x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - AGOLA free pages

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
Sultan yaki sai da Jiddah tayi masa magana, Rayyan ya kira Daddy a waya yace "Daddy kana part ɗin Hajiya har yanzu?" Daddy yace "Eh" yace "Toh gamu shigowa" daga haka ya katse kiran tare suka karasa cikin gidan jidda na rike da hannun Leena har suka karasa part ɗin Hajiya Rayyan yayi sallama ya shiga sai suma suka bisa Leena taje da gudu ta kama Hajiya daga Hajiya har Daddy kallon Leena suke baki buɗe Hajiya tace "ina nan ina tausaya miki daga zuwa zaki karya Ni Ko?" Leena ta fara dariya tayi missing Hajiya su Sultan suka gaishe su suka amsa da fara'ar su Daddy yana kallon Rayyan yace "Aina ka aka same ta?" Leena ta bar jikin Hajiya taje ta zauna a kusa da ƙafan Daddy tana kallon sa tace "Good morning, daddy" ya amsa yana shafa kanta Rayyan yace "fitan da nayi anan zanje school ɗin su ne to confirm ko an ganta sai kuma tun kafin na karasa fitar da motar naga waɗannan sun dawo da ita" Daddy yace "Alhamdulillah" sai ya mayar da kallon sa kan Sultan yana son karin bayani Sultan ya ɗan sosa kai sai ya fara narrating abunda ya faru Hajiya ta katse sa tace "shine bayin Allah baku dawo da ita tun jiya ba? Kasan yadda muka damu kuwa? Ni har yanzu na kasa cin abinci, cikin dare ma kuwa haka na kasa bacci raya daren nayi ina sallah ina rokon Allah ya bayyana ta" da sauri yace "Toh ai da magrib muka same ta, and bata san unguwar su ba tace mana so muka shiga da ita gidan mu gudun kar mu barta kuma ta faɗa hannun wanda bana gari ba, akan da safe zamu kaita Makarantar ta su acan nasan zasu bamu address ɗinku, sai kuma ashe unguwar mu ɗaya mun fito da niyyar kaita Makarantar kawai tace mana ga can gidan su, so mu muna Street C ne while ku kuna E ai da tun jiya mun dawo da ita, Mama" Daddy ya gyaɗa kai yace "kwarai kuwa kun mana halaccin da kun barta da kila ta faɗa hannun ba na gari ba, babu abunda zamu ce muku sai dai Allah ya biya ku" suka ce zasu tafi Hajiya tace "A'a daga zuwa kuma, A'a dai ku tsaya muyi karin kumollo sai ku tafi kunji" da kyar suka yi convincing Hajiya har ta bar su akan zasu tafi duk suka tashi zasu raka su, anan compound suka haɗu da Mummy da ta fito zata part ɗin Daddy Nisreen da Niswa kuma suna biye a bayan ta Mummy kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kai, Hajiya tace "ke kuma baki gan mu bane" sai sannan ta juya tace "ina kwana, Hajiya" daga haka ta juya ta koma part ɗin ta kallon daya Daddy ya mata ya ɗauke kansa, ya kama hannu Leena yana kallon su Sultan yace "ku ɗan jira Ni anan" daga haka ya wuce part ɗinsa Leena tace "Daddy they're so Nice" Daddy yace "Sure! Dear" tace "Daddy yaushe ne Ammi na zata zo?" yace "surprise zata Miki" daga haka ya wuce bedroom ɗin sa sai gashi ya fito da thousand notes guda biyu yasa a Black leda suka fito ya karasa inda suke ya mika musu duk suka ki karɓa dakyar dai da Daddy ya nuna musu bacin ran sa tukun suka karba Hajiya tace "ai yaba kyauta tukuici, Toh ai ba laifi bane dan kun karba" sukayi godiya Rayyan