wayar a DND tunani ya fara ko ya tafi asibitin su ne yaga shi ba zai iya kwanan asibitin ba kawai ya kira friend ɗinsa fu'ad yana ɗauka wa yace "how far fu'ad? Kana gida ne?" Fu'ad yace "Eh ina gida, zaka zone?" yace "Eh" daga haka ya mayar da wayan sa cikin Aljihun sa ya tare taxi ya Kaisa har kofan gidan, yana isa ya kira fu'ad, ya fito yazo ya same sa da masu gadi suna gaisawa fu'ad yace "kai fa ka iya munafurci gidan ne kullum idan kazo sai kayi tayi kamar bakon ka" Rayyan na dariya yace "Toh kawai saina kusa kaina ciki?" Daga haka suka kama hanyar BQ Rayyan yace "Wait, barin fara gashe da Mama tukun" fu'ad yace "Toh, muje" Sallama fu'ad yayi ya shiga tukun yace "Mama ga Rayyan yazo gaishe ki" tace "Toh ya shigo mana" yace "Toh ai sai ka shigo an baka izini ustazi" ya karasa maganar in funny tongue, Rayyan ya shiga parlorn da sallama daga Mama sai kanwar fu'ad Hasna ya zauna nan kasan carpet yana gaishe ta ta amsa da fara'ar ta tace "yau kuma wani rana ga Rayyan anan gidan" ya shafa kansa ɗan rabon sa da gidan ya ɗan jima kuma Fu'ad aini hin abokin sa ne tunna yaranta yace "wallahi Mama abubuwa ne suka ɗan sani gaba kwanan nan ga kuma aiki" fu'ad yace ba wanin na! Rayyan ya ɗan harare sa Mama tace "To Allah yayi jagora ade dunga zumunci dai" yana murmushi ya amsa gaisuwar Hasna tace "Yaya ina wuni" Ya amsa da fara'a yace "Lafiya kalau, ya karatu?" tace "Alhamdu Lillah" yace "Ma shaa Allah" daga haka yace "Mama bari mu shiga ciki" tace "Toh shikenan" suna fita Hasna ta tashi da gudu tayi cikin gidan ta ban kaɗe kofar Husna ta juyo tace "ke dalla wata irin mahaukaciya ce ke" tace "dalla Albishir na kawo Miki" tace "mene?" Hasna tace "Ya Rayyan ne yazo gidan nan" Husna tace "really? Wayyo Allah na". Rayyan yace "kai anan fa zan kwana sai gobe na koma gida" fu'ad yace "kace zuwan naka da biyu mana" Rayyan ya ɗan yi dariya yace "Not at all" Husna ce tayi sallama a kofar dakin sannan ta shiga taci uban wanka ga wani kamshi da take zuba wa kallo daya Rayyan ya mata sannan ya ɗauke kansa shi abinda yasa baya son zuwa gidan saboda Husnan nan ne Fu'ad ya mata wani kallo ganin yadda ta yi wani shiga ga kamshin da take yi , Nan ta zauna kan cushion ta wani karya murya tace "ya Rayyan ina wuni" ya amsa idon sa na kan wayan hannun sa tace "me za'a kawo maka ne?" ya ɗan kalle ta jin yadda take magana sai fari take da ido shi abun dariya ma ya basa amma ya maze yace "thank you, Husna. Daga gida nake so karki damu. Kiran sallahn isha da aka fara yi yasa ya kalli fu'ad yace "mu tafi masallaci ko" kai kawai fu'ad ya gyaɗa masa dan shi ya sani wannan iskan cin da Husna take idan taga Rayyan, gashi yana magana Mama zata hayyaya ko masa tace ina ruwan sa Husna tace "sai kun dawo kafin nan barin ɗaura muku abinci". Bayan Daddy ya dawo daga sallan isha'i ya shiga ɗakin sa ɗauko abu sai ga Mummy ta bi sa ta zauna bakin gadon sa tace "Daddyn Rayyan ina son muyi wata magana ne" ya juya ya bata full attention ɗin sa yace "ina jin