x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 43 - AGOLA free pages

  • 126001 words
  • 129000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
Zanje ba, nace ba zan je ba ko? Ko zaki sani dole ne?" ta mike tace "Kiyi hakuri Hajiya duk abin bai kai nan ba" daga haka ta bar Hajiya a dakin ta dan yanzu kallon Hajiya ta gama tsufa take abu kaɗan sai ta har zuka. Ganin lokacin yayi har an fara fita yasa Mummy kiran Layla, Layla da bacci yayi daɗi tasa kiran a silent ta cigaba da baccin ta, Hajiya Fatima tana kallon Mummy tace "Ki kuma kiran ta karfa tasa mu makkara a fara taro bamu" Mummy tace "Ai ina ga sun shanye ta ne, nace miki fa ɗazu kafin ki zo da ido na naga tana shiga parlorn na su wlh" Hajiya Fatima tayi tsuka tace "Dan Allah mu tafi ita taji wajan idan bata zo ba" daga haka Mummy ta saka wayar ta a ɗan karamin fos ɗin hannun ta me shegen kyau, ba karamin kyau ta sha ba, kana ganin ta kaga uwar Amarya. kukan da Babyn Leena ya fara yasa ta farkawa da sauri ta jawo sa jikin ta tana dan girgiza sa dan ya koma baccin da yake yi, ganin ba komawa zai yi ba kawai ta tashi itama ɗaukan sa tayi ta fara feeding dinsa kallon agogo da ke nuni da karfe huɗu tayi sai kuma ta juya tana kallon Layla da mamaki sai dai kuma bata ce komai ba, Ammi ce ta leko tace "Aah dama bacci Laylan ke yi?" Leena ta gyada mata kai Ammi tace "Ai da kin tashe ta" daga haka ta tashi Layla, bayan ta farka Ammi tace "Layla karfe 4 fa yayi naga kuma tun dazu kuma mutanan gidan ke tafiya fa" Layla ta murja idanun ta tace "Toh Ammi yanzu zan shirya" daga haka Ammi ta bar bakin kofar, ta jawo wayan ta tana kallon missed call ɗin Mummy da Maman ta sai kuma wannan numbern mutumin da ya kira ta ranan, ɗan Satan kallon Leena tayi ganin ba direction ɗin ta take kallo ba yasa ta sauke ajiyan zuciya ta kashe wayan baki daya dan bata bukatar ya sake kiran ta yanzu, tace "ya tashi ne?" Leena tace "Eh fah, ban jima da kwanciyar ba fa amma Kinga ya tashe Ni" tayi murmushi tace "me ku ke ce masa?" Leena tace "Babu" Layla ta mike tsaye tace "Haba ke kuwa, sai kace You're not famous, ai kamata yayi ace a waye kike dan Allah sa masa nickname me daɗi" Leena Murmushi kawai tayi ba tare da ta ce mata komai ba, kayan jikin ta take cirewa da niyyar shiga wanka tace "Toh ke ba zaki bane?" Leena tace "ba fa muyi 40days ba fa" ta gyada mata kai tace "Wallahi na manta ne" sai kuma ta ja tsaki tace "yanzu sai ya zama magana idan mutun bai yi attending ba, beside bana son Rayyan yaji ba daɗi ne amma da ta sune wallahi ba Zanje bikin shegiyar nan ba" Leena bata ce mata komai ba har ta gama cire kayan cikin ta ta wuce toilet. Sai bayan Magrib suka gama kamun su, kowa sai san Barka yake dan biki kam an yi shi bana kananun mutane ba, duk suka dawo gida lilis, Mummy kam bragging din da take zaka ɗauka su suka kashe wannan uban kuɗaɗen, ta faɗa ta maimaita Yadda aka bada kudin buɗan kai 20mil. Niswa da few friends ɗinta suna zaune duk suma sun gaji barin ma Niswa, wata friend dinta tace "Kai Niswa ai na kika samu miji irin wannan?" yar dariya tayi tace "God sent am" duk dariya sukayi, wata tace "gist us please" tace "toh nace me kuma? Nima da farko wallahi na ɗauka yaudara ta zaiyi shiyasa ko faɗa banyi ba" wata tace "amma