x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 37 - AGOLA free pages

  • 108001 words
  • 111000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
galabaice take nan kofar parlorn Ammi ta yi sallama Ammi dake dakin ta ta fito da sauri ta buɗe kofar tace "toh ki shigo mana Hajiya" Hajiya tace "A'a ai ba zan iya shigowa a haka ba, jiki na duk dotti ne wallahi, baki ga kauyen bane da zaki san nayi kokari" Ammi tace "Ayyah toh sannu da hanya" Hajiya tace "Wallahi Hauwa'u muna cikin tashin hankali, matar nan makira ne, yanzu haka duk binmu take da sharri, duk sauyin mijin ki ba a banza ba, amma Alhamdulillah an bani magunguna da hayaki da kaina zanna turara dakin sa wallahi yana dawowa daidai ya sallame ta kawai tayi gaba" Ammi tayi shiru tana jin Hajiya sai kuma tace "toh barin kawo Miki abincin ki, idan kika huta" Hajiya tace "toh" daga haka ta kama hanyar part dinta tana magana ita kadai dan abinda aka faɗa mata bata taɓa sanin Mummy muguwa bace irin yau. Sadeeq anan unguwar su yayi sallahn Magrib ana idar wa gidan Mami ya shiga, ko kallon Sultan dake zaune a Parlorn be yi ba, ya wuce ya kwanta akan resting chair Sultan ya dinga kallon sa dan yanzu tausayin Sadeeq ɗin ya fara ji, yanzu ya fara yarda da Maganan Mami gwara a duba sa kawai idan kuma suka ce lafiyan sa kawai su koma na gida, yana wannan tunanin har Mami ta fito ta same su, haɗe rai tayi tana kallon Sadeeq tace "Me ka zo yi min a gida?" ya daga kai yana kallon Mami kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace "Anan zan kwana" Mami tace "tashi ka bar min gida" kallon ta yake tace "kasan da anan zaka kwana shine zaka dauke 'yar mutane ka mayar da ita can gidan ita kadai?" Sadeeq bai kuma cewa komai ba ya gyara zaman shi ya jingina da cushion ɗin ya lumshe idon sa, Mami ta kalle Sultan sai kuma tace da Sadeeq "Tashi ka bar min gida ba zaka barta ita kadai ba, idan wani abun ya taso cikin dare fah?" ya buɗe idanun sa sai dai bai ce komai ba dan yadda zuciyarsa ke masa zafi, in a serious note Mami tace "Magana nake maka, ka tashi ka bar min gida or else ka kawo ta nan" ya mike without looking at them idon sa yayi mugun Ja, ɗaukan keyn motar sa yayi a Centre table ya fice ba tare da ya jiyo ba, duk suka bi shi da kallo, Mami ta sauke ajiyan zuciya so speechless Sultan yace "amma Mami gaskiya labarin Sadeeq da mamaki" Mami ta gagara magana kawai ta mike ta shiga dakin ta wayan ta ta ɗauka ta shiga kiran Kanwar mahaifiyarta. Tun da Sadeeq ya tunkari gidan sa damuwar sa ya ninku, gaba ɗaya ya nemi wata nutsuwa ya rasa ta, gaskiya dole ne ya nemi wani Alternative dan yaga basu fahimtar sa, bayan ya shiga bata parlorn, shima dakin sa direct ya wuce bayan yayi wanka yayi sallahr isha'i da bai samu yayi ba, bayan ya idar ya jingina da bangon dakin yayi shiru yana kallon waje daya shima kansa yasan ba lafiya ba but ya rasa damuwar me yake ciki, abu ɗaya kawai ya sani da zaran zai shiga gidan sa sai yaji tsanar gidan kuma damuwar sa ya ninku, ana ambaton Leena kuma ji yake kamar wanda ake saka ma wuta a jiki ya lumshe idon sa yana