x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 41 - AGOLA free pages

  • 120001 words
  • 123000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
da alama dai daga asibiti suka dawo" Mummy tace "kuma sun shiga?" tace "Toh karewan ta ma Layla ke rike da Babyn" Mummy tace tama manta ta sake abin hannun ta tana kallon Niswa.
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧



Hauwa Jibrin Sulaiman
(Jiddatul-khayr)


Wattpad © Jiddatulkhayr


Young talented writers association (YOTA)


Chapter 47

____Layla ta mika wa Ammi Babyn hannun ta sannan ta mike ta musu sallama. Tana fita a compound ɗin ta sami Rayyan da alama dai daga part ɗin Daddy ya fito, ta karasa har inda yake tsaye tana masa murmushi, ganin ta yasa ya zare wayan kunnen sa yace "Bari mu gaisa da Mummy sai mu wuce" bata ce masa komai ba ya fara tafiya tana bin bayan sa har suka karasa part din, da sallama ya shiga Layla na biye da shi a baya, Niswa da ta fito daga dakin Mummy kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta a hankali tace "Yaya ina wuni" ko gama amsa mata bai yi ba ta wuce ciki abinta, Layla tayi murmushi sannan ta zauna akan kujera shi kuma ya wuce ɗakin Mummy yayi knocking, tattara abin da ta sake kasa take yi ta cusa shi kasan gado sannan tace "ina zuwa" bayan ta buɗe kofar ta tsaya kallon sa ya gaishe ta ta amsa masa a dakile yace "Mummy Layla na parlorn zaku gaisa" ta taɓe baki sannan ta fita ta kulle dakin bayan ta karasa parlorn ko da Layla ke gaishe ta ta amsa mata a dakile ba yadda ta saba mata ba, Layla kuma bata damu ba as far as mijin ta zai so ta it's okay for her, daga haka Mummy ta wuce ciki, Rayyan ya kalli Layla yace "Let go" ta mike bata kuma damu da ta musu sallama ba tabi bayan sa. Leena ta fito a wanka ta samu Ayaan yana makale a jikin gadon jaririn yana kallon Babyn tace "Kana so ne?" ya juya da sauri yana kallon ta sai kuma yace "Eh Addah" tace "Toh na baka dukka, je ka zan sa kaya" ya mike yan jin dadi ya fita da gudu yana cewa Addah ta basa Babyn, Leena ta karasa jikin gadon Babyn ta duka tana kallon kyakkyawar fuskan sa, toshe bakin ta tayi da sauri jin kukan da ya zo mata, ta zauna ta dinga rera wa, muryan Anty Binta tajiyo har tsakiyan kan ta tace "Yanzu saboda mutumin da bai damu da ke bane kika zauna kike masa kuka?" Leena ta share hawayen fuskan ta taki kallon direction ɗin anty Binta ta wuce zuwa inda kayan ta ya ke. Bayan Hajiya ta fito daga toilet da alama dai alwalar bacci tayi, ta haura kan gadon ta bayan ta gama azkar ɗin bacci ta shafe jikin ta, maganganun Anty Binta ne da ta faɗa musu a asibiti game da abin da Jiddah ta faɗa mata akan Sadeeq ne ya fado mata tayi shiru tana ta tunani haka dai har dare ya raɓe Hajiya ta kasa bacci daga baya bacci barawo ya ɗauke ta. Washe gari da safe Hajiya da wuri ta wuce part ɗin Daddy dan karma ya wuce aiki bata sani ba, tana sallama ta buɗe kofar ba tare da ta jira ya bata izinin shiga ba, bata gansa a parlorn ba hakan yasa ta zauna jiran sa ba'a dau lokaci ba sai gashi ya fito Hajiya ta dinga kallon sa bayan ya karaso ya zauna