ki dear" tace "Naga kowa yayi wasi da maganar ne babu me yinta shine nace barin zo na same ka da ita" yace "am all ears , just go ahead" tace "dama maganan auren Rayyan ne naga Kai baka ce komai ba gidan su yarinyar ma sunyi shiru, shine nace tunda tambaya akayi kawai yanzu kuje a sa rana, dan ni wallahi na gaji da Rayyan a cikin gidan nan" Daddy yace "In shaa Allah zan muje a sana ranan, amma zance kin gaji da shi a gidan nan kina uwa be kamata ki faɗa haka ba saboda bacin rai, kuma a wannan lamari Ni banga laifi yaron nan ba, sai dai akasarin laifin nasu Nisreen ne sai dai ban san wani kalan ɗaukan mata ki yayi ba, zan ja masa kunne, kema ki jama ƴaƴan ki kunne su fita harkar Leena, ke kuma ki kama girman ki dan Kinga tun sirbajo bata tanka miki yanzu harta fara Kinga wata rana zaki ji kunya sannan kuma me na zuwa har part ɗinta idan banda jama kai raini?" Tace "ai kasan matar ka ƴar gold ce baka kwanar a taba maka ita" daga haka ta mike ta fita tana kudirin sati 4 kawai za'a sa na tare wa dan ita ba zata iya juran ganin Rayyan yana iya dukan kannansa akan Leena...
Washe gari, Friday! ana idar da Sallah ya zauna yayi lazimin shi tare suka koma gida da Fu'ad suka shiga suka gaida Mama sannan suka koma BQ in da ɗakin Fu'ad yake, suna shiga Rayyan ya Kuma komawa kan gado yana dannan wayan sa sai can ya tashi ya zauna yana kallon Fu'ad yace "Yau short day ne, gashi zan tafi office, yanzu kuma idan nayi wanka anan ban san kayan da zan sa ba, so, I think zan tafi gida kawai" Fu'ad yace "ka tsaya kayi breakfast mana idan ya so sai mu fita tare nayi dropping ɗinka" Rayyan yayi shiru yana tunanin yanzu ta'ina ma zai fara shiga gidan yanzu idan ya koma yasan Mummy na nan shi kuma ya fi so ya koma lokacin da bata nan idan ya so ita ta zo ta same sa, tunawa da yayi da kayan sa a wajen me Laundry yasa ya tashi yana kallon Fu'ad yace "ban keyn motar ka zanje na karɓo kayan na awajen mai wanki" Fu'ad yace "da sassafen nan?" ya karasa maganar yana mika masa keyn, ya amsa ya fice. Ammi ta sake leka ɗakin Leena taga har sannan tana kwance tace "Leena makarantar fah? Ko ba zaki je bane ina tashin ki kina komawa ɗin" tashi tayi ta zauna tana murza idon ta tace "Ammi ni bazan je school yau ba" lokacin da take ba Ammi amsa Already ta bar wajan ma taje tana sa abincin da ta dafa mata a lunch box ɗinta, Ammi ta shigo da niyyar ta taya ta ta shirya amma kuma still ta kuma kallon Leena kwance ta karasa ta tana cewa "Leena yau dai lafiyan ki klau kuwa?" ta yaye duvet ɗin dake jikin ta ta taɓa jikin ta taji da zafi tana kallon ta tace "Baki da lafiya ne?" ta gyaɗa mata kai tace "yau ba zan iya zuwa school ba" Ammi tace "Toh shikenan barin ma yayanku magana idan zai rubuta magani ne ba sai muje asibiti ba fine" daga haka ta gyara mata kwanciyar ta ta rufe ta sannan ta fita taci gaba da aikin da take yi. Husna ce ta shiga ɗakin yayan nata hoping zata ga Rayyan ajiye tray ɗin hannunta dake ɗauke da breakfast ɗin da ta kawo musu tayi, ta