take yi, Hajiya tana godewa Allah a ranta da tun farko bata taɓa nunawa Ammi wani hali ba, Granny tace "Ina Yariman yake?" Ammi ta sake fashewa da kuka ta ɗaga kai tana kallon Leena sai kuma ta cigaba tace "Wasu daga cikin labaran Mahaifana ne suka bani. Wata rana Abbah ya samu aiki sai aka kira sa interview wanda Leena ta dinga kuka tana cewa bata so ya tafi ya barta, shi kuma yana bata hakuri wai idan ya samu aikin zai mayar da ita makaranta mai tsada wnada da haka ya samu ya lallaɓa Leena muka raka sa har bakin kofa, bayan tafiyar Abbah ban taɓa shiga tashin hankalin da na shiga ba bayan wani number ya kira ni, ina ɗauka aka sanar da ni sun yi accident kuma ya rasu, na gigice ba kadan ba wanda a lokacin sai da Leena tayi dogon jinya duk da bawai lokacin tana da shekaru ba, a haka dai Mami ta cigaba da daukar nawin mu saboda Alhaji bayi da kuɗi lokacin, kwatsam wata rana aka wayi gari Alhaji ya bar duniyar wanda sai daya gigita mu gaba ɗaya, Mami ta shiga takaba akan idan ta gama zamu koma Niger tare da Iyaye na ita kuma zata koma Bauchi cikin 'yan-uwan ta saboda Allah bai taɓa bata haihuwa ba, a lokacin jira kawai muke ta gama idda mu koma inda muka fito sai wata rana ta aike ni office ɗin inda tayi aiki, na tafi da niyyar karɓan sako sai Allah ya haɗa ni da Baban Rayyan wanda a lokacin sai da ya biyo Ni yaga gidan mu, daga nan kuma ya dage aure na zaiyi wanda su Nyaama basu yarda ba saboda suna ganin taya zasu barni Ni kaɗai a Nigeria amma Mami ta nuna musu mace bata da gari sannan suka hakura, Haduwa na da Baban Rayyan bai ko kai wata 2 ba aka daura mana aure kuma ya cigaba da rike 'ya ta. Mami ta koma Bauchi su iyaye na kuma suka koma Niger.... Sannan ta ɗaga kai ta kalli Granny da itama tana kuka mai tsuma rai, gaba ɗaya parlorn duk jikin su yayi sanyi barin ma da Yarima bai sake haduwa da familyn sa ba har ya koma ga Allah. Kowa ya kasa cewa komai, Mai martaba ya yanke shirun na su yace "Yanzu ina iyayen naki suke?" Tana kallon sa tace "Suna Niger" yace "Mamin fah?" Tace "Tana Bauchi" yace "Ina so na haɗu da ita Mamin da kuma iyayen naki" Ammi ta gyaɗa kai, Granny ta rungume Leena da take kukan jin tarihin Mahaifin ta, Suhaif kuma ya riƙe Suhail, wanda Amira ma tana rike da shi, Mai martaba yana kallon su Umma yace "Mungode kwarai, Allah Ubangiji ya saka muku ya biya ku, dan mu kam bamu da abin da zamu biya ku sai dai tukuici" Umma tana kallon ɗanta dan bata taɓa tunanin haka historyn sa yake ba, Mai martaba yana kallon Daddy yace "Kwarai muna godiya dan kaima ka taimaka mana, Allah dai yabar zumunci" murmushi kawai Daddy yayi, Mai martaba yana kallon Suhaif yace "Suhaif kamar kace Suhail da matar sa aiki suka je nema a Abuja ka haɗu da su ko?" Kai ya gƴaɗa masa, Mai martaba yana kallon Malik yace "Ka zaɓi duk inda kake so kayi aiki sai na aika da bukatar a baka a can" Malik ya kasa cewa komai, ya mayar da kallon sa kan Leena yace "Ke kuma fah?" Ta girgiza masa kai da muryan ta da baya fita sosai dan kuka tace "Ban cigaba da karatu ba, amma dama ynx zan koma" ya gyaɗa mata