suna da Bala'in kuɗi, ko da yake Prince ne ai" Niswa tace "Hmm Kinga yadda yake spending min? Toh da farko har na fara tsoron kudin sa amma tun da suka zo gaisuwa anan aka san wanene shi, ke most of the furnitures ɗin na a jikin shi na cire" duk suna mamakin yadda suka gansa da kuma familyn sa dan kallon farko zaka san cewa kudi ya zauna musu, dan ba sai sun yi bayani ba, wata friend dinta da tun ɗazu bata sa baki ba a maganar na su ita ce tace "Wallahi ban so ace yau Friday bane, dama Jiya akayi Event ɗin nan da yanzu mun caske kudin mu a hannu, 20mil? ai ba wasa ba" nan suka fara hauka suna dariya. Yau da ya kasance ranan daura aure, tun asuba Niswa ke waya da mijin ta Ashraft, kallon karfe bakwai yayi tace "kasan yanzu zan fara zuwa gida daga can sai na wuce wajan makeup ɗin, kai kuma daga daura auren sai ka zo idan mun gama hotuna sai na tafi gida tunda kasan dole acan za'a dauke ni" yace "Uhm baby, yanzu dai in barki kenan?" tayi murmushi tace "ka ga makeup na ɗaukan lokacin" yace "Okay, sai munyi waya" daga haka ta kashe tana kallon friend dinta da ta sata a gaba tana harararta tace "ke Malama ai na gama wayan yanzu ko?" tace "Ke kika sani, Kinsan yana da kyau ace duk abinda zaki yi kiyi da wuri saboda karfe biyu suka ce jirgin naku zai tashi ko?" Niswa ta mike tace haka ne fa, brush din ta da ta sa masa toothpaste ta ɗauka ta wuce toilet. Ganin part ɗin Ammi ba kowa hakan yasa Daddy anan yayi breakfast dinsa ya dauki babban riga da ya musu anko shida Ayaan yace "Madam dan Allah ki shirya Ayaan cikin kayan nan" Ammi tace "Toh shikenan" daga haka ya fita zuwa nasa bangaren dan shirya wa. Manyan kuloli da aka gama hada hadaddiyar breakfast wa dangin miji Niswa Mummy ta fito tasa driver ya kwashe su tana fada masa idan ya isa hotel ɗin da suka sauka ya kira drivern su ya fito ya kai musu breakfast din, daga haka ya wuce. Dakyar Rayyan ya samu ya lallaɓa Layla ta yarda zata gidan Mummy, sai narke masa take yi wai bata da lafiya, kasan marar ta na damun ta, bayan yayi parking tare suka sauka, har part din Ammi, bayan yayi sallama Ammi tace Su shigo, bayan sun gaisa Ammi na kallon Layla tace "baki jin dadi ne?" ta girgiza mata kai tace "Kawai dai ciki na ne ke ɗan ciwo" Ammi tace "Allah ya sauwake" Rayyan yace "Ammi zan samu breakfast?" Ammi tace "kadan ne wanda ya rage, shima sauran na Daddyn ku ne bari Binta ta daura maka" yace "No, na Daddyn ma is Okay zan haɗa da tea" dan yanzu ya daina cin duk wani da ya fito daga sashin su, dan Hajiya ta hana sa ga kuma Layla ma, Leena ce ta fito sanye da Hijab tana rike da Babyn ta ya mike ya karasa har inda take ya karbi Babyn ya koma ya zauna yana ma Babyn wasa, Leena tace "Yaya ina kwana" ya daga kai yana kallon ta sai dai bai amsa ba Layla tace "gaishe ka fa take yi" a takaice yace mata "Na sani" Leena ta kura masa ido ya kalle ta yace "Kina kuka kenan har yanzu?" ta girgiza masa kai yace "Toh tunanin me kike yi?" ta ɗan kalle sa sai kuma ta ɗauke kanta tace "Babu fa" yace "kamar yaya zaki ce min babu gashi kin wani rame" Ammi da ta gama hada masa tea a dinning area tace "Ahtoh kai ma ka tambaye ta" tayi shiru tana wasa da fingers ɗinta Layla ta mike ta wuce dakin Leena dan ita yanzu ba kanta zasu gane ba, Ammi tace kaje ka karya