ke faruwa wanda a lokacin Sarauniya Zainabu kiris ya rage bata tsine mata ba wanda daga baya kuma su kan su suka yi ta samun sa'in sa sakanin su da Waziri wanda abin ba kyan ji daga nan kuma Masarautar ta ɗauki mata ki akan su sannan duk suka yi nisa da Masarautar" ta numfasa tana kallon Leena wanda take jin soyayyar ta yana huda zuciyar ta dan tasan cewa tabbas jinin ta ne, a hankali ta kama hannun Leena wanda Leenan ma ta zuba mata ido tana kallon kamar da take da Malik da kuma Suhaif, a hankali ta ɗora "Da akwai wani lokaci wanda duk muna zaune a Parlorn muna kallon right child advocacy da Leena ke gabatarwa, tun daga lokacin nasan cewa ita ɗin jinin nane, da nayi magana sai suka gwada min cewa kila kama ne amma Ni na san ba haka bane shiyasa nace su nemo min ita duk inda take a faɗin duniyar nan" At this point Mummy sai zara ido take tana bin kowa da kallo, Mama kuwa ita ma ta shiga ruɗani amma tana hoping Leena jinin su ne dan taga ya Mama zata yi, Mai martaba yayi gyaran murya yana kallon su a hankali sannan ya maida kallon sa ga Umma da Abbah da aka ce masa sune mariqan Malik ne, yace "Ko zamu iya jin yadda kuka samu Suhail?" Umma ta fashe da wani sabon kukan, Abbah ya ɗaga kansa yana kallon Mai martaba Sannan ya numfasa...... Yana zaune akan wani bola inda kurciyan ta tsaya a kan wata bishiya, dake karamar hukumar Rimi a jihar Kaduna, duk yaran wajan shi kaɗai suke tsokana wanda har sannan baya kula su yana rike gam da Suhail, wani babban motar ce ta parka a wajan ta sauka tana kallon yaran lokacin ɗaya mutumin ya daka musu tsawa wanda hakan yasa duk suka tsorata suka bar wajan, Mutumin ya karasa inda Yarima yake zaune ga kuma Suhail a jikin sa, yace "Bawan Allah me kake anan kuma?" Yarima ya ɗaga kai ya Kalle sa sai kuma ya kwashe da dariya, nan wannan Mutumin ya fahimci ba kalau ba, ya mike ya koma wajan motar sa ya ɗauko masa wani ruwan gora ya mika masa amma ga mamakin sa sai yaga ya buɗe ruwan ya bawa Suhail da har ya gaji da kukan yunwa, nan take Suhail ya dinga kwankwaɗan ruwa sai kuma ya cire masa a baki, har sannan Mutumin yana tsaye yana kallon ikon Allah, bai tashi mamaki ba sai daya ga yana alwala da sauran ruwan, at this point ya gama shiga ruɗani dan bai san ko yana da hankali ko babu ba, a hankali ya taka zai janye Suhail da zai sa ƙasa a bakin sa kawai Yarima yayi kansa kamar zai dake sa wanda hakan yasa mutumin ja baya da sauri saura kaɗan wani mashin ya buge sa wanda mutumin mashin ɗin yaja burki, Matar bayan sa tace "Malam lafiya?" amma bai kula ta ba, wanda aka kusa bigewa ya tsaya yana kallon sa yace "kayi hakuri ban kula da kai bane malam" Malam ya gyaɗa masa kai yace "Bakomai" sai kuma ya kalli Yarima wanda ya sake mayar da Suhail jikin sa yace "Amma lafiya? Me kake anan wajan?" Mutumin yace "Wallahi yau wajan kwana biyu idan nazo wucewa nake ganin mutumin nan anan wajan, sai na fahimci ba lafiya ba" Kawai matar da ke bayan mashin ɗin ta sauka tana kallon Malam tace "Malam idan ba'a son yaron ina so dan Allah" ya mata wani kallo yace "kin san sane?" Mutumin yace "Toh ko za'a