yana gaishe ta Hajiya tace "Rike gaisuwar ka Malam, jiya kwanan mu bakwai Leena kwance a asibiti amma baka ko leka mu ba" ta karasa maganar fuskar ta a tsuke Daddy ya zauna kan cushion yace "Just that abubuwa ne suka min yawa" Hajiya tace "Abubuwa ? Abubuwa zaka ce min? Tabbas abubuwa ne suka maka yawa daga kai har Khadijan, amma da Niswa ce a kwance ai ba zaka ce abubuwa bane suka maka yawa" yace "Sirbajo ta same ki da maganan kenan? Ita bata hakuri ne ko bata san bawa mutun uzuri bane, kwata kwata bata da hakuri a rayuwar ta, na gaji gaskiya" ya mike saboda ɓacin rai Hajiya ta mike ta sake baki tana kallon sa tace "Tabbas Khadija ta shanye ka, yanzu har kana da bakin cewa Hauwa bata da hakuri? wani irin hakuri ne tun farkon zuwan ta gidan nan bata yi ba? wani irin wulakanci ne bata gani ba daga wajan ka har da matar ka? ka hana ta aiki amma kabar Khadija na yi, ka hana ta motar amma ka siya wa Khadija, idan ta hau motar a gidan nan to motar yara ne yanzu ya kai da ya kawo ko motar yaran ka hana ta hawa sai dai ta hau na 'yarta, wallahi toh karshen zaman ka da Khadija ne yazo a gidan nan sai dai ko ka zaba ita ko Ni" daga haka ta wuce fuu sabar yadda ranta ya ɓaci a nan compound ta haɗu da Mummy da fitowar ta kenan zata aiki amma ko ta kan Hajiya bata bi ba, itama bata damu ba ta wuce part ɗin ta. Duk suna zaune a parlorn, Ammi na rike da Babyn Leena kuma tana breakfast Anty Binta sai faman faɗa take mata idan zata daina wannan kukan gwara ta daina, jikin Ammi yayi sanyi sosai gani take kamar ita ne ta yi wasa da rayuwar 'yar ta da ta bari Rayyan ne ya aure ta kila hakan ba zai faru ba ganin yadda Leenan ta zabge ko irin jikin haihuwa babu, tun da tayi kwana uku kuma kumburin haihu ya sabe ta, sallamar Mami suka ji duk suka daga kai suna kallon ta har ta karasa ciki ta ajiye basket ɗin hannun ta bayan sun gaisa Mami ta karbi Babyn tana kallon sa, Ammi tace "Ya mai jiki?" Mami tace "A'a yanzu kam ya warware" Leena ta sauke kanta kasa, Mami tace "kun ji Jiddah wai gobe da yamma za'a yi hotunan suna" Anty Binta tace Allah kaimu, ta mike tace "barin wuce office kar na makkara" har zata fita kuma sai ta dawo ta buɗe jakkan ta ta ciro wayar Leena tace "Daughter ga wayar ki ana ta kira yasa kawai na kashe" Leena ta karba a hankali tace "Nagode" Mami na fita ta kusan cin karo da Hajiya da zata shiga dakin Ja baya tayi ta gaishe da Hajiya, Hajiya ta amsa mata sannan ta tafi, Hajiya kuma ta karasa cikin dakin, bayan ta zauna tace "Leena ina son sanin me ya haɗa ku fada har ya kai ga saki" Leena ta sauke kanta kasa Ammi ta zuba mata ido dan itama amsar da take son ji kenan a hankali tace "Muna zaune lafiya kalau ba wani abu da ya taɓa shiga tsakanin mu na fada ko sa in sa, wata rana ya dawo a aiki Cousin ɗin sa ne ya kawo sa, tun daga wannan ranar kuma shikenan kullum yayi ta min faɗa ta sawa" ta sauke idon ta kasa haka nan taji ba zata iya cewa yana marin ta ba, Hajiya tace "Ya akayi ya sake ki?" tace "Nima ban sani ba, kawai yace baya son gani na shiyasa ya koma gidan Mami da zama, toh akwai ranan da Jiddah