Rayyan" ta karbi dan hannun nasa tana cewa "Wallahi Ni da Binta ba irin bakin da bamu ba ma yarinyar nan daga karshe hakura mukayi" yace "we need to talk Leena, bari a gama taron nan" daga haka ya karasa dinning ita kuma ta wuce dakin ta, tana kallon Layla data kwata a kasa tace "ga gado amma sai kiyi ta kwanciya a kasa?" Layla tace "Kinga wallahi kasan yafi min daɗi ne, beside ga ciwon cikin da ya sani a gaba". Yadda Mummy tayi Bala'in kyau tasha gwalagwala kaɗai ya isa ya nuna maka cewa Uwar amarya ce wannan, Hajiya Fatima ba ba'a barta a baya ba, Yadda Nisreen tayi kyau itama sai ka ɗauka amarya ce. A bangaren amarya Niswa kuwa yadda tayi kyau tana stunning ba sai an fada maka wacece ita ba, kuma kasan ba karamin gida zata shiga ba, dan kaya mai bala'in tsada ta saka, harta makeup artist din sai kallon Niswa take yi tana 'Awww' Friends dinta sai daukan ta hoto suke tun kafin ango da photographer su iso, tsadaddan motar da ango da ya bayar dan yawo da ita yana parke a bakin kofar makeup shop din, tafiya take kamar ba zata taka kasa ba, a haka suka bar shagon, drivern da gudu ya karasa ya buɗe mata motar ta shiga friends dinta ma duk shigan suka yi, be tsaya ko ina ba sai kofar gidan su, kowa ya sake baki sai kwallon ta yake yadda ita kadai sai wani sheki na musamman take, tun daga nan suka fara daukar hotuna. Screaming hannun sa yayi da karfi har sai da jijiyoyin jikin sa suka tashi raɗaraɗa a jikin sa, ya sake shiga Whatsapp dinsa for the countless times yana kallon videos da aka turo masa babu ko kiftawa, buga wayar yayi da kasa ya hura iska a bakin sa ya dunkule hannun sa ya dake iska yace "Why Niswaaa??" Idon sa yayi mugun ja, cousin ɗin sa dake zaune tun dazu shima speechless ya mike ya na kallon dan uwan nasa cike da tausayi yace "Prince pls calm down, kar ka jima kan ka ciwo" yadda ya juya yana kallon sa hakan yasa shima masa baya da sauri. Daddy ya kalli agogon hannun sa sannan ya kalli Rayyan shi dai kawai yayi shiru dan gaba ɗaya sai yaji hankalin sa yayi mugun tashi, abinda ya faru lokacin daura auren Leena ne kawai ya fado masa a kai, da sauri ya dafe bangon ya zauna yana Salati a hankali, Rayyan ya kalle sa yace "Is everything alright, Daddy?" Ayaan ma sai kallon Baban nasa yake dan kana ganin sa kasan akwai abun da ke damun sa a wannan moment ɗin, yana kallon Rayyan yace "Rayyan ba kuyi waya da su bane?" Rayyan yace "da zu dai munyi waya da Ashraft ɗin, sannan kuma ai an kai musu breakfast" Daddy yace "kalli agogo, time fah yayi ba kowa nasa" Rayyan yayi shiru shima dan yanzu ya fahimci me Daddy yake nufi, kallon body guard din su yasa Daddy sauke ajiyan zuciya, Rayyan da yaji shigowan messages wayan sa duk tunanin sa Layla ce yasa ya shiga Whatsapp ɗin sa, wani sabon numbern da ya gani haka nan yaji zuciyar sa sinke wa yana shiga yaga videos ne wajan 10, fara kallon da yayi yasa ya kifa wayan sa ba shiri yana rintsa idanun sa ya fara salati, Daddy duk hankalin sa na kan dan aiken, bayan ya isar masa da sakon su Daddy yaji wani sanyi na shigar sa, toh me zai duba a Whatsapp ɗin bayan yasan karshen sa a kuma yadda aka yi wa Leena, amma hakan yasa ya daure ya kunna wayan nasa kallon sabon layin da messages ɗin sa ya shigo ya tsaya yi amma ya gagara buɗewa.



