x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 33 - AGOLA free pages

  • 96001 words
  • 99000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
sai kuma yace "Na meye?" Sultan yace "Result ɗin Leena mana, ai jiyan ban samu na Ciro ba saboda na manta scratch card ɗin a gida" Sadeeq yace "Oh, Okay" ya karba ya buɗe yana kallon excellent performance din wife ɗin sa Sultan yace "Congratulations to her, yarinyar she's so genius wallahi, is hardly ka ga mutum with flat A a WAEC ɗin sa" a takaice Sadeeq yace "Thank you" ya wuce, Sultan yaja tsaki yace "zaka kuma nema na ai" Sadeeq bai tanka sa ba. Bayan kwana uku har sannan Leena na gidan Mami, ba yadda Sadeeq be yi ba amma Mami ta hana sa matar sa saboda jikin nata.

*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr



38......
Bayan Sadeeq ya koma da matar sa, har sannan jikin nata yaki sauki gaba ɗaya Sadeeq he is so disturbed babu wani peace tattare da shi, daga karshe ma hutu ya ɗauka a wajan aiki yana jinyan ta. Ya fito daga kitchen rike da cup din tea da soyayyen egg a plate, ya karasa har cikin parlorn ya duka gaban ta yana kallon ta yace "Sannu Wifey" da idanu kawai take bin sa yace "Gashi na gama ki daure ki sha Please" ta dauki cup din ta kai bakin ta ta ɗanyi sipping sai kuma ta ajiye ta dauki egg ɗin tana kaiwa baki da sauri ta cire tana kallon sa sai kuma ta marairace masa tace "toh baka sa pepper ɗin ba" yace "Baby na saka, kila toh be fita bane" ta ture plate ɗin gefe ta fara sipping tea a hankali har ta gama yana kallon ta yace "toh baki taɓa egg ɗin ba" kai kawai ta gyaɗa masa ya ɗauka yana mika mata tace "ba zanci ba, be yi min yadda nake so ba" Sadeeq kallon ta kawai ya ke yace "To na sake soya Miki wani?" ta girgiza masa kai ta kwanta nan kasan parlorn, yayi tagumi yana ta kallon ta shi gaba daya tausayi take basa gashi bata iya cin komai sai zallan tea shi dinma mara Madara. A daidai kofar gidan su yayi parking ya juya yace "Mu shiga" Fuskar ta a daure ya ke ta sauka shima ya sauka, gatekeeper ya buɗe musu gate yana gaishe su, bayan sun shiga parlorn Niswa ce kadai a parlorn tana kwance tana danna waya da sauri ta daga kai jin an buɗe kofar da mamaki take kallon Rayyan sai kuma ta ga Layla a bayan sa ta mike da sauri taje ta rungume sa tana cewa "Ohh, I miss you tons, Ya Rayyan" sannan ta sake sa murmushi yayi yace "ban yarda ba" Layla ta daure fuska kamar bata taɓa dariya ba a rayuwar ta, Niswa ta saci ganin ta, ganin har ta zauna yasa tace "Yaya ka san sai yanzu naga alert ɗin, dan tun dazu data na a kashe" yace "It's Okay, ba kowa ne?" tace "Suna nan" daga haka ya fara tafiya dakin Mummy sai kuma yace "baku gaisa ba" tace "Ahh ai zamu gaisa" daga haka ya wuce ta koma ta zauna kan kujera ta ci-gaba da chatting dinta tana wakan ta. Bayan ya shiga dakin Mummy, Mummy ta saya kallo sa da mamaki tace "Rayyan kai ne?" ya zauna akan wani stool yace "Ina wuni, Mummy" tace "Rayyan shikenan daga aure ka manta mu, har ya kai ga blocking dina kayi? Saboda yanzu kuma baka buƙatar mu?" yayi shiru yana kallon ta sai kuma yace "Mummy I don't know what comes over me, but mostly manta komai nake, gaba ɗaya I'm not myself" sai kuma ya karasa inda take zaune yace "Mummy kina min addu'a, Please" Layla sai hararar ta take yi sai kuma tayi ƙwafa, Niswa ta mike tace "Say your mind kar ki mutu da bakin