kai shi wajan Mai gari ne?" Malam yace "Toh ina ga hakan zai fi, idan da wani taimako da za'a masa sai a masa kawai" a haka dai suka tsayar da magana har aka je wajan Mai gari. Bayan kwana biyu duk suka fahimci kurciya aka masa wanda hakan yasa suka rike sa sannan aka kama kurciyan aka rufe wanda a lokacin bata da lafiya, Har sannan Matar Malam tana kan rokan Malam da su karbi Suhail wanda shi bai so ba dan yana tunanin za'a iya samun dangin sa, kuma har sannan Matar Malam kullum sai taje ta ma Suhail wanka da basa abin ci. Ranan Al'hamis, waye wan Jumu'a, misalin ƙarfe 2:30am na dare Kurciyan nan ya samu ya fice daga cikin kejin da aka kulle dan ana son a warware sihirin da ke jikin Yarima, tunda ya samu ya fice daga cikin kejin Yarima dake dakin a kulle yana bacci ya farka a firgiji, ganin kofar a kulle yasa ya raɓa ta jikin window duk da ya masa kaɗan amma haka ya jima kansa ciwo ya fita, ya cigaba da bin kurciyan nan duk inda ya tafi nan shima yake bin sa kamar yadda ya fara bin sa tun daga cikin Masarautar Yola har zuwa wannan karamar hukumar Rimi. Tun da gari ya waye aka lura babu wannan kurciyan hakan yasa zuciyarsu tsinkewa dan sun san ba lallai kuma a samu Yarima dake dakin ba, ai kuwa hakan ne bayan an buɗe aka ga babu Yarima balle labarin sa ga kuma Suhail da ya bar musu, kowa ya tausaya ma Yarima amma babu yadda zasu yi hakan yasa Matar Malam ta dinga rokar Malam akan ya yarda tunda har Allah bai taɓa basu haihuwa ba, Malam yace ta samu Mai gari tukun, bayan ta samu Mai gari da maganar yace taje zai neme su. Bayan kwana biyu Mai gari da wasu Dattawan garin suka zauna akan maganar suka tattauna bayan kowa yasan Malam mutum ne mai addini gashi kuma mutum ne mai gaskiya duk da shima assalin sa ba ɗan Nigeria bane ɗan Sudan ne wanda suke tsoro kuma kar wata rana ya dugu da yaron, amma da sun tuna Matar sa assalin 'yar Rimi ce sai su kwantar da hankalin su. Malam na zaune da Matar sa aka aiko masa da takardar Mai gari na neman sa shi da Matar sa, hakan yasa suka tafi har fadar Mai gari wanda aka hada da police suka yi rubuce rubuce sannan aka yarda aka basu Suhail, wannan Ranan Umma ta gagara bacci sabar murna ta kuma cigaba da rainon ɗan ta wanda suka saka masa suna Malik...... Duk kallon su ake a parlorn, kowa da abinda yake tunani a hankali Umma ta ɗora "Ga Malik nan, ban taɓa rike sa da Mugunta ko wani abu da ya shafi na halin ko in kula, aka'sari ma na mayar da shi assalin ɗana na ciki na ɗan banta nuna masa cewa ba nice na haifaisa ba ko kuma Malam ya nuna masa cewa shi ba ɗan sa bane, tun tasowan Malik na fahimci abu guda ɗaya wanda tun a lokacin nasan cewa dole yana da alaka da gidan sarauta wanda hakan yasa idan Malam ya samu kuɗi kafin mu ci sai Malik yaci sau 20, tun Malik na karami baya son raini, baya son kaskanci, sannan yana son cin me kyau, yana son saka mai kyau, sannan yanayin sa yana nuna cewa daga gidan sarauta yake wanda hakan yasa ake masa kallon mai girman kai a unguwar mu" ta numfasa Malik ya zuba mata ido bai taɓa ɗauka abun har haka bane cos zai ce bata taɓa basa door din