na kallon Sultan yace "ashe muna kusa ma kenan?" Sultan yace "Eh fah, ai duk rashin sani ne da tun jiya mu ka kawo ta" Jiddah tace "street biyu ne a sakanin mu" Rayyan na kallon ta yace "haka fah" Leena na kallon jidda tace "zanyi missing ɗin ki Anty jidda" jidda tace "Nima dear, amma kinyi min Alkawarin zaki na zuwa min weekend ai" Leena tace "Eh ai zan fada ma Ammi na" sai kuma ta ɗaga kai da sauri tana kallon ta tace "dan Allah ki tura videos Dina na wayan wanca uncle ɗin da baya dariya zuwa wayan ki kar ya goge please" tana murmushi tace "toh" daga haka suka fita Leena na ɗaga musu hannun su ka juya zasu koma cikin gidan suka ga Nisreen da Niswa suna fitowa daga part ɗin Daddy Leena ta kama hannun sa tace "yaya ba zasu jira Ni na shirya ba, kuma kila anyi important abu bana nan" yace "let them go, ni zan kaiki da kaina sai muje nayi maganar test ɗin can da kikayi missing" tace "Toh" Nisreen da Niswa suka gaishe sa daga nan suka wuce parking space shi kuma yace "Leena je ki shirya, idan kin gama kije wajan Hajiya kiyi breakfast sai ki jirani a parlorn ta idan na gama zan zo na kira ki" tace "Toh Ya Rain" daga haka ta wuce "shi kuma ya wuce part ɗin su ya shiga da sallama ya samu Mummy na breakfast ya ja kujerar dake gefen nata ya zauna ya ɗaura kansa a shoulder ɗinta yace "Mummy fushi kike da ni?" taki tanka masa yace "Haba Mummy, dan Allah kiyi hakuri wallahi Daddy ne yasa ni akan lamarin Toh Kinga ba zance masa A'a ba" tace "ba za kayi breakfast ɗin bane?" yace "A'a bani da apatite ne" zai tashi tace masa "Me ke damun ka? Ko dai har yanzu zazzaɓi shekaran jiyan ne?" Kai kawai ya gyaɗa mata sai ya mike yace "barin ɗan kwanta Mummy" tace "kasha magani ne toh?" yace "yanzu zan sha, Mummy yanzu zaki tafi aiki ne?" tace "Eh yanzu zan tafi" yace "Toh, sai kin dawo bari na ɗan kwanta" tace "kasha maganin dai, ba dole zazzaɓin yaki sauka ba ka tashi kaje kakai wajan 12 na dare a station da sassafe ka kuma tashi kuma jiya duk a zirga-zirga ka kare, sai kace wacca kanwar uwar ka ne ta ɓata" da sauri Rayyan yayi ɗakin sa dama da gangan yayi haka dan ya san idan har ba haka yayi ba toh yau sai yadda Allah yayi dan ya san Mummy baki ne kawai ba zata masa ba gashi yama Leena alkawarin zai kaita Makarantar kuma yasan ba zata basa dama ba bayan ya shiga ɗakin sa yana zaune yana duba abu a waya yana jin footsteps ɗin Mummy yayi saurin kwanciya ya rufu da duvet Mummy ta buɗe ɗakin nashi ta shiga taɓa jikin sa tayi sai ya buɗe idon sa yana kallon ta tace "kana doctor kana zama da yunwa da kin shan magani taya Zaka ji sauki, ka tashi ka nema abunda za ka ci sai kasha magani idan kasha sai kayi bacci zaka huta kaima" yace "Toh" tace "ko me aiki ka sata ta dafa maka abunda zaka iya ci" yace "in shaa Allah Mummy, Allah tsare sai kin dawo" tace "thank you" daga haka ta fice kallon agogon sa yayi yaga 8am saura yana hoping ta tafi yanzu saboda kar Leena tayi latti, ya sauka ya wuce dining ganin me aka bar masa. Hajiya tace "Ni wallahi Leena gwara uwarki tayi ta zo Ni gaskiya ba zan iya ba yarinya sai manyan cen banza