x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - AGOLA free pages

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
damun sa uwa ta? Niswa tace "ko ƙaffara ba zanyi ba Yaya saboda Leena ya kwanta rashin lafiya, kalli baya tashi rashin lafiya sai sanda kika masa baki akan ta da lokacin da aka kawo gaisuwan ta sai kuma yau da za'a kawo lefen ta, aure kuma jibi za'a daura, kin yarda?" Mummy tayi shiru tana tunani gaba ɗaya hankalin ta be taɓa kawowa nan ba Niswa ta taɓe baki tace "Ni wallahi har ya fara bani tausayi, ciwon so zafi gare sa, kuma wallahi suna son junan su, tun farko da kika raba sune amma da kila shi zata aura yanzu" Mummy ta daka mata wani tsawa har sai da Niswa ta tsorata Nisreen dake bacci ma ta farka a gigice Mummy ta mike tana kallon Niswa tace "kika sake dangan ta ta da ɗana zaki sha mamaki ba ina faɗa Miki wannan" daga haka ta wuce ta fita daga daki. Leena na kallon Anty Binta da Amty Mairamah dake kanta tace "wallahi anty yace baya son wani event ɗin da za'ayi, yace harda na karɓan Lefen ma baya son ayi" Anty Binta ta taɓe baki tace "na karɓan Lefen kuma yayi karya shi yaji wajan, Abunda ba agidan sa za'a yi ba, so wannan kam be isa ya hana ba" Mairamah tayi kasa da murya tace "Leena ba wai me hayaniya za'ayi ba kawai dan karrama ƴan-uwan sa ne kinji?" Leena ta gƴaɗa kai kawai Anty Binta ta mika mata roban hannun ta tace "cinye a gaba, na yau kam ba zaki samu asara ba" Leena ta karba tana bata fuska ta gutsura takai maki tana taunawa kamar magani. Mummy tayi tagumi a bakin gadon dakin ta tayi nisa cikin tunanin da take yi harga Allah yanzu hankalin ta ya fara tashi ita bata ga wani progress a abinda take yi ba zufa ne ya fara zarya mata da ta tuna ashe jibi daura auren, tana nan haka, kiɗan masu ganga ta fara ji, sun cika gidan da kiɗe kiɗen gargajiya hankalin ta taji ya ninku ana da ta jawo wayan ta tayi dialing numbern Fatima ji tayi akashe bata san sanda tayi wulli da wayan ba ta figi makullin motar ta ta yafa gyallen sannan ta kama hanyar fita, anan parlor taci karo da Daddy da Colleague ɗin Rayyan, yana kallon ta yace "ina zaki kuma?" kame kame ta fara daga karshe tace "En dama, dama zani gidan Fatima ne an kwantar da Layla a asibiti ne" Daddy ganin Abokin Rayyan da suka shigo tare yasa bece komai ba tana fita a parlorn ta sauke ajiyan zuciya, dakin Rayyan suka wuce samun Rayyan suka yi yana bacci Daddy yana kallon sa cike da tausayi dan yasan meke damunsa ko da be faɗa masa ba abokin nasa ya karasa ya cire masa drip din hannun sa yace "inaga Daddy wannan ya isa sai muga zuwa anjima ya jikin nasa tukun sai asan next move din" Daddy ya gƴaɗa masa kai ya kama hannun abokin Rayyan suka fita yace "tunda naga ya samu bacci toh bana so surutun mu ya ɗaga sa dan baya bacci da daddare" Daddy ya karasa maganan cike da damuwa dan be san ya zaiyi da wannan lamarin bane kuma kwata kwata yasan bayi da power addu'an sa shine Allah basa hakurin jurewa da kuma cin wannan jarabawar sannan Allah yaye masa, Colleague ɗin Rayyan yace "ina ga sai in shaa Allah da daddaren na shigo" Daddy ya masa godiya tare suka fita dan be san nema zeyi a gidan ba bayan baki na shigowa anjima. Fatima ta ɗaga kai tana kallon Mummy ta ta shigo mata ko sallaman kirki babu