kai yace "Toh ba zaki fara aiki ba, duk abin da kike so ba zaki rasa ba, yanzu makaranta zaki koma" ta gyaɗa masa kai, Hajiya tace "Mai martaba ga nan Mamar Leenan ma tun da tayi karatu babu aiki ko zaka haɗa da ita a sama mata" Daddy ya dinga kallon Hajiya haka ma Mummy, Mai martaba yace "Why not?" Sai kuma ya mayar da kallon sa ga Ammi yace "Me kika karanta?" Tace "Biochemistry" yace "Then, ki shirya in shaa Allah zaki fara aiki a NNPC" sai kuma ya kalli Hajiya yace "An bata kujerar Hajji guda biyu sannan an bata 20M" Hajiya tayi sujjada tana gode ma Allah, Mummy at this point zata iya cewa bata fahimtar komai, Mai martaba yace "ina so zamu biya Bauchi wajan Mami kafin mu koma palace" Granny tace "Leena zaki bi mu palace ko?" Ta sauke kanta kasa, tana kallon Suhail tace "Tare zamu tafi ko? Yan uwan ku su san da ku mana" ya kalli Umma sai kuma ya gagara cewa komai, Mai martaba yace "Sai a hankali kin san ba zasu sake jiki yanzu ba" Suhail yana masa murmushi yace "Na baka gida na na Maitama a Abuja tun kafin su Granny su mayar da ku 'yan Yola" duk sukayi dariya, Mai martaba ya miƙe yace "Kar a shiga sallahr Magrib muna nan" daga haka suka wuce duk suka fita, Hajiya ta wuce da su Granny da Amira dakin ta dan yin sallar, bayan ta bar su ta sake wuce parlorn Abbah wanda har sannan su Ammi suna zaune, Leena na gefen ta ga kuma Ayaan suna kewaye da Mamar su, ta kalli Mama dake zaune itama abin na bata mamaki, ga kuma Mummy kamar wanda aka ma dashe a wajan, Hajiya tace "Idan Ni na haifi Mijin ki toh zama ki yazo karshe a gidan nan, dan tun farko kike abin da kika ga dama na kyale ki, amma Yanzu abin naki yayi yawa" Mummy ko fahimtar ta ma bata yi, tana kallon Ammi tace "Ammi kuje kuyi sallah kafin su dawo ko?" Ammi ta miƙe tace "Toh Hajiya" Hajiya tayi gaba ko sake kallon Mummy ko Mama bata yi ba, bayan fitar su Mama ta ƙwashe da dariya tace "Sannu Khadija nasan yanzu kina bukatar akai ki asibiti ko?" sai kuma ta mike, Mummy ma tayi sauri ta miƙe tana kallon ta tace "Dan Allah ki tsaya ki faɗa min me zanyi yanzu kuma?" Mama ta harare ta tace "Kina jin duk wanda suka taɓa kulla makirci asirin su ya tonu, sannan duk an sallame su, shine yanzu kike so na sake ? Ai sai ke dai ɗin ne amma inaaa banda ni Fatuu" daga haka itama ta fita.
Share it Fisabilillah
#Jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*
Kafin Mai martaba da su Granny su tafi sai da suka cika gidan da abun arziki dan ba wanda bai samu abin arziki ba sai Mummy da taki fitowa ta musu sallama, Su Hajiya suka raka su jikin mota, Granny na rungume da Malik da Leena, Amira ma ta karasa ta rungume su ji take kamar za'a sake raba ta da ɗan ta, Amira tana kallon Malik cike da kauna tace "Suhail ina goben zaku zo ko?" Ya gƴaɗa mata kai yace "In Shaa Allah" Granny ta sakar musu murmushi tayi kissing hannun Leena da na Malik tace "Allah kawo mana ku lafiya, ka fin nan ma muma har mun dawo daga Niger ɗin tunda yanzu Yola zamu, kuma ba daɗewa zamu yi ba" Leena tace "Allah kai ku lafiya" Malik ma yace "Safe trip" tace "Amin" Suhaif