x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 23 - AGOLA free pages

  • 66001 words
  • 69000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
"toh sai da safe, Allah sauwake" ya ja masa kofar daki. kusan cin karo yayi da Mummy a dinning kallonta yake ganin gaba ɗaya kwana biyun nan she's not herself ya wuce ya fita ita kuma ta banka kofar dakin su Niswa ta shiga ganin haka yasa Niswa ta mike tana kallon ta tace "Allah sa lafiya dai Mummy?" Mummy tace "Ni zaki ba wa kunya Niswa? Ashe abinda kika wa Mutumin nan kenan? Toh gashi ran Aminiyata ya baci ta kira tana ta magana akai, wallahi ko ki koma kina kula sa ko Kiga abinda zan Miki" Niswa tace "ina yanzu kowa sai mamakin mijin da Leena ta samu ake yi sai nine zan kula wannan? Ni ina ruwa na da kudin sa, ita kawar taki ta bawa daya daga cikin ƴaƴan ta mana" Mummy ta sake baki tana kallon Niswa mug ɗin dake kusa da ita ta ɗauka Niswa na ganin haka ta mike da gudu tayi hanyar toilet sanda Mummy ta wurga kuma be same ta ba dan har ta shige, kulle toilet din tayi ta fara rusa kuka ita ba zata aure wannan ba, tunda ta ke jin maganar auren Leena bata taɓa biin hankalin ta ya tashi ba sai ɗazu da ta gwada searching mijin da Leena zai aura a IG ji take ba zata iya bari Leena ta mallake sa ba kuma tayi alƙawarin ko da bayan bikin ne ba zata fasa bibiyan sa ba, dan tun lokacin ta tura masa da messages kuma ba zata hakura ba dan ita ce tayi deserving not Leena, bayan some minutes ta share hawayen ta tasan sannan Mummy bata nan ta buɗe kofar a hankali ta fito tasa ma kofar su key, ita data san haka ne da ta taimakawa Yayan ta ya samu Leena ita kuma ta makalewa MD, daukar wayan ta tayi ta shiga IG hoping yaga sakon ta. Har sannan Leena taji bacci ya kasa daukan ta gashi bata so tayi wani abinda zai sa Anty Binta ta gane ba bacci take ba, kuma Muhammad yace ze kira amma har sannan be kira ba, ta ja wayan ta ta shiga Whatsapp hoping zata ga Muhammad online tana masa magana taga message ɗin yayi delivered taji hankalin ta ya ɗan kwanta at least ba zai barta ita ɗaya ba, har wajan 10 min bata ga yayi replying dinta back ba dama ta san sa da barin data always On ta shiga call log dinta tayi dialing numbern sa har ya gama ringing be ɗauka ba ta sake kira nan ma be ɗauka ba sai kawai ta kashe wayan ta kwanta, tana son tayi forcing kanta tayi bacci dan tasan gobe da sassafe zata tafi kitso da Lalle. Wani irin zabura yayi lokacin guda har sai daya kusa faɗuwa kasa, da kyar ya iya rike kansa, wani sabon tururi yake ji wanda hakan sabon yana yi ne game da shi ya runtse idon sa amma sai kuma ya gagara addu'an da ke bakin sa....
Join me on Wattpad: a free, mobile app for reading and sharing stories. https://www.wattpad.com/user/jiddatulkhayr?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_campaign=invitefriends

Follow the JIDDATUL-KHAYR BOOKSHELF DIARIES📚💕! channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z

*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧



27........
