x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 56 - AGOLA free pages

  • 165001 words
  • 168000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
parlorn ba hakan yasa Nisreen bin bayan ta Niswa na kallon Mama a hankali tace "Mama dan Allah kiyi hakuri, hakan duk bai kai kuyi musanyen yawu a gaban mu ba" Mama tace "Ta shi ki tafi kar su tafi su barki" Niswa da duk jikin ta yayi sanyi ta bi bayan su Mummy, Layla tace "Mama Kiga matar nan ko kallon yarinyar fah bata yi ba" Mama tace "Mugun halin ta ina zai bar ta, idan har da Ni Khadija zata yi wallahi sunan auren ta matacce" Layla tace "Abun ta kam mamaki yake bani" Mama tace "wallahi naga dama na fitar da ita a gidan ta sannan na aure mijin ta muga ta tsiya" Layla tace "Toh Mama me ya kawo wannan kuma?". Mummy bata tsaya ko ina ba sai inda Rayyan yake aiki, Niswa ta juya tana kallon ta kafin ta fita tace "Mummy dan Allah kar ki ɗaga masa hankali a wajan aiki, ki bari ko ma menene sa ki kira sa gida" Mummy ta juyo a mugun fusace tace "Idan kika sake sa baki zaki sha mamaki na" daga haka ta sauka, ta wuce cikin asibitin, Nisreen tace "Anty Niswa ki bar Mummy tayi abin da tayi niyya, haka kawai dan sun san dole Mummy ran ta zai ɓaci sai su saka mata Leena" Niswa tayi wani murmushi tace "Baki son gaskiya ke ma, sannan har sannan ke yarinya ce baki san komai ba, So zan baki uzuri" daga haka ta fito da wayan ta ta fara danna wa. Tun da Mummy ta nufa hanyar office ɗin sa sanin wacece ita yasa ba wanda yayi kokarin hanata sai ma gaishe ta da suke yi, da zuciya ta banka kofar taci sa'a kuwa a buɗe yake, ya ɗaga kansa da sauri jin yadda aka buɗe masa kofa, da sauri ya mike tsaye yana kallon mahaifiyar na sa, kafin yayi magana ta rika sa  " So, Rayyan ashe ma Leena ka ma takwara?" Ya ji tambayar na ta har tsakiyan kan sa yace "Mummy.." ta katse sa "Saboda kasan ba son yarinyar nake yi ba shine zaka yi haka dan ka bakan ta min?" Ya ɗan kalli kofar office ɗin nasa jin yadda take magana da ɗan karfi yayi gathering courage yace "Ba ita nayi wa ba Mummy, beside ashe sun taɓa magana da Layla ne, so Laylan ne tace haka za'a na kiran ta shiyasa, but Ni sunan Hajiya na mata huɗu ba da" Mummy tayi murmushi mai wuyar fassara tace "Wato Laylan ce tace haka ko? Wato da Ni Layla zata yi? Ko da yake kai ne ka bata door din raina Ni" a hankali yace "Mummy ki tuna Layla fah zaɓin ki ce amma kullum sai kina ganin kamar ina using ɗin ta wajan bata miki rai, dan Allah kiyi hakuri Mummy, sannan ki taimaka ki daina ɓacin rai da Ni" Tace Rayyan dole a ukun nan zaka zabi daya, duk wacca ka zaba ma kan ka ya rage naka" ya dafe kansa da ya fara sara masa, yana kallon ta tace "Rayyan, ko ka saki Layla, ko ka kara aure, ko kuma kaki dukka na tsine maka" da sauri ya ɗaga kai yana kallon ta, har hawaye ya fara taruwa a idon sa, be san me yasa yanzu abu kaɗan