ta tambaye Ni na boye mata, sai kuma wata rana da Mami taje ta ga halin da nake ciki shine ta mayar da Ni gidan ta, ashe shima ya koma gidan ta ne saboda baya son haduwa da Ni, bayan...." A haka Leena ta gama basu labarin tsakin ta , Anty Binta tayi murmushin takaici tace "kana jin labarin nan kasan ba yin kansa bane" Hajiya ta mike tace "kiyi hakuri Lina, ki ɗauka wannan jarabawar ki ne, kuma zan dauki mataki in shaa Allah" daga haka ta fita da tunanin yadda zata fara bullowa lamarin nan. Bayan ta gama lunch ta dauki Babyn ta tana kallon sa dan ita bata gajjiya da kallon sa Anty Binta tace "Oh ai mun shiga uku kuma, ke bakya jin kunya ne? Kamar ba jinin Fulani ba?" ta ajiye Babyn a gefen ta itama ta kwanta, gatekeeper ne ya ke magana Ammi ta fita bayan ya isar mata da sakon da ke tafe ta shi, ya koma bakin aikin sa, Ammi ta wuce dakin Leena tana kallon ta tace "Wani mutum ne wanda ranan ya kawo ki gida?" Leena ta daga kai tana kallon Ammi ita sai yanzu ma ta tuna da Malik a hankali tace "Okay, Malik ne, wanda Zahra ta taɓa baki lamarin wai muna kama kuma ni banga kamar ba" Ammi tace "Toh wai yazo gaishe ki da jiki" Leena tayi ta kallon Ammi sai kuma tace "ya zo gaishe Ni da jiki kuma?" Ammi tace yana can car park ai sai ki je" anty Binta tace "tashi mana ana magana kina sime sime" ta ki kallon Anty Binta ta mike ta dauki wani Hijab dinta har kasa ta sa, bayan ta isa inda yake har an ajiye masa kujera ya zauna Leena ta zauna kan plastic chair ta gaishe shi, tana jin ya sauke ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah" da accent ɗin sa na larabci yace "Ya jikin kuma?" A hankali tace "ina wuni" ya kuma cewa "Ya jikin na ki and the Baby?" tace "Alhamdu Lillah da sauki sosai" yace"Allah kara muku lafiya ya raya mana shi bisa suna" tace "Amin" ta kagu ta koma ciki, nan Malik ya dinga bata shawarwari da words da za suyi calming ɗin ta down dan jinta yake har zuciyar kamar yana da bond da ita, Leena kuma kalaman sa sunyi tasiri sosai a zuciyar ta, ta mike ta masa godiya daga haka ta koma ciki, anty Binta na kallon ta tace "Kar dai ya tafi?" ta gyada mata kai "Anty Binta tace "Oh Ni ban san yaushe zaki girma ba, ace bako yazo ai sai ki kai masa Babyn ya gani" Leena bata bi takan fadan da take mata ba ta wuce dakin ta kawai. Ammi na zaune rike da Babyn tana sa masa kaya taji sallamar Zahra, Ammi ta amsa mata har ta karasa ciki ta zauna tana kallon Ammi ta gaishe ta bayan Ammi ta amsa tace "Ammi kar dai Leena ce ta haihu?" Ammi tayi murmushi tace "Eh, ki shiga ciki ta na nan" Zahra ta shiga taga Leena na fitowa a toilet, ta karasa tana tace "Kawata" Zahra ta Harare ta tace "Wallahi Leena baki da mutunci, har ki haihu babu labari?, kuma ayi ta kiran ki baki ɗagawa balle ki kira mutum back" Leena ta marairace tace "wallahi dazu aka kawo min waya ta. Jiddah da Sultan sai labarin wani Film suke, Mami tana zaune tana jin su amma bata ce wa komai haka Sadeeq ma da bai dade da dawowa daga waje ba yana kallon su, amma tunanin sa yana waje daban Mami tace "Jiddah kin sake magana da masu snacks ɗin?" tace "Eh