Wayan ta ne ya fara ringing kafin ta kai ga buɗe ido har ya yanke mikewa zaune tayi ta kalli agogon ɗakin da ke nuni da karfe 6:30am da sauri ta fara murza ido bata san ta makkara har haka ba ɗaukan wayan tayi dan ganin wanene, ganin Aminiyarta ne zata yi dialing back sai ga wani kiran yana shigowa, ɗauka tayi ta kai kunne kafin ta kai ga magana Aminiyarta ta riga ta tace "wajajen sha biyun daren jiya mutumin nan ya kira wai aiki ya fara, so yanzu zaki bada Miliyan daya" Mummy tayi shiru dan yanzu ko tsisi bata magani, dan kusan kullum sai ta kashe kusan hakan Aminiyar ta tace "Hello!" da sauri Mummy tace "Toh, shikenan yaushe ake bukata?" tace "yanzu yace yake so" Mummy ta mike tace "barin yi sallah zaki jini" tunani ta fara ko ta shiga kasuwa ta sayar da gold dinta ne, da wannan tunanin ta shige ban ɗaki. Zahra ce tayi sallama Ammi ta amsa mata ta gaishe ta Ammi tace "Yaushe kika dawo Zahra?" tana murmushi tace "Jiya Ammi" Ammi tace "Ayyah sannu da zuwa, ki shiga ciki suna can" tace "Toh, Ammi" tana shiga ta same su Anty Binta ta gaishe su suka amsa tace "Leena fah?" Anty Binta tace "tana wanka" bata daɗe ba sai ga Leena ta fito bata san sanda taji wani relief ba da taga Zahra tace "na ɗauka ai ba zaki iya fitowa da sassafe ba ai" Zahra tayi dariya tace "Na'isa Amarya?" Leena ta Harare ta daga haka ta fara shiri cikin sauri tana gamawa ta saka hijab ɗinta ta daura Niqab tana kallon Zahra tace "Muje ko?" Zahra ta mike Anty Binta tace "Ya maganar me lallen mu ɗin" Leena tace "mun kara magana tace zata shigo amma sai karfe 9am" daga haka suka fita tayiwa Ammi sallama. Daddy yadda ya ganta hakanan yasan da magana a bakin ta yadda tayi wani calm da ita dama sai tana da bukata take zama very calm yace "Yau ba zaki office bane?" ta ɗan kalle sai sai kuma tace "zani mana" yace "Okay, naga baki fara shiri bane har pass 7am" tayi kasa da murya tace "Dama yallabai, 1 mil zaka taimaka min da shi yanzu?" Daddy ya dinga kallon ta baya kiftawa sai kuma yace "Me zakiyi har da 1 mil?" tace "ina son zanyi Using ne" Daddy yana kallon ta yana son studying dinta, ai yasan tana da kudi toh ina suke me ze sa ba zata yi using ba? duk tunanin sa ya tafi kan kila saboda kayan daki da yayi wa Leena ne take son itama ta fara zaran kudi a jikin sa, tana kallon sa tace "kayi shiru baka ce komai ba" yace "Khadija kiyi hakuri gaskiya ba zaki samu wannan kudin yanzu ba, Kinga dai na gama kashe kudaɗen wajan biki kuma kinga ba'a ma gama ba" ta mike tana masa wani kallo tace "Amma dake ai wancan matar taka ka ɗauke ta ƴar gold ce ji rawan kafan da kake yi a bikin ƴarta, ji uban kayan daki da ka mata kowa sai magana yake dan na tambaye ka miliyan daya shine zaka tsaya kana kallo na ka na bani wani banza Excuse ɗin ka" daga haka ta ja tsaki ta fice Daddy ya girgiza kai ita ko kunya ma bata ji idan tana neman abu zata kashe murya amma idan akasin haka ne maganar arziki ba zata haɗa ku ba. Mummy tayi shiru tana tunani gashi inda take zuwa tsayan gold a kasuwa ba su fitowa sai 10 na safe balle tace zata jira gashi Fatima ta addabe ta da kira wai mutumin yace zai lalata aikin idan ba suyi sauri sun tura kudin ba, sake checking account balance dinta tayi for the countless