da zai yi tunanin basu ne suka haife sa ba, dan ta sha ce masa yana kama da kakannin sa na Sudan ne, tabbas yasan da akwai abun da take ɓoye masa amma ko da wasa bai taɓa ɗauka har ya kai wannan stage ɗin ba, Umma ta kuma sake ɗaurawa "A lokacin da ya bani labarin Leena hankali na ya tashi matuka wanda har nake tsoron kar asiri na ya tonu, shiyasa tun kafin na ganta naki amince wa auren, ina tsoro kuma kar ya kasance 'yan uwa na jini ne ace dangin Leenan su gane ko kuma ace ba aure sakanin su, amma...." Sai kuma tayi shiru tana kallon Mummy wanda tayi zuru zuru da idanu, kallon Umma na kallon ta nan da nan ta birkice a hankali Umma ta nuna Mummy tace "Zuwan wancan Matar gida na akan tana roko da na bari ayi auren Malik da Leena acewar ta ai itama kamar Mahaifiyar Leenan ne, har tana cewa kar rabo ya kashe Ni sai na fahimci abu guda ɗaya wanda daga baya na gane cewa ita kishiyar Uwar Leenan kuma aka ce ba son ta take ba" Abbah ya mata wani kallo yana taɓa ta, amma inaa Umma ta ɗauke kai tayi kamar bata fahimce sa ba, Mummy kuwa sai zufa, Rayyan da Malik suka kafe ta da kallo, Abbah yace "Toh dole sai an kawo Wannan cikin maganar ne?" Calmly Daddy yace "Barta mana, duk ai muna bukatar ƙarin bayani ne, You can go on Ma", Mummy tayi caraf ta fara magana"wallahi Ni na roke ta akan ta bar su suyi aure ashe na gama haɗa alkhairi tunda har ta hakan ne aka san waye su" Umma ta mata wani kallo ta cigaba "Da farko har cewa tayi zata biya Ni, Ni kuma naki, ganin shi Yayan Leenan yace zai nema masa aiki yasa na yarda saboda a jiki na nasan Malik zai yi kuɗi kuma ina so naga ranan da ita wannan makiran zata yi" Daddy ya dinga kallon Mummy zata yi magana yayi saurin tare ta yace "No need please", Granny ta gyara zaman ta tana kallon Leena tace "My Love, ina Maman ki?" Leena tayi pointing Ammi, Granny ta sakar ma Ammi murmushi, wanda har sannan Ammi bata dawo daidai ba itama ta mayar mata, Granny tace "Ko zamu so muji Labarin wacece Leena, sannan kuma wanene Mahaifin ta? Yana ina kuma yanzu ?" Mai martaba ya gyaɗa kai dan shima yanzu amsar da yake son sani kenan, dan yasan dama Already Suhail shine Malik, Daddy ma ya kura mata ido dan shima bai san komai game da hakan ba, zuwa sannan Mummy ta rasa duk strength ɗinta kuma ta gagara guduwa, Ammi ta gyara zaman ta tana kallon Leena, a hankali ta sauke idon ta kasa tace ".......
Yarima har suka shiga cikin garin Kaduna yana biye da wannan kurciyan, ya sauka kan wani bishiya saboda kurciyan bashi da lafiya hakan yasa Yarima zama a karkashin bishiyan, wasu yara dake wasa a waje wani daga cikin su ya ɗauki dutse yace "Barin jefe wancan tsunsuwar" ya ɗauki dutse ya jefa mata, nan take ta faɗi kasa tana shure shure, kawai Yarima shima ya fara shure shure kamar yadda wannan kurciyan ke yi, hakan yasa yaran ja baya suna kallon ikon Allah hakan yasa suka yi calling attention din wani majalisa, duk dattawan suka yi wajan suna kallon exactly abin da kurciyan ke yi shi Abdul-aziz yake yi, hakan suka fahimci ba lafiya ba, bayan kurciyan ta mutu sai Yarima Abdul-aziz ya dawo hayyacin sa