x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 65 - AGOLA free pages

  • 192001 words
  • 195000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
ku roka min yafiyar Hajiya da Maman Leena" Niswa ta ɗaga kai tana kallon Rayyan da shima kana ganin sa kasan daurewa kawai yake yi, ta fara tari wanda yasa da sauri Rayyan ya gyara mata kwanciyar ta yace "Dan Allah Mummy ki samu kiyi shiru maganar nan tun jiya kike forcing kan ki ke nanata magana ɗaya" har sannan hawaye na zuba tace "I failed you as a mother, ku nema min gafarar Daddyn ku ma" Niswa ta miƙe ta koma can karshen wall ta zauna tana kukan ta, Sai yanzu take kara nadama ganin dagaske bata da kowa gashi duk kuɗin ta bata ci sai Malamai wanda at long last ta tashi a tutan babu, hakan ke sa jinin ta sake hawa gashi yadda take jin jikin ta gani take ai mutuwar ta ne ya zo, Can sai gasu Layla da Hasna wanda sai da suka tsaya suka yi breakfast sannan, bayan sun shiga dakin duk sai da Mummy ta basu tausayi ba kaɗan ba basu ɗauka jikin nata ya sake worst akan na jiya ba. Da yamma bayan Ammi ta gama arranging warmers ɗin a cikin basket ta ɗaga kai tana kallon Nisreen dake tsaye jikin cabinet ɗin absent-minded tace "Nisreen ɗauka ki kai mota ko" Nisreen ta gyaɗa mata kai ta wuce tayi kamar yadda Ammi tace mata, ta kwala ma Ayaan dake dakin ta shi da Nawaf suna playing game tace "Ko ku fito ko kuma kuji mun tafi" daga haka ta wuce dakin Hajiya ta samu Hajiya na zaune yarda ta barta sai ma shan Fruits ɗin ta take hankali kwance dan tun da Ammi ta fara aiki ba ranan da gari zai waye Ammi bata tsaya ma Hajiya kaza ko fruits ba, ta zauna kan kujera tace "Hajiya mun gama shiri" Hajiya ta ajiye Apple ɗin hannun ta tana kallon ta tace "Toh sai aka yi yaya?" Ammi ta sake baki tana kallon Hajiya kamar ba ita bace ɗazu ta gama convincing ɗin ta tace "Hajiya maganar duba jikin Maman su Rayyan ne, Ni wallahi tun da naji Niswa na kuka tana gayawa 'yar uwarta nasan abun yayi tsanani" Hajiya ta naɗe hannun ta kirjin ta tana kallon Ammi tace "Baki san makircin Matar nan bane Hauwa, yanzu haka tayi da gangan ne dan na tabbatar bakin ta ɗaya da yaranta, so kawai take Muhammadu ya maida ta bata san yanzu kuma ya mata nisa ba tunda saki uku kam ya cika" Ammi tayi kasa da murya tace "Hajiya dan Yaranta zamu yi ba dan ita ba, wallahi yadda Niswa take faɗa jikin yayi tsanani kuma shi kansa Rayyan da muka yi waya nasan pretending yake yi" Hajiya ta suke fuska tace "Toh ma da kika saka ni a gaba kin sanar da mijin ki ne?" Ammi tace "Eh ɗazu na kira sa yace zamu iya zuwa" Hajiya tayi suka tace "Jaraba gare ki na rantse Hauwa, Matar da ta tsane ki, Matar da kallon kaskantacciya take min, Matar da ta raina kowa don Allah kalli yanzu da kika fara aiki yadda kika murmure Nima kaina yadda na koma hatta Nisreen baki barta a gantale ba amma ke lokacin da taki 'yar take zuwa bangaren ta duka ai take mata idan ke kin manta Ni ban manta ba, yanzu kar ki sha mamaki wallahi Hawan jini ne ya mata yawa saboda sanin cewa Lina pamilin sarki ne ita da mijin ta, wai fah har da tsayar da gidan da Mijin ki ya basu dan taga yadda zasu ta gayyara bayan bata san hakan zai zo da Alkhairi ba" Ammi tace "Kowa da halin sa dama Hajiya yanzun dai ki daure Ko dan su Rayyan ne" Hajiya ta miƙe tana daukan Hijab ɗin ta dake ninke akan kujera tace "Allah kawai darajar ki taci amma idan ta nine yaushe zan sake waiwaiyan