wanda na masa laifi? Ji yadda kake min magana mana" yace "Ki bari idan na koma gida zan kira ki" daga haka ya katse kiran ya jinginar da kansa ya lumshe ido abokin aikin nasa ya tsaya kallon sa. Bayan ya cire Wayan a kunnan sa yana kallon ta yace "Baby, Kinga wajan aiki suna nema na akan nayi resuming" bata kalle sa ba kuma bata ce masa komai ba, yayi murmushi yana leka fuskan nata yace "wai har yanzu fushi ake da Ni Leena?" still bata ce masa komai ba ya mike yace "I think gobe zaki gida ki ma Ammi sallama next tomorrow in Shaa Allah sai mu tafi Abujan tare, Jiddah ma Nasan ta kusan resuming dan itama pass ta karɓa so ba zaki ji boring ba" sai sannan tace "gida ɗaya kake da Anty Jiddahn?" ya ware ido sai kuma yace "No, ita tana Quarters ɗin su ne, ni kuma ina gida na" daga haka bata sake ce masa komai ba. Da yamma Niswa dake kwance kan 3 seater taji ana sallama amma taki amsa wa, Layla da ta gaji da sallama ta gwada buɗe kofar kawai taga a buɗe yake ta shiga ciki da sallama ganin Niswa kwance kan kujera yasa ta sake baki tana kallon ta da mamaki sai kuma tace "Shegiya dama kina kwance nake doka sallama ba zaki amsa ba?" Sai sannan Niswa ta janye wayan daga fuskar ta ta mata kallo daya sai kuma ta mike ta zauna ta cigaba da danna wayan ta Layla tace "Banga laifin ki ba, ai ba tarbiyya kuka samu ba" sai sannan Niswa ta mike tace "Toh kuma sai kawai ki fara zagi na? Ni Naji Sallamar ki ne?" Layla ta mata tsawa tace "uban ki zanci idan kika ce zaki min ƙauɗin baki anan wajan, Shegiya mara tarbiyya har Ni zaki kalli sabar idon na ki ce zaki fadawa magana?" Mummy ta fito daga dakin ta, Niswa ta wuce dakin ta fuu kamar zata tashi sama, ita tun farko ta tsana wannan Laylan, Mummy tace "Layla ashe kece ke tafe?" ta zauna akan kujera tace "Eh mummy, ina wuni" tace "Lafiya kalau" sai kuma bata sake cewa komai ba Mummy na Murmushi tace "Naji kamar magana kike da Niswa?" ta gyara zaman ta tace "Allah Mummy bata da kunya 'ƴarnan, sallama fah nake yi amma ta share Ni" Mummy tayi murmushi tace "hakuri zakiyi Layla, kanan naki ne sai a hankali" daga haka ta kwalawa me aikin su kira tana zuwa tace "ki kawo mata ruwa" daga haka ta juya, Mummy tace "Rayyan ɗin ma baya nan amma ya kusan dawowa dan lokacin zuwan sa yayi" tana murmushi tace "Ai Ni ba wajan sa nazo ba, ke nazo gaisarwa" Mummy tace "Ayyah, Toh Allah yayi albarka" tace "Amin" tun kafin ta gama rufe baki sai ga Rayyan yayi sallama tun daga bakin kofar Layla take ta kallon sa ganin yadda yayi kyau a kananun kaya shi kuma kallo ɗaya ya mata ya karasa cikin parlorn ya gaida Mummy ta amsa tana tambayar sa ya aiki yace "Alhamdulillah" Layla ta ɗan sauka daga kan cushion ɗin ta gaishe shi, yana danna wayar sa ya amsa ko kallon ta be yi ba daga haka ya wuce ciki, Layla ta fara kuka tace "Mummy ina kingani da idon ki ko? Haka fa yake min ko kallona baya son yi" Mummy da ranta yayi mugun ɓaci tace "Layla kiyi hakuri, kuma bana son Maman ku taji wannan maganar dan Allah" daga haka ta mike tace "ina zuwa" Mummy ta buɗe dakin nasa ta shiga, kana ganin ta kasan