tace "Lafiya dai? Meya faru kuma?" Mummy ta zauna tana maida numfashi tace "kenan kika ganni kinsan ba lafiya bane, hankali na ne ya katse kwanciya gashi ƴan iskan kannan nata ba su da kunya nake gaya miki dan wallahi su suke zuga ita shegiyar uwar Leenan" Aminiyarta dake kallon ta kashe tvn tace "yanzu kuma meya faru? Ke da gidan ki ba zaki ci uwar su bane" Mummy tace "Uhm, ba zaki gane bane, Ni yanzu ki tashi ki shirya mu kara zuwa gun mutumin nan muji ya ake ciki" Aminiyar ta ta sake baki tana kallon ta tace "Wallahi ni rashin hakurin ki ya fara damu na kalli yadda kika wani susuce? Mutumin nan yace muyi hakuri zamu ga aiki da cikawa amma ke kinki sama kanki salama" Mummy tace "Idan kuma aikin beyi ba fah? Kinga fah jibi ne ɗaura auren" Aminiyarta tace "Okay, kina ganin ba zaiyi ba kenan ko?" Mummy ta girgiza kai cike da confusion Aminiyarta ta dafa ta tace "na miki alkawari zaki sha mamakin aikin sa kuwa, just calm down" fitowan Layla daga ɗakin ta yasa duk suka yi shiru ta karasa cikin parlorn tana kallon Mummy ta zauna kan hannun cushion tace "ina wuni, Mummy" Mummy na Murmushi karfin hali tace "Lafiya kalau, fita zaki yi kenan" tana taunan chewing gum tace "Sure" ta kalli uwarta tace "Toh sai na dawo" daga haka ta mike ta ɗaura sun glasses dinta a kanta, suka bita da kallo, wani kalan shiga tayi na fitted gown tasha kitso attached har baya gashi ta wani sako Labombom sannan gyallen ma ba ya fawa tayi ba, rataya shi tayi a gefen kafaɗa bayan fitan ta Fatima ta sauke ajiyan zuciya tace "wallahi Layla kyar take kallon mu, na kosa naga ta bar gidan nan" Mummy tace "Toh yanzun ina zata?" tace "Ohon ta kila wajan kawayen ta ne" Mummy ta jinjina kai ita damuwan ta yafi wannan Aminiyarta tace "yanzu an kawo lefen ne?" Girgiza kai kawai tayi Aminiyarta ta kuma cewa "ina son gaskiya yanzu Rayyan ya fara zuwa wajan Layla, in ma bayi da lokacin hira ne hakan ma ba damuwa ba ce, Ni yanzu gaskiya kiyi wa Daddyn su magana su zo neman auren Layla kuma gaskiya bana son bikin ya wuce wata ɗaya" Mummy tace "wannan fa duk me sauki ne, damuwa na wancan yarinyar ce, muddun komai ya rushe wannan ba me sauki bane ko da 2weeks kike so za'ayi hakan". Niswa ta buɗe dakin nasa ta shiga sannan ta rufe ta tsaya tana kallon sa daga bakin kofar, shi kuma jin an buɗe dakin an shigo kuma beji alamar Mummy bace ko Daddy yasa ya buɗe ido dan kallon wanene, ya buɗe ido yana kallon Niswa da ta kafe sa da ido tun daga bakin kofar alamar menene ya mata da hannu hawaye taji ya taru a idon ta, ba zata juri kallon yayan nata a wannan sabon yanayin ba ta karasa har jikin gadon sa ta durkusa tana kallon sa kamar yadda shima kallon nata yake yi, tace "Yaya nasan saboda Leena zata yi aure yasa kake kwance ko?" ta karasa maganar hawaye na gangaro mata kallon ta yake ba ko kiftawa.....

Assalamu Alaikum, everyone!

Da fatan anyi sallah lafiya? Allah Ubangijin ya maimaita mana, yasa muna cikin bayin sa da yayi wa Rahama, Amin ya hayyu ya qayyum.

Share, please.
https://www.instagram.com/jiddatul_khayr_?igsh=MW8yeXBveXRlOTg5Yg==Follow the JIDDATUL-KHAYR BOOKSHELF DIARIES📚💕! channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z

https://www.instagram.com/jiddatul_khayr_?igsh=MW8yeXBveXRlOTg5Yg==


26........