ta balle taga munyi kyau ta sake saka mu a gaba" Tuni Ammi ta fita dan karma Hajiya ta sake ɓata lokaci dan ta lura Hajiya ba kaunar zuwa take ba, ko da ta isa motar ta samu already yaran suna ciki ta buɗe driver seat ta shiga ta zauna can sai ga Hajiya ta fito tana mita a haka dai har suka isa asibitin. Ba Ammi ba hatta Hajiya sai da ta girgiza da suka kalli halin da Mummy take ciki wanda yanzu ma jikin yafi rikicewa dan ko magana bata iyayi sai dai tayi ta binku da kallo tana zubar da Hawaye, Nisreen tun da ta kalli Mummy sau ɗaya ta ɗauke kanta ta dinga shan kuka dan ba karamin fita tayi a hayyacin ta ba, Hajiya tace "Nikam toh Riyan ba za'a fitar da ita kasar waje ba kuwa?" Yace "Eh yanzu ma abun da ake processing kenan da sun gama cike ciken su zamu kama hanyar India" Hajiya tace "Gwara dai kam" Ammi kam she was totally speechless Dan bata ɗauka abin ya kai ga haka ba, ko da za su koma gida sai kawai tace da Nisreen ta zauna ganin kamar Uwar na bukatar dukkan yaran ta a wajan. Bayan kwana biyu su Rayyan da Layla suka yi India da Mummy wanda har sannan babu wani improvement wanda hakan ke kara tayar ma da Rayyan Hankali, kafin tafiyar nasu sai da Ammi tasa Daddy yaje ya duba ta amma yaki sai dai ya turawa Rayyan enough Money da yasan zai ishe su. Leena na zaune a study area din ta dake parlorn wanda take karatun last paper da ya rage mata, Malik ya buɗe kofar ya shigo da sallama ta ɗaga kai ta Kalle sa har ya karasa ciki ya zauna tace "Sannu da zuwa Yayan Leena" yayi dariya yace "Yau kuma 'yan tsokanan suna kusa kenan?" Tace "Baka san me ba wallahi na gaji da karatun nan kuma har yanzu ban gama covering ba" yace "Let me eat first, zan zo na taya ki, dole ma ki fahimta" tayi dariya dan idan yana masa mata akan karatu sai ka ɗauka ma shi take wa karatun, ya wuce daki ba'a dau lokaci ba sai gashi ya fito da alama har ruwa ya watsa daya zo wuce wa ta gaban ta yace "Hey you" taki kula sa dining ya wuce ya fara serving kansa, Wayan ta ne ya fara ringing ta kalli me kiran ganin Ammi ne yasa ta ajiye text book ɗin hannun ta ta ɗauki wayan, bayan sun gaisa Ammi tace "Nikam Leena kin kira su Rayyan ɗin kiji ya jikin Mummyn kuwa?" Leena ta dafe goshin ta tace "Oops.. wallahi na sha'afa ne Ammi, amma bari na kira yanzu" Ammi tace "Idan aka ce kiyi abu baki son yi a lokacin" tace "Wai dama jikin nata har yanzu ne?" Ammi tace "Baki ganta ba, gaba ɗaya kamar ba ita ba ta gama fita a hayyacin ta gashi ko magana bata yi" Leena tace "Allah sarki, Allah bata lafiya da sauran Musulmai baki ɗaya" Ammi tace "Amin, dan Allah kar na sake kira kice min kin manta" tace "In Shaa Allah Ammi" Ammi tace "Toh ya Exams ɗin naku?" Tace "Alhamdulillah gobe In Shaa Allah zamu gama" Ammi tace "Toh Allah bada sa'a kenan a satin nan zaki bar Abuja ki koma Yola kenan ko?" Tace "Eh haka dai Granny tace" Ammi tace "Toh Madallah ki gaishe min da Malik ɗin" tace "Uhum" daga haka ta katse kiran, a take tayi dialing numbern Rayyan tana hoping zai shiga yana fara ringing ya ɗaga bayan sun gaisa tace "Ya Rayyan ya jikin Mummy? Yace "Alhamdulillah Leena, yanzu ana samun improvement dan tana iya motsa jikin nata" Leena tayi shiru duk jikin ta yayi sanyi tace "Toh Allah kara mata lafiya Yaya" yace "In Shaa Allah" ta kalli Malik da yanzu ya zauna a gaban ta da alama har ya gama da lunch ɗin sa tace "Ga Ya Malik zai gaishe ka" daga haka ta mika ma Malik wayan