zama tace "kuna waya da Yayan ku kuwa?" Niswa ta tabe baki tace "Ranan na kira sa shegiyar matarsa ta ɗauka wai ce min tayi nasa shi bacci yana yi, so karki sake kira dan bayi da bukatar ki kuma" Mummy ta sake baki tana kallon ta, tace "Amma ai baki taɓa faɗa mana haka ba" tace "Sau nawa idan nayi magana sai ki ce kishi nake da shi? Shi yasa na ja baki na alaikum" Nisreen tace "Ni dai muna chatting dan shi ko jiya ma na tambaye sa kuɗi yace zai tura min" Mummy tace "Niswa gwada kiran shi da waya ta ki ji, kamar blocking dina yayi" Nisa ta karba yana fara shiga sai ya kashe kansa ta kira both lines din sa samething tace "Chap, ai kuwa wallahi blocking dinki yayi, tun ba'a kai ko ina ba?" Mummy tace "Dan Allah tashi ku shirya kuje gidan nasa" Niswa tace "Allah ni ba inda zani" Mummy ta sake baki tana kallon ta ita yanzu abun Niswa har tsoro ya fara bata tace "Wallahi Niswa idan baki daina mayar min da magana ba zaki sha mamaki na, nace ki tashi ku tafi, ku je kuga wani hali Yayan naku ya ke" ta mike tace "Ai sai da tun farko na fada amma kullum Ni ake gani kamar ina da bakin hali while Yayan ma ba son ta yake ba amma ai gashi tun yanzu sun shanye shi" Mummy tace "Toh akan ki, karki tsara wa ɗana baki" daga haka Niswa ta shige ciki baya dau lokaci ba ta fito Nisreen itama ta dauki nata veil ɗin, Niswa ta fita tana mita. Bayan sun isa gidan Niswa ta ja baya ta tsaya tace da Nisreen ai sai kiyi knocking, Nisreen ta fara knocking sun kai wajan 10 mins kafin suka ji muryan Layla tace "Wai su waye ne?" Nisreen tace "Mu ne, Anty" bayan ta buɗe kofar ta tsaya kallon su daga sama har kasa kuma bata ba su damar shiga ba tace "Yane?" Nisreen tana murmushi tace "Dama mun zo ne kawai" ta kalli Niswa take danna wayar ta ta Harare ta sannan tace "kun zo kuyi uban me?" tace "A'a anty muzo gaishe ki ne, sai kuma mu gaisa da Yaya" still tana rike da kofar tace "And so?" Sai sannan Niswa taja dogon tsaki tace "Naga dai gidan ba na uban wani bane, sannan wajan Yayan mu muka zo ko baki ji bane?" tace "Okay, Toh ai sai ku shigo mu gani, fitsararriya" ta mayar da duban ta kan Nisreen tace "Next time Karki sake zuwa min da wannan shegiyar in har kina son ganin Yayan na ki" Nisa tace "Wallahi sai dai kece Shegiya tunda ba wanda yasan da uban ku, ai kuwa ke kinyi kadan ki kirani shegiya dan kin san waye uba na" Layla ta sake baki tana kallon ta daga haka Niswa ta wuce fuu, ganin sauyin Layla lokaci ɗaya yasa Nisreen tsorata tabi bayan Niswa, Layla ta buga gate ɗin da karfi tace "Ai kuwa ganin Yayan naku sai ya gagare ku" daga haka ta shige cikin gidan zuciyan ta na ku'na saboda takaicin rashin yiwa Niswa wani abu dan kalmar ta ya dake ta sosai.
_A taya ni sharing 'yan uwa_❤️😁🙏🏼
Hauwa Jibrin Sulaiman
Jiddatul-khayr writes
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
37.......