times taga duk abinda ke ciki be kai 200k ba duk kudin sun tafi a hanyar aikin da ake mata. Buɗe dakin Rayyan tayi ta shiga ita sai yanzu ma ta tuna da shi yana kallon ta ya gaishe ta ta amsa tace "ya jikin naka kuma?" yace "da sauki Mummy, yau ba aiki ne?" tace "yanzu zan tafi" ya gyada mata kai tace "kasan me, 1 Mil nake son kamin transfer yanzu wani abu nake son yi kuma kudina ba zai kai ba" yace "Toh shikenan, a wani account ɗinkin zan sa?" tace "Samin a Opay" daga haka ta fita shi kuma yaja wayan shi zai mata transfer yaga datan shi ashe ya kare, Daddy ya shigo duba shi yaga jikin da ɗan sauki yanzu yana taba goshin shi dan yaji temperature ɗin sai ga Mummy ta kuma buɗe kofar dakin tace "Rayyan ba zaka turomin ba ne, kaima?" yace "Mummy, datan nawa ne ya kare, ki buɗe min hotspot sai na tsaya data sai na Miki transfer din" Daddy kallon ta kawai yake daga inda take tsaye a bakin kofar, ta buɗe masa Rayyan ya mata transfer a take tace "Ya shigo, Allah maka Albarka" daga haka ta kulle masa kofar ta wuce parking space. Leena da ake wanke mata kai ta sake dialing numbern Muhammad har yanzu baya picking call dinta, zuwa yanzu ta fara damuwa dan be taɓa mata haka ba, infact tana kira zai bari ya yanke sai kuma immediately ya kira ta back amma tun juya take kiran sa yaki daga wa kuma ko message dinsa bata gani ba as usual Kuma hakan be taɓa faruwa ba, she looks so disturbed Zahra tayi dariya tace "Haba amarya ai kya bar shi ya huta mana, kika san ko suna ta hidima acan ya bar wayan a daki ne, kalli yadda kika wani ruɗe" Leena ta sake baki tana kallon ta ita bata ɗauka har Zahra ta fahimci abun da ke damun ta bama ta Harare ta ta ɗauke kai, me mata gyaran gashi tace "A'a barta tayi waya da ango ta" Zahra ta kwashe da dariya ita bata san yaushe Leena ta koma haka ba. Mutumin da suke gaban sa ya mika musu magani a bakar leda yace Wannan kuma ki tabbatar kinsa a abinci gidan yadda kowa zai ci, toh hakan zai sa yarinya kowa ya tsane ta tayi bakin jini a idon mutane daga ita har uwar ta ta" Mummy ta mika hannun dama zata karɓa ya daka mata tsawa yace "ba'a aiki da hannun dama anan" jiki na bari tana murmushi ta mika matsa hannun hagu ta karba, a hanyan su ta dawowa gida Mummy tace "ke baki ga yanda hankali na ya kwanta lokacin da ya hasko mana yaron na ta fama da kansa ba" duk suka kwashe da dariya Aminiyarta tace "yanzu kuma maganar auren Rayyan da Layla zamu fara facing, kuma banji kince min wani abu ba" tace "ki kwantar da hankalin ki yau ina komawa gida maganar da zan ɗago kenan, jikin nasa yau din naga da ɗan sauki ai" . Gaba ɗaya Ummi ta tsorata da lamarin Muhammad, tana kallon Nawaal tace "yanzu mu Muhammad yake son tonawa asiri a duniyan nan" Nawaal ta share hawayen ta tace "Ummi ko ƙaffara ba zan yi ba wallahi Muhammad ba haka nan yake faɗin abun ba kin sa ba, kamar fa baya hankalin sa ne, amma kiyi shiru muga zuwa anjima kar Abba yaji zancen nan, muyi ta addu'a kawai". Ba Zahra ba hatta wanda ke saloon ɗin sai kallon Leena suke ganin yadda red and black henna ya mata mugun kyau ga yadda take ta wani sheki kana ganin ta kasan amarya ce Amma gaba ɗaya hankalin Leena be kwanta da wannan shirun Muhammad ba ace yau har Magrib be