ciki" Layla tace "wallahi uwar ki zanci idan har kika ce zakiyi da ni toh" Niswa tace "Allah ko? Toh ai Hajiya Fatima zata fi matching da zagin nan" Layla ta mike ta daga hannu zata mare ta sai ga Rayyan ya buɗe dakin Mummy yana fitowa, Mummy na biye da shi a baya da sauri ta sauke hannun ta ta koma baya ta zauna Niswa taja tsaki tace "Ashe karyan iskanci ne" daga haka ta wuce ciki abin ta. Mummy dake amsa gaisuwar Layla Rayyan ya wuce sashin Hajiya ya bar su nan. Hajiya ta daga kai tana kallon sa har ya karasa cikin parlorn ya zauna tace "Alhamdulillah, wallahi ashe abun da mutumin nan yace min gaskiya ne" Rayyan sai kallon ta yake da mamaki, ya gaishe ta tace "Rayyan ka dage da addu'a, sallahn dare da sadaqa" yayi shiru yana kallon ta yana nazarin me take cewa, tayi mishi tsawa tace "Ina maka magana zaka mayar da shi shashasha, rabon ka da gidan nan tun yaushe? Ina ko Uwar ka bata damu ba, Ni ne nan da naga abun ya fara wuce misali tun kafin tafiyan tayi nisa naje na karbo maka magani, so ake a juya tunanin ka da kuma hankalin ka, amma ina maka magana zaka wani tsare Ni da ido, waye bai san uwar Layla ba da bin bokaye" Har ta gama magana Rayyan be daina kallon ta ba at this point mamaki ne karara a fuskar sa yace "kiyi hakuri Hajiya, ban fahimta bane da farko" tace "Ah toh, ji yadda ka wani zabge lokaci daya, saura kiris ka manta da mu ma gaba daya a rayuwar ka amma dake Allah na son ka sai ya tura ni" tayi shiru sai kuma da sauri tace "Kana ma addu'a kuwa?" yace"ina yi, Hajiya" tace "Toh ka kara, dan kana cikin masifa tukuru" ya gyada kan sa yana son ya fahimci me take nufi. Bayan Sadeeq ya dawo daga siyo mata yalo, tana nan kwance ya mata sannu sannan ya wuce kitchen ya wanke yalon ya yanka mata ya zuba a plate sannan ya sake dawowa parlorn da kyar ta iya tashi ta jingina a jikin cushion dan yanzu bata ma iya zama yana mata sannu ta dauki slice daya ta kai bakin ta tana taunawa a hankali har ta cinye ta kara kai hannu zata dauki daya da sauri zata mike ta gagara kawai ta fara amai a nan wajan Sadeeq yaji ina ma zai iya dawo da laulayi kansa sabar yadda yake tausayin ta, bayan ya gyara wajan ya feshe da air freshener yana mata sannu yace "Baby toh ko zamu zubar da cikin ne, sai ki samu ki huta da wanna laulayin?" da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka a fuskar ta yasa hannu ya share mata yace "Shikenan ida mun zubar zaki ihuta" ya jata jikin shi ta kwanta nan da nan bacci ya ɗauke ta. Sai yamma Rayyan ya sake komawa gidan da niyyar daukan Layla su koma gida ya shiga parlorn be ga kowa ba sai Niswa a spot din ta yace "Ina take?" ta taɓe baki tace "tana dakin Mummy mana" yace "ki mata magana ta fito" ya zauna akan kujera yana kallon ta ganin haka yasa ta mike taje ta sanar mata sai gashi ta fito Mummy na biye da ita yace "Kin ma shiga kin gaishe da su Hajiya?" ta ɗan kalli Mummy sai kuma tace masa "A'a" yace "and then Why?" Mummy tayi carab tace "Toh ita kuma ina ruwan ta da su? Naga su ai ba dolen ta bane zaka wani sa ta gaba kana tambayar ta?"  