ta dinga masa barazana da tsinuwa ba, yana mata biyayya daidai gargodo, zai yi magana ta katse sa da cewa "Na gama magana Rayyan, zaɓi ya rage naka, sannan na baka nan da 2weeks, wallahi ba zan iya daga maka kafa ba" daga haka ta juya ta bar office ɗin na sa ya kifa kansa a desk din gaban sa yana jin yadda kansa ke sara masa ga kuma bugawan da zuciyar sa ke tsanan ta. Leena ta fito a kitchen ta tsaya kallon Malik da ya dawo daga aiki, kallon agogon tayi taga karfe 10am ta san yanzu ba lokacin taso wan sa bane, kuma yanayin sa ya nuna yana cikin damuwa ba kaɗan ba, har ta karasa cikin parlorn bai san ta shigo ba, ta zuba masa ido yana zaune amma ya jingina jikin sa da sofa idon sa a lumshe, envelope ɗin hannun sa ta kalla kamar ta ɗauka sai dai kuma tana tunanin kila sirrin sa ne ba lalle ya so ta gani ba, tace "Hey, is everything Okay?" Malik da yayi nisa cikin Thoughts ya tsinkayi muryan ta da sauri ya buɗe ido ya zauna sai kuma ya fara faking murmushi yace "Sure" ta ɗan masa hararar wasa tace "A hakan? Ko kuma ban kai na san damuwar ka bane?" Yace "Kin san ko nace baki kai ba nayi karya, kawai dai bansan taya zan fara ba" ya mika mata envelope ɗin da sauri ta karɓa ta buɗe papern cikin ta fito da shi ta fara karanta contents ɗin ciki, duk da yadda zuciyar ta ya karaya amma sai bata nuna hakan ba akan fuskanta ta dake tace "Me ka musu da suka kore ka? Ko dama haka suke?" Ya girgiza mata kai yace "Ban taɓa jin sun kore wani bama balle nace halin su ne, kawai ina isa, na shiga office zanyi signing sai wani ɗan aiken principal ya mika min, ina duba wa naga wai sun dakatar da Ni" Leena tace "Tun da ba wani abu ka musu ba ai shikenan, aiki kuma zaka samu wanda ya fi wannan daraja ma, su je suci kan su" Malik ya sake lumshe ido dan shi yasa kalar tashin hankalin da yake ciki, ga iyayen sa da suka dogara da shi, ga yanzu kuma yana da Mata, bai ma san ta ina zai fara ba" Leena tace "Wallahi idan baka dai na wannan tunanin ba ba zan yafe maka ba, akan ka aka fara korar Mutum a aiki da zaka sama kan ka wani damuwan" ya buɗe idon sa ya mata Murmushi ta mike ba tare da ta kula sa ba. Da rana Leena na zaune tana ta jan Malik da hira dan ta lura ba kaɗan ba ya shiga damuwa hakan yasa sai tayi ta kawo silliness dan kawai ta kwantar masa da hankali. Da yamma suna abinci dare tare, duk da abin na damun sa ganin yadda take son tayi cheering ɗin sa yasa sai kawai yake acting babu komai, wayan sa ne yayi ringing ta ɗauka ta mika masa yayi picking call ɗin da sallama a bakin sa, sai kuma yace "Okay gani fitowa" bayan ya gama wayan yana kallon ta yace "Barin ɗan fita wani colleague ɗina ne ya zo" tace "Okay, sai ka dawo" yayi kissing forehead ɗinta tana murmushi ya fita, yana buɗe gate ɗin ya kalli colleague ɗin na sa a bakin gate ɗin ya karasa da murmushi a fuskan sa suka gaisa, Abokin na sa yace "Ashe