bayan sun gaisa ya tambaye sa ya jinki Mummy daga haka ya katse kiran, ya ajiye wayan nata a gefe yana kallon ta ya ɗaga mata gira ɗaya sama yace "Tell me zamu iya fara karatun?" Ta girgiza masa kai tace "Dan Allah ka bari sai dare kawai yanzu na gaji" kallon ƙafafuwan ta da suka kumbura tsuntum yayi a hankali ya kama kafar ya daura kan cinyar sa ya shiga matse mata su da hankali, karar door bell suka ji, ta ɗaga kai tana kallon sa tace "Kana da bako ne?" Yace "Nope" daga haka ya miƙe hijab ɗinta ta saka shi kuma ya wuce ya buɗe kofar kallon Muhammad da Mamaki yake sai kuma ya matsa masa ya shigo, Malik yace "Gaskiya munji kunya tunda ka riga mu zuwa" Muhammad na dariya yace "Not at all, ai bana kasar ne dan i think zuwan ku Abuja akan za'a muku interview the following day na bar kasar idan ban manta ba" Leena dakyar ta karasa cikin parlorn tana murmushi tace "Sannu da zuwa Ya Muhammad" yace "Yauwa Madam" Muhammad na kallon Malik yace "Ashe kai ɗan uwan Suhaif ne kasan wallahi ko dan ban sanka ba time ɗin amma yanzu da na kalle ka nasan photocopy ɗin sa ne" Malik yayi murmushi, Muhammad yana murmushi yace "Congratulations on reuniting with your family" duk murmushi suka yi Malik yace "Thank you, though kaine tsila" daga haka Leena ta wuce kitchen dan dauko masa ruwa kafin ta fito taga har yayi bakin kofa tace "A'a ba zaka tsaya ka sha ruwa bane?" Yayi dariya yace "Thank you, daga gida nake" har zai fita sai kuma ya tsaya yana kallonta yace "Yauwa su Nawaal sai damu na suke wai na kawo su wajan ki" Leena na Murmushi tace "Dan Allah ka kawo su" Malik ya raka sa har bakin motar. Washe gari kamar karfe sha biyu Leena ta fito daga Exams hall tana taku a hankali, Malik dake motar tun dazu yana jiran ta, hango ta da yayi ya sauka ya karasa har inda take ya karbi bottle water din hannun ta, yana rike da ɗayan hannun nata yana mata sannu har suka karasa jikin motar sannan ya buɗe mata ta shiga ya zaga shima ya shiga daga haka ya tada motar suka wuce gida. Bayan kwana biyu Hajiya Amira da kanta tazo ta dauki Leena a Abuja suka bi flight zuwa Yola, tunda Leena ta koma Yola ko motsi tayi sai taga ana mata sannu ita abin har dariya yake bata, gashi bayan kusan ko wani hour ɗaya sai ayi ta kawo mata abinci iri da kala ko zata ji yunwa, abin da aka san masu ciki na kwaɗayin su kuma kullum cikin tsiya mata ake, wata sa'in Leena har kuka take ganin ashe tana da wannan gatan? dama haka 'yan uwa suke?, Ranan Jumu'a da yamma Hajiya Amira na rike da hannun Leena wanda ta fita da ita dan zaga palace acewar Hajiya dole kullum take yi saboda haihuwar karta bata wahala suna cikin tafiya Leena taji wani sharp pain wanda hakan yasa ta tsaya cak Hajiya Amira tace "Lafiya daughter?" Leena ta kirkiri murmushi kawai zata ɗaga kafar ta ta gagara, Hajiya Amira ta ɗan tsaya tana studying dinta sai kuma tayi dialing numbern Mijinta wato Yarima Abdallah yana ɗaga wa tace "Yarima muna backyard da Leena ka taho da mota ina ga asibiti zamu yi da ita" bata jira cewar sa ba ta katse kiran ta duka kamar yadda Leena ta duka tana mata sannu. Tunda Malik yaji labarin Leena na asibiti shikenan hankalin sa ya tashi a ranan ya bar Abuja zuwa Yola, haka Leena ta kwana tana labour, wannan daren Malik ko rintsawa bai yi ba ya zauna sai addu'a yake ta mata, dakyar da safe Abbah ya kora sa gida dan ya huta yana barin asibitin sai ga Leena ta haifi 'yar ta Mace...