Tun a hanya Niswa ke ta daman masifa Nisreen ta gaji da masifan ta ta sa Bluetooth a kunnen ta ɗan tana gani kamar Niswa ta manta ba ita bane ta hana ta shiga gidan. Bayan sun isa gida suka sami Mummy na zaune a nan parlorn tana tunani iri da kala ganin sun dawo ta daga kai tana kallon su da mamaki tun kafin su yi magana tace "Ba su nan ne?" Niswa ta kwanta a kan 3 seater dan yadda take ji zata iya sauke haushin ta akan kowa Nisreen tace "Ai ce mana tayi ba zamu shiga ba, wai uban me muka je yi? Sannan next time kar Anty ta sake zuwa mata" Mummy tana kallon Nisreen tace "Toh ina shi Yayan na ku?" tace "Toh ai ta tare gate ɗin ko compound ɗin bata barmu mun shiga ba tace wai me muka zo yi, nace mun zo gaishe su ne tace wai 'And so'?" Mummy ji take bugun zuciyan ta ya tsananta tace "Ita Laylan ce tayi muku haka?" Nisreen tace "Wallahi Mummy" tayi shiru tana kallon wani waje tace "Toh ko bata gane ku ba ne?" Niswa ta mike tace "Dan uban ta mune zata ce bata gane ba, wai shegiya ma takira ni, ai wallahi duk laifin ki ne Mummy, kina ganin ai yadda take Kiga dage sai Yaya ya aure ta" daga haka ta wuce dakin ta Mummy dai at this point kan ta ya kulle bata son tayi believing abinda tunanin ta yake bata, ta juya tana kallon Nisreen sai kuma ta mike ta wuce dakin ta.
Ga ba ɗaya ta rasa me ke mata daɗi ita dai jinta kawai take a sama tana bin Sadeeq ta idanu har ya karasa shirya mata kayan ta a trolley, suna haɗa ido ya sakar mata murmushi, ta mayar masa yace "But, Meke damun ki ne?" tana kallon sa tana tunanin me zata ce dan tasan halin sa tana ce masa tana jin jiri zai ce an fasa tafiyar ganin kallonta yake alamar yana jiran amsar ta yasa tace "kawai fah ciwon kai ne, amma idan na sha magani zan ji sauki" daga haka ya wuce inda first-aid box ɗin su yake ya ɗauki paracetamol ya wuce inda ruwa ya ke ya ɗauka sannan ya koma cikin dakin yana kallon ta ya mika mata ta karba ta hadiya yana mata sannu.
Mummy ji tayi ba zata iya hakura ba ta dauki veil dinga sabar yadda take jin zuciyan ta na bugawa har ta fito ta tuna bata dauki makullin motar ba ta koma ta ɗauka sannan ta wuce inda motar ta yake, gaba ɗaya hankalin ta baya kan tukin tunani ce fal a ranta har ta isa gidan Aminiyarta Fatima, ta shiga cikin gidan tana sallama dan rabon ta da ita tun a wajan event ɗin biki kuma tunda akayi biki ba basu sake waya ba, Ayrah ce ta fito tana murmushi ta gaishe ta Mummy, ta amsa mata ta fara'a tace "Maman ku fah?" tace "ki shiga tana ciki" Mummy ta wuce ta shiga Ayrah na bayan ta, Bayan Mummy ta zauna Ayrah tace "Ina Nisreen Mummy?" Mummy tace "tana gida, amma kun je gidan Layla kuwa?" tace "Eh mun je Mummy" Mummy na Murmushi tace "Sau nawa kuma? Kun san yana da kyau kuna zuwa" Ayrah na Murmushi tace "Ai ina ga mun je ya kai sau hudu ma, ko jiya ma acan muka wuni, Ni da Addah Mimin mu" Mummy taji wani abu ya tokare ta ta gagara magana kawai tayi dariyan dole, sai ga Hajiya Fatima ta fito da alama waya take yi ganin Mummy yasa tace "Ina zuwa Layla, zan kira ki back" ta yake kiran ganin Mummy tace "Ki ce kina tafe kenan" Mummy tace "Iyyi naga shirun yayi yawa ne ko waya babu tunda akayi bikin yaran" ta karasa cikin parlorn ta zauna gefen Mummy tace "wallahi nake gaya miki kina raina" Mummy tace "Ayyah naga kamar da Laylan kike waya, ina fatan dai suna lafiya?" tayi wani murmushi tace "Eh lafiyar su kalau" Mummy zata yi magana ta riga ta tace "Yauwa, dama ina so na je gidan ki, mutumin nan ya kira wai yanzu ya fara ɗayan aikin ki shine nace dole na zo takanas na miki baya ni" Nan da nan Mummy ta manta meya kawo ta ta gyara zama don jin yaushe za'a fara mata aiki.
