x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 53 - AGOLA free pages

  • 156001 words
  • 159000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
katse. Daddy yace "Naji har ka samu gida ko?" Yace "Eh Daddy" Daddy yace "Toh ka sake gidan, dan akwai gida na da na sa already anyi mata jere a can" yayi shiru sai kuma ya ɗago ya kalli Daddy, haka nan yaji ba zai iya gardama da shi ba kawai sai ya fara masa godiya. Washe gari da yamma Leena ta fito daga gidan da ake mata spa, dake a unguwar su ne yasa kawai ta ke tafiya da kafa ta karasa da kafa, tun da ta fito take tafiya absent-minded, tana cikin tafiya ta ji mota na bin ta a baya amma sai bata damu ba kuma bata ko juya ba, dan ita yanzu damuwar gaban ta ya ishe ta, tana ji mota ya parka da sauri ya karasa inda take ya kama kafaɗar ta ya juyar da ita yadda zata na facing dinsa, a fusace ta juya dan ganin wanene amma sai tayi mutuwar tsaye ganin Sadeeq ne, idon sa yayi mugun Jaa yace "So, You're getting married Leena?" ta dinga kallon sa ba ko kiftawa tace "Are you Okay da zaka rike Ni haka?" Yace "ban sani ba, just tell me aure zakiyi?" Ta dinga kallon sa sai kuma tace "tunda ka sani me kuma na tambaya ta?" ta karasa maganar tana kokarin kwace kanta daga gare sa amma ta kasa saboda rukon da ya mata, yace "you're going to choose one, ko your so called aure, ko kuma ki cigaba da rike Nawan inma gidan Baban sa zaki koma ya fi miki" Leena ta dinga masa wani kallo tace "Bangane ba? Yace "ai ba zaki taɓa gane wa ba Leena! Wallahi kina aure zan dauke ɗa na, just know this" ta tsaya tana kallon sa da wani expression tace "ka min sakin wulakanci a lokacin da nake tsananin neman taimako, sannan ko da wasa baka taɓa kayi nadama ba ko da bani hakuri ko ka nemi da na koma gidan ka, amma ji yadda kake magana please, baka ji kunya ba?" yace "Leena.." sai kuma ya bi inda take kallo babu kiftawa, yaga Malik ne ke tafiya da alama dai gidan su Leenan za shi,yadda yake kallon ta haka itama ke kallon sa, ta kwace hannun ta a hannun Sadeeq amma inaa har ya juya, ta tsaya kallon Sadeeq sai kuma ta bi bayan Malik da saurin ta amma har ya fice a layin dan da zuciya ya juya...



Jiddatulkhayr
08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*



Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes

Young talented writers association (YOTA)