kira ba ana gobe daura auren su. Basu suka koma gida ba sai wajajen karfe takwas na dare, su Anty Binta Suna ta yaba kyan Lallen Ammi nata lura da yanayin ta amma dai ta dangan ta hakan da cewa ko wacca amarya takan sinci kanta a haka, dakin ta ta wuce. Har 12 na dare ba kiran Muhammad, Leena ta shiga toilet ta kulle ta fashe da kuka sai da tayi me isarta sannan ta rubuta masa message tana gamawa ta tura masa ta wanke fuskan ta ta fito. Rana bata karya sai dai uwar ɗa taji kunya, yau Saturday ranan ɗaura auren Leena da angon ta Muhammad kenan, tun asuba aka hura wuta aka daura breakfast, Anty Jidda ana idar da asuba ta shigo gidan, kallon yanayin Leena yasa tayi ta bata baki dan ta ɗauka tunanin barin gida take, Anty Mairamah dake bakin murhu ta daura tukunyan ruwa ta koma ciki dan kiran Binta da Jiddah su taya ta kulla alalen da aka kawo a wajan markade. Mummy tana idar da Sallah ta dauki kullin maganin jiya dama ta daure a bakin riganta gudun karya bata, ta fito compound tana bin ko ina da kallo ganin ba kowa saboda ko haske garin be gama yi ba backyard ɗin Mummy ta nufa inda aka hura wuta, tana murmushi tana bin ko'ina da kallo ta kunce Ledan garin da ke Ledan ta juye a cikin bokatin markadan alalan ta garwaye da muciyan dake ciki tana murmushi ta ɗago zata bar wajan, ido huɗu tayi da Anty Mairamah da Jiddah dake bayan ta a take ta fara ɓari bakin ta na rawa tace "En nazo taya ku aiki naga baki nan shine na taba taste ɗin" Jidda sabar shock ta gagara ɗauke idon ta akan Mummy anty Mairamah tayi kukan kura ta chakuwo wuyar Mummy dama akwai ƴar tsana a tsakanin su tace "Uban me kika zuba mana a cikin abinci?" Mummy tace "Dan uwarki ki sake Ni Ko na baki mamaki, har ni zaki wa sharri?" Anty Mairamah tace "okay mamakin nake son gani, ko ki fadi abinda kika mana ko wallahi yau me raba Ni dake sai Allah" Jiddah tayi saurin cewa Dan Allah ki sake ta kawai sai azubar a sake wani" Jiddah kallon girman Mummy yasa tace haka dan ba daɗi a tsile babban mutun Anty Mairamah tace"idan na hakura yau toh uwata Shegiya ta haife ni" da sauri Jiddah ta koma parlorn Ammi ta tsanar musu da abinda ke faruwa duk suka fito Anty Binta harda sauri dama suna rike da ita a rai, ganin Mutane sun fara taruwa kuma har sannan Mairamah taki sake ta yasa Mummy ta bata kyakkyawar mari, Ammi ta karasa wajan tana kallon Mairamah da tayi wani kukan kura zata rama tace "Mairamah idan na isa dake ki take ta" ina tuni har ta kai mata maruka har biyu Hajiya ta fito da sauri ta na tambayar abinda yake faruwa tuni har Anty Binta ta bada labari kamar tana wajan tace "wallahi Hajiya fah, ashe guba ne duk mu mutu take so" Hajiya ta sake baki tace "wallahi zata aikata, dan bata da tsoron Allah kwatakwata" Ammi ta wanke Mairamah da mari tace "ban ce ki sake ta ba?" sai sannan ta sake ta Anty Binta tayi ƙwafa tace "wallahi wannan bashi ne" Mummy ta wasa wa Ammi wani kallo tace "We shall see, kuma sai kinyi nadama, ina me tabbatar Miki" zata wuce Binta ta sa mata kafa ta fadi da sauri ta matsa dan tasan Ammi zata iya marin ta ita ma, Anty Binta tace "gashi kinji me tace Miki ai Ammi" Mairamah na kallon su tace "wallahi ba sharri ba ai ga Jiddah na gani, in ba haka bane uban me ya