x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 63 - AGOLA free pages

  • 186001 words
  • 189000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
me abun kunya?" Farida ta ɗan Kalle ta dan ta ɗauka ta first maganganu zata gaya mata, a hankali tace "I'm sorry Amma kunyar ki nake ji, gani nake kamar naci amanar ki duk da Nima bawai ina son shi bane su Mami da Mamana suka hada kayan su" Leena ta riko hannun ta tace "Ki daina min wannan kallon dan Allah, dan Ni kam tuni na manta da shi balle ma Kinga har aure na sake, dama rabon Nawaf ne ya kawo ni gidan sa, kuma ki daina masa kallon wanda haɗa ku aka yi saboda Sadeeq bashi da matsala ko ɗaya zaki ji dadin zama da shi in shaa Allah" Farida ta gyaɗa mata kai tace "Thank you Anty Leena" daga haka Leena ta koma parlorn ta samu har su Ammi sun tashi zasu tafi da sauri tabi bayan su. Washe gari da safe sai ga Niswa da Zahra sun zo mata sallama, Zahra tana kallon Leena dake breakfast a parlorn Ammi tace "Ahaf, kin tuna?" Leena tace "Me kenan?" Zahra tace "Lokacin da nace kuna kama?" Leena tayi dariya ta cigaba da breakfast ɗin ta Zahra tace "Nace miki kuna kama kamar wasu Twins kika ce idona baya aiki ne, toh yanzu kin tabbatar idon na ki ne baya aiki" Leena tayi murmushi kawai, Niswa tace "Congratulations Leena" Leena tace "Thank you Anty Niswa", bayan ta gama shiri har Malik ya dawo daga gidan Umma hakan yasa suka fita compound wajan da mota da zai kaisu airport suka karasa sai ga Layla da Hasna, Leena ta karasa da sauri taje ta rungume Layla sai kuma ta sake ta ta karɓi Leena dake hannun Rayyan tana ma yarinyar dariya, Ta gaishe da Layla ta amsa tana mata murna magana suke suna dariya sai kuma taji ba daɗi data share Hasna dan takan tuna lokacin da suke zuwa gidan su da Fu'ad sai Hasna na mata wani gani gani dan lokacin gani take Rayyan na son Leena shiyasa baya kula ta, Leena ta mayar da kallon ta ga Hasna tace "Anty Hasna ina wuni" Hasna ta jiyo da murmushi akan fuskanta ta amsa mata, Hajiya ta miƙa mata wani roban dambun kaza guda biyu tace "Kinga Wannan na Mai martaba ne" Leena tace "Toh" sai kuma ta sake miƙa mata wani tace "Wannan kuma na ganni suke ce mata ko me Oho" Ayaan ya fara dariya yace "Granny ake cewa" tace "Uwaka, nayi da kai?" sai kuma ta mayar da kallon ta ga Leena tace "Idan kinje ki basu kice inji kakar ki, sannan kafin lokacin Hajjin mu yayi zanzo na gaishe su da kai na" Leena tace "In Shaa Allah" Hajiya Amina da ta shigo gidan ne yasa duk suka bita da kallo wanda bata ce musu ko cikan ku ba, daga haka duk suka shiga Mota Rayyan yana tuka ɗaya dayan kuma driver ke ja daga haka suka fita daga compound ɗin , Ammi sai yanzu take jin Leena tayi aure dan gani take shikenan ita da 'yarta yanzu kuma sai ziyara, Hajiya ta kalli Ammi sai kuma ta juya kan Daddy tana kallon sa tace masa "Yanzu kuma saura ka sauwake wa bakar matar naka da ta raina Ni"...