amma ya manta komai dan duk mutanen wajan suna tambayar sa lafiya amma baya cewa komai, suka tambaye sunan sa amma ya kasa faɗa, wanda daga karshe aka kira mai unguwa ya shiga maganar. Washe gari bayan an idar da sallahr asuba Limami ya miƙe ya fara jawabin abin da ya faru game da Abdul-aziz, bayan Alhaji Muhammad ya dawo gida yake sanar da Matar sa Hajiya Saratu, Hajiya Saratu tace "Yanzu ba'a san inda ahalin sa suke ba?" Yace "ko sunan sa fah baya iya tunawa so Kinga babu zancen zai iya tuna ahalin sa" Hajiya Saratu tace "Toh Alhaji kawai ka karɓo sa mu rike sa har sanda Allah zai bayyana mana ahalin sa" ya Kalle ta sannan yace "Abin da nake tunani kenan, Allah ya bamu ikon rike sa" ta amsa da "Amin" a haka har Alhaji Muhammad ya samu yayi convincing Imaam da a basa Yarima su rike wanda ba'a sha wahala ba aka basa saboda a lokacin Alhaji Muhammad yana da mugun kuɗi, a haka ne har Yarima ya koma gidan da zama wanda kusan komai sai da aka sake koya masa daga farko. A haka har Yarima yayi shekara guda a gidan Alhaji Muhammad, wanda ya gama ɗaukar gidan ne assalin sa. Alhaji Muhammad yana da Mai-gadi wanda ya dauko sa daga Niger shi da matar sa, a gidan suke da zama wanda suke da yarinya Hauwa Mai hankali da sanyin hali tun assalin ta wanda Alhaji Muhammad ya saka ta a makaranta, wanda ko wani shekara itace overall student shiyasa baya jin kyashin biya mata kuɗin makaranta, wanda a lokacin Yarima ma ya koma makaranta a KASU. Wata rana kamar kullum Hauwa Sirbajo ta shigo gidan da gudu tana "Nyaama, Babaajo" Babanta wanda ke matsayin gatekeeper ya fito yana kallon ta sai ga mahaifiyar ta ma ta fito ta tsaya tana mika musu papern hannun ta tace "Kalli result ɗina na wancan term ɗin ne aka bamu, shima duk A naci" Nyaama ta karbi tana kallo tace "Toh Hauwa ai mu bamu san komai ba" Babaajo yace "Allah kara miki Albarka da basira Hauwa" tace "Amin" ta karɓe a hannun Nyaama ta wuce dakin Mami dake main gidan da gudu, zata shiga parlorn tayi karo da Yarima wanda suke kira da Abbah, ta ja baya sai kuma tana murmushi tace "I'm sorry Yaya" shima murmushin ya mata ta raɓa ta shige ya bita da kallo sai kuma ya fasa fitan shima ya bita cikin parlorn ta karasa da gudu ta duka gaban Mami tace "Mami kalli result ɗina" Mami ta karɓa tana kallo sai kuma tace "Hauwa Medicine ya kamata ki karanta" Abbah(Yarima) shima ya karasa inda suke ya karɓa a hannun Mami yana kallo sai kuma ya sakar mata murmushi yace "Kanwata ba daga nan ba" ita dai sai murmushi take, Mami ta ɗaura "Wai an sake WAEC ɗin ku ko?" Tana kallon Mami sai kuma tace "Wallahi Mami ban sani ba, amma ɗazu wata kawata tace karma haka taji" Mami na kallon Abbah tace "Abbah anjima idan ka fita sai ka gwada zuwa ka duba idan an sake sai ka Ciro mata" suna cikin magana sai ga Alhaji ya shigo da murmushi a fuskar sa yace "Congratulations daughter" Hauwa ta ɗaga kai tana kallon sa dan kamar yadda su Mami ma ke kallon sa ya karasa cikin parlorn ya zauna ya mikawa Mami papern hannun sa yace "Kiga WAEC result ɗin 'yar ki" Mami ta karɓa tace"Yanzu fah nake maganar Abbah idan ya