Strictly yana kallonta yace "Muje" tama Mummy sallama suka fita daga haka, hanyar side ɗin Hajiya ya fara yi, Layka tana harararsa tabi bayan sa bayan sun shiga ta gaishe da Hajiya, Hajiya ta amsa mata, Rayyan yace "Dama zamu tafi ne" wuff Layla ta mike Hajiya tace "Toh Nagode" Layla na fita Hajiya ta ja Rayyan har dakin ta shi dai yana bin ta da kallo ta dauki wani kullin laida tace "Ka tabbatar kana wanka da shi Riyan har na tsawon kwana bakwai, kuma ka dage da addu'a da sadaqa dan wallahi ana shirin halaka ka" ya gyaɗa kai yace "Nagode Hajiya" tace bakomai. Bayan ya fito ya samu Layla har ta wuce parking space ya karasa dakin Ammi yayi sallama Ayaan ya fito da gudu Rayyan ya daga sa yana masa dariya yace "ina Ammi?" murya ta ya ji tace "toh ka shigo mana Rayyan" Rayyan ya shiga parlorn da sallama ya zauna yana gaishe ta ta amsa tana tambayar sa ya amarya murmushi kawai yayi, ya mike ya sauke Ayaan yace "bari zan wuce Ammi" tace "Toh ma shaa Allah, Allah bada zaman lafiya"  Rayyan ya tsinci kansa ya gagara cewa Amin yana wasa ma Ayaan ya fita. Bayan ya shiga Mota yaga ta haɗa rai ko tanka ta bai yi ba ya tada motar. Sadeeq yayi parking a kofar gidan su ta dalilin kiran da Mami ta masa ya shiga parlorn da sallama ba kowa, Farida ta fito daga kitchen ɗan ware ido yayi yana kallon ta tana murmushi ta karasa cikin parlorn tace "Ya Sadeeq, oyoyo" yace "Yaushe kika zo kuma?" tana murmushi tace "Jiya da daddare Flight dinmu yayi landing" yace "Toh Ma shaa Allah, karatu fah?" tace "Na gama ai, just of recently na rubuta paper" yace "Ma shaa Allah, sai kuma University yanzu ko?" Sultan ya sauko kallo ɗaya ya musu ya ɗauke kansa ya wuce dinning tace "Eh, da ina tunanin tafiya Harvard university, da ke Cambridge america ne" yace "Success lil sis" tace "Thank you, sir" ya wuce dinning yana kallon Sultan yace "Ba magana ne" yace "How are you doing?" Sadeeq yayi banza da shi ya wuce dakin Mami bayan sun gaisa ya sunkuyar da kansa yace "Mami dama wani tunani mukayi shine muka yanke shawarar cewa kawai zamu cire cikin jikin Leena saboda ta samu sauki" Mami ta sake baki tana kallon sa without blinking ya ɗan daga kansa jin Mami tayi shiru yaga kallon sa take ya sauke kansa kasa Mami tace "Ban taɓa ɗauka cewa girman ka na banza ba ne sai yau, dama baka da tunani kwatakwata? Yanzu ace wannan cikin kaɗai Allah ya baku sai kuma kuka cire ya zaku ji daga baya? Mutane da yawa suna nema Allah be basu ba amma ku kun samu Allah ya baku shine sai ku cire?" ya shafa kansa yace "Mami wai naga wahala take sha ne, ga shi na gagara komawa aiki kuma ba abinda take iya yi sai an taimaka mata" Mami ta masa tsawa tace "Toh kuje ku cire tunda kaima ba hankali gare ka ba, naga saboda da ita nasa aka kawo Farida tunda kace ba ka son mai aiki" yayi shiru sai kuma yace "In Shaa Allah Mami ba zamu cire ba" sabar yadda ranta ya ɓaci ta mike ta fita without uttering a word, Sadeeq ya bita da kallo sai shima ya mike ya bi bayan ta. Da daidai kofar gidan su Yayi parking Babban motar sa Pagani Zonda HP Barchetta, escort ɗin sa motar guda biyu su ma sukayi parking, ya cire ƙafan sa daya sannan ya sauka daga motar, Yana sanye da sleek black suit da crisp white shirt, idanun sa sanye ya ke da black designer shades, takalmin sa pair of luxurious black leather oxfords, polished to perfection. Hannun sa yana daure da simple yet elegant watch adorned his wrist, ciro wayan sa yayi a aljihu and dialed her number, tana daga wa tace "Darling! Ka iso ne?" Instead sai yace "I'm outside your place" tace "Alright, boo" daga haka ya kashe ta mike tsaye da sauri tana kallon Mummy tace "har ya iso" Mummy tace "Toh yi maza