jin gaba ɗaya duniyar ta masa zafi, ga Mami ta gagara fahimtar sa, 'Ya Allah' ya furta a hankali, jin wayan sa ke ringing yasa ya buɗe idon ganin Mami ke kira ya sake rufe idon har wayan ya katse, haka kira ya dinga shigowa yana yanke wa wani zai shigo amma ba shi yasa ya daga kiran ba daga karshe jin kiran ya fara damun sa yasa ya dauki wayan gani yayi ba missed call ɗin Mami kadai ba har da na Jiddah da Sultan kawai yasa wayan a silent, ya kalli agogo dake nuni da pass 12am, shawaran da ya yake kawai yake ji zai aiwatar kawai barin garin zai yi. Tunda tayi sallahr isha'i take zaune ana wajan fama kawai take da kanta wani azabebben ciwon ciki da baya ne ke damun ta hawayen kawai ke sauka daga idon ta da ta tuna ba waya a hannun ta sai ta fashe da kuka gashi ta gagara daga kafar ta balle ta iya fita waje ko da makota ne su taimaka mata, a haka har taji shigowan Sadeeq amma ba bakin magana dan karfin ta ya kare, can da ta ji ciwon maran ya ɗan sake ta ta kama rarrafe lokacin yayi daidai da fitowan Sadeeq daga dakin sa saboda yunwar da yake ji tana durkushe bakin kofar dakin ta tace "Dan Allah ka taimaka min, ka dubi condition dina kar ka share ni" Sadeeq ya juya yana kallon ta da mamaki nan take yaji wani kalar sanyi na shigar sa daga nan kuma sai jikin sa ya dau zafi, ya fara shivering, ya faɗa mata itace baya son kallo amma ya lura sai tayi abinda zai sa ya kalle ta da kyar ya iya buɗan baki yace "Wai ma dole ne zama da ke? Ki je ki na sake ki" Sabar shock Leena sai taji kamar ciwon bayan nata ma ya ɗauke ta dinga kallon sa har ya shiga kitchen idon ta na kan kofar kitchen din after some minutes sai gashi ya fito da cup din tea a hannun sa, be san sanda ya sake cup din ba, ya faɗi kasa ya tarwase yace "kina nan har yanzu? Nace na sake ki ko baki ji ne? Na baki nan da 2 min ki bar min gida" daga haka wa wuce ciki, dakyar Leena ta iya kokari ta mike amma still tana rike da cikin ta, dakyar take iya jan ƙafan ta har ta koma daki ta dauki hijab ta sa, inda zata samu aron waya kawai take so, gashi har sannan Mami bata kawo waccan zata zauna da ita ba kuma basu da mai gadi, tana durkushe sai ga Sadeeq ya kuma fito wa shima daurewan kawai yake yi, barin gidan kawai yake son yi, Leena dakyar ta buɗe bakin ta tace "Ban taɓa tauye maka wani abu ba ko shiga hakkin ka, amma ka sani Allah zai saka min" daga haka ta fita ba tare da ta jira me zai ce ba, tafiya tayi sosai sai data fita bakin titi taji wani murɗewan ciki da yasa ta durkusa nan kasa ba shiri, hawaye na sauka a idon, ambaton Allah kawai take yi, dama aim dinta ta tare abun hawa ya kaita gida idan yaso sai su biya mata kudin tricycle, duk addu'an da ya shiga bakin ta yi kawai take yi. Tun da ya fito a shagon yake kallon har ya tada bashin ɗin sa da niyyar tafiya sai kuma yaji ba zai iya kyaleta haka nan ba, ya karasa inda take durkushe ya parka mashin ɗin sa a gaban ta yace "Baiwar Allah lafiya?" tace "ka taimaka min For Allah's sake" ta dago kanta, with shock yake kallon ta yace "Leena!" Sai sannan ta kalle sa amma ita damuwar ta ya taimaka mata.