Chapter 62


Tunda Leena ta koma gida ɗakin ta ta wuce without letting Ammi notice her, bakin gado ta zauna ta zabga tagumi, Maganganun Sadeeq ne yake dawo mata, ta rufe fuskan ta fashe da kuka, sosai take kukan dan yanzu kuma bata san what next ba, jin ana kiran sallahr Magrib yasa ta wuce toilet tayi alwala ta fito zata shimfiɗa sallaya sai ga Ammi ta buɗe takin tace "Shi ne zaki shigo ba tare da magana ba?" tana avoiding eye contact da Ammi tace "kai na ke ciwo Shiyasa ban yi magana ba" Ammi tace "sai ki sha magani ai" daga haka ta wuce dan itama sallahr zata yi. Dakyar Malik ya iya komawa gida, dan wani irin jiri yake ji ga yadda idanuwan sa ya masa nawi har wani dishi dishi yake gani, ya buɗe kofar gidan ya shiga ba tare da ya lura da Umma da few mutanen da ke tsakar gidan ba, direct ɗakin sa ya wuce, yana shiga ya faɗa kan gadon sa, yayi nisa sosai cikin tunani har yana ganin is like bai kyauta mata ba, ko kuma yayi gaggawa, which is ba son ran sa bane face yana tsoron rasa ta, "Wai lafiya kake Malik?" Ya tsinkaye murya Umma a kunnuwan sa, ya mike zaune yana mai sauke idon sa kasa yace "Lafiya Umma" tace "kar ya kake Malik, Ni zaka ma karya? Ko kuma abu zaka fara ɓoye min?" Ya ɗan kalle ta sai kuma yace "Umma babu komai fa nace miki" ta dinga kallon sa sai kuma ta mike ba tare da ta kuma ce masa komai ba, a hankali yace "Umma me yasa baki son aure na da Leena?" Ta kalle sa sai kuma ta koma ta zauna tace "Ina tsoro ne Malik, Ina tsoron wulakanci ne da abun da bamu sani ba nan gaba zai faru" ya ɗaga fararen idanun sa da suka zama ja ya zuba mata dan bai fahimci me take nufi ba yace "Wulakanci kuma Umma? Sannan abun da zai faru gaba da bamu sani ba?" taki kallon sa tana kallon wani waje ya sake je fa mata tambaya "Umma ko akwai wani abu da ya kamata na sani ne?" Ta kalle sa tace "Me ya kamata ka sani kuma? Kawai ka san yadda masu kuɗi suke ne, Ni kuma bana fatan ka faɗa cikin su suna maka gori" ya dinga kallon ta zuciyar sa cike da tambayoyi kala da iri amma baya jin zai iya mata waɗannan tambayoyin a wannan lokacin, Umma ta mike tace "Ka tabbatar kaci abinci ka" daga haka ta wuce ba tare da ta sake kallon sa ba, ya bi ta da idanu har ta rufe masa kofar sannan ya jingina da wall ɗin ɗakin yana jin zuciyar sa na kuna, wayan sa ya jawo kamar zai kira ta sai kuma ya yi cilli da wayar ya mike dan yin alwala. Leena gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi ganin har zata kwanta bata ga kiran Malik ko text ɗin sa ba, which is unusual to her, bayan tayi alwalar bacci ta shafa coconut oil ta wuce kan gadon ta tayi addu'a sannan ta kwanta amma gaba ɗaya sai ji take kamar rana ne dan babu ko ɗigon bacci a idon ta, tayi ta juye juye amma bacci ya kaurace mata, daga karshe ta mike ta zauna kawai ji tayi ta fashe da kuka, ta rasa me ke damun ta, zuciyar ta yayi mata nawi sosai, ga kuma shirun da Malik ya mata wanda ya kara mata damuwar ta at least ya kira ko bayani ne ta masa amma shi bai damu ba balle ya kira, da ta tuna hakan sai taji sabon kuka, tana nan a haka har ta kai karfe ukun dare, kawai ta mike ta wuce toilet bata daɗe ba ta fito da alwala, shimfiɗa sallaya tayi ta yi raka'a biyu tana addu'an Allah ya shige lamarin ta, bayan ta idar ta kwanta kan sallayar