A taya Ni Sharing dan Allah
*AGOLA (Behind the palace walls)*



*YOTA*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes

Chapter 74

With shock Daddy ke kallon Hajiya dan ɓai ɗauka zata iya faɗin hakan ba yace "But Hajiya ai naga kamar yanzu idan na rabu da ita ban kyauta mata ba duba da yadda sufa ya fara tunkaro ta" Hajiya ta riƙe haɓa tana kallon sa da mamaki tace "Amma duk tsawon zaman ku tare zaka ce baka san ta raina Ni bane? Ko kuma baka kallon ko gaisuwa baya shiga tsakanina da ita balle yaranta dan gwamma Rayyan kaɗai ke gaishe Ni sai kuma bayan da Niswa tayi aure" Ammi ta juya ta koma part ɗin ta jiki a sanyaye dan ba kaɗan ba Hajiya ta bata mamaki bata dau zata kawo wannan babban hukunci ba amma da ta tuna yadda Mummy tayi ta treating Hajiya sai tayi shiru dan Hajiya bata da wani say gwamma ma bayan da aka auro ta itake kai mata abinci. Hajiya tana kallon Daddy daya sauke idon sa kasa tace "Muhammadu ba zaka iya abin da nace maka bane?" Ya girgiza kai yace "Ba wai ba zan iya bane Hajiya kawai dai..." Ta katse sa "Shikenan tunda ban isa da kai ba daga haka ta juya zata bar wajan, yayi saurin shan gaban ta ya duka yana rike ta kafafun ta yace "kiyi Hakuri Hajiya ba wai ba zan iya bane, amma tunda kince haka yanzu zan aiwatar da abin da kika so" daga haka ya miƙe har Sannan bata sake kallon sa ba tayi wucewar ta ciki, Daddy kuma ya karasa sashin Mummy ya kai hannu zai buɗe yaga parlorn a buɗe yake hakan yasa ya shiga parlorn kansa tsaye sai dai yana jiyo muryan mutane biyu daga dakin Mummy. Hajiya Amina ta ma Mummy wani kallo tace "Daɗi na dake gaggawa" Mummy tace "Hmm ba zaki taɓa fahimta bane yanzu shegiyar Uwar san nan nake so a fara nane min bakin ta sannan kuma duk abin da zata ce masa idan ba nawa maganar bane toh ba zai bi ba, ita kuma Uwar Leenan asa tsanar ta a zuciyar sa har ya sake ta" Hajiya Amina tace "Baki da damuwa dan yanzu haka ma ya fara aiki nake gaya miki, ai dama matsalar tun farko da ya haɗa ki da Uwar sa ce amma yanzu da kansa zai ce ba zai iya zama da ita ba dole wani gidan zai nema mata ko ta koma kauye" Mummy tayi wani dariya sai kuma tace "Toh ya za'ayi da Leena? Nifah na haɗa auren nan" sai kuma tayi tagumi tace "Ai naga ta kaina dole ma a raba auren nan tunda Ni na haɗa idan ya so yazo ya auri Nisreen ɗina" Hajiya Amina tayi dariya tace "Sai dake wato ma ya auri Nisreen?" Tace "Wallahi toh Ni ina ruwa na" Hajiya Amina ta miƙa mata wani kullin laida tace "Toh ki tabbatar dai Daddyn su yaci, ki haɗa a cikin abinci" Mummy ta karɓa tace "Yanzu ma zan shiga na dafa masa Lunch Kinga sai na zuba" tace "Sure" ta dauki jakkan ta ta rataya Mummy tace "Please ki sake tunatar da shi muhimman abubuwan sune, Ya sake matar sa sannan a rufe bakin shegiyar uwar nasa sai kuma ya kora ta koda kauye ne ko kuma ya nema mata wani gidan sai ita kuma Leenan a haɗa faɗa sakanin ta da Malik ɗin yaji ya tsane ta har su rabu daga baya kuma yace Nisreen yake so" Hajiya Amina tayi dariya tabi hanyar fita tana cewa "Sai da ke, wato kin jima kina abu, yau wajan shekaru 20 fah, Chap sai dai ke ɗin matar M...." Maganar tane ya kafe ganin Daddy a bakin kofar yana tsaye