ɗaga kai tana kallon yayan ta tace "Yaya ina Ya Rayyan ɗin?" Sai sannan ya ɗaga kai ya mata wani irin kallo yace "ke wacca irin yarinya ce mara kamun kai, kina tunanin a haka ne zaki burge sa Look! Rayyan ya tsana irin mata masu halin ki, and I'm warming you wallahi kika sake idan ya dawo kika shigo nan kina wannan abun naki zan iya kakkaryaki" wani irin kallo take masa ta kasan ido ta tashi kenan zata fita sai ga Rayyan ya shigo da sallama ja da baya tayi tana washe baki sannan ta gaishe sa kallo ɗaya Rayyan yayi mata sannan yace "yau ba lectures ne?" tayi fari da ido tace "sai 10am muke da shi" daga haka be kuma ce mata komai ba yayi wuce War sa cikin dakin ya shiga toilet, bayan ya gama shiri ya fito Fu'ad na kallon sa yace "shikenan ai yau ka gama min da turare, kai gashi fesawan hauka kake yi" Rayyan yace "Dalla ba wani fesawan kirki nayi ba fa". Nisreen da Niswa suka fito a sashen su suka karasa wajan motar suka shige Nisreen tace "Anty, Leena ba zata je bane? Naga yau mun riga ta shiri ne" Niswa tace "toh ke ina ruwan ki da Ita? Driver na karaso wa wallahi tafiya zamu yi" Nisreen ta rufe bakin da hannayen ta da sauri tace "Kin manta me yaya yace?" tace "ai bata isa tace dukan ta nayi ba kuma waya hana ta fitowa da wuri" sai ga driver ya karaso Nisreen na kallon sa tace "Tafiya zamu yi yanzu" yace "Okay, dama gani nayi kamar baku gama haduwa ba ne" tace "kayi Abunda nace maka kawai" daga haka ya shiga ya tada motar suka bar gidan. Suna cikin breakfast yaji wayan sa na ringing dubawa yayi yaga Ammi ke kiran sa ya katse kiran sai ya kira ta back tana daukawa ya gaishe ta ta amsa tace "Ka fita ne Rayyan?" yayi shiru sai kuma yace "Menene Ammi?" tace "Dama Leena ce bata jin daɗi nace ko zaka Duba ta kafin ka fita" yace "bani gida amma yanzu zan karaso na dubanta ɗin" daga haka ta masa sallama. Tare da Fu'ad suka fita akan Fu'ad zai yi dropping ɗin sa suna hanya daidai mashigan unguwar ta su suka yi clashing da motar Mummy amma ita hankalin ta na kan gaban ta ne sai da Rayyan ya sauke ajiyan zuciya dama can baya so ya haɗu da ita a gidan dan zata iya hana shi duba Leena a bakin gate ɗin gidan su Fu'ad yayi parking Rayyan na kallon sa yace "Thank you guy, sai munyi waya" fu'ad yace "Okay, ka gaida su Mummy" daga haka ya shiga cikin gidan yana amsa gaisuwar da masu gadi ke masa direct part ɗin su Leena ya wuce yana bakin kofa parlorn yayi sallama Ammi ta amsa masa tace "shigo mana" yana shiga parlorn tace "mu wuce ciki kawai" yana shiga ya ganta kwance ya ɗan taɓa ta yaji jikin nata yayi mugun zafi yace "Ammi tun yaushe ne ta fara jin jikin?" Ammi tace "tace min tun jiya da daddare ne ya fara mata Amma Ni kuma sai da safe take faɗa min, ban ma ɗauka jikin yayi serious ba sai da nake bata breakfast haka ta dinga amai yanzu tayi ya kai sau uku" yana kallon Leena yace "ina ke Miki ciwo" ta fara pointing masa wajajan da take jin ciwo da hannun ta" Rayyan ya tashi yana kallon Ammi yace "Ammi barin je sai na