*AGOLA (Behind the palace walls)*



Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


*YOTA*



Chapter 77 & EPILOGUE


Bayan kwana biyu da dawowar su Mummy daga India wanda yanzu ta gama warkewa sai dai abin da ba za'a rasa ba, tana zaune tayi tagumi ga Niswa a gefen ta, Rayyan kuma yana ɓalla mata drugs, bayan ya gama ya miƙa mata yace "Mummy gashi" ta sa hannu ta karɓa ta dauki robar ruwan gefenta ta sha tana kallon Rayyan tace "Rayyan idan da hali ka kama min koda karamar gida ne wanda zan zauna a ciki amma ba zan iya cigaba da zama cikin matan ka ba" Rayyan yayi shiru sai kuma yace "Shikenan idan hakan kike so" Niswa tace "Amma Mummy a wajan aiki sun san baki da lafiya kuwa?" Tayi murmushin takaici tace "Ai sun sallame Ni" with shock Rayyan ke kallon ta kamar yadda itama Niswan take kallon ta yace "Kamar yaya Mummy?" Tace "Ina ga har da shi a damuwar da ya kwantar da Ni" duk shiru suka yi suna kallon ta. Da yamma sai ga Hajiya da Ammi wanda suka zo duba ta, bayan sun shiga da sallama, Hasna da Layla suna gaishe su suka mike suka basu waje, Mummy tana ta avoiding eye contact da Hajiya, Hajiya tana kallon Rayyan tace "Amma yanzu jikin da sauki sosai ko?" Yace "Alhamdulillah da sauki sosai wallahi" Hajiya tace "Toh Madallah, Allah ya kara sauki" duk suka amsa da Amin, Mummy ta ɗan kalli Hajiya sai kuma tayi kasa da murya tace "Hajiya dan girman Allah ki yafe min abubuwan da na miki" Hajiya mamaki kusan kashe ta yayi dan bata ɗauka haka daga Mummy ba, Hajiya tace"Wallahi babu komai Ni ban rike ki a rai ba, Allah mana mai kyau kawai" ta juya tana kallon Ammi, Ammi tayi saurin taran numfashin ta tace "Allah yafe mana baki ɗaya" Mummy tace "Amin, Nagode" Can tace "Leena fah?" Hajiya tace "Ta haihu ma tana can dangin ubanta a Yola, yau kwana uku kenan da haihuwar" Mummy tace "Allah raya abin da ta samu, ya bata lafiyar shayarwa". Bayan kwana biyu Rayyan ya nima mata wani gidan kusa da gidan sa. A palace, Ranan suna yarinya taci sunan Granny wanda ranan sai da Leena ta sha kuka ganin soyayyar da ake nuna mata a baya ba komai bane, gift boxes ta karba ba adadi ga kuma manyan gift da ake ta bata, wanda duk wannan hidimar da Hajiya akayi sa washe gari zata koma Kaduna Mai martaba yace ta zauna ta huta tukun nan.

EPILOGUE

Bayan shekaru bakwai.....
A wani babban hall dake cikin Nile university of Nigeria..