ran ta ya ɓaci Rayyan ganin ta a haka da yayi ya mike da sauri kafin yayi magana ta dakatar da shi tace "Rayyan idan har kana son farin cikin na kuma kana son gamawa da duniya lafiya toh sai ka so abinda nake so, anan wallahi muddun kace zaka cigaba da wulakanta ta ban yafe maka ba" zata fita yayi saurin shan gaban ta ya duka ya rike kafafun ta yace "Mummy me yasa kullum kike son min baki akan wasu? Kin zaba ki cigaba da kallon na ina rayuwar da ba na farin cikin ba ne? toh kiyi hakuri" taji tausayin sa har ranta amma bata son nuna masa hakan, tace ka shirya kai zaka mayar da ita" yace mike tsaye yace "toh" ta fito lokacin Layla na waya ganin ta fito yasa ta yanke wayan, ta mike tace "zan tafi Mummy" Mummy tace "ki ɗan zauna Kinsan yanzu ya dawo a aiki bari ya wasa ruwa sai ya maida ki gidan" ta zauna tace "toh shikenan" bayan wajan 30 mins sai ga Rayyan ya fito fuskar sa ba yabo b fallasa yana kallon ta yace "Mu tafi" daga haka ya wuce abinsa tama Mummy sallama sannan ta bi bayan sa da sauri, ta buɗe front seat ta shiga, tun da suka fara tafiya ba wanda yace da wani kala sai can tace "Ya Rayyan, wai saboda ina son ka ne yasa kake wulakanta Ni?" Ya ɗan kalle ta sai ya mayar da kansa kan titin yace "Haka kike gani?" tace "gashi ina gani ƙarara rubuce a fuskan ka, kamar wadda za'awa auren dole? Haba mana try to be romantic mana" yace "Ko?" tace "i mean it" yace "Okay" daga haka ba wanda ya sake magana, bayan yayi dropping dinta yace "ki gaida Mama" tace "toh". Bayan Leena ta idar da sallar Asr tana evening zikr ɗinta sai ga Sadeeq ya shigo tana kallon sa ta tsunkuyar da kanta yace "wife kinyi bakuwa" tace "bakuwa kuma?" yace "Eh tana parlor" tace "babba ce?" Yace "No, mate ɗinki ce" tayi shiru tace "kila Zahra ce" ta mike yace "Zahra friend ɗinki ai na santa" da sauri ta juya tana kallon sa tace "kenan ba ita bace ?" yace "Sure" ta juya zata ajiye counter dinta akan mirror yayi hugging dinga ta baya da sauri ta janye kanta ta bata rai ita yanzu ma tsoro yake bata ma, murmushi ya mata, taki mayar masa, daga haka ta fita zuwa parlor, tunda ta shiga parlorn take kallon ta da mugun mamaki har ta isa cikin parlorn tana son gaskata abinda idon ta yake gaya mata, kallon ta take daga sama har kasa, taci wani uban masassan straight gown, gata da hips daya sa straight gown din ya mata kyau nan da nan Leena taji wani kishi wato Sadeeq ya ganta a haka kenan?, Niswa ta yanke mata tunanin ta tace "Kamar kina mamaki da zuwa na fah? Leena tace "Ya kike? Ya su Mummy" tace "kalau" Leena ta yi shiru tana mamakin zuwan ta Niswa tayi murmushi tace "Leena matar aure" Leena ta ɗan kalle ta, ta cigaba tace "Na ɗauka ai har zuwa sannan kina kuka sai naga akasin haka, ashe de kina son auren kike ta raina ma mutane hankali" Leena tace "Ba wanda nace masa bana so, kawai dai saboda na fi shakuwa da Muhammad ne than Sadeeq, beside na ta taso da son sa a raina" Niswa tayi ƴar dariya tace "Allah ko? naga alama kuwa, toh ko ruwa da abinci ba zaki bani bane ko haka ake wa baki?" Leena ta tashi ta dauko mana ruwa ta ajiye