yana jin duk conversation ɗin na su, Mummy dake bayan ta tace "Karasa mana, Ai gidan nan nawa ce Ni kaɗai kamar yadda nake tun farko" tana kallon Hajiya Amina tace "Mu tafi mana" zata kama hannun ta ganin reaction ɗinta kawai taga Daddy tsaye a bakin kofar, bata san sanda ta kwala kara da duka kan kafafun ta ba sai kuma ta miƙe tayi wajan sa cike da shagwaba tace "Yaushe kazo dear?" zata kwanta jikin sa ya sauke mata marin daya sa taga stars hakan yasa Hajiya Amina ja baya da sauri dan ta fahimci ya gama jin su, Mummy ta ɗaga kanta zata yi magana hawaye na sauka kan kuncin ta yace "Hold on, kije na sake ki" Mummy tayi wani ihu a gigice kamar zata yi hauka tana kallon sa sai kuma da sauri ta duka kasa ta rike kafar nasa tana kuka tana cewa "Dan Allah ka rufa min asiri, duk abin da kaji tsausayi ne" Daddy ya kwace kafar sa yana mata wani irin kallo yace "Make sure kin kwashe komai naki kin bar min gida cos ba zan lamunci ganin ki a gida na ba" daga haka ya fita part ɗin sa ya wuce yana jin zuciyar sa na wani irin zafi. Bayan jirgin su Leena ya sauka a airport dake cikin jihar Yola, wannan ne karo na farko da Leena ta fara zuwa garin, wasu Manyan motoci ne ke fake waje guda wanda sai ka ɗauka wasu manyar kasa aka zo ɗauka, wani ke leading ɗinsu har suka karasa wajan motar daga Malik har Leena suna mamakin irin tarban da za'a musu duba da yadda motoci ke jiran su sai kace sun kai goma, bayan sun shiga mota ɗaya sannan ta fara tafiya sai kuma escort ɗin motocin suka fara bin su a baya, a cikin Masarautar Yola aka parka motocin, suka sauka wanda duk mutanen dake Safa da marwa a cikin Masarautar suka fara dukawa suna gaishe su, tun kafin su isa kofar Babban parlorn Masarautar Leena suka kalli Granny da ahalinta sun fito duk suna tsaye, Granny ta karasa ta rungume su, tayi cikin parlorn dasu a hannun ta duk kowa ya juya ya bi bayan su zuwa parlorn kowa da murmushi a fuskar sa,  parlorn a cike yake da 'yan uwa kowa sai magana suke musu wanda zuwa sannan har sun gaji da amsa wa, Buɗe kofar parlorn aka yi ya shigo ciki fuskar sa ɗauke da murmushi, wani zabura Leena tayi ta miƙe tana kallon sa without second thought tayi kansa da gudu ta rungume sa tace "Abbah!" Kawai yaji hawaye ya cika idon sa amma yana kokarin hana kansa zuba, duk parlon kallon su ake cike da tausayi, Hajiya tana kallon Malik tayi karfin halin cewa "Suhail, Baban ka ne" Suhail ya kalli Mutumin dake kama da Leena sai kuma ya kalli Hajiya, Leena lokaci guda jikin ta yayi sanyi ta juya tana kallon Hajiya sai kuma ta tuna cewa  Twin bro din Abbahn tane ta sake fashewa da kuka ya fara patting bayan ta ya tallabo fuskanta yana kallon ta ya gagara magana amma fuskar ɗan-uwansa yake kallo ya sakar mata murmushi yana rike da hannun ta ya karasa cikin parlorn ya buɗewa Malik hannu alamar yazk, Malik yayi shiru a jikin sa sai kuma ya tsinci kansa so emotional, hawaye kawai ya fara dan bai taɓa zaton wannan ranan ba, nan take yaji wani irin calmness na shigar sa, anan ya tabbatar da tabbas wannan Mahaifinsa ne dan ya lura yadda yake magana da kuma yadda yake murmushin sa irin nasa ne, Hajiya Amira ta karasa itama ta rungume su baki ɗaya, yana rike da su ya zauna sai ga Hajiya Indo ta shigo fuskar ta cike da fara'a tana "Ina yaran nawa suke?" ta karasa ta rungume su, can Hajiya tace "Toh ku tashi kuje kuyi wanka kuyi sallah sai kuzo muyi lunch ko?" 