ce ta kawo ta, Mummy ta dinga dariya tace "Kai Amina kina son gulma haka?" Hajiya Amina tace "Toh wallahi ban daɗe da shigowa garin nan ba, cewa nayi idan ban zo nan ba hankali na ba zai kwanta ba" Mummy tace "Ah toh, da kinyi missing" tafawa suka yi suna shekewa da dariya, Hajiya Amina tace "Can you imagine, na haɗu da Fatima ta ɗauke min kai, ina da niyyar mata magana naga tayi kamar bata sanni ba shi yasa na kama kaina Nima amma abun da mamaki wallahi" Mummy tace "Toh ai sai tayi, ke kika biye mata da har zaki mata magana yanzu ai maganin ki" Hajiya Amina tace "wallahi Banga laifin ta ba, ni na ja ma kaina". Daddy bai taɓa jin ransa yayi mugun baci ba irin na wannan ranan, akan meyasa Khadija zata masa haka? Gidan nata ne da har zata sayar dan taga yadda Malik zai yi, ya shiga motar sa a zuciye yana jin komai ma zai iya faruwa dan bai damu bama, tuki yake amma yana tunanin hukunci da zai dauka. Hajiya ta fito ga Leena a bayan ta sai Ammi dake rike da hannun Ayaan zasu je gidan Mami duba Nawaf, anan compound suka haɗu da Mummy ta fito raka kawarta Hajiya Amina sai shekewa suke da dariya kamar basu gansu ba, buɗe gate ɗin mai gadi yayi Daddy ya shigo da motar sa ko gama parking bai yi ba ya sauka, Hajiya ta kalle Ammi ganin yadda Daddy ke huci, sai ga Mama ta shigo gidan ita ma, ganin kowa a compound ɗin tayi hamdala dan yayi mata daidai, hakan ne zai sa ta fasa kwan kowa yaji warin, Daddy yayi kan Mummy kamar zai tashi sama yana huci dan shi hankalin sa baya kan Hajiya Amina infact bai ma ganta ba, Mummy ta ja baya ganin yanayin sa tace "Lafiya?" Daddy da karfi ya fara magana yace "Akan wani dalilin zaki tsayar min da gida sannan kisa a kore su daga gidan???" Rayyan da buɗe gate ɗin sa kenan ya tsaya kallon Daddy wato shima ya samu labarin kenan da sauri ya dafe kansa dan baya son ace sun samu matsala, jin furucin Daddy yasa Leena ta kalli Ammi da Hajiya, Ammi tace "Mu tafi Hajiya kar yamma yayi" Hajiya ta mata wani kallo tace "Kina jin abin da ke faruwa zaki ce mu tafi?" Daddy na kallon Mummy da wani expression yace "Ba zaki bani amsa ba?" Ta ɗan kalli mutanen compound ɗin sai kuma ta marairace masa tace "Haba dear, ka tsaya kaji mai ya faru amma sai ka hauni da faɗa a cikin mutane? Idan ba kuma Ni na sayar ba fah? Na tabbata wannan makircin matar ka ne" Daddy ya ɗaga hannu zai mare ta sai kuma ya sauke da sauri, Mummy wani kallo take masa, Hajiya Fatima ta matso kusa ta zube gaban Daddy ta fashe da kuka hakan yasa hankalin Mummy tashi tace "Ke kuma me haka? Ki tashi mu shiga ciki" ta karasa zata ɗago ta Mama ta warfe hannun ta, su Ammi dai suna tsaye suna kallon ikon Allah, Nisreen kuma jin hayaniya yasa ta fito dama tazo gida weekend, Mama ta fara kuka tana "Dan Allah Baban Rayyan ka yafe min" Daddy da mamaki yake kallon ta dan reaction ɗinta abin mamaki ne, Hakan yasa ke ɗaga wa Mummy hankalin, Hajiya ta gyara tsayuwar ta tace "wannan matar makira ce, kawar Khadija ce tun budurci, yanzu haka kila ta zo tonan asiri ne", Daddy yace "Please ki tashi, sannan yafiyar me kike magana akai? Kin min laifi ne?" Mama ta fara share hawayen tana sheshsheka tace "wallahi, tun da ka auri Maman Leena babu