kawo abubuwan da za'a mata magani" tace "Toh" yana fita parlor zai fita ya ci karo da Daddy ya gaishe sa ya amsa masa yace "ka duba Leena ɗin?" yace "Eh, yanzu zanje na dawo da abubuwan da ake bukata dan sai an sa mata ruwa ma" Daddy yace "Okay" Rayyan ya fice daga parlorn ido huɗu yayi da Mummy da tayi mantuwa tazo ɗauka ji yayi kamar kasa ya tsage ya shige da kyar ya iya kirkiran Murmushi ya bi bayan ta tana buɗe kofar parlorn ta juya tana kallon sa tace "bashi kake bi na da zaka biyo NI ka tsare ni?" Dariya yayi yace "kai Mummy bashi kuma? Na shigo ɗazu zan gaishe ki sai kuma naga gidan a kulle" bata ce masa komai ba har ta karasa buɗe gidan ta shiga still yana biye da ita a baya yace "yanzu fah zuwa na, ina shigowa Daddy yace inje in duba Leena bata da lafiya shine muka karasa part ɗin nasu tare" still bata ce masa a komai ba har ta wuce ɗakin ta shima ya bi ta ya rike hannunta yana kallon idon ta yace "Mummy fushi kike dani ko? Sorry jiya na bar waya na a gida Ni kuma saboda kira na da akayi ana nema na urgent a asibiti da zan tafi sai na nance wayan kuma lokacin baki nan ne yasa ban faɗa Miki ba" Allah ya sani tana sananin son Rayyan fiye da yadda ake tunani duk cikin ƴaƴanta tafi son sa ko dan da ta haife sa bata sake haihuwa ba sai bayan 12 years. Ya ɗaura kansa a shoulder ɗinta yayi shiru tace "Me su Nisreen da Niswa suka maka da zaka dake su?" yayi shiru be ce mata komai ba ta ɗaga kansa ta karasa ɗaukan file ɗin da zata ɗauka sai sannan ta kalle sa sauke idon sa kasa yayi yace "Mummy dukan Leena sukayi har sai da ta fasa mata hanci Kinga yanzu ta tashi bata da lafiya" tace "Rayyan idan har kana so na daga yau na raba ka da Leena har abada ba ruwan ka da ita, tin da akan Leena kake dukan kanan ka" daga haka ta fara gaba yana biye da ita a baya suna fita parlor tana kallon sa tace "kayi breakfast?" yace "Eh" daga haka ta karasa fita shi kuma yana biye da ita kusan tare suka fita daga gidan Rayyan yana fita asibiti ya wuce duk wani abu da zai bukata ya ɗauka, ganin bayi da wani aki sosai ranan yasa ya fita yace wa abokin aikin sa idan wani abun ya taso shi baya nan daga haka ya wuce gida yana zuwa yayi sallama parlorn muryan Ammi yaji tace "shigo mana ya Rayyan" ya shiga ciki Ammi ta tashi tana biye da shi a baya yana shiga ɗakin Leena yaga Hajiya na zaune a gefen ta tana rokan ta da taci egg ɗin da ta soya mata tana kallon Rayyan ta tsuke fuska Murmushi yayi yace "Hajiya yau fushi kike da ni kuma? tace "A'a zo ka duba ta, ai Ni tunda naga Leena bata je ta gaishe ni ba nasan ba lafiya ba amma kai fa rabon ka da gida na tun jiya, ina ta damuwa ashe garau ɗin ka" ya haɗa alluran hannun sa ya ɗaga kai yana kallon Hajiya yace "toh ai tun jiya bana gidan nan ɗazu shigowa na a asibiti na kwana" ya gama hada abun da zai hada yana ma Leena Murmushi yace "Toh Leena bari muyi allura ko?" nan da nan ta fara hawaye tana girgiza masa kai ita bata so Ammi ta mata wani kallo tace "ko ki tsaya yayi Miki ko kuma