Hall din taro ya cika da mutane  iyaye, malamai, abokai, da dangin dalibai. Ranar graduation ce na ɗaliban Nike University, kuma an kawata wajen da kyawawan flowers, banners da hotunan graduating students. Amma kusan kowa da kowa yana magana ne akan wata mace guda: "Leena!". "She's the one that broke the record, right?" wata Mata ta tambayi wata da ke gefenta.
"Yes, itace kamar princess ce ma" aka amsa. "Ten years, and no one has ever graduated with a first class in MBBS. Leena just made history"....
Leena ta tsaya a stage, cikin gown ɗin ta da cap, tana murmushi amma idonta cike da hawaye. Lokacin da aka kira sunanta, aka ce: "The overall Best Graduating Student of the Year goes to… Leena Abbah"
Dukan wajen ya ɗauki ihu da tafi musamman zugan dangin Leena.  Abbah daga wani kofa ya shigo yayi kan stage ɗin wanda tunda Leena ta hango sa ta fara murmushi mai kamar kuka.. Ammi ta miƙe da hawaye a idonta amma ta zama frozen kallon sa da tayi har ya isa stage, zuciyar ta ya shiga duka uku uku, ya karɓi award tag da wani lecturern su ya miƙa masa ya saka mata a wuya sannan ya rungume ta yayi kissing forehead ɗinta, a hankali Ammi ta furta 'Abbah!' Granny kallon yanayin Ammi yasa ta fahimci kila Ammi bata taɓa haduwa da Abdallah bane hakan yasa tace "Abdallah ne, twin bro din Ex husband din ki" Ammi ta juya ta Kalle Granny sannan ta samu ta sauke ajiyar zuciya ta wuce stage inda ake kirar Mahiafiyar Leena. Hasumiyar daraja ta sauka a kanta, An bata award guda bakwai, ciki har da 'Best in Surgery', 'Best in Internal Medicine', da 'Best in Community Health'
Khairat Mai shekaru Bakwai yanzu da haihuwa ta kwace hannun ta ana Amira tana murmushi tace "Thats My Ammah, granny" ta gyaɗa mata kai. Leena na makale jikin Abbah har suka iso inda suke, ba karamin Mamaki tayi ba da taga Nisreen, Niswa harda Mummy ta karasa ta gaishe su suna taya ta murna. Juyawa da zata yi taga mijinta Suhail, ta sakar masa murmushi , ya tsaya yana kallonta da alfahari. Ya matso kusa da ita, ya zaro key ɗin mota daga aljihunsa, ya miƙa mata.. "Ina alfahari da ke, Dr. Leena. Wannan kyauta ce gare ki" Yace yana murmushi. Leena was totally speechless ta rufe bakin ta da hannayen ta biyu tana kallon sa
Mota ce sabuwa, Lexus SUV, farin launi, an ɗaura balloons a jikin ta da ribbon mai launin zinariya. Dukan wajen ya ɗauki da ihu, "Allahu Akbar!"
Leena na tsaye kusa da motar, har yanzu tana jin kamar mafarki take. Balloons sun zagaye sabuwar Lexus ɗin da Suhail ya bata. Idanunta suka sauka kan wani ƙaramin envelope da aka ɗaura da ribbon a jikin balloon ɗin.. Ta ɗauke shi da mamaki, ta buɗe envelope ɗin a hankali. Takarda ce mai tsabta, rubutaccen saƙo da hannun Suhail Contents ɗin cikin:-
"Thank you for believing in me when I had nothing. 
Thank you for choosing me when I wasn't anyone. 
I promise to keep making you smile, for the rest of My life."

Ta runtse ido, zuciyarta na dukan da ba ta saba ba. Hawaye suka gangaro fuskarta, ta juyo gare shi, ta rungume shi kamar ba zata sake shi ba, bata damu da duk wanda suke wajan ba.. itama ta furta
"Suhail… you have no idea how much this means to me," ta furta cikin sanyi. "Wallahi, if not for your support, I wouldn’t have made it, You stood by me when I nearly gave up. You reminded me who I was when I forgot. I love you more than words can say”
Ya dafa
End Ads