Mami" Mami na kallon Sadeeq tace "Baba ba zaka je ka ga me sunan ka bane?" yayi murmushi kawai bai ce komai ba Mami tace "dan Allah ka daure ka je, wallahi ba su da matsala sun fahimce mu" yace "just that ina jin kunyan su ne amma zan je in shaa Allah, dan Nima ina son zuwa" Mami tace "toh yaushe kuma zaka mayar da ita" a hankali yace "Mami bana tunanin zan maida ta" Mami tace "Bangane ba?" Jiddah tace "ko dai har sannan baka warke bane?" hararan ta yayi yace da Mami "Mami duk yadda Allah ya ƙaddara kawai, amma bana tunanin zan iya kallon ta da maganar nan" daga haka ya jingina da kansa yana kallon sama, Mami tace "ina maka addu'a abin da yafi maka alkhairi" Sultan ya kalle sa har sannan yana tausayin ɗan uwan nasa, Jiddah tace "Mami ga shawara, ina ga Ya Sadeeq ya tafi Umrah kawai dan wallahi yana cikin damuwa baya son bayyana hakan ne". Da yamma Hajiya ta fito a dakin ta tana kallon Ayaan tace "Kai baban ku ya dawo?" Ayaan dake game da wayan Leena yace "Eh yanzu zuwan sa" Hajiya daga haka ta wuce dakin ta ta ɗauki wani laida ta fito, kitchen dake compound ta nufa ta dauki kasko ta zuba gaushi a ciki ta wuce sashin Daddy ba tare da tayi Sallama ba ta shiga kanta tsaye, yana zaune a Parlorn yana aiki da system ɗin sa ta wuce bedroom ɗin sa ya ɗaga kai yana kallon ta, tana shiga ta ajiye kaskon ta buɗe laidan hannun ta ta ciro wasu garin maganin hayaki ta zuba a gaushi sai da ya kone tass sannan ta ɗauka ta wuce toilet dinsa ma haka ta kuma yi ta fito parlorn har sannan yana zaune inda ta barsa ya gagara cigaba da abinda yake yi kuma sannan ya kasa magana na, nan parlorn ma ta zuba, Mummy ta shigo da sallama turus ta tsaya tana kallon Hajiya tace "Hajiya me haka kuma?" Hajiya bata tanka ta ba ta dauki kaskon tana zaga parlorn da shi ta kalli Daddy da sauri tace "Dear, kana zaune kana gani tana banka maka wani magani a dakin ba zaka ce komai ba?" Hajiya ta ajiye kaskon a kasa Mummy ta toshe hancin ta ita duk damuwar ta Daddy ya fita a parlorn, Hajiya tace "Har kina da ikon sa baki a lamarin Ni da ɗa na?, wallahi idan baki yi hankali ba zaki sha mamaki na, zan gwada miki nike da iko da shi ba ke ba" Mummy ta juya ta fita fuu ranta yayi Bala'in ɓaci, Hajiya dadin ta kuma yadda Daddy bai yi reacting ba, daga haka ta wuce dakin Ammi, bayan ta mata bayanin maganin da ta karbo a kauye ne ta mika mata, Anty Binta ta karba da sauri ta kai dakin Ammi, ba inda Anty Binta bata sa ba a gidan. Bayan Mummy ta koma daki wayan ta ta ɗauka da sauri ta shiga kiran aminiyarta bayan ta ɗauka ta shiga narrating mata abinda ya faru, Hajiya Fatima ta kwashe da dariya tace "kice de matar nan kar take kallon mu" Mummy ta bata rai tace "Mafita fa nake nema, Ni ban damu da kar da kika ce tana kallon mu ba" tace "ki bari gobe zan shigo" daga haka ta katse kiran. Washe gari aka yi suna ba karamin kudin su Mami suka kashe ba, sai da suka mata akwati set, gurin ba karamin kyau yayi ba, daga karshe Leena ta gaji ta koma ciki. Da yamma tana kallon some pics and vids da aka yi a wayan ta suna labarin yadda su Mami suka kashe kudin, Jiddah