wai bata cin abinci ba nama bata karin kumollo sai da kwai bata cin wancan sai da wancan" Leena ta turo baki taki ce mata komai tace "Toh ba zaki ɗauka ki ci bane kina kallon na?" Rayyan ne yayi sallama Leena ta tashi da sauri yana kallon Hajiya yace "Toh Hajiya barin kaita Makarantar sai na wuce aiki" Hajiya tace "bari kaji wai dan na bata ganda ba me yawa ba shine tayi fushi nace tasha tea din kuma tace wai ita sai da kwai yarinya kamar ƴar gold wallahi Uwarki bata baki tarbiyya ba" Rayyan yace "Hajiya toh tunda Allah yasa akwai ai sai aci tunda dan aci ɗinne ake siyowa" Hajiya tace "Eh lalle ai kuwa mantuwa nayi nake baka labari dama can bakin ku a haɗe yake ai, Toh kai ka sani Ni ba ruwa na" yace "Hajiya kiyi hakuri kar tayi latti mun tafi" daga haka ya kama hannun Leena suka fita sai daya tada motar yace "Leena me yasa kike zuciya da abinci yanzu haka zaki wuni without breakfast" tace "Ya Rain Hajiya fah zallan ruwan naman tasa min wai ko yanka daya ba zata ban ba shine tace zata ban tea and bread nace harda egg tace toh ta fasa hada min" yace it's okay" a hanya ya tsaya a wani restaurant ya siya mata chips and egg ya karbo mata a takeaway har cikin makarantar ya shiga da Leena tunawa yayi da Nisreen ajin su ɗaya da Leena yasa ya tsaya a bakin gate gudun kar ta gansa ta bawa Mummy labari tace ashe playing ɗinta yake yi, wani malami ne ya shigo da sauri ya tare sa suka gaisa yace ɗan Allah yayi ma Head of JSS 1 magana mana malamin yace "In Shaa Allah" daga haka ya wuce sai can gashi ya fito a wani office yana nufo su tun daga nesa ke murmushi dama Rayyan ya saba musu kyauta idan yazo school ɗin, bayanin komai ya masa yace yana so duk wani abu da Leena tayi missing a mata makeup as usual ya masa kyauta malamin ya karɓa yana ta godiya yana kallon Leena yace "Let's go, little girl?" Daga haka Rayyan ya wuce aiki. Da yamma Daddy yana ɗakin Hajiya dake ta masa mitan Leena bata cin kaza sai da kaza Daddy yayi murmushi yace "Hajiya idan akwai kawai kina mata idan ya kare kina min magana zanna tsiyowa tunda yarinya ce" Hajiya ta yi ƙwafa tace "Toh ai Ni ba rowa nake ma yarinyar ba dama matar kace idan zata samun abinci sai ta zuɓa dayawa amma idan abun daɗi ne tasa kaɗan Ni kuma kaga na tsufa gwamna ita yarinya ce zata iya cin komai amma Ni ba zan iya ba, kuma dama tun da uwar yarinyar ta tafi aka dena bata abinci a gidan nan dama idan aka bani sai na rage mata kaga ai ba rowa nake mata ma" Daddy yayi shiru yana mamakin hali irin na Khadija yace "Toh Hajiya ina ga kawai za'a na kawo Miki duk wani abu da zaki bukata nan idan ya so abinci kawai zasu ke zuba Miki idan be Miki ba kuma shikenan sai ki dafa naki da ban, ina ga za'a nemo me Miki girki kawai" da sauri tace "A'a Ni kam, kawai ka tsiyo ka zuba min a nawa kitchen din amma banda me girki ɗin" yace "Toh shikenan" Leena ce ta shigo da sallama da uniform din Islamiyya a jikin ta gashe da Daddy tayi ya amsa ta fara'ar sa yace "yauwa zo nan dear" ta karasa kusa da shi tace "gani Daddy" yace "daga yau duk ranan da aka hanaki zuwa school karki kuskura ki