Jiddatul-khayr ✍🏼
08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧



Wattpad © Jiddatulkhayr

YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION


Chapter 43


______Mami ta mike tsaye daga zaunan da take yi tace "Sultan barin tafi gidan na shi kawai" Sultan ya sake baki yana kallon ta sai kuma ya ga agogo da ke nuni da pass 12am tun ɗa zu yake son komawa gida amma ganin yanayin da Mami ta shiga yasa ya zauna har sannan, yace "Mami dare fa yayi, pass 12am ne fah yanzu" Mami ta dauki hijab ɗin ta ta saka tace "Gwamma kawai naje, baka ga yadda ya fita ba ne? gaba daya fa kamar baya cikin nutsuwa, kuma damuwa ta halin da yarinyar zata shiga ne, gashi sai bugun zuciya ta tana kara tsananta" Sultan ya mike ya ɗauki keyn motar sa yana kallon ta yace "Bari ni zan tafi, duk yadda ake ciki zan sanar miki, daga can kuma sai na wuce gida" Mami ta sauke ajiyan zuciya tace "toh sai ayi ta kiran sa ba zai daga ba? Kuma aina aka taba haka? Duk laifina ne da kawai kai na sa kaje ka dauki yarinyar ka kawo ta nan kawai, da kaga yanzu tana nan ai" Sultan yace "barin tafi Mami, amma Please ki samu ki kwanta yanzu, saboda kina bukatar hutu, dare na yi" tace "in shaa Allah, Nagode! Allah tsare ka" ya amsa da Amin. Tuki kawai yake yi amma gaba ɗaya tunanin sa ya cunkushe, toh ko gaskiyan Mami ne ko kuma ya samu tabin hankali ne, a bakin gate ɗin gidan yayi parking yana tunanin taya zai sanar da shi yana bakin gate bayan baya picking calls ɗin su, a hankali ya sauka a motar ya karasa jikin gate mamaki ya kama sa ganin gate ɗin a bude, kawai ya shiga gidan amma bai tashi jin mamakin gaskiya ba sai ganin parlorn ma a bude ya ke ya shiga da sallama at this point yama rasa wani tunani zai fara, kuma mai ya kamata yayi? A hankali ya karasa jikin kofar dakin sa ya kai hannu zai yi knocking yaga kofar a buɗe yake tsaya for some seconds yana bin kofar da kallo daga karshe kawai yayi karfin buɗe dakin, ya shiga da sallama yana bin ko ina da kallon sai kuma ya fita ganin alamun ba kowa a dakin, a haka ya fita ya koma mota bai kai ga tada motar ba sai ga kiran Mami, ya daga tun kafin yayi magana tace "me yace maka?" ajiyar zuciya ya sauke yace "yanzun nan na barsa agidan but everything is fine, ki samu kiyi bacci Mami" Mami tayi shiru for some seconds kamar tana son gano wani abu sai kuma tace "Toh Sultan" daga haka ta kashe. Bayan ya isa gidan sa yana bude kofar parlorn ya shiga ga mamakin sa Jiddah na zaune da alamar dawowan sa take jira, ta taso ta karasa inda yake tayi hugging ɗin sa, yayi kissing forehead ɗinta sannan ta sake sa yace "baki yi bacci bane?" tace "Taya zan iya? amma ka same sa agidan, I mean me yace maka?" yana rike da hannun ta suka kama hanyar bedroom yace "Everything is alright, babe". Tun a hanya take ta kuka gaba ɗaya ya rasa yadda zai yi da ita, dakyar ya daure yace "I'm sorry to say Leena, ko mijin ki shaye-shaye ya fara da zai barki cikin daren nan ki fito" dakyar ta iya buɗan baki tace masa "Ai saki na yayi" bai san sanda ya parka mashin ɗin sa ba ya juya yana kallon