ganin har Rayyan yana bada cup wai a kara masa pineapple juice ɗin Mummy ta figi jakkan ta tayi hanyar kofa Daddy yace "ina zaki?" tace "Gida mana ai ina da abin yi na zauna anan kuma naga ai ya samu sauki" tana gama magana ta fita ko jiran me zai ce bata tsaya ba. Da rana Sadeeq na dinning yana cin abinci Sultan ya karasa inda yake ya na masa magana yayi banza da shi Mami ce ta shigo dinning ɗin ta zauna tana ta video call da Jiddah bayan zaman Mami ta mika ma Sultan wayan suka gaisa Sultan yace "Ke ban baki labari ba, yayan ki de yayi market wata shuwaArab ce ke son sa, ta makale masa kina ganin ta kinsan takai 40 years" ya kare maganar yana dariya Jiddah tace "Ai haba dai shine ba labari? Kace taga handsome shine ta ruɗe" duk abin nan ko kallon direction ɗin su Sadeeq be yi ba cin abincin sa yake hankali kwance Mami ta karbi wayan tana cewa "Ai yanzu kam ba zaku cika min 35yrs a gida ba idan ma baku da ra'ayi gwara kusa himma idan ba haka ba saidai kuji na kawo muku mata" Jidda ta fashe da dariya tace "Haba Mami ki musu hakuri ai gwara su kawo ɗin, ai shi ya Sultan da budurwan sa ya Sadeeq ne kuma sai anyi da gaske" daga Sultan har Jidda dariya suke Mami tace "Ah toh dai, gashi ɗazu aka kawo min goron tambayar Leena" wani zabura Sadeeq yayi har sai da Sultan ya tsorata kallon Mami yake yi ko kiftawa bayayi Kallo ɗaya Mami ta masa ta ɗauke kai Jidda tace "Eh lalle Leena kuma fah jiya sai da muka yi chatting bata faɗa min ba" Mami na dariya tace "toh taya zata faɗa Miki" Sadeeq ya sake spoon ɗin dake hannun sa Sultan sai studying ɗinsa yake ya ɗauki wayan sa dake kan dinning ya tura abincin baya ya bar wajan without saying anything daga Sultan har Mami suka bi shi da kallo Mami tace "ikon Allah" Jiddah tace "menene kuma" Mami ta bata labarin abinda yayi Jiddah tayi dariyar me isar ta ta fara ba Mami Labari..
Bayan Leena ta dawo a makaranta ta cire kayan ta tayi wanka sannan ta ɗauro alwala sai da ta fito ta duba wayan ta ganin missed call ɗin Muhammad har 3 kamar zata kira sai kuma ta ajiye wayan ta kama sallah bayan ta idar taci abincin sai kuma ta koma sashen Hajiya, Hajiya bata parlorn hakan yasa Leena ta karasa fridge ɗin Hajiya ta buɗe ganin kilishi Leena ta cire tana magana ita ɗaya tana mitan Hajiya tasa kilishi a fridge Hajiya ta fito ta kyankeshe ido tana nuna Leena ta yatsa tace "kin ga ko zanna hana ki shigo min daki tunda idan kika shigo sai dai ki ɗauke min abu ba dama nayi Ajiya sai kin lallaɓa kin ɗauka" Leena ta turo baki tace "bayan ma kin sa kilishin a fridge" Hajiya tace "nasa ɗin naki ne ko nawa" Leena tace "bayan ma yaya nane ke tsiyo Miki" Hajiya ta rike haɓa tace "ji wani munafurci sai yau kuma kika san da yayan ki? Ina ce rabon da kuyi magana tun yaushe?" Leena taki cewa komai ta mayar ma Hajiya kilishin ta fridge sai kuma tace "yauwa Hajiya yaushe zamu tafi duba yaya? Hajiya tace "ban sani ba" Leena tace "Haba Hajiyan mu, toh kiyi hakuri nayi alkawarin zan kawo Miki kaza anjima" Hajiya nan da Nan ta sake fuska tace "ni gaskiya bani da ra'ayin tafiya amma ki bari muyi sallan la'asar sai mu tafi ko?" Leena tace "toh shikenan nan