ba zaki warke ba har ku fara exams ke kika sani" jin haka yasa ta tashi ta zauna Hajiya ta tashi ta fice tace "sai kuma na sake leko ki Lina" Ammi tana kallon Rayyan tace "Kaima Rayyan ji yadda kake abu, be like a man yadda zata ji shakkar yi maka gardama amma a hakan ne zaka ce zaka ma Leena Allura?" daga haka ta fice a ɗakin da kyar ya samu ya mata allura ta sha magani sannan ya kwantar da ita, a parlor ya samu Ammi na zaune tace "ka gama" yace "Eh, Allah ya bata lafiya" Ammi ta amsa da Amin mungode. Around 2 Rayyan ya sake zuwa daga office ya wuce yaje ya duba jikin Leena yaga da sauki zazzaɓin ma ya fara sauka, ya wuce part ɗinsu ya shiga da sallama Nisreen da Niswa suka gaishe sa ya amsa yace "kuna wani abu ne yanzu"?" duk suka ce A'a, yace "okay na baku 10 minutes ku shirya sai ku same Ni a wajan mota na" daga haka ya fice suka fara jin daɗi coz duk sanda yace musu zai fita da su toh shopping zai kai su tare da ice cream heaven ba'a ɗau lokacin ba sai gashi duk sun fito suka shige motar, Rayyan mall ya fara kai su yayi parking sannan ya kalli Niswa dake gaban motar yace "ku shiga ku ɗauki abunda zaku ɗauka" ya karasa maganar yana mika mata ATM card ɗinsa ta amsa tana murna tace "toh Yaya Rayyan" ta kama hannun Nisreen suka shige ciki shi kuma ya ciro wayar sa yana danna danne kamar wanda aka tuna wa abu da sauri ya sauka a motar ya rufe sannan ya shiga mall ɗin, inda yasan Leena na fara zuwa a mall ɗin yayi ya ɗauka mata favorite turaren ta sai zai bi wajan chocolate ya hadu da su Nisreen tana murmushi tace "yaya kaiman ka shigo ne?" ya yi mata Murmushi kawai duk wani abu da yasan Leena zata so sai daya ɗauka mata bayan sun biya kuɗi yace akai musu kayan booth ya buɗe aka zuba a ciki yana rike dana Leena yasa a gaban motar daga nan ya wuce da su ice cream heaven suka shiga tare yace "kuje ku ɗau abun da kuke so" ya ɗauka wa Leena sanin Mummy na son country yoghurt da pizza ya ɗauka mata basu suka koma gida ba sai daf Magrib yana parking duk suka sauka kana ganin su kasan suna cikin murna ya mika wa Niswa na Mummy yace "gashi ki fara kai na Mummy sannan sai ki zo ki ƙwashe naki ta amsa ta kama hanyar part ɗin su, Nisreen ta fara kai nata ciki itama ya ɗauki na Leena ganin ta zaune a kofar ɗakin yasan ta fito shan iska ne hakan yasa ya karasa yana inda take. Mummy da ta fito zata raka aminiyarta suka ci karo da su Niswa a bakin kofar parlorn ja baya suka yi suna Murmushi suka gaishe ta ta amsa tace "ai da bangan ku ba nake tambayar Mummyn ku" suna Murmushi suka ce Ya Rayyan ne ya fita da mu shopping. Rayyan na kallon Leena da har ta rame yace "Toh kinci abinci" ta girgiza masa kai yace "meyasa toh?" tana masa shagwaba tace "Ni ba zan iya cin abincin ba" tana gama faɗa ta ɗauke kanta dama Leena da shagwaba barin ma bata da lafiya ai an shiga uku dariya ma ta basa ta tashi ta mike ganin su Mummyn sa sun fito ita da kawar ta though ba wanda yayi noticing ɗinsu a cikin su, ya mika mata siyayyan da yayi mata