ta, ji yayi inama zai ga wannan Sadeeq din yanzu yana jin zai iya kashe shi dan tsanar sa da ya fara ji, ya gagara cewa ko kala sai kallon ta cike da tausayi da yake yi, itama bata ce masa komai ba daga haka ya tada machine dinsa har suka isa gidan su Leena bai ce mata komai ba, dakyar ta iya sauka a mashin ɗin shima da taimakon sa da sauri ta duka kasa ya karasa jikin gate ɗin su ya fara knocking mai gadi ya buɗe kofar yana kare masa kallo yace "daga ina?, kuma wa kake nema" kallo ɗaya ya masa ya ɗauke kai yace "Leena na kawo" gatekeeper ya sake baki dan mamaki toh ai wannan ba mijin ta bane, toh me kuma alakar sa da Leena da har zai kawo ta gida, Malik ya bar mai gadi da tunanin da yake yi ganin yayi shiru ya karasa har inda Leena ke duke ya durkusa yace "zaki iya tashi kuwa?" Hawaye na sauka idon ta tace "A'a ba zan iya ba" ya karasa bakin gate ɗin yace ko zaka ma wata magana a 'yan uwan ta?" Mai gadi ya fara kare masa kallo sai kuma ya fito ya karasa jikin bicycle ɗin ganin Leena ya mike da sauri yace "toh..toh.. barin musu magana" daga haka ya karasa cikin gidan a kofar su Leena ya fara doka sallama, mai aikin Mummy data fito daga kitchen ɗin dake compound ɗin ta tsaya kallon mai gadin da mamaki, ko kallo bata ishe sa ba dan haka ko ta kanta bai sake bi ba, Anty Binta ce ta fito tace "kai malam lafiya zaka daga mutane a bacci?" yayi kasa da muryan sa yace "Kiyi hakuri, wani ne ya kawo Hajiya Leena kuma kamar ba zata iya tafiya bane yasa yace nazo na sanar da ku ko zaku shigo da .." ina Anty Binta ta katse shi "ban gane ba? Ina ita Leena take kuma" yace "Tana waje" muryan Ammi taji daga bayan ta tace "Leena kuma?" Ina har anty Binta ta fita tace "muje" tama manta cewa sleepwear ne a jikin ta har waje ta fita kallon Malik ta tsaya yi sai kuma da sauri ta duka tana kallon Leena ta kyar ta iya taimaka mata har ta tashi, Malik ya bi su da kallo har suka shiga cikin gidan anan parlorn anty Binta ta zaunar da ita, tashin hankali ƙarara rubuce a fuskan Ammi tana kallon ta tace "Leena lafiya?" tana sheshsheka tace "Ya sake ni ne?" Ba Ammi ba hatta anty Binta bata taɓa jin wani abu da lokaci guda ya buga zuciyar ta ba, ta durkusa hawaye har sun fara sintiri a fuskan ta zata yi magana Leena ta sa musu wani ihu saboda wani azabebben ciwon baya da bata taɓa jin irin saba, Anty Binta ta mike da sauri tace barin kira driver kawai yayi asibiti da mu, Ammi na rike da Leena tana tofa mata addu'a har anty Binta ta dawo dakyar suka iya daga ta suka kaita motar, har suka isa asibiti Ammi na mata addu'a. Da safe Ayaan ya farka bai ga Ammi ba ya duba dakin Leena inda Anty Binta ta sauka nan ma bai ganta ba, ya wuce kitchen still bai ganta ba, kawai ya fara sheshshekan kukan, ya wuce part ɗin Hajiya lokacin tana zaune tana lazimi ya shiga, ta daga kai tana kallon sa tace "me kuma?" ya karasa ya zauna a gaban ta yace "ina Ammi na?" Hajiya ta tsaya kallon sa tace "Ammi ka kuma?" yace "bata nan, ban ganta ba" simbil Hajiya ta mike tace "kamar ya baka ganta ba?" ya buɗe mata hannayen sa alamar bai sani