ta shiga tana kallon anty Binta ta faɗa mata magana a kunne, sai kuma ta mike ta fita, bayan fitan ta tace "Ammi Sadeeq ne ya zo" Leena ta kalle ta sai kuma ta ɗauke kai ta mike zata dakin ta Ammi tace "Leena baki ji me Binta tace miki bane?" Leena tace "Toh me zan masa? Idan Babyn yazo kallo ai gashi a hannu ku, no need na tsaya ai" sai da Ammi tayi da gaske sannan Leena ta tsaya bayan Sadeeq ya shiga parlorn anty Binta ta kai masa Babyn daga haka ta koma ciki, kallon Babyn yake ba kiftawa nan da nan yaji hawaye da kyar ya iya daurewa, sallamar Leena da yaji yasa ya daga kai yana kallon ta, har ta karasa ta zauna bai ɗauke idon sa akan ta ba, ita kuma taki yarda ta kalle sa, a hankali tace "ina wuni" bai amsa mata ba har sannan ya gagara daga idon sa daga kanta, jin shirun yasa ta daga kanta ta kalle sa, Leena couldn't help but stare at him...
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr


YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA)


48.......
Bayan tafiyan Sadeeq suka kasa gane kan Leena, sai ta zauna ita kadai tayi ta kuka daga karshe daga Ammi har Anty Binta kyale ta suka yi. Bangaren Hajiya kuwa bata fasa aikin ta ba, dan ba ranan da gari zai waye bata turare dakin Daddy da hayaki ba. Rayyan ya tsaya yana kallon ta, ta marairace masa tace "light food zan daura kaga ba daÉ—ewa zai yi ba" yace "Don't stress yourself please, idan muka je can gida nasan by then an gama Lunch" ta masa wani kallo tace "A tunanin ka sai na barka ka ci abincin gida? No, never" daga haka ta wuce kitchen dan daura musu abinci. Bayan yayi parking ta juya tana kallon sa tace "Na shiga na gaishe da Ammi?" yace "Why not" ta sake masa murmushi ta sauka, shi ma saukan yayi ya zaga ta inda take yace "Bari na fara zuwa dakin Hajiya kin san dama ita ta bukaci da nazo" kai kawai ta gyada masa. tayi sallama Anty Binta dake zaune a Parlorn ta amsa mata bayan ta shiga ta gaishe, Anty Binta ta mike tace barin ma Ammin magana, ba'a dau lokaci ba sai gashi sun fito tare, Ammi ta zauna tana amsa gaisuwar ta, tace "Ammi ina mai jego?" Ammi tayi murmushi tace "ki shiga tana dakin ta" daga haka Layla ta mike ta wuce dakin Leena, da sallama a bakin ta ta shiga, Leena ta daga kai tana kallon ta da mamaki, bayan ta zauna Leena ta gaishe ta, ta amsa tana tambayar ta ya karfin jikin, duk Maganan nan idon ta na kan gadon Baby, ganin haka yasa Leena mike wa ta dauko mata, ta karba tace "Allah bani nima irin wannan" Leena bata ce mata komai ba, dan ita ba wani haduwa suke yi ba balle su saba, ta mike rike da Babyn tace "Ina Zuwa bari na gaishe da Hajiya da Mummy" kai kawai Leena ta gyada mata, ta É—auki wayan ta tana karanta sakon Malik da ya shigo, dan yanzu kusan ko da yaushe sai ya tura mata message da zai kwantar mata da hankali, ta manta past ta fuskanci Future with good faith. Anty Binta ta sake baki ganin fita zata yi da Babyn kasa hakuri tayi tace "Ina kuma zaki?" ta juya tana kallon Anty Binta da murmushi shinfiÉ—e a fuskar ta tace "Hajiya da Mummy zan gaisar na dawo" tayi shiru bata ce mata komai ba daga haka
End Ads