sake cewa zaki da kafa, ki zo ki faɗa min ko ki samu Hajiya, kinji Ni Ko?" ta gyaɗa masa kai yace "islamiyya zaki?" tace "Eh" yanzu jirgin su Ammin ki zai sauka ita zanje ɗauko wa a airport zamu je tare?"da sauri ta ɗaga kai sai kuma tasa sallar tace "Yes, Daddy, na fasa zuwa islamiyyan dama revision ake mana" yace "Toh je ki canza kaya" da gudu ta wuce part ɗin su ta cire uniform ɗin jikin ta ta wuce toilet sabon wanka ta sake yi ta ciro wani sabon kayan ta tasa ta fito a compound taga Abba na waya ta wuce wajan sa da gudu ta kama hannun sa yana gama waya sai ga Rayyan ya shigo yana parking Daddy na shiga nasa motar ya fito yana kallon Daddy yace "Daddy har Anty ta karaso ne?" yace "kunyi waya ne?" Leena ya nuna masa yace "Daddy ai yadda Leena taci kwalliya bakin tan nan yaki rufuwa Toh nasan Ammi za'a je ɗauko wa" yana murmushi yace "sure! Airport ɗin zamu" yace "Toh kawo nayi driving ɗin mana" yace "No Rayyan, kana bukatar rest just go and have rest" daga haka Abbah yaja motar suka fita...

Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧

Chapter 6


Suna cikin tafiya duk sunyi shiru Leena pouted, "Daddy , why did I even come to pick Mummy up? She didn't even tell me she was going and she didn't care to know how I was doing?" Daddy yayi murmushi while driving yace "Sorry dear, she used to call me and ask me how you're doing, but mostly I'm in the office and you're in school too, so Kinga laifi nane da bana isar miki" ta girgiza kai tana kallon bishiyoyin kan hanya can tace "Daddy! But what about her traveling without telling me baka ce komai a kai ba? At least she should have told me. I was really upset when I found out, I even cried" yace "Leena rasuwa aka yi shiyasa kuma su Mamin ki zasu tafi a ranan bayan wannan jirgin ne kawai available bayan shi sai na washe gari so nace tabi wannan din su tafi tare da su Mami kawai" ta gyaɗa kai kawai har suka karasa airport ba wanda ya sake cewa komai
As Sirbajo emerged from the arrivals area, she spotted her loved ones waiting for her. Her love of her life Leena's face lit up with a bright smile, and the little girl exclaimed, "Ammiiiii!" before rushing towards her Ammi. Sirbajo ta ɗurku sa opened her arms, and Leena launched herself into a tight hug, hawaye ne taji suna sauka a fuskar ta Ammin ma taji kamar hawayen nason saukowa amma sai ta rike Leena ta ciro fuskar ta ajikin Ammi tana kallon idon Ammin tace "I'm so happy to see you, Ammi!" holding her mother back tightly. Daddy smiled, watching the reunion. Shima ya karasa yace "Welcome home, Sirbajo," he said, his voice filled with warmth. Leena let go of her mother and stepped aside as Daddy wrapped his arms around Sirbajo, holding her close. Ammi ta fara kalle kalle ganin ba wanda yake kallon su ta ga kowa ta kansa ya ke hakan yasa ta ɗan sake jiki Daddy yayi murmushi ganin reaction ɗinta yace "I really miss you, dear. Welcome back, my peace of mind" Murmushi tayi tace "thank you, yaya na" daga haka suka kama hanyar inda motar Daddy yake, suka kama hanyar Gida Leena sai bawa Ammin labarin take