ba Hajiya tace "Toh ita Kanwar Ammin naka fah?" yace "ai duk bangan su ba" Hajiya tayi shiru tana tunani, nan take taji gabanta ya fadi, toh ko dai kurciya da aka ce ana shirin ma Ammi ne har ya afku, kawai Ayaan ya bar sashin Hajiya ganin waje daya take kallo ya kama hanyar sashin su tun bai kai ga karasa part ɗin nasu ba yaga Ammi da gudu yaje ya rungume ta, saboda tashin hankalin da take ciki ko magana ta kasa masa sai ma rike hannun sa da tayi suna tafiya ciki, da sauri ta kunna water heater, ta wuce kitchen dan daura breakfast, ta fito da niyyar shiga ta haɗa masa ruwan wanka taji sallamar Hajiya ta amsa ta tsaya ta jira ta har ta karasa cikin parlorn, Hajiya tace "Ayaan dazu ya bar gidan na wai baki nan babu ita Binta ma" Ammi da damuwa ya cika ta ta zauna tana kallon Hajiya tace "Eh, ban dade da dawowa gida ba" Hajiya ta gwalo ido tace "Allah sa lafiya?" Ammi tace "Eh toh, Leena dai muka kai ta asibiti tun cikin dare amma har yanzu shiru" Hajiya tace "Ayyah toh Allah ya sauke ta lafiya" Ammi ta amsa da Amin Hajiya ta mike tace "barin je na shirya ai ta zama bai kama ni ba sai idan yaso mu koma asibitin táre" Amin tace "toh", kafin karfe 8 har sun koma asibitin, bayan sun shiga ward ɗin da suke Anty Binta ta nufo su da sauri tace "Ammi kina ji fah, wai ba zasu bari ta haihu da kanta ba saboda za'a iya rasa ta da kuma abinda zata haifa, so aiki za'a mata" Hajiya ta sake jakkan hannun ta Ammi ta ajiye basket in ba shiri tace "Toh suyi mana, su mata CD din mana" Anty Binta tace "Ai sai mijin ta yasa hannu" Hajiya tace "toh ana maganar rasa rai shi mijin nata ba zai sa hannu bane har sai mun rasa ta? Ko bashi da imaani ne?" a hankali Ammi tace "ai ya rabu da ita, jiya ya sake ta" Hajiya ta dinga maimaita Salati. Tun kafin Mami ta fita aiki sai ga Sultan da matar sa Jiddah, ga mamakin su Mami ko shirin aiki bata yi ba tana zaune, ko breakfast ɗin ta kasa yi, bayan sun gaisa tace "kun yi waya da Sadeeq din ne? Sultan yayi kasa da murya yace "Mami ai Sadeeq baya gidan sa, yanzu ma kafin mu taho nan sai da muka koma can gidan na su Jiddah har bedroom ɗinta ta duba ita ma Leenan bata nan?" Mami with shock take kallon sa sai kuma ta kalli Jiddah tace "ban gane me kuke nufi ba?" Sultan ya shafa kansa yace "Mami dan Allah ki kwantar da hankalin ki, nothing will happen in shaa Allah" Mami na kallon sa tace "kana nufin na kwantar da hankali na bayan bamu san whereabouts ɗin su ba? How Please?" Yayi shiru Jiddah tace "Mami koma ina suka je ai tunda matar sa ce it's okay, dole zasu dawo gida" Mami ta mata tsawa tace "Dama ke hankali gare ki? Me kika sani a rayuwa ma tukun? Duk kuna ganin yadda ya koma, damuwa ta yarinyar da tsohon ciki amma kice ai matar sa ce, naga da cikin ma bai daina harming dinta ba" taja dogon tsaki ta mike dakin ta ta wuce ta dauki hijab ɗinta ta fita ba tare da ta sake cewa wani acikin su kala ba, Jiddah ta sauke ajiyan zuciya tana kallon Sultan, ya shafa fuskar ta yace "Sorry, Mami dole ta damu, so ki daina kawo unnecessary things pls" Jiddah ta jinginar da
End Ads