ki shigo da shi". Tana karasa gate ta hau masu gadi da masifa akan meyasa ba su buɗe masa gate ba sai kuma tayi sauri ta buɗe don karta bata masa lokaci, tana buɗewa ta gansa tsaye nan da nan murmushi ya cika fuskan ta ta karasa har inda yake tsaye sai kallon ta yake kamar me raɗa yace "Babe, you look beautiful" ta rufe bakin ta da hannu biyu tace "Awwwn, You're stunning as well, ka gan ka ne?" still yana kallon ta yace "Your style is gorgeous Niswa, and you're the sunshine in my life" ta rufe fuskan ta sai kuma tace "Mu shiga kar kayi ta tsayuwa" ya juya yaga daya daga gard dinsa without saying a word sai gashi ya karasa da sauri daga haka ya bi bayan Niswa. Bayan sun shiga parlorn Mummy ya zauna kan kujera itama ta zauna tana facing dinsa tace "Ya hanya" kai kawai ya gƴaɗa mata hade da murmushi sanin kuma ba zai ce komai ba ta kira mai aikin su a waya ta fito ta jera masa kuloli da ke dauke da different dishes, a hankali yace "No, Niswa! I'm full, naci abinci a guest house dana sauka" ta ɗan bata rai yace "Haba mana" daga haka ta mike zuwa kiran Mummy. ya ɗan ja akan kujeran amma be sauka ba ya gaishe ta ta masa tana tambayar sa ya hanya daga haka ta koma ciki abin ta. Yana kallon Nisreen da take gaishe shi yace "Nisreen, right?" ta gyada masa kai yace "Good" daga haka ta koma ciki. Bayan ya gaishe da Hajiya da ya tashi tafiya ya ajiye mata 1k notes a gaban ta Hajiya zata yi magana yace "It's Okay Kaka" daga haka ya fita har bakin motar Niswa ta raka sa tana kara jin son sa. Bayan ya buɗe parlorn suka shiga yaa kallon Farida yace "Farida ga can dakin da zaki zauna" tace "Okay, Yaya" yana nuna mata corridor yace "zaki samu kayan mopping sai ki gyara dakin Please" tace "Okay, Anty amaryan fah Yaya? Sai na gaishe ta" yace "I guess tana bacci ne" daga haka ya wuce dakin sa ya sami Leena na kwance amma ba bacci take ba ya karasa har inda take yace "Baby, ya jikin?" ta juya masa baya yayi murmushi ya zaga inda ta juya yana kallon ta kamar zata yi kuka tace "ba zamu je a cire ɗin bane?" ya zauna yana kallon ta yace "Mami tace kar a cire, Leena" ta dinga kallon sa ya jata jikin sa ya fara mata bayanin yadda suka yi da Mami tayi shiru tana tana kallon wani waje, yace "Yauwa tare mu ke da Kanwar Sultan, sunan ta Farida, Mami tace zata na aiki kafin ki samu sauki, itama yanzu ta gama paper" ta tashi ta zauna tace "Ayyah, thanks to Mami, maganar nema min makaranta kuma fah?" ya ja hanci ta yace "sai kin haihu tukun nan, not now da baki da lafiya" ta bata rai ta kwanta ta juya masa baya, murmushi yayi kawai ya mike dan yaga alama yanzu abu kaɗan ke bata mata rai. Mummy tace "toh ke yanzu ba zaki ce masa ya turo iyayen sa bane? Ga dama ta samu zaki sa ya gudu" Niswa tace "Haba Mummy, kawai sai na ce masa ya turo iyayen sa? Haba mana tunda yana so na ai da kan sa zai fada ma" Mummy tace "So kike ya kubuce mana? Ke baki jin yadda ake ta maimaita Leena ta shiga familyn masu kuɗin ne wai" Niswa tayi ƴar dariya tace "Lallai kuwa ashe idan sun sa waye Ashraft zasu kasa bacci" Mummy tayi dariya tace "toh ai shi yasa nake so mu kama sa dam a hannu" tace "Mummy Kinga yadda ƴan mata ke son sa? Toh wallahi tunda kika ga har ya zo nan ina mai tabbatar Miki yana mugun so na ne, da hankali zan fada masa Daddy na neman sa" Mummy ta tashi tana guda ta wuce dakin ta farin ciki fal a ranta.