abin da ya faru kenan?" Ya gyaɗa kai yace "Eh fah" Abokin ya numfasa yace "Ka taɓa samun matsala da wani ne?" Ya Kalle sa sai kuma yayi murmushi yace "Yanzu idan aka ce maka na taɓa samun matsala da wani sai ka yarda?" Ya girgiza kai yace "Toh Nima abun da mamaki ne wallahi, dan na san halin ka baka ko shige wa mutum kuma baka yarda a shige maka but wani abu ne ya tsaya min a rai ya sa na tambaye ka ko ka taɓa samun matsala da wani" Malik yace "Me wannan?" Yace "Kasan messengern principal ne ya faɗa min wani magana wai akwai ranan da yaga wasu Hajiyoyi biyu da suka zo yaji dai suna magana akan korar wani daga aikin but shi bai ji sunan wanda ake magana akai ba" Malik yayi murmushi yace "It's Okay, ko ma waye ne ya sani bashi yayi sanadiyar barin aiki na ba, dama Allah ya rubuta na gama cin abinci a wajan" Mutumin sanin halin Malik yasa kawai yayi murmushi dan yasan ba zai kuma cewa komai ba. A bangaren Leena kuma ganin Malik ya fita yasa da sauri ta ɗauki wayan ta ta shiga kiran Rayyan yana ɗauka wa tace "Yaya ina son zan yi magana da kai if possible" yayi shiru sai kuma yace "In zo ne?" Tace "A'a ka faɗa min inda kake yanzu" yace "Is everything Alright?" Ta ce "Eh amma sai munyi magana tukun nan" yace "Okay, ko zaki zo gida na?" Tace "Toh, Thank you" daga haka ta katse, ba'a dau lokaci ba sai ga Malik ya dawo, murmushi ta sakar masa shima ya mayar mata, tace "Anty Layla ta kira Ni yanzu wai dan Allah tana son gani na" yayi shiru kamar mai nazari sai kuma yace "Okay, sai kin dawo" tace "Thank you" daga haka ta wuce kitchen ta kwashe abincin a warmer sannan ta wuce dakin ta ta shirya ta sanya hijab ɗinta har kasa ta dauki keyn motar ta ta fito yana kallon ta kamar zai ce wani abu sai kuma yayi shiru ta masa sallama ta wuce, Leena na parking sai ga Rayyan ma ya shigo layin, parking shima yayi a bakin gate ɗin, ta sauka ta wuce inda yayi parking, zai sauka ta buɗe front seat ta shiga hakan yasa ya fasa saukan yana kallon ta bayan ta gaishe sa ya amsa sai kuma tayi shiru yace "Speak out, Menene?" A hankali ta shiga narrating masa abin da ke faruwa yayi shiru yana kallon ta bayan ta gama ta kalle sa shima kallon nata yake yi amma da tunanin da yake yi dabam tace "Dan Allah kama Daddy magana ya samar masa wani aikin, ka ga Ni ba wai karatun na yi ba, gashi ba ko da yaushe kuɗi ke shigo min ba har sai nayi performing poem" tunanin bakin da Mummy ta masa idan ya sake ma Daddy maganar samar ma Malik aiki yasa yaji hankalin sa ya tashi gashi ba zai iya turning offern Leena down ba, kuma shine ya fara haɗa auren, nan da nan ya fara zufa.

It's Long, Masoyan Sadeeq Ina kara baku hakuri, so this chapter dedicated to you Dudes.

#Jiddatul-khayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧



YOTA


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Chapter 66

Bayan wata takwas....