Daddy yana addu'an kar ta bata labarin ɓatan ta ga Leena kuma idan kace mata karki faɗa kaza ma wane Toh ita kuma nan kake jawo hankalin ta sai ta faɗa kawai dai yana hoping Allah ya mantar da ita ko da zata faɗa ya kasan ce not now. Kusan tare motar Daddy da na Mummy suka kusa kan su cikin layin yau ma, Daddy ne ya fara shiga da motar yayi parking Ammi na sauka mai gadi da drivern yara suka zo kara ma Ammi ta'aziyya Mummy na parking ko kallon idan su Ammi su ke ba tayi ba tayi wucewar ta ciki, Daddy ya bita da kallon, da kansa ya dauki jakkar Mummy ya wuce da shi su kuma suna biye da shi a baya a bedroom ɗinta ya ajiye ita kuma nan sofan dake parlorn ta zauna Daddy ya fito nan suka sake sabon gaisawa yana sake mata ta'aziyya kallon Leena tayi tana murmushi tace "Me haka kuma Leena?" tace "ai Ammi na manta ne na miki oyoyo a airport" Ammi tace "na san kina fushi da ni Toh kiyi hakuri, kuma naga ai ga Hajiya kuma Ya Rayyan yana nan" taki kallon direction din Ammi ita sai yanzu ma take jin zafin abinda Ammi ta mata because she never expect, Ammi ta mike tana kallon Daddy tace "barin watsa ruwa sai na chanza kaya" tana kallon Leena sai kuma ta ja mata kumatu tace "shikenan zan koma gidan mu ai idan kika ci-gaba da fushin" tana gama faɗar haka ta wuce ciki, kallon ɗakin tayi ɗan 3 days da tayi bata nan kalli wajan har ya soma kura dole ita zata gyara kafin mai aiki su zo gobe. Ana idar da Magrib Daddy direct part ɗin Ammi ya wuce da sallama ya shiga Leena na zaune tana rubutun da ta saba yace "Leena kinyi sallah kuwa?" ta girgiza masa kai yace "Toh tashi kije kiyi idan kika fito sai ki ci gaba" ta gyada masa kai sannan ta wuce ɗakin ta, Zama yayi akan sofa ya ɗauki littafin Leena yana ganin Abunda take rubuta wa mamakin yadda rubutun Leena yake da kyau yake yi ga ilimi sannan ga baiwa Ammi ne ta fito a ɗakin ta ta tsaya bakin kofar tana kallon sa tace "ya ka tsaya a can kuma" yace "Naga ba hakura zakiyi da share share da kike yi bane, ki bari gobe masu aiki su gyara miki sai ki kwana a part ɗina ba sai kin wahalar min da kanki ba" Ammi ta ɗauke kanta tace "ai harna gama ma kuwa" daga haka ta karaso cikin parlorn tana kallon sa tace "me wannan kuma?" yace "talent ɗin Leena nake karantawa" Sallama akayi Ammi ta ɗaga kanta tana kallon kofar ta amsa tace "Shigo mana ya Rayyan" karaso wa cikin parlorn yayi zai zauna a kasa tace "haba ya Rayyan dan Allah karka zauna a kasa na sha faɗa maka haka" Murmushi yayi ya gaida ta ya kara mata ta'aziyya sannan ya kalli Daddy yace "Sannu da zuwa Daddy" Daddy yace "yauwa, amma ba anan kayi magrib ba ko?" ya gyaɗa masa kai yace "eh a hanya nayi" Leena ta fito da gudu "Ammi tace "Amma Leena ban hanaki wannan gudun ba ko?" tace "toh Ammi ai kar ya Rain ya tafi ne" ta maida dubanta kansa tace "Ya Rain na rubuta wani abu ina zaka ban wayan ka nayi video ko?" ya gƴada mata kai ta kuma cewa kasan me za ayi inter school debate kuma an sani" yace "Ma Shaa Allah, dear. Haka nake son ji kullum " ta gyada masa kai sai kuma ta juya tana kallon Daddy tace "Daddy ina kace idan
End Ads