Assalamu Alaikum, daga ina ma zan fara? Kunyar ku ma nake ji gaskiya, well! Jina shiru da ku ka yi jinya wata dan matsala aka samu, amma ina fatan zaku yi enjoying wannan chapter din, Thank you.


Naga ruwan votes please.
*AGOLA (Behind the palace walls)*



Wattpad © Jiddatulkhayr

Young talented writers association (YOTA)


Chapter 51


He was extremely shocked and deeply disappointed in her because he never saw this coming from her, mike wa tsaye yayi ba tare da ya kalli Rayyan ba, ya ɗan juya ya kalli colleagues ɗin sa da wasu few friends din sa dake tsaye suna magana, ya juya a hankali ya wuce zuwa inda yayi parking motar sa, be ma kula da Ayaan dake bin sa a baya ba, zai shiga motar nasa ya jiyo muryan wani daga cikin bakin da suka zo daga masarautar, da kyar ya iya tsayuwa ya jingina da motar nasa har mutum ya karaso, bayan sun gaisa yace "It's good mu shiga motar sai muyi magana ko?" Daddy ya gagara basa amsa sai dai ya buɗe motar ya shiga shima wannan ya shiga yama rasa ta ina zai farawa Daddy bayani ta yadda zai fahimce sa, bayan sun yi magana mai tsayi daga karshe Daddy yace "tana da wata sister idan zaku yarda sai a ɗaura da ita" ya girgiza kai yace "bana tunanin mai martaba zai iya yarda". Rayyan kam gaba ɗaya ji yayi wani zazzaɓi ne ya lulluɓe sa, dan ya gagara ta shi a yanda Daddy ya bar sa. kan kace me gidan har ya fara daukar rumors ɗin fasa bikin amma kowa yana tsoron a fara ji a bakin sa saboda yadda aka ga daga amarya har uwarta suna ta ɗaukar hoto. Ayaan ya zuba wa Daddy ido ganin yadda yake gudu da motar, a kofar gidan sa yayi parking dan baya jin zai iya shiga da motar nasa cikin gidan, ya buɗe motar ya sauka ko lock bai sawa motar ba ya kama hanyar cikin gidan, Ayaan ma ya sauka yabi bayan Daddyn nasa da gudu, bayan ya shiga part ɗin sa ya wuce direct ganin yadda aka cika a gidan, masu gulma, ganin yanayin Daddy ya kuma tabbatar musu da zargin su, zaga parlorn nasa yake yi, zuciyar sa na kuna, dialing numbern Mummy yayi har ya katse bata ɗaga ba, ya kuma kiran ta har sannan bata amsa ba ya kira wata cousin dinsa tana dauka ko Sallamar ta bai amsa ba a takaice yace "Amina ki je kice wa Khadija ita da 'yarta Niswa su same Ni yanzu a part din na" yana gama isar da sakon ya katse kiran, Amina ta cire wayan a kunnan ta tana kallon wayan tana mamakin yadda taji muryan Daddy ta kalli mutanen dake cike a parlorn Hajiya sai kuma ta mike ta fita, bayan ta shiga part ɗin Mummy ta same Niswa na gefe da kawayen ta sai kuma Mummy tana dakin ta da wasu few friends ɗinta hakan yasa ta karasa har inda Mummy take tayi kasa da murya tace "Anty Hadiza, Yaya yace wai yana neman ki ke da amarya" Mummy tace "Oh har an daura auren kenan?" kai kawai ta gyaɗa mata ta mike fuskar ta cike da annashuwa ta fito parlor, Niswa da haka nan