Leena da Malik sunga jarabawar rayuwa, har sannan Malik baya aiki, gashi kuma Daddy kamar ma ya manta da batun nema masa aiki, Rayyan kam avoiding duk wani abu da zai haɗa sa da Leena da Mijinta, avoiding ɗin sa yake yi, sai dai bayan ko wani karshen wata yakan ma Leena transfern 70k, duk da cewa yanzu mata biyu gare sa Leena duk san da ta samu kuɗi kuma food stuff take fara siya tunda ba aiki yake yi ba, hakan yasa Umma ɗan sauko wa, Ammi ma duk sanda ta samu kuɗi akan Leenan yake kare wa, duk wani abu da ya shafi Malik Daddy yama mance balle ya sama masa aiki, gaba ki ɗaya rayuwa ta juya musu baya. Leena tayi sallama a parlorn Mami, Sultan yace "Shigo mana Maman Nawaf" tana kan shiga ta ga Farida ta mike ta wuce ciki da ɗan saurin ta, hakan ya bata mamaki dan ta taɓa ganin ta a wani taro amma ta ɗauke kai hakan yasa tace kila bata gane ta bane, ta karasa cikin parlorn taga ashe ba Sultan kaɗai bane harda Sadeeq, hakan yasa kawai tayi gaisuwar in jam'i tace "Ina kwanan ku" Sultan yace "Lafiya klau, Leena" ta ɗan kalle Sadeeq taga danna wayan sa yake ba tare da ya ɗago ba ta taɓe baki tana kallon Sultan tace "Uncle Mami fah?" Yace "Tana ɗakin ta, ki shiga mana" hakan yasa ta karasa bakin kofar ɗakin Mami tayi sallama, Mami tace "shigo mana" Leena ta shiga, Nawaf ta kalla yana kwance jikin Mami, ta karasa ta zauna bayan sun gaisa tace "Ya jikin nasa kuma Mami?" Mami tace "da sauki Leena" Leena idon ta na kan Nawaf Mami tace "Nawaf je ka gaishe da Amma ko?" Sai ya mika mata hannu Leena ta ɗauke sa tana kallon sa duk surutun Nawaf da bakin sa yau tunda ta gansa haka ta san yana jin jiki, a hankali tace "Sannu Babyn Amma ko?" Ya gyaɗa mata kai, sai kuma ta mayar sa wajan Mami ta miƙe, tana kallon Mami tace "Bari zan tafi Mami dama nazo duba jikin na sa ne" Mami tace "Yanzu baki son zama idan kika zo, ko fah ruwa baki sha ba amma kike maganar tafiya" tayi yake tace "Wallahi Mami gidan kawata Zahra zan tafi, tun da akayi bikin ta ban taɓa zuwa ba" Mami tace "Ayyah, ki gaishe min da ita" Leena tace "In Shaa Allah" har ta fara gaba sai kuma Mami tace "Idan yayi hutu a school zai zo miki" Leena ta tsaya tana kallon Mami tace "Ni Mami nake ga da an bari ya cika shekara uku tukun nan amma yanzu me Nawaf zai iya?" Mami tace "A'a babu ruwan ki, ko asara ne zan biya wa jika na" Leena na dariya ta mata sallama ta fita ganin yadda Mami ke son Nawaf har mamaki take, Mami ta bita da kallo ganin kamar ciki ne da ita, a compound ta ga Sadeeq shi kaɗai har zata buɗe gate taji yace "Leena!" Ta ɗan saya sai kuma ta juya tana kallon sa ya karasa inda take sai dai ya ɗan bada distance between them yace "I'm sorry" tace "For?" Yace "Everything" ta dinga kallon sa da mamaki a hankali yace "Na san nayi making mistake, let bygones be bygones, kawai dai at least da nace sorry tun daga farko, tun da nasan ban kyauta ba" tayi murmushi tace "Ni nama manta dan ban rike komai a raina ba shi yasa nayi moving up" yace "Thank you" bata kara ce komai ba ta fita, ta shiga Motar ta da tayi packing a kofar gidan kallon inda ta taɓa zama a wajan years back, yadda Sultan ya tsaya yana mata magana, murmushi tayi ta tada motar ta bar wajan. Bayan tayi parking a kofar gidan Zahra ɗaukan wayan ta tayi ta duba address ɗin dan ta tabbatar da house no. Ganin gidan ne yasa ta sauka gatekeeper ya buɗe mata gate ta shiga a kofar parlorn ta danna bell