Assalamu alaikum, 'yan-uwa na mutanan arziki! Da fatan kuna cikin koshin lafiya? If so then, Ma Shaa Allah. Satin nan gaskiya zaku na jina On and off ne, saboda nayi tafiya ne muna da biki, ina fatan zaku fahimce ne, Nagode.

*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


*Hauwa Jibrin Sulaiman*
_Jiddatul-khayr_


*CHAPTER 39*

Assalamu Alaikum everyone, I'm back! I want to apologize for the short break and lack of updates. I know it's frustrating for readers to be left hanging, and I'm truly sorry for that. Life got busy with my sister's wedding, but that's no excuse. I promise to make it up to you and won't stop writing until we reach the end of this book. Thank you for your understanding, patience, and support. May Allah grant me the strength and opportunity to continue sharing this story with you. May He bless us all.

Gaba daya Rayyan tun daya dawo daga gidan su maganganun Hajiya ne ke yawo akan sa, gaba ɗaya ya kasa samun sukuni, yana zaune sai tunani yake yi, kallon agogo da yayi ganin lokacin tafiyan sa aiki yayi yasa ya mike ya shiga toilet wanka, kamar zai yi amfani da maganin da Hajiya ta basa sai kuma ya bari dan shi be yi wani believing da wannan ba. Yana cikin shiryawa Layla ta buɗe kofar dakin ta shiga kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, da sauri ya juya yana kallon ta ya kura mata ido for almost 2mins har ta karasa kan gado ta kwanta ta lumshe ido, har ya gama shiryawan sa tana nan a haka ya juya yana kallon ta, baya son yayi believing da abinda idon sa ke faɗa masa, daga haka ya wuce ya fita without saying anything to her. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta jawo wayan ta ta shiga kiran Mama, tana daga wa Layla ta sake mata kuka hankali tashi tace "Ke Layla meke faruwa ne?" Layla tace "Mama gani fah nake kamar abun nan ya bar jikin sa" Mama ta zabura tace "me kika gani?" tace "gashi ya canza min, kwata kwata baya ma son gani na" Mama tace "kin ga abinda nake faɗa Miki ko? Kin fara amfani da magani tun ba'a je ko ina ba amma kika ce ya'isa, toh ga irinta nan" Layla tace "Toh taya zan so kullum ayi ta masa abu" Mama taja tsaki tace "Toh shikenan tunda baki so sai kiyi ta zama a haka ai tunda kin san ba son ki yake ba"
End Ads