x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 20 - AGOLA free pages

  • 57001 words
  • 60000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
call ɗinsa Sadeeq ya dinga kallon screen ɗin sai kuma yace "Do you think you're ready, considering your age?" Leena tunanin toh shi kuma me na sa da zai tsare ta da tambayoyi shi da ko magana baya son mata jujjuya wayan hannun ta ta fara yi tana son ta bar wajan amma sai kuma taji ta kasa ba zata iya ba, ta ɗan sacikallon sa taga har sannan kallon ta ya keyi yace "If you're comfortable getting married now, that's perfectly fine, Leena. If you believe you've made the best choice, I wish you all the very best throughout your marriage journey!" Leena taji hawayen da bata san ko na menene ba, tayi kokarin rike shi back, jin Muryan Sultan da Jidda da suka fito daga parlorn suka ji, Sadeeq ko kallon su be yi ba ya bar wajan, parking space ya wuce ya shiga motar sa sannan ya fita, Jidda ta bishi da kallon tausayi Sultan kuma yace "Oops yaushe kuka fara hira bamu sani ba? Kila ma gulman mu kuke yi ko?" Sai sannan Leena ta ɗan kalle su ganin yanayin mood ɗinta yasa sai suka bar wasa, Leena ta mike tace "Anty barin ma Mami sallama kawai" daga haka ta shige ciki har ɗakin Mami ta shiga ta mata sallama ta fito anan wajan ta kuma ganin su tace "Anty Jidda, Uncle Sultan sai da safe" Jiddah tace "sai goben na shigo, in shaa Allah" Leena ta gƴaɗa kai sannan ta fita, tana fara tafiya few houses tsakanin su da gidan su Jidda taga motar Sadeeq a parke tazo daf da zata wuce yace "Leena!" ta tsaya kanta a kasa kuma bata amsa shi ba yace "Get in, I'll drop you off" ba musu ta shiga, a daidai gate ɗin su yayi parking sai ga Rayyan ma da zuwan sa kenan, Leena zata buɗe gate ɗin yace "wait..!" ta gaban glass ɗin motar yake kallon Rayyan yace "Is he your fiance?" Ya mata tambayar still idon sa na kan Rayyan, Leena ta kalli Rayyan da kallo ɗaya ya musu zai shiga gida sai kuma ta sauke kanta kasa tace "No!" Yace "well, take care" tana kallon sa taga har sannan idon sa na kan gate bayan Rayyan ya shige tace "Nagode" daga haka ta sauka tayi cikin gida a compound ta haɗu da Niswa da ta fito a part din Daddy hararan Leena tayi, Leena ta ɗauke kanta ta wuce sashin su ita duk jikinta ya mutu tunanin tambayoyi da Sadeeq ya jero mata take yi, Samun Ammi tayi a kitchen tana Haɗa dinnern Daddy Leena ta gaishe ta, Ammi tace "kin same ta ɗin ko?" tace "Eh" tace "toh Kinga ai hakan ya fi". Bayan Magrib Leena na dakin Hajiya da taki kula ta da kyar Leena ta roki Hajiya sannan ta ɗan sake mata tana kwance kan sofa tana chatting da Muhammad tana basa labarin saukan da zata yi Rayyan ya shigo parlorn da sallama ta amsa masa sannan ta tashi daga kwancen da take yi amma still idon ta na kan waya ta ajiye wayan a gefe tace "Ina wuni Ya Rain" be amsa mata ba ta ɗaga kai taga kallon ta yake yi, yace "Is he your fiance?" Leena tayi shiru tana mamakin tambaya daya da suka mata ta girgiza masa kai tace "No" yace "Then why is he jealous all the time? Ko fa a masallaci muka haɗu muna gaisawa da Sultan but ban da shi" tana mamakin jin furucin sa Sadeeq kuma? To Meyasa kowa