ganin ba'a zo an buɗe ba yasa ta kira Zahra tana dauka tace "Ke gani a kofar parlorn ki" tana katse wayar aka buɗe kofar, mamakin ganin wanda ta buɗe mata kofar yasa ta tsaya kallon ta, Niswa tace "Ohh really? Da gaske Leena kece kika zo min?" Leena ta sake zama frozen jin furucin Niswa, ta kirkiri murmushi Niswa ta kama hannunta ta ja ta suka shiga parlorn sai ga Zahra ta fito daga dakin ta ita ma tsayawa tayi, ganin inda Leena ke kallo yasa Niswa kallon wajan, sai kuma ta ga Zahra, ta sake hannun Leena har sannan kuma murmushin fuskanta bai ɓace ba tace "Ashe ba waje na kika zo ba ko?" Leena taji wani iri tace "Kai Anty Niswa" Niswa ta kama hanyar ɗakin ta tace "Eh mana, Nima nayi mamakin ganin ki, ai baki taɓa attempting zuwa min ba" sai Leena ta ji wani iri, jiki a sanyaye tabi bayan Zahra, bayan ta zauna tana kallon Zahra tace "kar dai Niswa ce kishiyar ta ki da kika bani labarin ta?" Zahra tace "Eh Nima ban san hakan ba sai bayan da aka yi bikin sannan nake ganin cewa ita ce, amma kamar ita bata gane Ni ba" Leena tace "Ai da kin gaya min" Zahra ta harare ta tace "Na faɗa miki? Ai na san idan kika sani ba zaki zo ba" Leena tace "Dan Allah Zahra kuyi zaman lafiya, ki bata respect tunda dama ta girme mu, beside Kinga ko a wajan mijin ku itace uwar gidan" Zahra tayi dariya tace "Sannu Leena uwar son a zauna lafiya, toh ce miki nayi ina raina ta? Ai naga ta canza ba kaɗan ba dan Kinga yanzu wajan 5 months nake gidan nan daga ni har ita muna avoiding abun da zai shiga tsakanin mu na raini" Leena tace "Sure, yanzu ba kamar yadda take a da bane" Zahra tayi dariya tace "Ashe dai mun sake samun karuwa?" Leena ta harare ta tace "Ban sani ba" tana kara jan veil ɗin jikin ta, Zahra ta mike, taje ta dauko mata drinks da snacks, can Leena kuma ta wuce parlorn Niswa, bata daɗe ba tayi mata sallama. Leena na shiga parlorn Ammi ta zube akan kujerar Ammi tace "Oops wallahi nagaji" Ammi tace "Sai kace wadda tayi tafiyan kafa" Leena tace "Ammi ba kin san Zahra mai mata ta aura ba?" Ammi tace "Eh Meya faru?" Leena tace "Wallahi ashe mijin Niswa ne, shi kuma ɗan uwan su Zahra ne" Ammi tace "Ikon Allah". Leena bata wani dade sosai a gidan Ammi ba ta wuce gidan ta, tun kafin ta gama parking motar ta taga ana waso da kayan su waje, da sauri ta sauka tana "Malam lafiya?" Ganin Malik yana zaune a gefe yayi tagumi yasa ta yi wajan sa da sauri tace "Zauji, meke faruwa ne?" Ya ɗaga jajayen idon sa ya zuba mata a hankali kamar mai raɗa yace "Wai mai gidan ne ya bada umurnin su fitar mana da kayan mu sbd yana bukatar gidan sa" Leena ta dinga kallon sa da wani expression tace "Mai gidan kuma? Ina gidan Daddy ne?" Yace "Sun ce an sayar da gidan ai" Leena ta mike tsaye tana unlocking wayan ta, Malik yace "Me zaki yi?" Tace "Zan kira Daddy mana" yace "No, don't" ta kalle sa sai kuma tace "Sai muyi ta zuba musu ido?" Masu fitar da kayan na aikin su basu fasa fitarwa ba duk da yadda Malik yace su basu notice ɗin kwana biyu amma sunce A'a suma umurni aka basu. Daddy with shock ya tsaya kallon Ammi yace "An sayar da gidan kuma? Yanzu ina ita Leena?" Ammi tayi shiru tana kallon wani wajen, Daddy ya fara kiran Rayyan, yana ɗaga wa Daddy yace "Rayyan ko zaka je gidan Leena, wai an sayar da gidan so masu gidan suna fitar da kayan su, kaje gidan kaga meke faruwa kafin na tura lawyer na dan ni ban sayar da gida ba" Rayyan was shocked
End Ads