abin da be faru a gidan nan ba, yanzu na tuba kafin na mutu shine nake son kai, Hajiya, Maman Leenan, da ita kanta Leenan ku yafe min, kai hatta har da Rayyan ma ina so duk ku yafe min", Gatekeeper da gudu ya wangale gate ɗin motoci suka shigo compound ɗin wanda hakan yasa duk suka ɗaga kai suna kallon su da mamaki, dogare ne suka fara fitowa da gudu suka je suka buɗewa Granny kofar motar ta sauka, ga jakadiyar ta ma ta sauka daga wani motar ta karasa inda take da gudu, wasu daga cikin dogare suka wuce buɗewa mai martaba, Sannan sai ga wata mata wanda har sannan idon ta yayi mugun ja, ga kuma wani namiji da yake mid 60s ɗin sa, Ammi zuciyar ta ne ya fara bugawa da karfi ganin yadda gaba ɗaya mutanen suke kama da Leena, sai ga Suhaif wanda shima ya sauka kana ganin sa kaga Malik, hakan yasa Ammi taji kamar ba zata iya tsayuwa ba, Mummy tsabar yadda ta galalo ido waje zaka ɗauka wani abun ne ya faru, ta dinga bin mutanen da kallo dan kana ganin su kasan tabbas jinin su Leena da Malik ne, sannan kuma ka san cewa daga gidan sarauta suke, Malik da ya shigo gidan ganin su yasa zai juya, wannan matar da take mid 50s ɗinta ta kwala masa kira "Yarima!" cak Malik ya tsaya sai kuma ya juyo da gudu ta ta karasa wajan ta rungume sa tana mai fashe wa da kuka tace "Yarima kai ne wannan?" Mummy bata san sanda ta zauna dirshen a kasa ba, mai martaba ya taka har inda Daddy yake ya mika masa hannu, haka nan Daddy yaji shakkar sa da kimar sa ya mamaye sa, Mai martaba yace "Kai ne mai gidan?" Daddy yayi gathering courage yace "Eh nine" yace "Da farko ina mai baka hakuri shigo maka gida ba tare da izinin ka ba sannan har muka taso muka zo ba tare da consent ɗin ka ba" Daddy yace "ba koma" Mai martaba yace "Idan babu damuwa ina son zamu yi magana mai muhimmanci ne, ko zamu samu karɓuwa?" Daddy ya gƴaɗa masa kai yana nuna musu hanyar parlorn sa, Granny tana hango Leena ta karasa wajan ta ta rungume ta tana mai fashewa da kuka, sai kuma ta daga kai tana ma Malik magana da hannu yazo kuma har sannan tana rike da Leena, tace "Yarima kazo mana" Malik ya karasa wajan Granny wanda ta haɗa da shi da Leena ta rungume su tana kuka, duk mutanen haraban wajan suka garzaya zuwa parlorn Daddy.
Ban san ya ake yi ba nake long chapters two days ba, so please ayi min Voting Sannan a taya Ni Sharing.
*AGOLA (Behind the palace walls)*
A week later, Duk suna zaune a parlorn Daddy har ma da Mama ta tayi takanas dan jin ƙwaƙwaf, Rayyan ya mika wa Suhaif envelope ɗin hannun sa, shi kuma ya mikawa Family Doctor ɗin su, Dr. Saminu adjusted his glasses, cleared his throat slightly, then unfolded the paper slowly. Ga baki ɗaya parlorn was silent, especially Mummy tayi kuru dan ganin gwajin ba haka bane, All eyes were on him as he read aloud, "The DNA analysis reveals a 99.9% match between Malik and Baban Yarima... This confirms a biological parent-child relationship.’ Sai ya numfasa, duk parlon kallon Baban Suhaif da Malik suke cike da mamaki, Dr saminu glanced at Leena, Ammi taji bugun zuciyan ta ya tsananta, Dr saminu then continued, "Additionally, Leena’s DNA shows a strong genetic link with Hajiya Hauwa'u, known as Granny, indicating she belongs to the same family lineage. Ammi ta fashe da kuka, Malik ya dinga kallon Leena baya ko kiftawa, Umma ta kalli Malik sannan ta kalli Abbah, sai itama ta fashe da kuka, Granny ta sauka akan kujera tayi sujuda-shukr, Maman Malik ta tashi taje ta rungume Malik tana kuka kamar ranta zai fita, Malik felt a kind of peace and calmness wash over him, a feeling he had never experienced before, Without thinking, he wrapped his arms around her too, holding on tightly as if he never wanted to let go, Muryan ta na rawa tace "Yarima? Dama zan sake ganin ka?" Mai martaba yama Leena hannu akan ta je, ta kalli Ammi dake kuka sai kuma a hankali ta mike ta isa wajan sa, Granny bata yi wata-wata ba ta rungume Leena tana kuka mai tsuma zuciya, Mummy nan take taji wani zazzaɓi ya rufe ta, Rayyan kan sa ya mugun kulle wa, Does that mean Malik and Leena are actually siblings?, ya girgiza kai dan baya son ya fara believing nonsense thought ɗin sa, Mama ta furta "Alhamdu Lillah" tana kallon Mummy da ta gama haɗa zufa kamar wacca ta fito daga wanka, Suhaif ya taka har inda Maman sa ke rungume da ɗan-uwansa ya rungume su baki ɗaya yace "I'm truly happy to have you back with us" ya faɗa a hankali cike da kamewa a harshen sa sannan ya ɗaura "Alhamdulillah da Allah ya sake haɗa ka da mu a karo na biyu" Daddy ya kosa yaji meke faruwa dan gaba ɗaya a ruɗe yake kuma bai taɓa jin Ammi ta basa wani labarin game da Leena ba. Mai martaba yayi gyaran murya hakan yasa kowa nutsuwa, In very calm tongue ya fara magana duk da yawan shekarun sa hakan bai hana calmness ɗin sa bayyana ba yace "Nasan we all need karin bayani right? Dan nasan dole duk muna cikin ruɗani" yayi shiru, duk suka zuba masa ido, ya juya yana kallon Granny a hankali ya furta "Gare ki, Habibty na" Granny idon ta na kan Leena ta numfasa......! A cikin babban Masarautar Yola..*Mai Martaba Modibbo Barkindo* sarkin Yola, Bafulatani ne na asali, daga zuriyar Fulani masu sarauta. Mutum ne mai hankali da natsuwa, da son talakawan sa, yana da Mata biyu, amma yana da ɗabi’ar nuna ƙaunar uwar gidan sa a fili, har a gaban fadawa da 'yan majalisar fada yakan nuna mata tsantsan so, dan ya kan kira ta da "Habibity", abin da ke ƙara tayar da gwiwar amaryar sa.*Gimbiya Hauwa’u*, uwar gida, mace ce mai tsantsar tarbiyya da halin natsuwa. Ita ce garkuwar gidan masarauta kuma jigon zaman lafiyar Sarki. Ta haifi ’yan biyu *Yarima Abdallah Modibbo ɗan fari cikin 'yan biyu, Ana kiransa da "Yarima Mai shiru"* saboda yawan zama cikin natsuwa da rashin burin mulki. Shi ya fi son karatu da aikin office *Yarima Abdul-Aziz Modibbo ɗan biyu, mai kuzari da ƙwazo. Ana kiransa da *"Yarima Jallube"*, saboda irin rawar da ya ke takawa a fada da kuma sha’awarsa na gadon sarauta.