ke haɗa ta da Sadeeq? Kallon sa tayi tace "Jealous? How?, please" Rayyan yayi murmushi yace "Sure, I can see it written all over his face whenever he sees me with you, or not" Leena tace "Amma, baka fahimce sa bane" yace "It's Okay, then," sai ga Hajiya ta fito daga ɗakin ta Leena ta mike tana kallon Hajiya tace "sai da safe Hajiya" Hajiya tace "har zaki tafi?" tace "Eh" daga haka ta kama hanyar fita Rayyan ya bita da ido sai de be ce komai ba, Hajiya ta zauna suna gaisawa. Leena da ke zaune da Ammi tana bata labari akan Jidda tace ta bar mata komai a hannun ta, zata mata organizing suna cikin magana wayan ta ya fara ringing kallon numbern take Ammi tace "ɗauka mana ko sai ya yanke?" Maganar Rayyan ne na ɗazu yake yawo a kanta Zahra ta taɓa faɗa mata Jidda ma ta mata rantsuwa akan magana hakan yasa ta kasa ɗagawa har ya yanke Ammi na kallon ta tace "lafiya?" Leena ta gyada kai Ammi tace "waye ne? Ba Muhammad bane ?" Leena tace "Uncle sadeeq ne" Ammi tayi shiru tana kallon ta sai ga wani kiran nashi ya shigo ɗagawa tayi ta kai kunne da sallama a bakin ta ya amsa mata sai kuma yayi shiru a hankali tace "ina wuni, ka koma lafiya?" be amsa mata ba sai ma cewa yayi da "There's an organization, similar to an NGO, focused on climate change. They're looking for a young poet to represent the nation and advocate for children's rights. I sent them your details and some of your work. Once they're done with the flyer, they'll likely contact you. Be prepared!" Leena feels loved dama tana da burin tana gama exams zata ci-gaba tace "Wayyo! Thank you so much, Uncle Sadeeq. But when is it going to take place?" yace "idan sun kira zaki ji ai" tace "Okay, thanks again" ji tayi ya katse kiran tana kallon Ammi tace "Uncle Sadeeq ne!" Ammi tace"Ayyah" Leena tace "wai ana neman young poet ne ya bada details ɗina and some of my works" sai kuma tayi shiru tana tunanin dama yana da videos ɗinta ne sai kuma tace kila yayi downloading ne a Instagram muryan Ammi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa Ammi tace "Amma yaushe ne? Anya Leena ba zaki hakura ba? Kinga ana gama walimar ki sai maganar biki fa ba lokaci nake ga gashi kin ce kina son tafiya Catering school" Leena tace "toh ai Ammi naga wannan na rana ɗaya ne kuma ina ga acikin kaduna ne da wani gari ne ma ba zai taɓa bayar da info ɗina ba, dan wancan lokacin ma yayi ta masifa wai Meyasa na tafi Abuja, shiyasa na tsane sa ai" Ammi tayi shiru tace "toh bari muga yadda abun zai kasance amma ki tabbatar kin sanar da Muhammad kin san ba kowa yake son wannan abun ba idan yace ki hakura, Leena kawai ki hakura" Leena ta gƴada kai dan tasan Muhammad ba zai taɓa hana ta ba.
Mummy ce ta shigo gidan wujiga wujiga kana ganin ta kasan a gajiye take duk tayi kalan tausayi banka ɗa kofar parlorn tayi ta shiga Daddy dake ma Rayyan magana suka ɗaga kai tare suna kallon ta Daddy ya mike yace "Lafiya Khadija?" Mummy tace "Lafiya" daga haka ta kama hanyar ɗakin ta Rayyan ya bita da kallo tana shiga ta sama kofar key ta fashe da kuka, toh ita yanzu ta'ina ma zata fara ne. Rayyan ya kalli Daddy Who was Speechless, Daddy yace "bari ta sauko tukun nan".