fita ya dubo ko an sake.." maganar bakin ta ne ya kafe ganin Result ɗin Hauwa flat A, tace "Ma Shaa Allah, Daughter kinci kyauta wallahi, ki faɗi me kike so na baki as gift" Alhaji yace "Sure! Ta zabi duk school ɗin da take so zan kai ta as gift" Abbah ya karɓi result ɗin yana kallo, Hauwa kam hawaye ne yake gangaro mata, ta dai san hawayen Farin ciki ne. A haka har Hauwa ta zana JAMB wanda a lokacin taci, amma Nyaama da Babaajo suka nuna basu son ta cigaba da karatu sai dai tayi aure wanda sai da Alhaji da kansa ya musu magana sannan suka hakura. Wata rana Hauwa ta fito daga dakin Mami da kayan wankin Mami ta wuce laundry zata wanke mata a machine, Abbah ne ya biyo ta, ta ɗaga kai tana kallon sa da murmushi tace "Yaya ina wuni" ya karɓe kayan hannun nata sannan ya fara haɗa kayan, yana kallon ta sai kuma ya mayar da da kallon sa kan abin da yake a hankali yace "Hauwa na miki wani tambaya mana?" Tace "Ina jin ka" tana kallon sa amma shi kuma yaki yarda ya Kalle ta, yace "What's your goal now that you've finished secondary school?" Tace "Karatu mana Yaya" yayi murmushi still tana kallon sa amma har sannan bai jiyo ba yace "A'a, I mean apart from studies, what do you want? Kamar, when do you want to start settling down?" Ta ɗan yi frowning face tana kallon bayan sa taki cewa komai dan bata gama fahimtar sa ba ya, ya ɗan juyo yana kallon ta sai kuma ya cigaba da sa kayan a machine yace "When do you want to get married?" Tayi dariya tana kallon sa tace "Wait.. wai aure? Toh ai actually, I don't have a boyfriend" yace "Idan kika samu kuma fah?" Tayi dariya tace "Not now, though Nyaama da Babaajo sunce sai nayi" ya jiyo yana kallon ta a hankali yace "Hauwa idan nace zan aure ki fah? Zaki yarda?" Jin tambayar nasa tayi ba zata, ta sauke idon ta kasa dan tsintar kanta tayi tana mugun jin kunyar sa, tun daga wannar ranan Hauwa bata yarda ta haɗu da Abbah, sai ta fake baya nan sannan zata dakin Mami a haka har ta fara karatu wanda bata samu MBBS ba kawai ta fara Biochemistryn ta. Bayan Abbah ya sanar da su Mami kudirin sa ba karamin daɗi suka ji ba, wanda har kamar sun fi sa farin ciki da hakan, Alhaji da kansa ya tunkari Babaajo akan maganar wanda shima yayi farin ciki, wanda Hauwa tana level 2 aka yi auren ta da Abbah, wanda Alhaji da Mami suka musu komai dan hatta gidan da suke na Alhaji ne. Hauwa bata haihu ba har sai da ta gama makaranta, anan ta haifi 'yar ta LEENA wannan yarinyar tun tana karama take da mugun wayo sannan ta kwaso ilimin mahaifiyar ta, kama take da Abbah ba kaɗan ba, daga nan kuma Allah ya jarabci Alhaji da karayan arziki, daga nan kuma ya fara jinya. Leena tun da ta fara karatu ita ke ɗaukan overall kamar Mahaifiyar ta Hauwa Sirbajo, wanda Abbah da kansa yake mata lesson har suka fahimci yarinyar tun tana karama take da wani talent, dan haka kawai sai ta dauki wayan iyayen nata ta dinga videos ko kuma tana rubuta su a littafi wanda Abbah ke bata goyon baya... Ammi ta fashe da kuka duk parlon ita suke kallo, wanda Granny sai share hawayen da ya ki tsaya mata take yi, Leena sai kallon Ammin ta