Hajiya" daga haka ta koma sashen su kitchen ta wuce tana tunanin me zata dafa masa yanzu kuma. Fatima dake kallon Mummy tace "toh ban gane ba?" Mummy tace "Nima ina na gane, wallahi Uwar san nan tana shiga min gona da yawa ya za'ayi in haifi ɗa in gwada bana son yaci abu sai ta wani soma min bakin ta a magana ta wai ba ƴar uwar sa bace" Fatima tace "Kinga abin da nake faɗa Miki na cewa kinyi wautanci da kika gwada baki son Leena tayi aure yanzu" tace "Dan Allah mubar maganan nan wallahi bana son tunawa" sai kuma tayi shiru tana tunanin yadda tayi magana wancan ranan ta kalli fatima tace "mukam yaushe zamu je wajan mutumin nan ne? Ni wallahi na kara tsanar yarinyar, Shegiya har da dafa masa abincin dan uwar ta" Fatima tace "toh kuma kince basu magana" tace "wallahi har masu aikin gidan nan nasa su sakamin ido koda bana nan idan ya mata magana amma sunce tun ita ke masa magana har ta hakura, kuma duk su Nisreen sun shaida hakan" Mummy tayi shiru Fatima na wani tunani a ranta Mummy ta cigaba tace "Kinga ko sabar haushin da ya bani shiyasa na bar asibitin ai sai uban nasa yayi ta zama da shi" Fatima tayi wani dariya tace "Ni fah a gani na ki bar ƴar nan kawai ta aura mutumin nan dan wallahi Ni de a hasashe na naga kamar Agolan tana son ɗanki ne Kinga kar ki lalata auren ta, ta koma soyayya da ɗanki, idan tace tana son sa tun baya kula ta har ya fara kula ta ɗan wallahi ba'a shaidan na miji akan mace" ta kare magana tana dariyar mugunta Mummy ta mata wani kallo tace "ai dadin abun Wallahi Rayyan baya sallake maganata kuma maganan na hakura ai kenan na yarda naga ci gaban tane dole na sa a fasa auren kuma ina da tabbacin Rayyan ba zai kula ta ba saboda baya taɓa sallake magana ta, idan auren nema yake so me zai hana a haɗa shi da ƴarki Layla" Fatima da ta fara hango possibilityn hakan jin za'a haɗa da ƴarta layla yasa tayi shiru tace "wallahi kuwa dan Layla ba zata ki zabi na ba, kawai shiryawa zaki yi muje wajan mutumin nan ayi mana aiki yi da gamawa" Mummy tace "kamar anyi an gama ne" ta kare maganar tana murmushin mugunta. Har Leena ta gama dafa tuwon semovita and vegetable soup ta zuba a kula ta wuce toilet tayi wanka tasa kaya tana cikin sallah taji Hajiya na magana a parlorn su tace "Ni ba haɗa abu da Leena bane kayi ta jiran ta sai sanda ta ga dama zata shirya" Ammi ta fito jin muryan Hajiya tace "barin duba Miki ita" Ammi na shiga ɗakin Leena taga Leena ta idar tana evening zikr ne tace "toh Kiyi sauri ko kuma ki karasa a mota" sannan ta koma parlorn tana cewa Hajiya gata nan fitowa, after some minutes sai ga Leena ta fito cikin royal blue Abaya sai da Ammi ta sake kallon ta dan wani kyau na musamman ta kara Hajiya tace "Ah dole ki daɗe irin wannan kwalliyan Leena? Mara lafiya fa zaki je gaisar wa ba gasan kyau ba" Leena bata bi ta kan ta ba ta wuce kitchen sai gata ta fito da Abinci a cikin basket Ammi sai kallon ta take dan bata ma san sanda tayi abinci ba ma Leena ta sauke kanta kasa bata so su haɗa ido da Ammi ta karasa cikin parlorn tace "Ammi sai mun dawo" driver ya buɗe booth yasa basket ɗin abinci Leena ta shige gaban mota Hajiya kuma ta zauna a baya....