mata ita har sannan bata daina mamakin zuwan ta ba, Niswa ta ajiye veil ɗinta a gefe ta mike tace "Kinga yunwa nake ji barin dafa ko da indomie ne" Leena tace "Ai ban fara girki ba" tace "Toh ai dama bance ke ba, na'isa nasa Amarya aiki?" Leena tace "Toh ai saboda baya so nayi girki da kaina siyasa ko gas be yi refilling ba" ta rike haɓa tace "Toh fah" sai kuma ta koma ta zauna, Leena tana ta Allah, Allah ta tafi taga kamar bata da niyyar tafiya daga karshe ma ta mike a kan cushion ɗin ta fara chatting, Sadeeq ya fito daga dakin Leena yana kallon ta yace "Baby, zan ɗan fita na dawo" wuff Niswa ta mike, tana wani rangwaɗa, daga haka Sadeeq ya fita, Niswa ta dauki jakkan ta da veil ɗin ta tace "See yah" daga haka ta fita da saurin ta, Leena taji hawaye yana gangaro mata da sauri tayi bakin kofa ta tsaya tana kallon ta har ta fita. Sadeeq na kokari tafiya Niswa tayi saurin tsayar da shi ta kashe murya tace "Please kayi min lift mana, kasan unguwar ta ku ba'a samun taxi" Strictly yake kallon tace yace "Saboda Ni na kawo ki?" tace "Toh ai taimako zaka m.." tun kafin ta karasa magana ya ja motar sa a mugun speed, Nisa ta bi Motan nasa da mugun kallo tana jin wani bakin ciki....
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
*I'm touched by Ur concern and all the get well wishes. Thank you for being so amazing! I love and cherish every single one of you, and I'm grateful for your kindness. You're all truly special, and I appreciate each and every one of you Dudes. Oh, and I'm now doing fine, Alhamdulillah.*
_I dedicate this Chapter to you Fatima isma'eel Ibrahim (Noor Imaan)_
34.........
Tunda Sadeeq ya dawo Leena taki kula shi, da farko shima ya so share ta sai yaga ba zai iya ba, ya bita dakin ta, tana zaune akan darduma daga gani bata jima da idar da Sallah ba, har inda take zaune ya karasa ya zauna yana facing dinta ya kama fuskan ta da hannu biyu yana kallon ta yace "Toh me kuma nayi ma wife ɗina?" Nan da nan Leena ta fashe masa da kuka, ya ɗan ja baya yana kallon ta sai kuma ya rike fuskan ta yana kallon ta a ɗan ruɗe yace "What is it, Baby?" ta sakaita kukan ta tace "kai ka mayar da Niswa gida ko?" ya yamutsa fuska yace "who is she?" tace "Kanwar Rayyan da ɗazu ta zo mana" be san sanda ya fara dariya ba, shi gaba daya abun da ya gani a fuskar Leena kishi ne, ita kuma ganin ya fara dariya ya sa taji haushi ta mike zata bar wajan yayi saurin riko ta yayi hugging ɗin ta yadda ba zata iya kwace kanta ba yace "Haba dear, I thought kin san hali na, ni ba ma zance miki Nasan fuskar ta ba ma yanzu haka, and I don't want to know, to Meyasa zan mata lift? Ko kin manta Sadeeq ne?" Sai yanzu Leena taji hankalin ta ya kwanta, kuma Sadeeq din da ta sani ta san ba zai kula ta ba, tayi shiru tana shakan kamshin sa me daɗi. Washe gari tun da wuri Leena ta shirya, tun kafin Sadeeq ya karasa parking Leena take kokarin buɗe kofa, ya juya yana kallonta yace "ki gaida min da Ammi na, anjima in shaa Allah zan shigo na gaishe ta" ta gyada masa kai tana murmushi tace "Nima ka gaishe min da Mami" be amsa