Yau tunda Leena ta dawo daga exams suka fita ita da Jidda don siyayya and other stuff, kayan da zata yi fita da shi ma sun fasa kaiwa ɗinki ready made kawai suka je suka tsiya ganin lokaci ya kure ga kuma disappoinment ɗin toilers bayan Jiddah tayi parking a kofar gidan su Leena, Leena dake gaban motar, Jidda ke driving, Jidda ta gyara zaman ta yadda zata iya kallon ta da kyau tace "Leena, you think Sadeeq doesn't love you, right?" Leena ta ɗaga kai tana kallon ta to me ya kawo wannan tambaya kuma tace "Eh, kamar haka nake gani" Jidda ta girgiza kai tace You misperceive him, Leena, Ya Sadeeq loves you unconditionally, ina faɗa miki wannan ne ba wai dan wani abu ba, ina son kisan haka nature ɗinsa yake kuma baya taɓa shiga abinda be shafe sa bane, kalli reaction ɗinsa ranan da kika zo waje na a Abuja saboda ya damu da ke ne" Leena tayi shiru tana kallon waje guda Jiddah tace "I'm sorry, Nasan be kamata na kawo maganar nan ba amma kawai ne naga da kika shigo ko kallon sa be ishe ki ba balle gaisuwa" Leena ta tsunkuyar da kai sai taji duk ba daɗi amma ai ko baya amsa mata takan gaishe sa kawai avoiding issues take da shi, tana wasa da fingers ɗinta tace "naga yana waya ne kuma ko na gaishe sa ai baya amsa wane" Jiddah tayi dariya tace "nature ɗinsa ne haka, sai hakuri" daga haka tayi horn me gadi ya buɗe gate ta shiga da motar tayi parking duk sauka sukayi Leena ta kira masu sawa Flowers ruwa tace "su ɗan taimaka mata su shigar da kayan motar cikin parlorn su, Jiddah kuma tana tsaye a jikin motan har suka karasa kwashe kayan da suka sayo masu mugun yawa, Jiddah ta shiga parlorn tana gaida Ammi da yanzu ta fito jin shigowan su Ammi ta amsa tace "yau Leena ta wahalar da ke, sannu da kokari" Jidda na Murmushi tace "Haba Ammi, ai yiwa kai ne balle ni kam na ɗauki Leena a matsayin kanwa ce" Ammi tace "Munde gode sosai, sannu da kokari" kitchen ta nufa sai gashi ta kawo mata abinci Jidda tace "wallahi da ba dan abincin Ammi extra daɗi ne da shi ba da wallahi ba zan iya ci ba saboda bana jin yunwa" ta karasa maganar tana kallon Leena, Leena tayi murmushi Ammi tace "Toh ki ci kaɗan ɗin dai" Jiddah tana kallon Leena tace "Allah sa dai kin ɗauko Ammi a iya girki?" Leena tace "Toh ai cewa yayi ko ban iya ba ba damuwa shi zai nayi ina kallo har na iya, idan ya gaji kuma awaje zamu na ci" Ammi tace "Jiddah kinji kanwar ki ko? Ita fah ba kunya gare ta ba, sannan yanda kika san an mata baki akan shiga kitchen wallahi, sai kuna sata a hanya, dan wallahi ta iya abincin zun zurutun son jiki ne da ita" Jiddah na kallon ta tace "Ai kuwa alkawarin Muhammad ba zai ɗauki lokaci ba, gwarama ki fara shiga yanzu har ki saba".
Mummy da ke waya tace "Wallahi ni kam Fatima ba zan iya hakura ba, nace ko dai malamin ne be kware ba a aikin sa? Ki ga fah asarar kuɗin da nayi" Aminiyarta tace "Wallahi ya kware, baki ji yace yarinyar ta rike azkar bane, kuma an dafa ta da kariya tun tana karama shiyasa, kuma ke kika bata komai da sai ki tsaya muji wani Alternative ɗin, amma kika yi saurin cewa a baki maganin juya hankalin ta gashi barayi sun tare mu suka kwace mana komai" Mummy tace "Ni yanzu tsanar da na mata ita da uwarta wallahi har me kaunar su naji na tsane su, Ni dai dan Allah ki taimaka ki samo mana wani malamain" tace "Ni matsala ta da ke saurin ɗaga ma kanki hankali, kuma ki tsaya abi abu a hankula kin ki" Mummy tace "ba dole hankali na ya tashi ba? Aure sai kara matsowa yake yi fa" tace "Khadija kiyi hakuri ki huta zuwa gobe zan baki wani news ɗin".