taji hankalin ta ya fara tashi ganin yadda take kira Ashraft baya ɗauka wa abin yasa ta ɗan fara damuwa duk da bata bari hakan ya nuna a fuskar ta ba, Mummy na kallon ta tace "Niswa taso Daddyn ku nason magana da mu" Niswa ta mike tana tattare wedding gown din jikin ta tabi bayan Mummy suka fita zuwa sashin Daddy kai tsaye Mummy ta buɗe ta shiga Niswa na biye da ita a baya Daddy ya juyo yana kallon su expression ɗin fuskar sa kadai yasa duk zuciyoyin su bugawa barin ma Mummy, Daddy bai yi wata-wata ba ya sauke wa Niswa mari ta rike kuncin ta kafin ta gama fita a wannan shocked ɗin ya sake sake mata wani marin ya kuma hankaɗa ta da kafa tsabar yadda ranshi yayi mummunan ɓaci, Mummy tace "Kai, Uwar me ta maka zaka mata wannan " Daddy ya juya ya zuba mata rinanun idon sa yace "Ai gata, gata nan a gaban ki sai kije ki ma mutanen da kika tara cewa an fasa auren 'yar ta ki, 'yar da kika kasa mata tarbiyya" Niswa da take duke rike da kuncin ta ta ɗago da sauri tana kallon Daddy cike da mamakin jin furucin sa, Mummy tace "Bangane mai kake nufi ba?" Daddy ya buɗe wayan sa ya wurga mata wayan yace "ki duba ki ga irin tarbiyyar da kika mata" haka nan Mummy taji ba zata iya ɗauka ba, Daddy dake kallon Niswa ya mika mata wayan yace "waye wannan?" Niswa jiki na bari ta daga wayan ta sauri ta sake bayan taga nude videos ɗin ta ne da Farouq ta rintsa idanu hawaye ya fara sauka a kuncin ta, ya daka mata tsawa "get out of my sight" Niswa ta mike dakyar ta fita bata tsaya ko ina ba sai dakin Mummy tana shiga kuma ta kulle da makulli, Mummy bata san sanda hawaye ya gangaro mata ba ta mike tsaye tana kallon sa tace "wani shegen ne ya turo maka?" Daddy ya zauna zuciyarsa yana tafarfasa yace "whosoever ina ruwan ki da shi? Idan bata yi hakan ba har wani zai samu wannan galabar ne?" Mummy ta share hawayen da ya fara sintiri a fuskar ta yanzu ita damuwar ta yadda zata fita har ta fuskanci mutane. Amina ta kalli Hajiya da yanzu ake shafa mata tace "Toh ina ga da gaske ne dan ɗazu shi da kansa ya kira Ni a waya sounding pissed off yace na kira masa Anty Hadizan da ita da amaryan" Hajiya ta mike ba tare da ta tsaya jin me zasu kara cewa ba ta wuce sashin Daddy tun kafin ta karasa ciki ta haɗu da Mummy dake shirin fita kallo ɗaya Hajiya ta mata zata wuce ta sai kuma Mummy a hankali tace "ina wuni Hajiya" Hajiya ta karasa ciki ba tare da ta kula ta ba, dakyar Mummy ke iya daga kafan ta a cikin compound ɗin har ta karasa sashin ta mutane na binta da idanu dan yanzu kam kowa ma dake cikin gidan ya san da labarin abin da ke faruwa, bayan Mummy ta shiga parlorn kawar ta Maryam ta mike tabi bayan ta Mummy ta murɗa handle ɗin taji a kulle ta bubbuga tace "waye a ciki" Niswa data kifa kanta da wall ta mike a hankali ta karasa ta buɗe mata bayan ta shiga kawar ta ma ta
End Ads