Tace "Me yasa baka ce min kana son ta ba? Da na taya ka fighting Ya Rayyan" ya kamo hannunta trying hard to hold his tears back girgiza mata kai yayi sannan ya mata Murmushi, ya tashi daga kwancen da yake yi ya jinki na da gadon ya rufe idon sa kaman me whisper yace "Everything will be alright, then." ta cire hannun ta a nasa ta mike tsaye still idon ta na kansa tace "I wish you speed recovery'?" sai sannan ya buɗe ido yana kallon ta She gave him a reassuring smile shima mayar mata yayi daga haka ta juya ta fita. Mami dake tsaye akan sa Jiddah kuma na zaune a bakin gadon da plate ɗin fruit a hannun ta shigowan Sultan kenan, Mami ta ɗan ɗaga murya tace "ba zaka bude baki ka min magana ba?" sai sannan ya ɗaga ido ya kalli Jidda da Sultan Mami ta fahimci meya ke nufi dan haka tace "we need privacy, please" Jiddah ta kalli Sultan sum sum suka tashi ta ajiye plate ɗin hannun ta suka fita Mami karasa bakin kofar ɗakin ta kulle sannan ta dawo tana kallon sa tace "Uhm, I'm all ears" sai sannan Sadeeq ya buɗa baki kamar me whispering ya fara Magana. Masu algaita sai aikin su suke, Manyan motoci ne suka dinga shiga layin gidan su Leena suna parking. Hajiya dake zaune a parlorn Ammi anty Binta ta kalle ta tace "Hajiya kamar sune suka iso" Hajiya tace "Toh, yi maza kije sai ki karaso da su Nan" kafin ta karasa har sun fara shigowa. Daga cousins ɗin Ammi har few neighbors ɗinsu suka zo taya su karɓan kayan lefen Leena, sake baki su kayi suna kallo ganin har sannan ba'a daina shigowa da akwatinan ba, ana cikin shigarwa sai ga Jiddah da Mami ma sun shigo. Ammi dake zaune a dakin ta, ta fita zuwa dakin Leena ta karasa har ciki tana kallon yadda a ƴan kwanaki biyun nan ta wani zabtare ta zauna bakin gadon ta tana kallon ta tace "Leena tunanin me kike haka ne wai?" Ammi daurewa kawai take yi bata son wannan sabon canzawan Leena, Leena ta kalli Ammi sai kuma tayi faking murmushi tace "bakomai Ammi" Ammi tace "ni zaki fara boyewa abu Leena?" Sai sannan taga Leena ta fara kuka same thing da Anty Binta ta mata haka Ammi ma ta mata janta tayi jikin ta ta bari har sai sanda tayi shiru dan kanta sannan Ammi tace "ina jin ki?" Leena tace "Nima ban san meke damuna ba Ammi, kawai dai na san I'm just Scared" Ammi tayi shiru tace "kun samu matsala ne da Muhammad ɗin?" Leena ta girgiza mata kai tace "ko dazu ma munyi waya" Ammi tace "baki son sa yanzu ko?" Leena ta girgiza mata kai kawai Ammi tace "ki kwantar da hankalin ki ba wani abu da zai faru in shaa Allah sai alkhairi kuma ina nan ina Miki addu'a, duk sanda kika ji wani abu ki ambaci Allah, kar ki bari bakin ki ya zauna babu ambaton Allah, kin ji?" Leena ta gyada mata kai" har sannan Leena na jikin Ammi sai yanzu taji tasamu natsuwa sosai suna nan a haka suka jiyo buɗa da ake sakewa a can compound ɗin. Akwatina set biyar suka kawo mata kuma ba wanda aka sa mata kaya me arha a ciki duk kaya ne masu tsadan gaske, har bakin mota suka raka su Hajiya sai hamdala take tayi bayan sun dawo suna kara ganin kayan for the second time, gate Man ya buɗe gate Mummy ta shigo da mota tayi parking Hajiya ganin haka yasa ta tashi