ya sake rungume ɗan uwan sa yace "Can't wait to see you" daga haka duk suka shiga Mota, Daddy, Rayyan da kuma Malik suka raka su Airport, bayan sun sauka sun shiga cikin airport din, drivers ɗin su suka kama hanyar Yola, dama wasu kuma daga can Yolan sun kama hanyar Bauchi tun daren Jiya dan Mai martaba baya shiga bold ko kuma Motar da wata Masarautar zata aiko masa dan tun ba yanzu ba ya daina yarda da kowa daga Matar sa sai ɗan sa Abdallah, bayan tashin su su Daddy suka kama hanyar gida. Hajiya tace "Ikon Allah, Ni fah har sannan ina kallon abin nan kamar a mafarki ko kuma a Film, kalli yadda lokaci guda al'amura suka canza" Ammi tayi shiru tana kallon ta sai kuma tace "Hajiya Nima ban taɓa daukan haka abin yake ba duk da nasan cewa Abbah ba ɗan Mami bane dan lokacin ina da wayo aka tsince sa amma kuma nasan tabbas daga gidan masu hali ya fito" Hajiya tace "Ikon Allah, gaskiya a wannan zamanin samun kalan Mami da kuma su Umma ba da yawa ba kam, kalli yadda suka rike su cike da amana shiyasa Hausawa suka ce ɗa na kowa ne" Ammi tayi murmushi kawai sai kuma Hajiya ta kara magana tace "Kai har ma da iyayen ki na Nijar wallahi sun yi kokari, ace su ɗauki tsallaliyar budurwa kyakkyawa kamar ki su bawa wanda ba'a san assalin sa ba ai abin da mamaki" Ammi dai bata ce komai ba amma har sannan itama bata gama recovering daga shock ɗin da take ba but tasan tana ma Leena murnan haduwa da dangin mahaifinta sannan tana ma su Hajiya ma murna dan at least yanzu hankalin su zai kwanta tun da sunga jinin ɗan su duk da yanzu baya raye, Leena dai sai bin su take da idanu haka kawai take jin ta cikin wani peace sannan tasan auren Malik a gare ta alkhairi ne kuma haka Allah ya hukunta kila da tana gidan Sadeeq da bata kira Muhammad akan ya nema musu aiki ba balle har ta haɗu da Suhaif. A haka dai har su Daddy suka dawo gidan wanda har sannan yake avoiding eye contact da Malik dan yana ganin bai kyauta masa da bai nema masa aiki ba. Bayan sun shigo gidan suka wuce parlorn Daddy wanda har sannan su Hajiya suke ciki, Hajiya tana kallon su tace "Har jirgin nasu ya tashi kenan?" Daddy yace "Eh sun tashi" Hajiya ta kalli Malik ta kalli Leena tace "Ikon Allah, Ni wallahi sai yau naga kamar nasu, har ya ɓaci fah" Malik yayi murmushi Leena tace "Amma ai na fi shi kyau" Rayyan yace "Ta ina kenan?" Ta kalle sa sai kuma ta ɗauke kai tana turo baki, Malik ya miƙe tsaye sai kuma ya fita, Leena ta bi parlorn da kallo ganin ba mai kallon ta itama ta mike tabi bayan Malik, Hajiya ta rike haɓa tace "Ikon Allah, yaran yanzun ba kunya gare su ba, ji agaban mu zata bi mijin ta" Leena da har tayi bakin kofa ta ɓata rai ta juyo kamar zata yi kuka ta tsaya kallon Hajiya, Rayyan ya dinga dariya Daddy yace "Tafi abin ki, tsokanar ki take" Ammi tayi murmushi dan itama reaction din Leena ya bata kunya, daga haka Leena ta fita ba tare da ta sake bi ta kan Hajiya ba. A parlor ta same sa yana zaune, ta karasa ciki ta zauna gefen sa tace "I still can't believe this" ya Kalle ta yace "Nima, duk da yadda mutane ke magana but ban ɗauka