nan da nan bacci ya ɗauke ta. Yau tun da ta tashi gaba ɗaya jikin ta a mace yake, musamman idan ta tuna gobe Friday shine ranan ɗaura auren ta a karo na biyu, duk da ba wai da mutane a gidan bane dan Ammi bata gayyaci kowa ba, amma hakan bai sai wasu few neighbors ɗinsu sun shigo ba, ganin babu komai hakan yasa suka koma. Tun safe Ammi ke lura da yanayin Leena amma sai ta alakan ta hakan da ko fargaba ne, ɗaukan breakfast ɗin ta tayi ta wuce dakin ta, Leena ta ɗaga kai tana kallon Ammi har ta karasa ta zauna, tace "Leena baki yi breakfast ba fa" ta kalli Ammi sai kuma ta sauke idon ta kasa tace "Zan yi Ammi, kawai bana jin yunwa ne" Ammi ta kama hannun ta tace "Toh meke damun ki kuma?" Ta girgiza mata kai tace "Ammi ba komai" Ammi tace "Kalle ni kice min ba komai" ta gagara ɗaga ido ta kalle ta dan ma wani sabon kukan take ji, a hankali tace "Ammi kawai ina tsoro ne, ina tsoron wani sabon rayuwar kuma zan fara, ban san ko nayi gaggawar tunanin sake aure ba, kamata yayi ba yanzu ba tukun nan" a hankali Ammi tace "Koma menene Leena baki isa canza ƙaddarar ki ba, dole ki zama mai karɓan duk wani kaddara da Allah ya rubuta miki, baki isa canzawa ba Leena, mutuwar auren ki kuma ba dabaran ki bane Allah ya riga da ya rubuta aure ya kare tsakanin ku, kuma ba yadda zaki yi dole ki hakura, kuma ba wai wani abu bane na jin kunya ko mene saboda ba akan ki aka fara ba, abu na karshe da zan faɗa miki shine kiyi addu'a, ki roka Allah ya saka wa zaman ku Albarka yasa wa junan ku so, kauna da kuma juriyar junan ku, ri roki Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi duk da cewa ina miki addu'an amma kema ki kara" Leena gaɓa ɗaya jikin ta ya gama mutuwa, maganganun Ammi ba kaɗan ba ya dake ta, a hankali tace "In Shaa Allah, Ammi" Ammi ta mike tace "Make sure kinyi breakfast" daga haka ta fita, ta sauke ajiyar zuciya tana jawo wayan ta dan kallon ko Malik ya tura mata sako, da farko ta damu amma maganganun Ammi ya kwantar mata da hankali, ganin har sannan ba kiran sa balle missed call ɗin sa yasa ta ajiye wayar.  Da yamma Leena na zaune ɗakin Ammi tana evening Zikr ɗinta, kuma har sannan bata ga call ko message ɗin Malik ba,  Ammi ta leƙa ɗakin tace "Leena ki fito kina da bako" Leena ta ajiye Hisnul-Muslim ɗin hannun ta tana kallon Ammi da mamaki tace "Waye kuma Ammi?" Ammi tace "Ki fito ni ina zan san waye ne, Harisu ne ya sanar da ni" Leena ta gyaɗa kai ta mike, tace "Maybe kafin ki dawo zan wuce kasuwar" tace "Toh Ammi" daga haka Ammi ta bar wajan, tana tunanin toh kuma waye ne? Sai kuma tunanin kila Malik ne yasa ta fita, a compound ta ga Harisu zai wuce backyard ta tsaya tana kallon sa tace "Malam Harisu ina bakon nawa?" yace "Hajiya yana garden" daga haka ta kama hanyar garden, duk da ya bada baya yana tsaye hannun sa ɗaya yana cikin aljihun sa, amma hakan bai hana ta gane sa ba, nan take taji zuciyar ta ya fara bugawa da karfi, taji kamar zata faɗi, tunanin ta juya ta koma ta fara, hakan yasa kawai ta juya amma sai kuma shima ya riga da ya juyo, kallon ta yayi calmly yace "Leena!" Cak ta tsaya a hankali ta juya ta sauke idon ta a nasa da sauri ta ɗauke kanta daga kallon sa, bata karasa ba tana tsaye nan wajan, ya taka ya karasa har inda take yace "So, tafiya za kiyi?" Bata