Kar a manta ayi voting, please!
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
20.......
Rayyan da ke kwance shi kadai a ward ɗin, He can't get enough of her videos and keeps watching them over and over , ji yayi an buɗe da sauri He angled his phone downward to see who was entering, Hajiya na gaba Leena na biye da ita a baya suka shiga ɗakin, Rayyan ya kalli Hajiya sai ya mayar da duban sa ga wanda yake bayan Hajiya, He has been looking at Leena with admiration har sai da ta fara feeling self-conscious a ranta take ayyana meyasa ma tayi kwalliya Hajiya ganin rashin kunya Rayyan yasa taja kujera ta zauna tace "ya Jikin naka dai Riyan?" sai sannan ya kalli Hajiya yace "Alhamdulillah da sauki Hajiya" Leena na wasa da fingers ɗinta ta saci kallon sa taga ita yake kallo tace "ina wuni" yace "Lafiya kalau" tace "ya jiki?" Yace "Alhamdulillah" ta cigaba da tsayuwa anan wajan Hajiya tace "Toh ba zaki kai masa abincin da kika dafa masa ɗin bane?" sai sannan Leena ta ɗauki basket ɗin takai gefen gadon sa ta ajiye yana kallon ta still yace "Thank you, Leena" tace "it's a pleasure" sai ta koma jikin window ta tsaya, Hajiya ganin kamar yana son ma Leena magana yasa Hajiya tace "barin je wani daki zan duba jikan wata makwabciya ta itama ba lafiya" Leena ta ɗaga kai tana kallon Hajiya sai tace "in zo mu tafi tare?" Hajiya tace "idan kika biyo ni me zan Miki?" Leena ta koma jikin windown ta bayan Hajiya ta fita can wani waje ta samu ta zauna, Leena dake kallon waje ji kawai tayi mutun a kanta da sauri ta juya tana kallon sa ya dafe dayan hannunsa da gefen ta Leena ta tsorata sosai da ganin yana yin sa Leena's words came out in a shaky voice, "what is this, Ya Rain?" Rayyan yace "I've been hospitalized and medicated, all because of the stress and emotions You've stirred up in me" Leena ta girgiza masa kai da sauri, ganin zata gudu ya dafe ɗayan hannun nasa ta yadda ba yanda zata iya masawa ba tare da shi yayi niyya ba, yace "Leena why would you choose someone else over me? Don't you know how much I love you? Please don't marry him, Leena, My heart belongs to you.
