika tsaya kuma?" Leena tayi murmushi tace "Zan jira ku anan kawai" Layla ta mata alama da kar ta shiga, duk yadda Rayyan ya sata ta shiga amma haka taki daga karshe ya kyale ta nan tsaye har suka fito, taga Rayyan ya ɗaure fuska sai kuma bata ji dadin hakan ba bayan ta raka su har mota tace "Ya Rain kayi hakuri" bai san sanda yayi murmushi ba yace "Wai har yanzu baki iya faɗin Rayyan bane" tace "just that ya kama baki na ne wallahi" ta karɓi ɗan ta a hannun Layla tace "Anty Layla yaushe zaki sake zuwa?" Rayyan yace "ba za ta sake zuwa ba duk mai son ganin ta ya biyo ta" Layla tace "kyale sa, zan dawo kwanan nan kinji?" Leena ta ɗaga musu hannu tana musu bye-bye har suka fita. Bayan kwana biyu, bayan Daddy da Daddyn Farouq sun yi magana har Daddy yasa aka je akayi mata jere duk da gidan nasa ma da furnitures, da yamma Daddy na tsaye akan Niswa dake ta faman kuka yace "idan kika yarda na karaso har wajan nan zaki sha mamaki na" dakyar ta mike, Mummy tace "Haba mana, taya za'a ce kai zaka kaita? Ka bari idan aka gama shirya ta sai a samu mata su kai ta ai haka ake yi amma ina aka taɓa irin haka?" wani kallo ya wurga mata yace "Toh addini haka yace, ko kina da ja ne?" tayi shiru ta koma ta zauna amma har sannan ranta a mugun ɓace yake, ya karasa ya rike hannun ta ya wuce da ita sashin Hajiya, Hajiya ta ɗaga kai tana kallon sa tace "Ya haka kuma?" yace "ɗakin ta zan kai ta idan da abin da zaki ce mata ne to" Hajiya tace "Gaskiya kam, dan nima Jiya nace zaman uban me take mana a gida" tana kallon Niswa tace "Ni dai babu abin da zance miki sai dai shawara ta gare ki idan har kika ce zakiyi koyi da rayuwar auren mahaifiyar ki toh tabbas zaki sha wahala, biyayya da kuma girmama 'yan uwan sa ba gazawa bane, sannan kiyi abin da ya sa ki wanda kuma ya hana ki sai ki hakura, Allah ya maku zaman lafiya" har sannan Niswa tana sheshsheka a duke, Daddy yace "Ta so mu tafi" ta mike zata fita suka ci karo da Ammi itama tana kokarin shiga rike da kula a hannun ta, ta ja baya tana kallon Daddy tace "Lafiya?" yace "Zan kai ta gidan ta ne" Ammi tace "Toh Allah haɗa kan su ya basu zaman lafiya" a takaice yace "Amin" a kofar gidan Farouq Daddy yayi parking, ya sauka sai da yama Niswa tsawa sannan ta sauka kuma har sannan tana kuka, yana rike da hannun ta suka shiga cikin compound ɗin bayan mai gadi ya buɗe musu, Farouq ya fito har sannan yana jin nawin Daddy dan baya iya haɗa ido da shi ya karasa har inda yake, ya gaishe da Daddy, Daddy ya amsa ya kama hannun sa ya saka masa hannun Niswa a cikin na shi yace "ga 'yata na baka amanar ta idan har ka ci wannan amanar, Allah ba zai barka ba" Farouq yaji jikin shi yayi mugun sanyi, Daddy yaki shiga kuma cikin gidan, har sannan Niswa na kife a jikin sa yayi musu natsiha mai ratsa zuciya daga karshe yace "zai tafi" Niswa ta rike sa gamgam ta fashe da kuka tana rokon ya yafe mata, bai taɓa zaton zai iya jin tausayin ta ba sai kuma gashi ta karya masa zuciya yayi hugging ɗin ta back yace "It's Okay, na yafe miki nikam, saura ki nemi yafiyar Ubangiji da niyyar ba zaki sake aika kwatankwacin sa ba, kiyi wa mijin ki kuma biyayya kinji?" ta gyaɗa masa kai dakyar ta sake sa ya juya ya fita duk da yadda yake ji a zuciyar sa yasan hakan ne kawai gatan da zai mata, a hankali Farouq yace "Let's get in". Tunda Rayyan suka koma gida gaba ɗaya mamakin sauyin Layla yake yi, rashin Sallah akan lokaci da wasu dabi'u duk yaga ta canza, har mamaki yake idan yaga tana azkar ɗin safe da yamma, ga girkin ta ma ya canza, mamakin yadda har ta canza a wajan Ammi yake yi, sai kuma ya tuna Ammi ba daga nan ba, saboda makkara da suka yi yau, kuma ta dage ba zai fita aiki ba sai ya karya hakan yasa suke aikin tare, ta kalle sa tace "Toh yanzu sai kaje kayi wanka kafin ka