kalle sa ba tace "Ina da abin yi, ka faɗi dalilin nema na da kake yi" calmly yace"Leena mayasa zaki yi aure? Do you think you made the right decision? Baki tunanin future ɗin mu gaba ki ɗaya? Ba zaki tausaya min da Nawaf ba? Think about it, please" Tunda ya fara magana take kallon sa da mamaki meanwhile tana hana kanta kukan da ya so ya fara zuba, ta buɗe baki ta soma magana "Me zanyi tunani akai? Decision ɗin da na yanke In Shaa Allah is the best decision, duk abun da kake faɗa cewa you did that unintentionally to me ka taɓa texting ɗina ka cemin sorry about that? Ka taɓa nema na ka bani hakuri sannan ka nuna min cewa ba intention ɗin ka bane? Sau nawa ka zo ka duba Nawaf? ko ance maka kuɗin muke bukata da zaka na tura kuɗi without knowing Yaya yake, Imagine for Once baka taɓa min magana akan matsalar nan ba, So! Everything you did, I’ll assume it was intentional, since you’ve shown no remorse or explanation for what happened" ya dinga kallon ta ba ya ko kiftawa cos bai ɗauka abun har haka ba, nan da nan jikin sa yayi sanyi yace "Amma kin san ina son ki Leena, ki duba Nawaf bani ba ki tausaya mana ki fasa wannan auren na ki, kin san Ni ba zan taɓa barin ki kiyi rayuwar kunci ba, please Leena, think about it, bana so Nawaf ya taso as Agola shiyasa kika ga shekarar Jiya nace miki zan ɗauke sa idan aure zaki yi, kin san yadda ake ji, kin san raɗaɗin hakan, Ni kuma ba zan iya barin sa yayi wannan tasowan ba sannan ba zan so na raba ki da shi ba" wani murmushi me hawaye tayi tace "Good, sai yanzu ne zaka yi tunanin hakan? Wai Uncle kunya ta kake ji or what? Yanzu duk rayuwar da muka yi a baya dan ka zo kace kana so na koma gidan ka kana tunanin hakan zai jawo maka raini ne? Haba mana, dan Allah a ganin ka hakan yayi making sense? Ko ka manta akwai ɗa ne wai a tsakanin mu" ya marairace mata yace "I know I acted foolishly da rashin tunani but ai yanzun ma is not too late" Leena ta girgiza masa kai tace "Idan kai ne a shoes ɗin sa ya zaka ji? Nasan zafin a fasa auren ka, so ba zan taɓa zama sillar zubar hawayen wani ba, idan kana da abun cewa you can say it out dan zan koma ciki" ya dinga kallon ta ita kuma taki yarda ta kalle sa dan tasan zuciyar ta zata iya karye wa, ga mamakin ta kawai kallon sa tayi ya tsuguna kan gwiwowin sa, ta sake baki tana kallon sa yace "I'm begging you Leena ki fasa wannan auren na ki, don't break my heart for the second time" ta dinga kallon sa, wato ma itace tayi breaking heart ɗin sa ta girgiza kai bata son ta fashe da kukan daya taho mata, ta juya zata tafi ta tsinkayi muryan sa "Then, kar ki tafi min da ɗana gidan wani" ta juya ta kalle sa sai kuma ta bar wajan da gudu, a compound ta bugi mutu, ta ɗaga kai ta kalli Rayyan ne, ya rike ta ta kwace kanta ta wuce cikin gidan su tana kuka, Sadeeq na buɗe gate sai ga Malik dake kokarin shiga Zahra na biye da shi a baya, kallon juna suka tsaya yi, Malik ya ɗauke kansa, Sadeeq ya koma motar sa ya bar wajan da mugun gudu, Zahra dake jiran Malik ya shiga ta samu ta shiga saboda shine a gaban ta ga Mamakin ta kawai taga shima ya koma, sai kawai ta karasa cikin gidan, bayan tayi sallama Ayaan da yake wasa da Nawaf a parlorn ya amsa yace "Anty Zahra Oyoyo" ta karasa cikin parlorn tace "Ina Ammi?" Yace "Ta