*Gimbiya Zainabu*, amarya, mace ce mai zafin rai da ɗan hassada. Tana jin haushin cewa za a bar uwar gida ta haifi mai gadon Masarautar. Tana da yara biyu:*Karamin Yarima Usman* – ɗanta na fari. Ana kiransa da *"Yarima Fari"*, saboda siririyar fuskarsa da shigarsa mai kyau, Sai dai shima yana kishi da Yayun na sa. Tana da burin ganin shi ne zai gaji mahaifin sa. Sai *Gimbiya Indo* – ƙanwar Usman. Yarinyar da ke da natsuwa da biyayya, ta matuƙar shaku da Sarki. Ana kiranta da "Karama Gimbiya" a cikin fada. Masu tsatsuba a fada; Waliyi Musa Dankaka – ɗan uwan Sarki, wanda ke da ra’ayi cewa ‘ya’yan Hauwa’u ne suka fi cancanta da gadon sarauta. Fulani Rabi mai kula da gida, dafa abinci da ado. Ita ke cusa wa Gimbiya Zainabu shawara mai kaifi. Wasu daga cikin 'yan uwan Mai martaɓa duk suma basu goyon bayan yaran Hauwa`u da suke da gadon Masarautar, wanda hakan yasa suka haɗa kai da Zainabu suka ware Hauwa'u,. Wata rana Mai martaba na zaune duk suna zaune a gefen sa, ya kalli 'yan biyun nasa wanda Abdallah gaba ɗaya hankalin sa na kan wayar hannun sa, Hajiya Zainabu ta taɓe baki ganin kallon sha'awar da yake wa yaran sa kamar ita bata haifa masa yaran ba, Mai martaba a hankali furta "Yarima Abdallah" Abdallah ya janye idanun sa akan wayan hannunsa ya zuba wa Mahaifin na sa yace "Na'am Abbah na" Mai martaba yace "Kai ne Babba, kai ne kafi dace wa da Masarautar nan, kuma kai ne kake da aure, amma gaba ɗaya baka son wani abu daya shafi sarauta kalli kayan da ke jikin ka, baka kallon ɗan uwan ka Abdul-aziz ne?" Abdallah ya tsosa kansa yana kallon Mai martaba, dan shi a rayuwar sa bai fiye magana ba daga Mai martaba sai ɗan uwan sa ko kuma Ummin sa ta yadda mutane suke gane sa kenan dan ba karamin kama yake da ɗan-uwan nasa ba, a hankali yace "Ya Abbah na, a gafarce Ni, amma na sha faɗa bana son wannan Mulkin, akwai takura Ni kuma rayuwar 'yan ci nake bukata shi yasa nafi maida hankali na kan karatu da aikina" Mai martaba ya numfasa amma har sannan shi ɗin yake kallo saboda nutsuwar sa da hankalin sa yafi cancanci da ya hau kan kujerar sarautar fiye da ɗan-uwan na sa, ganin kallon da Mai martaba ke masa yasa a hankali yace "A gafarce Ni" Mai martaba yace "Abdallah ina ganin har yanzu baka gama tunani ba, zan cigaba da baka lokaci har sanda zaka fahimci menene Sarautar" Hajiya Hauwa'u tace "Ranka shi daɗe, a gani na tunda Abdullah ya furta baya so, ga kuma ɗan-uwan sa dake son duk wani abu da ya shafi sarauta gani na zai fi dace wa da shi" caraf Hajiya Zainabu tace "Abdallah aka ce ba Abdul-aziz ba, sannan ku bari idan har Abdallahn baya so ai shikenan, amma kiyi ta cusawa 'ya`yan ki" Mai martaba yayi gyaran murya ya mata wani kallo wanda hakan yasa tayi shiru Hajiya Hauwau tace "Kiyi hakuri idan magana ta tayi zafi" Abdul-aziz ya juya yana kallon Ummin sa sai kuma ya miƙe yace "Ummi kin mata laifi ne da har zaki bata hakuri? Ko kuma Shikenan ke baki isa kiyi magana akan ra'ayin ki ba?" daga haka ya bar parlorn, Abdallah ma ya mike ya bar parlorn duk Mai martaba yana kallon su amma bai ce kala ba wanda hakan be yi ma Yarima Usman daɗi ba. A yammacin wannan ranan Yarima Usman yayi sashin Mahaifiyarsa, a bakin kofar jakadiyar ta zube tana gaishe sa ba tare da ya amsa ba ya shige ciki, duk jakadan da suke ciki suka miƙe suka bar ɗakin, Hajiya Zainabu dake zaune tana shan fruit gefen ta kuma Gimbiya Indo ce, hankalin ta na kan chatting ta ɗaga kai ta kalli Yayan nata a hankali ta furta "Hey you" a takaice yace "Fine" Mahaifiyar ta su ta ajiye bowl ɗin hannunta tana kallon sa cike da so tace "Yarima mai jiran gado" da sauri Gimbiya Indo