Leena I'm begging you to consider my feelings, I don't want to lose you" Leena ta yi kuka yazo mata shima daurewa kawai yake yi tace "Ya Rai, if you truly loved me, you'd be there for me, not avoiding me, you've changed me in ways I never thought possible, but not for the better" ta share hawayen ta ta cigaba tace "I've had to find strength and overcome challenges on my own because you're been absent" Rayyan yace "Leena, I'm trying to be honest with you about how much you're affecting me, Leena ba zaki gane ba" tana kuka bata san lokacin da ta rike shi ba tace "I couldn't hide anything from you, I didn't know what love was back then, but I've grown up with the love you've shown me" Rayyan ya fara share mata hawayen ta yace "Leena ba zaki gane ba ne but You're the one I've been waiting for, Leena; that's why I never married" She was crying so hard that she hugged him tightly without even realizing it, He gentle patting her back, trying to calm her down, buɗe kofar ɗakin akayi da sauri Rayyan yayi baya Leena ta sunkuyar da kanta kasa Daddy ya karasa cikin ɗakin ya zauna yayi kamar be gansu ba Rayyan jiki ba kwari ya koma kan gado sai de be kwanta ba kawai ya zauna Daddy yace "Ya jikin naka Son?" Rayyan yace "Da sauki yanzu?" ji yake yanzu wajan 50% of his worries sun ragu Leena ta gagara ɗaga kanta balle ta gaishe da Daddy Daddy dake kallon ta yace "Daughter ba magana ne?" Sai sannan Rayyan ya ɗaga kai kalle ta sai daya kusan dariya ganin yadda take wani abu, Leena taki ɗaga kai ita ji take kamar katsan ya tsage ta shige ciki sabar kunya tana wasa da hannun ta tace "Ina wuni Daddy" yace "lafiya, ashe kin zo" kai kawai ta gyaɗa masa sai ga Hajiya ta shigo da sallama Daddy yana kallon ta yace "ashe kina nan Hajiya" tace "Eh, na ɗan fita na wasa kafa ne" yace "Ayyah, sannu Hajiya" tace "yauwa, dama fah Lina ce ta dafa masa abinci tace zata kawo masa shine na rako ta" yana kallon Leena yace "ai ta kyauta dan naga yau ya wuni yana cin couscous ɗin da ta masa da safe ma" Hajiya tace "bari toh mu tafi mun bar driver tun ɗazu" Daddy yace "Toh shikenan shima yanzu jikin da sauki colleagues ɗin sa ma sun ce yau zasu sallame sa ina ga dai yanzu za suyi ma" Hajiya tace "toh Allah yasa" tana kallon Rayyan tace "sai anjima Riyan" kai kawai ya gƴaɗa mata Leena har tayi sauri ta fita. Suna hanya Leena gaba ɗaya she's absent-minded Hajiya ta lura da hakan amma sai tayi burus da ita. Bayan sun dawo gida ta sami Ammi a parlor tana koyawa Ayaan karatu Leena ta sauke idon ta kasa gani tayi kamar Ammi taga scene ɗin ta da Rayyan ta karasa ciki tace "Ammi ina wuni" Ammi tace "Lafiya" daga haka ta cigaba da lesson wa Ayaan Leena ta ɗan kalle ta taga bata ko ta kanta sai kuma taji ba daɗi ta wuce ɗakin ta kawai ta kwanta a kan bed ɗinta ta rufe ido amma ba bacci take ba tunani iri da kala ke yawo a kwakwalwan ta tana nan a haka har aka fara kiran Magrib ta tashi ta shiga toilet dan yin alwala da ta tuna abun da ya faru kuma a haka Daddy ya shigo ya gansu sai taji kamar tayi kuka. Bayan Magrib sai ga Daddy da Rayyan da aka sallama a asibiti, yanzu Rayyan zai iya cewa yaji damuwar sa ya tafi sosai sai dai fargaba ne kaɗai ya ragu masa, anan parlorn ya zauna akan cushion ya jin gina da kansa ya rufe ido Niswa da Nisreen suka fito da gudu suka yi kansa sai sannan ya buɗe ido yana kallon su suna tambayar sa ya jiki yace "Ya school, ya studies ɗin?" suka amsa masa da Alhamdulillah Daddy na kallon Niswa yace "ina Maman naku?" Niswa tace "tana ciki". Bayan