tafi kasuwa" tace "Addah Leena kuma fah?" Yace "Tana dakin ta" daga haka ta wuce dakin Leena, cak ta tsaya a bakin kofar ganin Leena tana kuka sai kuma ta karasa cikin ɗakin da sauri tace "Leena lafiya?" Leena ta daga kanta sai kuma ta share hawayen ta tace "Bakomai, sannu da zuwa" Zahra ta mata wani kallo sannan ta zauna kan gadon tana kallon ta tace "Ban gane Bakomai ba? Bayan gashi kina kuka" Leena tace "Bansan ya zaki fahimta bane, Nima na rasa tunanin me zan yi Zahra" Zahra tace "Ko dai dangane da Sadeeq da Malik ne?" Leena ta dinga kallon ta sai kuma tace "Ya akayi kika tsani?" Zahra tace "Yanzu da zan shigo naga Sadeeq yana fita dama kuma na haɗu da Malik a kofar gidan so naga irin kallon da suka ma juna and then Malik ya juya ya fasa shigowa" Leena ta dinga kallon ta tace "Kina nufin Malik yazo ya koma saboda ganin Sadeeq?" Zahra tace "Eh, amma me ke faruwa ne Leena?" Leena ta bata labarin komai, Zahra ta girgiza kai tace "Leena Ni ba zan san abin da ke cikin zuciyar ki ba, but to be sincere idan Ni ce zan iya komawa gidan tsohon miji na, saboda abun da Sadeeq yace haka ne, ke kinyi tasowan Agolan ci kin san yadda raɗaɗin hakan yake, kuma sa'an da kika ci daga Daddy har Hajiya suna son ki, so ke yanzu baki san wani gida zaki shiga ba, ba lalle a so ɗan ki ba, amma maganar gaskiya Sadeeq bai kyauta ba, ya san yana son ki koma gidan sa shine ba zai fada miki ba har sai da zaki kara wani auren? Kuma yanzu idan kika ki auren Malik kin karya masa zuciya, kuma baki kyauta masa ba" Leena tace "Ni yanzu ban san yadda zan yi bane, ban san wani tunani guda ɗaya zan yi ba" Zahra tace "Addu'a shine kawai mafita" Leena tace "Wallahi kullum ina yi, ba na barin tahajjud ma, amma Kinga kuma Malik ne, gashi har gobe ne Fridayn, kuma ni gaskiya ba zan iya rabuwa da Nawaf ba" ta karasa maganar tana dafe kanta da hannu bibbiyu, Zahra tace "But ki kira Malik, kar ki bari zargin sa yayi tasiri tun da kince tun wannan incident ɗin baku sake haduwa ba balle waya and yanzu ma kin ga ya zo kuma ya sake haduwa da Sadeeq din, kinga zai yi tunanin saboda Sadeeq ne baki kiran sa" Leena ta suke ajiyar zuciya, tace "Toh me zance masa?" Zahra tace "Idan kika kira sa shi da kansa ma zai dauko maganar, so duk yadda zai ce just be real to him, ki gwada masa baki san da zuwan Sadeeq din ba" Leena tayi shiru, Zahra tace "Ki kira Leena, ya kamata Ku sasanta kan ku, kar ki manta gobe ne fa daurin aure" a hankali tace "Toh, amma zan bari idan ya koma gida" Zahra tace "But kar ki sake har sai gobe" Sallaman Ammi suka jiyo, duk suka mike zuwa parlorn, bayan sun gaishe ta, Zahra ta mike tace "Barin tafi Ammi" Ammi tace "Saboda kin ganni zaki tafi?" Zahra tayi dariya tace "Wallahi ba haka bane Ammi, an kusan kiran Magrib ne, bana so kuma a kira ina waje" Ammi tace "Toh Shikenan, ki gaishe min da Maman ki" tace "In Shaa Allah" Leena ta ɗan raka ta sannan ta dawo gidan.

#Jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Young talented writers association (YOTA)


Chapter 63

Leena na idar da sallahr Magrib ko tashi akan dadduman bata yi ba sai ga kiran Rayyan, tayi receiving da sallama a bakin ta yace "ki fito compound ki same ni" a hankali tace "Toh" ya katse kiran, ta mike ta fito parlorn, Ammi
End Ads