'yar Gimbiya Indo wacca ake kira da 'Khadija' ta miƙe tana cewa "Ni zan kai su" sai ga wasu 'yan uwan nasu ma sun mike kowa yana cewa shine zai nuna musu bangaren su, daga karshe Khadija ta kai su. Bayan sun fito duk suka wuce suka yi lunch tare, Leena har mamakin yadda ake nan nan da su take yi dan ba karamin soyayya suke nuna musu ba. Da Daddare aka shirya wani gagarumin liyafa saboda Leena da Malik wanda kowa ya fi son yaga yana jikin su, aka ci aka sha dan sai da Masarautar tasan da wannan liyafan har wanda suke wajan ta ma sai da aka dinga sadaka wa almajirai da marasa karfi. Duk a gajiye suka koma parlorn, Khadija na rike da hannun Leena sai ga wasu 'yan uwan nasu mata biyu suma sun shigo, Batul da Umaima, Hajiya na kallon su tace "Kuje ku kwanta nasan Leena ta gaji" Malik dake gefen dan uwansa ya ɗan saci kallon Leena sai kuma ya kalli Hajiya, Leena ta mike ta bi bayan su Khadija wanda duk suka ki tafiya dakin su wai da ita zasu kwanta, ai wannan ranan Leena anan tasan menene soyayyar 'yan uwa sai da tayi kuka saboda yadda kowa ke nuna masu kauna, duk yadda Leena taso tayi bacci da wuri amma haka suka hana ta kowa da labarin da yake bata wani sai dai kawai tayi murmushi wanin kuma tace "Hmm" a haka dai har ta fara jin bacci ya fara cin karfin ta wajan 2am bata ma san sanda ya kwashe ta ba. Bayan Daddy ya dawo daga sallar asuba ya wuce dakin Hajiya dan gaishe ta, ya samu tana tasbihi ne, ganin sa yasa ta sallame ta juya, bayan ya gaishe ta tace "Yaushe zata bar gidan?" Daddy da har sannan Manganganun Mummy basu bar brain din sa ba, ji yake kamar a sannan take maganar ya kalli wani direction dan shi yanzu baya kaunar wani abu da ya shafe ta yace "Ina ga zuwa anijima zata bar gidan" Hajiya ta mike tace "Better, sai ka kawo ɗan-uwan ka dake fama da gidan haya ya zauna a sashin nata" Daddy ya gyaɗa kai yace "Ina ga ma zamu bar nan gidan ma kawai" Hajiya tace "Toh Allah mana mai kyau" yace "Amin" daga haka ya bar parlorn Hajiya. Ammi ta fito da niyyar zuwa dakin Daddy sai taga ana fitar da kayan Mummy hakan yasa jikin ta yayi sanyi, yazo zata wuce ta ga Mummy tana tunkaro ta hakan yasa ta ɗan tsaya har ta karasa Ammi tace "Ina kwana" Mummy ta mata wani kallon kaskanci tace "ki faɗawa bokar ki yanzu wasan zai fara, ina kinyi winning yanzu ko? Ki jira zagayowa ta" Ammi bata yi niyyar kulawa ba amma sai kuma tace "Allah na rike dan bani da wata boka, kuma yafi karfin ki dan haka ki miƙa wiya kafin lokacin ya kure miki" Mummy tayi wani dariya tace"Ki gama murnan ki nan da sati zaki sha mamaki kuwa" Ammi bata kara bi ta kanta ba ta wuce sashin Daddy, tana shiga taga yana waya hakan yasa ta juya yayi saurin cewa "Hauwa" ta juya tana kallon sa ya sauke wayan yace "Ina zaki kuma?" Ta karasa ta zauna tana kallon sa tace "Ina Maman Rayyan zata kuma?" Yace "Please idan kina da wani abun cewa toh amma bana son maganar Khadija" tayi shiru duk jikin ta yayi sanyi. Bayan sun gama