mata ba sai kallon ta da yake yi, tace "what?" yayi frown face dinsa yadda take yi a baya tayi dariya ta sauka daga motar tana kallon sa, yayi kasa da murya yace "i'll miss you so much, boo" waving dinsa tayi ta wuce gidan da ɗan saurin ta, ta gashi da masu gadi sannan ta wuce ciki ta buɗe kofar parlorn na su, su anty Binta dake breakfast a parlorn suka daga kai suna kallon ta, Leena ta hango Ammi dake dinning area ita da Ayaan da gudu ta tsallake su Anty Binta ta suka bita da ido taje ta rungume Ammi, Ammi dan shock ta kasa magana ma, Leena tace "I miss you soooo much, Ammi na" Ayaan yace "Addah, i miss you, too" ta sake Ammi tayi hugging ɗin sa, Ammi sai kallon ta take tace "Leena, ina lafiya dai? Leena ta gyada ma Ammi kai tace "Eh, Lafiya kalau" Leena da take rike da hannun Ayaan zata koma wajan su Anty Mairamah ta gaishe su Ammi tace "Toh me kuma na zuwa?" Leena ta tsaya tana kallon Ammi tace "Ammi baki son gani na ne? Ashe ma ba kiyi missing dina ba" Ammi tace "Toh bamu waya ne?" Leena tayi ƴar dariya tace "kai Ammi, an fa kirasa ne a wajan aiki shine zamu koma Abujan tare shine yace na zo na Miki sallama" Ammi tace "Okay! Ayyah, toh Allah ya taimaka" su Anty Binta suka fara dariya Leena ta koma cikin parlorn tana gaishe su, sai kuma ta tsaya kallon su tace "Toh anty me nayi kike dariya?" Anty Binta tace "A'a baki yi komai ba Leena" Ayaan ya hau jikin ta yace "Addah tare zamu tafi?" Leena ta masa magana a kunne, Ammi sai bin Leena take da idanu, haka su Anty Binta ma, Leena zata shige dakin ta tace "I'm finally back in my own space, it feels so good to be home" daga haka ta shige dakin na ta, Anty Mairamah tayi ƴar dariya tana kallon Ammi da ta dawo cikin parlorn da kallon tace "Toh Yaya sai ki kwantar da hankalin ki yanzu, Kinga dai Leena alamar ma tana cikin farin ciki ne" Ammi kawai tayi murmushi ta mike ta wuce dakin Leena, Leena da har ta kwanta kan gadon ta tana tuna memories ɗin baya ta daga kai tana kallon Ammi, Ammi tace "Leena is good ki shiga wajan Hajiya yanzu ko?" Leena tace "Ammi da sassafen nan?" Ammi ta Harare ta tace "yanzu ne sassafe? Za ki tashi ne ko sai taji labarin kin shigo sai ita da kanta ta zo gaishe ki?" Leena tayi dariya tace "zuwa 11am zan shiga wallahi, amma yanzu Ammi barin ɗanyi bacci" Ammi tace "wato har yanzu kina nan da wannan baccin na ki ko?" daga haka ta bar kofar dakin. Sadeeq yace "ke kaɗai ne a gidan kenan?" Jiddah ta gyada kai tace "duk sun tafi aiki" daga haka ya fara haurawa stairs tayi gyaran murya tace "Ya Sadeeq" ya juyo alamar yana jin ta tace "shekaran jiya fah naga wata me kama dakai da kuma me kama da Leena a Couples Date Spot" kallon daya ya mata ya cigaba da haura stairs ɗin sa, Jiddah ta fara dariya, ya dauki abinda zai dauka ya sauko, ganin ba kowa yasa kawai ya koma gidan sa. Around 11am Leena ta fito zata part din Hajiya anan compound ta haɗu da Niswa, Niswa ta buɗe ido da ta ganta tace "Yaushe kika zo?" Leena tace "Ɗazu" daga haka ta cigaba da tafiya Niswa tace "Ikon Allah! Kamar baki son magana" Leena ta tsaya tana kallon ta