abin har haka ba though since from day one nake jin ki kamar wani bangare na jiki na, kamar kece wall ɗina" tace "Alhamdulillah ina mana murna most especially kai dan Ni na san Abbah na sannan nasan Ammi, kai ne abin tausayi" ya girgiza mata kai yace "But yanzu zan gansu ai, but Abbah fah? Allah masa rahama" tace "Amin". Da yamma Hajiya ta doka sallama a kofar dakin su Leena, Leena ta fito tana gaishe ta tace "Toh sai ki faɗa wa ɗan uwan naki zamu je duba jikin ɗan ki tunda Kinga zaku tafi cikin dangin uban ku baku ma san rannan zuwan ku ba, dama akan zamu je duba sa sai ga Mai martaba da tawagar sa" Leena ta gƴaɗa kai, Hajiya tace "Ji wani iskanci kuma, har yanzu dai ba canzawa zaki yi ba, ki buɗa baki kice toh ne sai ki wani gyaɗa min kai?" Leena tayi dariya tace "Toh Hajiya naji, barin shirya" daga haka Hajiya ta wuce dakin Ammi dan faɗa mata sakon. Mummy sai zufa take yi, ta gama rasa yadda zata ɓullowa wannan al'amarin, Hajiya Amina tace "Ki fah kwantar da hankalin ki, komai zai tafi yadda kike so" Mummy tace "Wani kwantar da hankalin? Ai sai naga aikin nan ya kammalu zan kwantar da hankalina, Ni dai yanzu dan Allah ki samu kije min" Hajiya Amina tace "Toh amma da ta nikam yanzu ki hakura da kishiyar ki da 'yarta a fara gyara naki auren tunda har kince ga abin da Mahaifiyar sa tace akan ki" Mummy tace "Shikenan sai na zuba ido suna walwala?" Hajiya Amina tace "Kinga idan kina ga kamar ba kokari nake miki ba toh kije da kanki" da sauri Mummy tace "Toh shikenan naji, ko nawa ake bukata just let me know" a haka suka yi sallama ta share zufan goshin ta ta ajiye wayan ta tallabi chin dinta tana kallon waje daya, tasan Hajiya Fatima ne kaɗai zata iya tsaya mata a mata aiki na gaskiya kuma sannan komai ya warware yadda take so amma gashi yanzu sun sami misunderstanding wannan Hajiya Aminan kuma ta kaita wajan wasu amma aikin su bai kai na Hajiya Fatima ba dan sometimes asara ma kawai take dan bata ganin Result, ta sake share hawayen ta ta miƙe tana zaga dakin dan ganin me kuma zata sake yi yanzu. Layla ta riƙe haɓa tace "Kai Mama?" Mama tace "Karya zan miki kenan" Layla tace "Abin ne da mamaki gaskiya, chap ɗin" Mama tace "Wallahi fah" Layla tace "Ban faɗa miki tun farko ba Mama? Nace yadda Mummy ta dake sai Leena ta aure sa wallahi sai tayi nadama dan Ni kam wallahi tun farkon ganina da shi nasan cewa ba daga karamin gida ya fito ba" Mama tace "Ai baki ga idon shegiyar ba" Layla ta kwashe da dariya tace "Kaiii wallahi zan so naga Mummy, Allah sarki ashe shi da Leena cousins kenan?" Mama tace "Iko fah na Ubangiji kenan, gashi ya sake haɗa su waje guda, shiyasa wallahi mugunta be yi ba, ai labarin Leena da Malik ya taba min zuciya wallahi Ni kam na gama shiryuwa kuma ina gode Allah da bai ɗauki rai na ba ina bin bokaye da masu tsubbu" Layla tace "Dama Ni duk iskanci na ban yarda su'ke bayarwa ba" Mama tace "Toh gashi wanda suka kulla tun can da ma gashi asirin su ya tonu, balle kai da baka da wata gata dama" Layla tace "Allah kyauta, Amma kin sanar da Hajiya abubuwan da Mummy ta dinga