isha'i, Leena ta wuce kitchen ta fito da kayan haɗa shayi duk ta zuba a tukunya ta ɗaura akan gas ta koma cikin parlorn tana jira ya tafasa after some minutes ta fara jin kamshin shayin hakan yasa ta wuce kitchen ta haɗa ta juye a wani ƙaramin tea flask ta fito zata kai masa taji Muryan Ammi har tsakiyan kanta "Where are you going, Leena?" Chak ta tsaya ta juya tana kallon Ammi and she remained silent, staring at Ammi, "Am I not asking you something that you're just going to keep mute for me?" Ammi said kuma a ɗan tsawace, Leena ta girgiza mata kai because Ammi doesn't sound funny today ta ɗan kalle Ammi ganin amsar ta take jiran ji tace "Ammi I'll take tea to Yaya" Ammi ta gyara tsayuwar ta tana kallon ta tace "Well, when did you become Rayyan's mother? I wasn't aware of that," Leena ta kalli Ammi jin abinda ta faɗa tace "Ammi kawai tea zan kai masa fah" Ammi tace And so? ba ke bace breakfast, lunch yanzu kuma harda Dinner? So I have to ask, when did you became his mother? Or should I say, his cook?" Leena ta girgiza kai Ammi tace "so, yanzu har can part ɗin nasu zaki je ki kai masa ko?" Leena tayi shiru Ammi ta mata tsawa tace "Aren't I asking you?" Leena duk ta tsorata da lamarin Ammin na ta tace "You are" Ammi tace "well, ki kai masa, amma daga yau karki sa ke zuwa nan kina kawo min karan Mummy or su Niswa, Okay?" Leena tayi shiru Ammi tace "ki faɗa min yaushe ne kika taɓa zuwa part ɗin su basu Miki illa ba?, ina akwai lokacin da kika bi shi Rayyan ɗin haka Mummy ta Miki duka ta fasa Miki baki, akwai lokacin da sai da ta tara Miki jini a ido, shi kansa Rayyan ɗin sai daya daina miki magana Ni kuma idan ba haɗuwa mukayi ba yaga mun haɗa ido ba to shine zai gaishe ni, ya daina shigo min nan kamar yadda ya saba, shine yanzu ga ki ƴar iya ko? Allah bada sa'a sai kin dawo" Leena stayed silent, ta san abinda Ammi ke faɗa haka ne and she was trying to protect her aware of Mummy's disapproval or perhaps even hostility towards her ta juya jiki a sanyaye ta kama hanyar kitchen zata mayar da flask ɗin Ammi tace "ko kaɗan bana hanaki yin aikin Alkhairi sai dai zuwa can ɗin ne gaskiya ba zan lamun ta ba, dan yanzu bana jin zan iya hakuri idan har ta sake Miki abinda take yi a baya" Leena softly tace "thank you Ammi, I know you're just protecting me from Mummy's harm, I'll not go" daga haka Ammi tace "kin kyautawa kan ki" ta wuce ɗakin ta bayan Ammi ta shige Leena ta fara tunanin ko ta kira shine a waya yazo ya karɓa sai kuma ta tuna bata da numbern sa fita tayi ta wuce ɗakin Hajiya ta same Hajiyan bata ma parlorn ta ɗaukan wayan tayi ta shiga searching Rayyan ganin number yasa tayi copying ta koma part ɗin su ta zauna a bakin gadon ta sannan tayi dialing numbern sa sai daya kusa katse wa taga ya ɗaga shiru yayi alamar be san numbern ba tace "Yaya" Rayyan dake kwance a ɗakin sa be san sanda ya tashi ya zauna ba yace "Leena" tace "Uhm, dama shayi na dafa maka ka, zaka fito ka karɓa ne?" yace "okay, right away" in da ta ajiye flask ɗin ta nufa ta dauka ta koma ɗaki tana jiran kiran sa sai kuwa ya kira tana ɗauka yace mata "Baby gani ta bayan part ɗinku" sai kuma taji wani iri da kiran ta da baby da yayi ta mika ta tafi inda yake ta mika masa ya karba yana mata Murmushi yace "Thank you, Leena" irin kallon da yake mata ne yayi flashing scene ɗin su na ɗazu a asibiti nan take taji wani iri bata gama fita a wanann self-conscious ɗin ba sai ga Daddy daya fito a part ɗin Hajiya za shi part ɗin sa Daddy kallo ɗaya ya musu ya wuce Leena sai kuma yanzu