ta ɗaga kai tana kallon Mahaifiyar tasu sai kuma ta taɓe baki, shi kuma Yarima Usman murmushi yayi ya zauna gefen ta yace "Umma kina ganin hakan zai iya tabbata kuwa? Ko baki ga kamar Mai martaba baya kaunar na hau kan Mulkin bane?" ta ajiye sauran berries ɗin hannunta cikin bowl ɗin sa tace "Yarima kenan, kana ganin hakan ba zai kasance gaskiya bane? Toh barin faɗa maka wani abu, da ace su waziri da Fulani basu goyan bayana ne sai nace da kamar wuya, amma muddin suma basu kaunar wancan ɗakin su gaje sa ai shikenan" Gimbiya Indo ta ajiye wayan hannun ta tana kallon su tace "A gafarce Ni, Amma hakan tamkar son kanmu da yawa mukayi, maganar gaskiya an haifi su Yarima Abdallah tun kafin Mai martaba ya san zai aure ki Umma amma ace yanzu sai mu tsaya kishi Dan yana son Yarima Abdallah ya hau kan kujerar?" Wani kallon da Yarima yake mata yasa ta ɗauke idon ta akan sa, Umma tace "Toh uwar masu gaskiyar duniya, naga har yanzu Mai martaba bai ɗaukan ku da daraja kamar ba 'ya'yan sa ba, amma kina ganin yadda yake nunawa Hauwa'u da 'ƴaƴan ta soyayya a gaban jama'a" Gimbiya Indo ta mike tace "Duk da haka mu kar mu shiga hakkin su" Yarima ya yunkuri da sauri ta fita tana kiran jakadiyar ta. Yarima ya maida kallon sa ga Umma yace "Umma ya kamata kiyi duk yadda zaki yi kafin lokaci ya kure" ta shafa kansa tace "Baka da matsala" washe gari da safe mai martaba yana zaune Hajiya Hauwau ta shiga da breakfast ɗin sa ta zauna haɗa masa, tana serving ɗin sa amma idon sa akan ta yake, yana mamakin yau wajan shekaru nawa amma bata taɓa yarda masu aiki su dafa masa abinci ba, da kanta take masa, bayan ta gama serving nasa tace "Ranka shi daɗe na gama" ya sakar mata murmushi ya riko hannun ta yace "Har da wasu ranka shi daɗe ba kowa anan fah" itama murmushi ta sakar masa, Yarima Abdallah da Abdul-aziz ne suka shigo, hakan yasa Hajiya Hauwa'u kokarin cire hannun ta ana Mai martaba, kallon ta har sannan yake da mamaki yana kara mamakin kunyar ta har sannan, Su Abdallah basu ma gwanda sun ga wani abun bama sai ma zama da suka yi suna gaishe su, kana ganin su kasan daga gym suke, bayan sun amsa Mai martaba yace "Ku kun karya ne?" Abdul-aziz kaɗai yayi magana yace "A'a Abbahn mu, yanzu zamu tafi sai munyi wanka kafin mu yi" yace "Okay, na ɗauka ko zaku jona ni ne" basu sake cewa komai ba suka miƙe, Mai martaɓa yayi gyaran murya hakan yasa duk suka koma suka zauna suna kallon sa, dan sun san akwai abun da yake son faɗa musu ne yasa yayi gyaran murya, yana kallon su cike da kauna yace "Yanzu kai Abdul-aziz da kake son sarauta a haka zamu baka baka da aure?" Ya tsosa kansa yana kallon Abba sai kuma yayi murmushi, Mai martaba yace "A ce ɗan uwan ka yana da Mata har da 'ɗa amma kai kayi shiru, ko dan kaga bana cewa komai ne? Gaskiya idan har baka fito da mata ba Habibity zan sa ta kawo maka koma wacece, in kuma ba haka ba ba lalle ka wakilci Masarautar nan ba, dan kasan dokar Masarautar" ya gyaɗa kai yace "Zan yi making effort Abbah" daga haka suka fita zuwa sashin su, duk fadawan sai zube wa suke suna gaishe su amma Yarima Abdul-aziz kaɗai ke amsa wa, dan shi Abdallah takura ya ɗauki hakan, bayan sun karasa part ɗin nasa Abdallah