kawo ta sashin nan?" Ammi tace ku zubar da kullum kawai sai a daura wani abun amma ku tabbatar kuna tsaye a wajan, kuma bana son wani ko kallon Banza ya sake mata, ai ta girme ku ko dan albarkacin ƴaƴanta be kamata Kuyi mata abunda kuka mata ba, Hajiya tace "Allah kyauta, ashe da yau duk mun mutu saboda bakin halin ta amma dake Allah na son mu sai yasa aka kamata" Jiddah tace "Kamar bata son auren Leena ne" har Anty Binta da Mairamah na hada bakin cewa "wani kamar? Ai bata so" Ammi tace "let bygones be bygones, please" daga haka ta wuce ciki. Abbah yayi jigum yana kallon waje daya Ummi tace "wallahi damuwa ta yanzu mutanan dake cikin gida ne" Drivern Abbah ne ya kira sa, Abbah ya daga ya kai kunne yana sauraron sa yace "toh gamu" ya cire wayan a kunnen sa yana kallon su yace "saura 30 minutes jirgin zai tashi, yanzu me abun yi I'm confused wallahi" Ummi tace "Mafita anan daya ne kawai ku tafi sai ace ango ba lafiya anyi admitting ɗinsa, ana daura aure sai ku dawo da amarya, daga baya sai mu san yanda zamu yi tunda ba kin yarinyar muke ba" Nawaal ta mike ta ɗau jakkan ta tana kallon Abbah tace "Abbah kuma haka ne, mu tafi kar mu rasa flight" Muhammad yace "Don't make me repeat myself again, wallahi ana daurawa zaku neme Ni har abada ba zaku sake gani na ba" zuwa sannan abun ba Ummi ba har Abbah ya fara tsorata da lamarin sa. Leena tayi wanka aka taimaka mata tayi shiga cikin farin wedding gown, ta sha makeup abunta sai ka rantse balarabiya ce, saboda ba inda take kama da Ammi balle kace buzuwace, sai hotuna akeyi da Amarya, ita gaba ɗaya hankalin ta baya kansu kamar ta fashe da kuka su Hajiya an gagara kyale Leena dan kyan da tayi sai hotuna ake musu, Jidda ganin yanayin ta yasa ta kama hannun Leena suka koma dakin Ammi dan nan ne ba mutane sosai tana kallon ta tace "wai har yanzu be kira ba?" Leena ta gyada kai Jidda tace"kila ko wayar sa ce aka dauke, amma haka nan ba zaiki daga kiran ki ba, kuma ai yanzu kam ma suna wajan daura auren" tayi shiru tana kallon ta, Zahra ta shigo dakin tana tsokanan Leena dan tayi cheering dinta up. Daddy sai duba agogon hannun sa yake lokacin zuwa lokaci, Sultan yana kallon Daddy yace "Toh Daddy ka kira su kaji mana" Daddy yace "wani kiran kuma Sultan? Bayan basa daga kiran" Daddy ya Ciro Wayan sa yaga sakonnin guda biyu, ya shiga wanda ya fara shigowa wayan sa tun kafin ya karasa karanta contents ɗin ya fara zufa baya son yayi believing da abinda idon sa ke nuna masa, yana shiga message ɗin Muhammad zuciyan sa kaɗan ya rage da ya buga, yana ta nanata 'Allahumma ajirni fie musi bati wakhlif Ni khayran Minha" ga dunbun jama'a an taru, Yayan sa ya dafa sa yace "meke faruwa ne? Nasan akwai matsala" Daddy ya mika masa wayan hannun sa, ya karɓa ya karanta, gagara magana yayi Daddy yace "Ni zasu tozarta?" Yayan sa yace "ya zamuyi da dunbun jama'an da muka tara?" Daddy yace "Abinda ya dace kawai zan yi" yace "ban gane ba?" yace "ba wanda zai bar nan, ba za'a fasa auren ba"......
https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA

28.........

Mummy taci kwalliyar ta, ta sha gwala-gwalai sai ka ce itace uwar Amarya sai washe baki take yi, tana ta zarya a cikin gidan ta shiga dakin Hajiya
End Ads