Tunda jirgi ya tashi Leena ta fara bacci sai da za suyi landing sannan ta tashi, bayan sun sauka Jiddah sai kallon Leena take dan kana ganin ta zaka fahimci bata jin daɗi ganin bata wani walwala, Sultan ne yazo ɗaukan su, da Jiddah zata shiga back seat Sadeeq yayi saurin cewa "No, ki shiga gaba" ta wuce gaba Sadeeq na rike da Leena suka shiga back seat nan ma ta kwanta a jikin sa sai bacci, ji tayi yana shafa fuskar ta da sauri ta buɗe ido sai kuma tabi motar da ido ganin ba su ciki yasa ta kalli compound ɗin tace "Ashe har mun iso" kai kawai ya gƴaɗa mata yace "Mu shiga mu gaishe da Mami sai mu wuce gidan mu ko?" Kai kawai ta gyaɗa masa daga haka ya sauka itama ta sauka, bayan su shiga parlorn, karɓan da Mami ta ma Leena ko kallon Sadeeq bata yi ba shi gani yake kamar yanzu Mami tama fi son Leena akan sa, yace "Mami Ni baki ganni bane?" tace "Toh kuma me zan maka?" ya shafa kai yana dariya Mami sai kallon su take dan daga Leena har Sadeeq ba wanda be yi kiba ba, Leena duk da yadda take ji haka nan tayi ta pretending, Bayan Jiddah ta fito a dakin ta daga gani har ta wasa ruwa tace "Anty Leena ko zaki wasa ruwa ne? Sadeeq yayi saurin cewa "No need tunda zamu koma gida" Mami tace "Toh an gama jera muku abinci a dinning sai ku je ku ci" Leena tun kafin ta karasa dinning area ta fara jin tashin zuciya kamar ta koma parlorn amma ganin Mami a parlorn yasa ta daure ta karasa ta zauna a gefen Jiddah, Jiddah na bude pepper soup din gaban ta aroman ya dake hancin Leena nan ta nan cikin ta ya hausine da sauri ta mike jin amai daya zo mata da gudu tayi toilet din da ke cikin parlorn, Sadeeq be san sanda ya ture abincin gabansa ba ya mike amma ganin Mami sai ya kasa motsi Mami ta bi bayan ta, Jiddah ma da sauri ta tashi ta bi ta, Leena ta dinga amai kamar zata amar da kayan cikin ta, Sadeeq yaga ba zai iya ba daga karshe shima ya bi ta, bayan ta gama zata wanke toilet din Mami ta kama hannun ta tana kallon Jiddah tace "Jiddah ki wanke ko kitsa me aiki ta wanke" daga haka Mami ta kai Leena da ta galabaita dakin ta tana mata sannu.
Mummy na shiga cikin compound da motar ta taga Niswa taci uban wanka zata fita, bayan tayi parking ta sauka tana kallon Niswa har ta karasa inda take tace "Ke kuma ina zuwa?" tace "Mummy ina da wani important abu ne a school" Mummy ta mata wani kallo tace "wani makarantar kuma?" Niswa tace "Na baki numbern HODn mu ki kira ki tambaya?" daga haka Mummy ta kama hanyar shiga ciki tace "Saura yau ma kiyi daren da kika saba" Niswa bata juya ba tayi ficewar ta. Nisreen ta fito daga dakin su jin Mummy ta shigo tace "Mummy kin shiga gidan?" Mummy tace "Ai ba gidan na tafi ba, gidan Hajiya Fatima na tafi" sai kuma yanzu ta tuna abinda ya kai ta, ga kuma abinda ya tsaya mata a rai wai Ayrah da Mimi suna zuwa gidan Rayyan jiya ma acan ta wuni, tunawa da aikin ta da aka fara yasa ta yi murmushi ta mike ta wuce dakin ta ko jin me Nisreen ke ce mata bata tsaya ji ba.