tana kallon ta har ta sauka tace Khadija karaso kizo ki ga abun arziki, Mummy data ke rufe motar ta tayi magana kasa kasa tace "ji shigeyar matan nan" ganin mutane da ɗan dama yasa ta karasa wajan amma da ba dan su ba ba zata ba, lokacin da idon ta ya kallin yawan akwatina bata san sanda ta durkusa da sauri ba sakamakon kafar ta da taji ba zasu iya daukan ta ba, zufa taji ta ko inan ta, murmushin da take faking bata san sanda ya tafi ba sabar ruɗu bata san sanda tace "kuma shi hauka yake zai yi wannan akwatina sai kace shago zai buɗe mata?" Duk aka ɗago ana kallon ta sai kuma tayi realizing mema tace ashe, Jiddah kallo ɗaya ta mata ta ɗauke kai anty Binta tace "Zunzurutun soyayya ce nake faɗa Miki, wani hauka kuma sai kace bakin ciki ake ma ƴa? Kin san gidan daula zata shiga" Mummy ta mike tace "Kaya kam sunyi kyau, Allah sanya Alkhairi barin shiga na ɗan wasa ruwa kafin Magrib" Dakyar ta mike Anty Mairamah tace "Yo ai baki tsaya Kinga kaya ba" Mummy ta wuce ciki, ko kallon Nisreen dake zaune a parlorn dake mata sannun da zuwa bata yi ba direct dakin ta ta wuce tana shiga ta danna kofar ta zauna nan kasan dakin tayi tagumi sai kuma ta daura hannu a ka tace "Nashiga uku ni khadijatu" da sauri ta share hawayen daya gangaro mata hannun ta har rawa yake yi ta ciro wayan ta a jakka ta gwada danna kiran Aminiyarta sai kuma ya shiga tana daga wa Mummy bata bari tayi sallama ba ta fara cewa "yanzu dawowa na na tarar wallahi akwatin sai kace wanda shago za'a buɗe baki gani ba expensive trolleys nake faɗa Miki, ya zanyi ne wai? Hauka kawai ya rage nayi" tace "kice yarinya de tayi goshi, toh ai zamu ga ta yadda abun zai kasance" Mummy tace "tun farko nice nayi wauta, da tun lokacin nasa ta zama ƴar iskangari na gaske yadda ba wanda zai yi sha'awar aurenta ta balle ya tinkare ta sai de da iskanci, ni yanzu babban damuwa ta ki kira mutumin nan kice masa kawai ya kashe yarinyar kowa ya huta! Idan yaso sai a haɗa ta aure da Niswa" Fatima tace "wata Niswan kuma bayan ga yarta Layla" Mummy tayi shiru sai kuma tace "Naji ni yanzu damuwa ta ki kira sa yanzu dan Allah" tace "anyi an gama" tace"aikin ita uwar Tata da muka ce ya bari sai bayan biki za'ayi nata ki ce masa ya yayi yanzu kawai" daga haka ta katse kiran, ga ba daya duniyar ta mata zafi. Da Daddare Leena na kwance ta lulluɓe da duvet duk da yanzu aka idar da Isha'i ba wai dare yayi nisa bane wayan ta dake ringing a bedside drawer ta kai hannu ta ɗauka ganin Zahra ne ta daga bayan sun gaisa Zahra tace "Ɗazu na dawo gari, in shaa Allah gobe zan shigo, Amarya" Leena tace "toh Allah kaimu" daga haka sukayi sallama sai ga kiran Muhammad ya shigo ita duk tunanin ta Zahran ce ganin Muhammad yasa ta ɗaga tayi masa sallama a hankali ya amsa yace "is everything okay, babe?" tayi shiru yace "speak up please, dear" ta buɗe baki zata masa magana kawai taji ta fara kuka a ɗan ruɗe Muhammad yace "Menene kuma babe, please ki daina kuka kimin bayani" Leena ta kasa yin shiru ya runtse ido yana jin kukan ta har zuciya sai daya tsaya yace "Baby ko na bi Flight ne na zo yanzu?" ta girgiza masa ka kaman yana ganin ta tace "A'a, I'm okay" yace "Baby" tace "Uhm" yace "tell me bana son ki boye min komai, menene?" tace "Nima ban san ko menene ba, kawai tsoro nake ji" yayi kasa da murya yace "please ki ajiye wannan tsoron a gefe idan ta nine, na Miki alkawarin ba zaki taɓa nadaman aure na ba, just calm down, Okay?" tace "Tohm, Allah ya yarda" yace "kinci abinci?" tace "yanzu zanci" yace "je ki ci, zan kira ki anjima" daga haka suka yi sallama toilet ta wuce tayi alwala sannan ta shimfiɗa sallaya. Hajiya dake tsaye bakin parlorn su Nisreen hannun ta ɗauke da kula tana ta sallama ba wanda ya bi ta kanta har zata juya sai ga Niswa ta buɗe kofar tana gaishe ta Hajiya ta fara masifa tace "Sai ku kama ku garkame kofa kamar wanda za'a muku sata ayi ta doka sallama kuna jin mutun kuyi banza da shi" Niswa tace "kowa ya koma dakin sa ne shiyasa" Hajiya na mata wani kallo tace "toh ba zaki masa min na shiga bane ko yaya?" Niswa ta masa gefe Hajiya ta shiga bata tsaya ko ina ba sai dakin Rayyan, Niswa ta zauna anan parlorn tayi tagumi ita duk damuwar duniya ya ishe ta, Hajiya ta karasa har inda Rayyan yake kwance ta taɓa jikin sa Rayyan ya buɗe ido yana kallon ta ya tashi daga kwance da yake Hajiya ta sake Salati tace "yanzu su iyayen naka haka suka zuba maka ido wato ka karata a haka kenan ko me suke nufi ne?" kallon ta kawai ya ke yi ta ajiye kulan hannun ta tace gashi faten dankali ne da alayyahu nasan zaka so yace "ki samin dan kaɗan Hajiya" Hajiya ta zuba masa ta mika masa tace "kira min shi uban naka" kallon ta yake alamun ta basa wayan ta ya fito mata da numbern Daddyn tace "ai da Wayan ka zaka kira min shi tunda ni na bar nawa a can" ɗaukan Wayan sa yayi ya yi dialing numbern Daddy yana fara ringing ya mika mata ta karɓa Daddy na daga wa ko amsa sallamar sa bata yi ba tace "yanzu fisabilillah saboda shi Riyan ɗin ba rai gare sa ba shiyasa zaku ta zuba masa ido ba zaku kaisa asibiti ba? Ji fah yadda ya koma, wannan wani irin rayuwa ne?" Camly Daddy yace "bari na shigo Hajiya" tace "Toh ina dakin Riyan ɗin sai ka same ni anan" Rayyan ya kalle ta yace "Hajiya ni nafi son gidan saboda duk kulawan da za'a bani a asibiti shi nake samu anan balle ma ni na warke" Hajiya ta dinga hararan sa har ya karasa magana bata tanka sa ba, can ba da daɗewa ba sai ga Daddy ya shigo ya gaishe da Hajiya ta amsa masa tace "ku yanzu baku ganin yadda ya koma ne?" yace "Hajiya shi yaki a kaisa asibiti kuma duk wani abinda ake bukata ana masa, sai dai ki ce masa ya cire duk wani abu dake ransa ya mika wa Allah lamarin sa sai komai yaga yana tafiya masa daidai" Hajiya ta mike tace "Ni kam barin tafi can, dan bana yarda da baki gashi na barsu su kadai" tana kai wa nan tayi hanyar fita sai kuma ta dawo dakin tana kallon Rayyan tace "Riyan kayi ta addu'a Abunda ba rabon ka ba baza ka taba samu ba kaji?" Rayyan ya gyaɗa mata kai kawai saboda zuwa sannan har ya fara gajiya da surutun ta tayi musu sallama ta fita tunawa da tayi da baki yasa ta fara tafiya da sauri dan Hajiya kwata kwata bata yarda da mutane. Daddy na kallon sa yace "Kana addu'an kuwa?" yace "Eh, in shaa Allah" daga haka yace
End Ads