aikatawa tun farkon auren Ammi?" Mama tace "A'a ban tona mata asiri ba, na kyale ta da halin ta" Layla tace "But why Mama? Kar ta cigaba da halin ta ne kuma, Kinga fah kince akwai sanda Daddy yafi shekara baya ko kallon Ammi" Mama tace "Kinga Layla, a labarin dangin Leena da naji na koya abubuwa da yawa, Ni ba zan tona mata asiri ba taje ita da Allah balle ma Hajiya ta rantse sai ta bar mata gidan ɗan ta, Kinsan ko gaishe da Hajiya fah bata yi sai ta shafe wata guda bata bi ta kan Hajiya ba balle ta gaishe ta" Layla ta gyaɗa kai tana mamakin Mummy. Hajiya ta fito rike da hannun Ayaan ba'a ɗau lokaci ba sai ga Ammi ta fito Leena na bayan ta a haka suka nufi gate, bayan sun shiga compound ɗin su Mami sai ga Nawaf da ya fito waje shan iska shi da Baban sa da gudu yayi kan Leena yace "Amma" Leena ta duka ya faɗa jikin ta tana dariya kamar yadda yake dariya tayi kissing ɗin sa ta ɗauke sa, Ammi tace "Baki da hankali ne zaki ɗaga sa sama ko baki san condition ɗin da kike ciki bane?" Leena taji kunya sai kuma ta sauke sa dan ita bata ɗauka Ammi ta san tana da ciki ba, Hajiya tace "Eh lallai yaro kam ya warke har hankalin mu ya tashi" Har sannan Leena na wasa da shi tana masa murmushi, Sadeeq ya karasa inda suke ya duka yana gaishe da su Hajiya, Leena ta Kalle sa tace "Ina wuni" yace "Lafiya kalau, ai ɗazu nake cewa za'a kawo miki shi hutu" Murmushi kawai tayi suka wuce ciki. Suna shiga parlorn Mami Leena ta Kalli Farida har da gudun ta ta wuce dakin Mami, Jiddah tayi dariya bayan sun gaisa, duk yadda Ammi taso karɓan Nawaf a hannun Leena ki yayi, Ammi ta dungura kansa tace "Naga Uwar taka ma bata wahala kamar yadda na wahala da kai ba" Leena dai sai dariya take yi, Hajiya tace "Ashe ya samu sauki, ai muka ce zaku jimu shiru bamu sake zuwa duban sa bane muka ce bari dai mu zo tunda Leena ma gobe zata yi tafiya" Mami tace "Ayyah wallahi babu komai, ai yaji sauki dama akan zai zo muku hutu ma" Hajiya tace "Ayyah, har mun shirya da zamu zo kwatsam sai ga Wani Manyya motoci sun shigo mana gida ashe daga faɗar Yola ne duk muka tsaya kallon ikon Allah dan mukam mun ɗauka ai wani rankafefen laifi muka aikata ashe wai Leena da mijin ta ɗan uwa ne sannan daga masarautar suke kai munga abin al'ajabi da mun daɗe bamu ga kamar sa ba" Ammi ta sake baki tana kallon Hajiya da Mamaki Leena tayi murmushi dama bata cire sammani daga Hajiya ba dan tasan saf sai kowa ya gama jin wannan labarin, Mami duk da bata gama fahimta ba tace "Ma Shaa Allah, na musu murna wlh" Leena tana kallon Jiddah da mamaki sai kuma tace "Lalle ma Farida" daga haka ta wuce dakin Mami da ta ga Faridan ta shiga ɗazu, ta buɗe kofar, Farida dake zaune bakin gado tana danna waya jin an buɗe kofar ɗakin yasa ta ɗaga kai ta kalli kofar ganin Leena ne ke tsaye yasa da sauri ta mike zata hanyar toilet Leena tayi sauri ta sha gaban ta tace "Sannu Farida" Farida ta sauke idon ta kasa ta gagara haɗa ido da ita Leena tace "Dan kin auri Sadeeq shine kike gudu na? Sai kace ina tare da Sadeeq din ne balle kice da kunya amma ace har aure na sake toh