breakfast sai ga Leena da su Khadija sun fito wanda ita bata so bin su ba amma da ta tuna dan ita suke sai kawai tayi zeroing mind ɗin ta zata bi su, Granny ta sake baki tana kallon su ganin duk sunyi shirin fita tace "Ina zuwa kuma?" Batul tace "Polo ground sai kuma ice cream date" Granny ta sake baki tana kallon su Umaima tace "Kai Granny, kawai muna son muyi cheering ɗin su ne fah" Ta juya ta kalli Leena da sai murmushi kawai take tace "Amma gaskiya Leena kiyi a hankali, kar suyi ta jan ki waje dan gwara su kalau suke amma ina dalili suyi ta janki da karamin ciki" Leena ta turo baki taki kallon direction dinta Batul tace "Ai harda Yaya Suhail zamu fah kuma zamu wuce Ice cream planet" Suhaif ya kalli Malik yace "Sai kuma ka bi su?" Malik ya masa dariya sai kuma ya gyaɗa kai yace "Dan mu suke kar muna discouraging din su " ya taɓe baki daga haka ya miƙe ya bar parlorn, Leena basu suka dawo gida ba sai bayan Isha'i duk ta gaji bayan sun yi dinner ta mike zata bi su Khadija Granny tace "Kyale su, ga can ɗakin Suhail nan zaki zauna kafin ku tafi" Leena ta sauke kanta kasa sai kuma ta gagara cigaba da tafiyar ta tsaya sai da Granny ta kaita da kanta Sannan ta tafi. Rayyan was so heartbroken bai taɓa ɗauka Daddy zai rabu da Mummy ba sai ma daya ga ta kwashe kayan ta a gidan kawai ya kaita gidan sa ya bata BQ ta zuba kayan ta kafin ya sama mata wani gidan, Nisreen da Niswa kam kuka suka dinga sha duk da duk yaran sun san halin Uwar su kuma sun san Daddy ba karamin kokarin yayi ba. Rayyan yayi sallama a Parlorn Daddy bayan ya shiga suka gaisa sai kuma yayi shiru yama rasa ta ina zai soma, can ya ɗan kalli Daddy ganin wani direction daban yake kallo, Daddyn ma yasan da magana a bakin sa amma ya nuna bai fahimci hakan ba, Rayyan ya miƙe ya karasa inda Daddy yake zaune ya duka kan gwiwowin sa yace "Dan Allah Daddy, ba dan halin Mummy ba, ka dube mu musamman su Nisreen dan Allah Daddy ka dawo da Mummy" Daddy ya gyara zaman sa ya juyo gaba ki ɗaya yana kallon sa yace "Rayyan Mummyn ku ita ta jawo ma kanta, tayi abubuwa da dama ina overlooking and the worst part shine bata daraja Hajiya ko kaɗan amma still na cigaba da zama da ita, ta sayar min da gida ba tare da sani na ba kawai dan ta wulakanta Leena amma still banji zan rabu da ita ba amma tunda naji next move din ta shiyasa na sauwaka mata wanda wannan zai zama sirri ne dan ko Hajiya ban sanar da ita ba, toh kaga anan ai na mata adalci ko?" Rayyan ya sauke wani ajiyan zuciya yana kallon Daddy, Daddy ya miƙe tsaye yace "Beside yanzu babu wani sauran zama a tsakanin mu dama akwai saki biyu" daga haka ya bar parlorn zuwa dakin Ammi, Rayyan was frozen. That same day, Mai martaba ya saka aka kira masa Leena da Malik Bayan sun gama dinner yana kallon Leena yace "Wani makarantar kike son zuwa?" Leena tace "Ko wanne ma" yace "Voice out, nan kakan kine ba wani ba, faɗi duk inda kike so" ta saci kallon Malik sai kuma tayi murmushi kawai, Granny tace "Toh a nema mata Nile mana tunda mijin nata a Abuja zai fara aiki" Mai martaba yace "It's Okay, hakan ma yayi" yana kallon Malik yace "Suhail kai kuma zaka fara aiki next week In Shaa Allah".
End Ads