Ammi dake ta dariya jin labarin da Hajiya ke bata yasa tace "Toh Allah kyauta" Hajiya tace "Amin" can tace "Oh ni, toh ko Ni kadai ce na lura da cewa Riyan tun da yayi aure ko leko mu be yi ba balle ya kawo amaryar ta gaishe mu" Ammi tayi murmushi tace "kila ya tafi honeymoon ne, shiyasa" Hajiya tace "Toh tafiya holimun ɗin ba sallama ake yin sa" Ammi de bata ce komai ba ganin agogo yasa ta mike tace "Hajiya barin je na daura girki wa Daddyn su" Hajiya tace "Toh Nagode Hauwa" daga haka Ammi ta wuce bangaren ta.
Mami gaba ɗaya hankalin ta ya tashi ganin Leena tayi amai ya kai sau hudu, Sadeeq kam ganin ba zai iya ganin ta a wannan yanayin ba daga karshe backyard ya wuce, Mami ta buɗe dakin ta da Leena ke ciki ta same ta kwance ta ajiye mata tea din hannun ta tace "Daughter please ki tashi ki sha ko da kadan ne" Leena ta mike ta karba ita yanzu bata bukatar komai dan tsoron ta karma ta kara aman, Mami na mika mata ta fita, ba'a dau lokaci ba sai ga Mami ta shigo mata da wani gown ta sami Leena yadda ta barta tace "Toh ko zaki wasa ruwa ne daughter? Sai mu tafi asibiti". bayan su Mami sun dawo a asibiti, ta kai Leena dakin ta tasa aka hada mata tea Leena tace "Mami bana so da madara zallan Lipton nake so" Mami tace "Toh dear.
Da Daddare Sadeeq ya shiga parlorn duk suna zaune parlorn suna hira Sadeeq ya shafa kansa sai kuma ya wuce ɗakin Mami direct duk su kayi pretending ba wanda ya kalle sa, bayan ya shiga ya kulle kofar ya karasa bakin gadon Mami da Leena ke bacci akai ya duka yana ta kallon ta, yau kadai yaga ta rame masa buɗe kofar akayi ya daga kai da sauri yana kallon Mami, Mami tace "tashi ka fito" ya shafa kansa ya mike yace "Mami wai da gida zamu koma" tace "sai kuma ka tashe ta?" yayi shiru tace "zo ka fitar min a daki, baka ganin yadda ta wuni ne yau, an samu bacci ya ɗauke ta zaka tashe ta?" haka nan Sadeeq ya bi ta gefen Mami ya fita, ta rage mata ACn sannan ta kulle mata kofa, Sadeeq ya wuce gidan sa, haka nan wannan daren ya gagara bacci yayi ta juye juye har daga karshe bacci barawo ya ɗauke sa. Leena kuma ba ita ta farka ba sai wajan karfe 2am ta dinga bin dakin da kallo ita kadai ce a dakin ta sauka a hankali dan gaba ɗaya bata jin dadin jikin nata ta wuce toilet bayan ta fito ta fara jin wani yunwa ta buɗe kofar a hankali ta karasa dinning ganin kula biyu ta karasa ta buɗe taga empty daga bayan ta taji Mami na cewa "Yunwa kike ji daughter?" Leena ta ju ya tana kallon ta sai kuma ta tsunkuyar da kai ta gƴada mata kai, tace "Me kike son ki ci?" A hankali tace "indomie amma wanda yaji ya yi masa yawa" Mami tace "toh zauna kar kiyi stressing kan ki" daga haka ta shige kitchen ɗin da kanta ta girka mata indomie yadda tace, bayan ta kawo mata duk da zafin indomie Leena bata tsaya jiran ya huce ba haka ta dinga ci Mummy ta haɗa mata tea