Leena na shiga IG taga many bloggers sunyi tagging ɗinta, wannan organization ɗin taga ni ashe su suka fara posting kallo picture ɗinta dake jikin flyer ta dinga kallon ita kanta tasan ba karya tayi kyau ba na kaɗan ba shiga tayi page ɗin su tayi godiya, followers ɗin da suka fara following ɗinta a rannan take kallo hankalin ta ya karkata kan wani suna *Malik Areej* a ranta tana mamakin balarabe kuma? Kallon hoton sa dake kan Don tayi kawai ta shiga cikin account ɗin pictures ɗin sa ta gani 1st picture ta shiga sai da taji gaban ta ya faɗi aranta tana ayyanawa kamar wannan mutumin rannan ne, amma kuma gani take kamar ba shi bane ko dan ranan kallon tsoro ta masa, amma ance suna kama ita kuma gani tayi ya ma fita kyau, scrolling ta dinga yi tana kallon pictures dinsa kuma tana mamakin anya ɗan Kaduna ne ganin duk location dinsa Kaduna ne, tayi screenshot ɗin wani picturen sa, kashe datan tayi ta ajiye wayan a gefe..
After some day.. Yau Sunday, ranan walimar Leena..


A danna star sannan a taimaka amin Sharing, thank you.
Follow the JIDDATUL-KHAYR BOOKSHELF DIARIES📚💕! channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z

I just published "Chapter 24" of my story "AGOLA (Behind the palace walls)". https://www.wattpad.com/1547254859?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=jiddatulkhayr

24.....
Yau tunda aka tashi ake ta hada hada a gidan, ko ina banda shaki ba ba abinda yake yi, masu decor sun yi tun da wuri, ga manyan banner guda biyu da aka ajiye a gefen, da akayi decor me ɗauke da picturen Leena da rubutu ajikin "Double Celebration for Leena! Congratulations on Your Secondary School Graduation & Qur'anic Completion"  yanda gidan yake kelli da yadda akayi mata decor sai ka rantse auren ta akeyi. Niswa da ta fito zata kaiwa Hajiya breakfast kallo ɗaya tayi wa compound ɗin ta ɗauke kai, tana sallama Hajiya ta fito tayi shiga na Alfarma na gani na faɗa tana amsa sallaman, Niswa ta gaishe ta Hajiya ta amsa tana cewa "Ni da tun ɗazu nake jiran ku, na ɗauka ai ba yanzu zaku gama ba, shine naje sashin su Leena dan na karya" Niswa bata ce mata komai ba ta je ta ajiye mata akan dinning ta nufi kofa da niyyar fita Hajiya tace "toh ya nagan ki haka? Ku ba zaku bane ?" "Eh" kawai tace wa Hajiya ta fita Hajiya tace ji mugun hali duk uwar ta su ta cusa musu. Jidda da ta gagara ɗauke ido akan Leena sabar wani kyaun ta da ya fito tsantsa cikin Alkebban dake jikin ta, Jiddah tace "SubhanAllah! Wallahi gwara ma da kika ce baki son wani makeup hakan ma kin fi kyau" Murmushi Leena kawai tayi. Ammi na kallon Jidda tace "zaku tafi yanzu ko? Idan yaso ma biyo ku abaya zuwa ɗan anjima" Jidda tace"Toh barin ma driver magana ya karasa ya ɗauke ta anan" sai ga Hajiya ta shigo da sallama duk suka amsa Jidda ta gashe da Hajiya sannan ta wuce dan kiran driver. Bayan driver ya karasa har kusa da kofar su Leena zai ɗauke ta, horn yayi, hakan yasa Jidda na kallon Leena tace "muje, ya karaso" Leena sai duk take jin wani iri haka nan, sun fita Jiddah zata buɗe mata kofar baya ta shiga suka ji Murya Mummy na ihu "Kai, Kai, kai tsaya nan" ta karasa da ɗan saurin ta kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kai tana kallon kallon mai tukin motar tace "ina da aika da zaka je min a can kubau yanzu" Jidda suka haɗa ido da Leena suna ganin ikon Allah jin inda Mummy ta aike sa, Driver ya tsunkuyar da kansa kasa yace "Toh, Hajiya" Jidda na kallon Mummy tace "Mama bari ya ajiye mu kafin ya tafi, tunda mu ba wani wajan ba ne" Mummy ta hayyako mata kamar zata dake ta tace "Sannu Me gidan, nace sannu ko? Ashe motar gidan ku ne ko kuma ke kika ajiye drivern da zan basa umarni kice sai dai yayi naki farko" Driver ya koma mota ya tada sannan ya koma can part ɗin Mummy yana gudun yanzu sai ta iya sa a kore sa, Jidda tana kallon Mummy da mugun mamaki, ita tun lokacin da Leena ta ɓata Sultan ya basu labarin Mummyn taji ta tsane ta, Mummy tace "Saina tsole Miki wannan idon naki da kika zuba min" Jidda ta kama hannun Leena suka shiga ciki, Hajiya ta mike tana kallon su tace "Ku kuma me ya haɗa ku da wancan matar?" Jidda kana ganin ta kasan ranta ya mugun ɓaci tace "Wallahi matar nan taci sa'an yau mutane na na mutunci suna kusa ne, kuma ina ganin girman ta ne, amma da wallahi sai tayi nadama rashin kirkin da ta min, ba ranan da zan shigo gidan nan bata min kallon kaskanci ba" ta zauna rai bace Ammi na kallon Leena tace "me ya haɗa ku?" Leena tace "ta hana driver ne kaimu wai zata aike sa" Ammi tayi shiru Hajiya tace "Lallai matan nan abinda take yi yanzu kuma ya fara yawa" Hajiya zata kira Daddy Ammi ta hana ta Jiddah ta ɗauki yawa ta kira Sadeeq bayan sun gama wayan ta kashe tace "zata ga kuwa mota nagani na faɗa ba ta tsaya tana wa mutane wulakanci akan wannan karamar motar ba" Ammi tace "dan Allah Jidda kiyi hakuri" ba'a ɗau lokaci ba sai ga Sadeeq ya karasa har compound ɗin ya shigo da motar yayi parking, ido ya kurawa bannern Leena sai gashi sun fito Jidda ta buɗe mata backseat ta shiga ita kuma ta zauna a gaba Leena tace "Good morning" yace "sun Miki magana?" tace "Eh, Thank you" be sake cewa komai ba ya tada motar suka kama hanyar fita sai sannan Leena taga decon da kyau sake baki tayi ganin bannern tace "Anty Jidda yaushe kuma akayi banner?" Jidda na Murmushi tace "Ya Sadeeq ne Nima da safe yake faɗa min shine masu decor suka je suka karba" Leena tayi shiru sai ta daga kai ta mirror suka haɗa ido tace "Thank you and may almighty reward you" a takaice yace "the pleasure is mine"
Ana gudanar da bikin yaye ɗalibai abun ba'a cewa komai sai Ma shaa Allah, pictures da Leena tayi ta shiga sending ma Muhammad, Leena ita ce zakaran kwajin gani kamar yadda ta saba a baya lokacin da zata karɓa prize dinta ita da Daddy suka fita tare Leena couldn't help but cry.
Leena zata gun su Ammi ta bar friends ɗinta a wajan da aka tanadar domin su, kamar ance ta kalli mutumin dake gaban ta kallon sa tayi taga yana tsaye ya zuba mata idanu She whispered Malik Areej, ta ɗauke kai zata wuce yace "Congratulations Leena, You're a prodigious talent, and it's inspiring to see" sai sannan ta kalle sa murmushi ɗauke a fuskan sa tace "Thank
End Ads