fito na karasa haɗa wa" yace "Alright!", Bayan ya fito ya samu har ta gama haɗa masa, tace "I'm done" yana murmushi yace "Weldon, Ma" daga haka ya zauna yana breakfast ɗin da sauri saboda gudun karya makkara, bayan ya gama ta raka sa har jikin motar sa tana ɗaga masa hannu har ya fita, bayan ta koma cikin gidan ta samu wayan ta na ringing tun kafin ta karasa ya yanke, ta ɗauka ganin Mama ne yasa ta zauna tana dialing numbern ta back, yana fara ringing Mama ta ɗaga bayan sun gaisa tace "Layla kin san matan nan har sannan bata kira ni ba balle maganar zubewan cikin ki ba" Layla ta taɓe baki tace "Dama what do you expect? Kaɗan daga aikin matan nan wallahi Mama, yanzu kuwa tana ganin Leena ko Ammi sun fara walwala zata zo neman ki ai" Mama tayi wani murmushi tace "Har ta isa? Wallahi zata sha mamaki na, na san yadda zan yi da ita" Layla tace "Wallahi Mama ki fita har kan ta kawai" tace "Shiyasa yanzu nake son na sake karbo miki wasu maganin saboda kar ta fara controlling Rayyan ɗin a kan ki" Layla tace "Mama gaskiya Ni bana so, bana son wani magana, dan Ammi ta ganar da Ni abubuwa da yawa, idan ta Rayyan ne kuma dan Allah kar ki ɗaga hankalin ki dan wallahi bata isa tace zata kashe min aure ba, dan babu abin da zan mance ba zan faɗawa Hajiya da Daddy ba, dama naga dangin Daddyn ma ba sa sonta suke yi ba, dan bata girmama su hatta Hajiya fa bata gaishe wa" Mama tayi shiru tana mamakin guts ɗin Layla sai kuma tace "Ki dai yi a hankali kuma Karki ɗauki raini daga kannan sa musamman shegiyar can" Layla tace "Mama, it's just the start, yanzu wasan zai fara" sun ɗan daɗe sannan suka yi sallama. Ammi tana kallon Anty Binta da ta goya Nawaf a bayan ta tace "Dan Allah kar ku daɗe" Anty Binta tayi dariya tace "Toh Ammi" ta kalli Leena data tsaya gaba ɗaya jikin ta ya mutu tace "Sai kun dawo ko?" Leena ta sauke kan ta har ga Allah bata so zuwa ba, amma ya zata yi?. Bayan sun isa gidan Mami tun daga bakin gate taji kamar numfashin ta yana son ɗauke Wa dakyar take tafiya har suka shiga parlorn, suka samu Sultan da Jiddah as usual suna parlorn suna hira duk suka juya suna kallon su, da sauri Jiddah ta mike tace "Aww, ina Babyn mu?" ta karasa Anty Binta ta zare sling ɗin da tayi backing Babyn, Jiddah tace "Wow, Ma Shaa Allah, ji yadda Babyn ya koma?" ta karasa cikin parlorn tana nuna wa Sultan, su Leena suka karasa cikin parlorn suka zauna, duk ta gashe su suka amsa mata da fara'a, ba'a ɗau lokaci ba sai ga Mami ta fito, bayan sun gaisa Anty Binta tace "Dama ta gama Arba'in ne shine Ammi tace tazo ta gaishe ku" Mami ta rike haɓa "har anyi 40days? wai fa ina nan ina jiran tayi akan zamu zo" Leena bata ce komai ba tana ta Allah Allah su bar gidan, Mami tana ta kallon Nawaf da bashi da maraba da Baban sa sanda yake kaman sa, Anty Binta tace "bari zamu tafi" Mami tace "A'a haba tun yanzu kuma" sai sannan Leena tayi magana "Dama zamu fita ne ana jiran mu" Mami tayi murmushi kawai, Jiddah tace "Kai Leena, kice dai you're not comfortable Dan tun shigowan ku naga hakan daga gare ki" Leena ta sauke kanta kasa ta kasa cewa komai. Yau wajan kwana Niswa huɗu a gidan Farouq, tana zaune a ɗakin ta tayi nisa cikin tunani taji karan shigowan message wayan ta, hakan yasa ta ɗauki wayan, with shock take kallon message ɗin Ashraft zuciyan ta na bugawa, hannun ta na rawa ta buɗe message ɗin ta fara karanta contents ɗin, bayan ta gama ta runtse ido abu daya a message ɗin sa daya tsaya mata a rai shine 'he is ready to marry her idan ta yarda amma ba ita kaɗai zai aura ba har da zaɓin mahaifin sa' taji hawaye yana sauka kan kuncin ta, Farouq ne ya buɗe dakin na ta ya tsaya kallon ta da mamaki yace "wai ke har yanzu baki gajjiya da kukan ne?" ta share hawayen ta yace "Ina jiran ki a kasa ki sauko
End Ads