ta sha tana kallon ta tace "Sai kuma me kike so daughter?" Leena da ke kallon kasa tana wasa da fingers dinga tace "Nothing Mami, thank you" Mami tace "toh je ki kwanta" daga haka Leena ta wuce dakin Mami nan da nan bacci ya sake daukan ta. Sadeeq na dawowa daga gym wanka yayi ya fito ya kulle gidan, gidan Mami ya nufa ya same ta tana shirin fita aiki ya gaishe ta ta amsa yace "Mami ya jikin na ta?" tace "Da sauki" Jiddah ta gaishe sa ya amsa, Mami ta mike tana kallon sa tace "Na roke ka Karka tashe ta a bacci dan naga kai ba sanin yakama ka yi ba" ya shafa kansa yana murmushi yace "Bacci take yi" Mami tace "tun da tayi sallahn asuba ta samu ya ɗauke ta" daga haka ta musu sallama. Sultan ne ya shigo shima alamar daga gym ɗin ya taho suka gaisa da Sadeeq dake breakfast a dining area ya wuce sama, Sadeeq na ganin Jiddah ta bar parlorn ya rufe plate ɗin sandwich ya wuce dakin Mami Luckily ya same ta ta farka amma still tana kwance ya karasa har inda take yace "Baby" ganin sa yasa ta mike ta zaune ya jawo ta jikin shi ta ja kanta baya tace "Dan Allah ka fita kar Mami ta shigo" yace "Mami ta tafi aiki ai" tayi shiru tana kallon sa ya kai bakin sa daidai kunnen ta yana shafa flat tummy ɗinta yace "Sorry Habibty, babyn mu ne ke wahalar min da ke ko?" ta sauke idon ta kasa taki ce masa komai still kallon ta yake yi tace "I'm hungry" yace "Me zaki ci?" tace "Irin indomie da Mami ta dafa min da Daddare" yace "Okay" daga haka ya fita knocking kofar Jiddah yayi ta fito tace "Gani" yace "Please indomie zaki dafawa Leena" tace "Ohh har ta farka ko ka tashe ta" wani kallo ya mata tayi dariya daga haka ta wuce kitchen bayan ta daura kafin ya nuna ta wuce ɗakin Mami ta buɗe da sallama, Leena dake jikin sa da sauri ta tashi bayan sun gaisa ta fita ta ja musu kofa , ganin shirun yayi yawa yasa Sadeeq ya mike yace "barin duba ko ta gama" daga haka ya wuce kitchen yana shiga sai ga Jiddah tana kan fitowa da plate ɗin indomie da boiled egg guda biyu akai, ganin sa yasa ta mika masa ya karba yace "Thank you Jiddah" tace "Most welcome" ya wuce dakin Mami ya mika mata yace "gashi baby" ta karba ta kai 1 minute tana kallon abinci sai kuma ta haɗa rai tace "Ni nace asa min kwai?" Sadeeq sai kallon ta yake ya cire egg ɗin yasa a plate cover, ta ɗauki be wuce 2 pics of indomie ta kai baki sai kuma da sauri ta kalle sa tace "Toh haka Mami ta dafa min?" yace "but kin ce indomie zaki ci" ta tura masa plate ɗin tace "ba zanci ba wannan ba irin na Mami ba ne" duk yadda Sadeeq yaso rarrashin ta daga karshe kuka ta sa masa tace ya fita bata son ganin sa ma, shi dai har sannan yana tsaye yana kallon ta ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta, daga haka ya fita ya kulle mata kofar. A parlorn ya tarar da Sultan, papern hannun sa ya mika masa Sadeeq ya tsaya kallon sa