tace "Thought ai shikenan" tana maganar ne babu yabo ba fallasa Niswa ta girgiza kai tace "Amma zaki wuni mana ko? Sai dare zaki tafi ina? Kin san gida da daɗi" Leena ta gyada mata kai kawai ta cigaba da tafiyan ta Niswa ta bita da harara daga haka ta koma bangaren su da sauri. Leena tayi sallama a kofar parlorn Hajiya ta shiga da gudu tayi hugging ɗin ta dake zaune a parlorn ta tace "Hajiya I really miss you" Hajiya tace "Dan Allah cika Ni, kwana biyu Allah yasa kin daina wannan karyan turanci daga aure kuma zaki fara" Leena na dariya, ɗaga kai da zata yi ta haɗa ido da Rayyan dake zaune, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa itama ta ɗauke kanta tace "Yaya ina wuni" be kalle ta ba yace "Lafiya" daga haka ya mike yace "toh Hajiya barin tafi" daga haka ya fita, Hajiya tana kallon Leena tayi kasa da murya tace "ki gode Allah ƴarnan, samun mahaifiya irin uwar ki kam sai an tona, yanzu kaf duniyan nan ba wanda nake tausayi kamar Riyan wallahi, yaro ya dade be yi aure ba ace a bari ya zabi zaɓin sa amma inaa uwar ta kawo masa wata, yanzu haka dazu Daddyn ku yace wai bikin saura sati biyu" Leena tayi shiru tana sauraran Hajiya a hankali tace "Allah basu zaman lafiya" Hajiya tace "Toh Amin, amma shi kam yace min baya son ta, uwar ne ke son aure, kuma kwatakwata bana kaunar ita mahaifiyar yarinyar amma ya zamu yi?" Leena tayi shiru tana kallon Hajiya. Sadeeq da har bacci ya fara ɗaukan sa yaji knocking ɗin da akeyi yayi yawa hakan yasa ya mike ya saka zallabiyan sa ya nufi compound dan zuwa ya buɗe gate ɗin, bayan ya buɗe daga sama har kasa yake kallon ta yace "Lafiya?" ta kashe murya tace "Toh kabari na shiga mana amma ka wani tare hanya" strictly yace "Who are you?" ta sake baki tana kallon sa tace "Leena's elder sister mana" wani irin kallon ya mata and he slammed the door in her face ta ja baya da sauri tana mamakin abinda ya mata. Leena dake ta game da Ayaan Ammi tace mata "Leena Daddyn ku ya dawo kije ki gaishe shi" Leena ta mike tace "Toh" tana kallon Ayaan tace "tashi ka raka Ni" ya mike ta kama hannun sa suka wuce har part ɗin Daddy tana sallama Ayaan ya shige da gudu ya fada kan Daddy da ke cin abincin, Leena na biye da shi a baya Daddy na masa wasa yace "Oh yau Addah ta zo shiyasa ban ganka ba ko?" Yana dariya yace "Eh Daddy" Leena tsintan kanta tayi tana jin kunyan sa, ta sauke kai ta gaishe shi, ya amsa yace "Ya me gidan na ki?" Leena tayi shiru kuma taki ta daga kai, Daddy yayi dariya yace "ina ba wata matsala ko?" tace "Eh Daddy" yace "Ma Shaa Allah" ta ɗan zauna sai kuma ta mike ta masa sallama ta fi, tana fita taga Niswa ta shigo gidan Fuu kamar zata tashi sama, ta bi ta da kallo tana shiga parlorn su tagan su suna hira Leena ta zauna tace "Yauwa Anty Binta kin san ranan kawai sai ga Niswa ta zo min wai, ita da fah da can ko magana bata min" Basu Anty Binta ba hatta Ammi dake can zaune sai data ɗago tana kallon Leena da mamaki, har haɗa baki aunts dinta suka yi wajen cewa "Uwar me taje yi kuma?" Leena ta buɗe hannu alamar bata sani ba Anty Binta tace "Daga yau duk