x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - AGOLA free pages

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
taɓa yiwa ba, he is so wicked" Jiddah tace "Wallahi Leena kin ma Sadeeq mummunar fassara, he is so nice yadda baki tunani kawai dai saboda baku saba bane" Leena ta ɗauke kanta tana kallon wani wajan Jidda ta mike tace "barin barki ki huta daga haka ta fice "Leena ta jawo wayan ta Mutumin da ya shiga da ita cikin hall ɗazu ta tura masa voice note da ya tura mata da videos ɗin da aka ɗauka. Rayyan har wani dishi dishi yake gani da kyar ya samu yayi parking, yana sauka part ɗin Hajiya ya wuce ya same ta tana shan fura da nono ya zauna yace "yanzu Hajiya idan har Daddy da ita Ammin basu hana Leena zuwa Abujan nan ba ke ba zakiyi magana ba?" Hajiya tace "Yo Ni nawa a me? ɗazu ma yaron nan Ayaan yana ta murna wai yaga Yayar sa a Tv ni na ɗauka ma karya ne can kuwa ina cikin kallon labarai naga an saka ta sai turancin nan take yi kamar baturiya" Rayyan yace "Hajiya dan Allah na roke ki, kiyi ma Daddy magana kar ya sake yarda Leena ta cigaba da wannan abun" Hajiya ta kwalo ido tace "A'a wallahi ba ruwana Nikam, so kake mu taru mu tsana yarinya diflashon ya kama ta? Da acikin gidan nan kai kaɗai kake mata magana toh kai ma yanzu ka tsane ta, a tunanin ka ban san abinda yake faruwa bane dan kawai na zuba ido, toh Abunda yake sata farin ciki bazan zama sillar ruguza mata ba" Rayyan ya dafa kansa dake sara masa yayi kusan 2minutes a haka Hajiya ta harare sa sannan ta cigaba da shan furan ta, ya ɗanga jajayen idon sa ya kalli Hajiya da su wanda hakan sai da ya ba ma Hajiya tsoro tace "Lafiya Rayyan?" Ga Mamakin ta hawaye ta gani a idon sa tashi yayi ya fice a parlorn nata tana kiran sa amma ko tsayawa be yi ba, yana shiga parlorn su yaga Mummy da Hajiya Fatima suna magana ko kallon inda Hajiya Fatima take beyi ba balle ya gaishe ta ya wuce ɗakin sa Fatima ta sake baki tana kallon sa har ya shige sai sannan ta mayar da duban ta gun Mummy tace "iyyee, shi kuma yaushe Rayyan ɗin ya zama haka?" Mummy tace "is like akwai Abunda yake damun sa" daga haka ta tashe ta bishi har ɗakin sa to her surprise ta burɗa handle ɗin kofar taji shi a rufe, ta bubbuga tayi magana still Rayyan be amsa ba ta koma ta zauna a parlorn amma hankalin ta ya tashi Fatima ta taɓe tace "kila yaga yadda yau ake ta posting Agolan nan ne shine zai wani shigo kan mutane haka?" Mummy ta girgiza kai tace "bana tunanin haka ne" tayi shiru tace "Nikam anya shegiyar matan nan bata asirce min ɗa ba yaro fah yanzu shekara da shekaru ya gagara zama yadda yake da ko fah walwala bayi da shi, Abunda yafi damu na yanzu shine ko maganar aure baya so a mishi" Fatima tace "Tabbacin da baki ɗauki wannan shawaran raba su ɗin ba da yanzu kila har ya aure ta" Mummy tace "ai wallahi ko bayan raina Rayyan ya auri ƴar nan ban yafe masa ba". Leena da ke video call da Ayaan, Ammi na sa musu baki lokaci zuwa lokaci tace "see you later" daga haka ta kashe wayan, Maganganun Jidda ne yake ta yawo mata a kai ita kaɗai ta fara Magana tace "How?" Sai kuma ta kyabe baki, ɗaukan hijab tayi ta saka sannan ta fito parlor ta tarar da Jiddah dake jiran ta har ta gaji ta fara game tana kallon ta tace "Anty Jidda gani" fita su kayi. Bayan sun gama sayyayan su, bolt yayi dropping ɗinsu a bakin Quarters ɗin, suka sauka su ka fara taka wa zasu karasa block ɗin Jidda wani mota ne ya shige su Leena na bawa Jidda labarin ɗazu ai ta shiga wani gida daidai inda ɗazu akayi parking nan yanzu ma mutumin yayi parking ya sauka ganin su Leena yasa ya tsaya be shiga cikin gidan ba ya jingina da motar sa Leena nata kallon sa ganin kamar ta san fuskar sa sai sannan ta tuna shine mutumin da ɗazu tayi mistake ta shiga gidan da yake ta ɗauke kanta suka cigaba da labari sai da suka iso daff sannan ya karasa inda suke yayi sallama Jiddah kaɗai ta amsa yace "Excuse me Ma'am, idan ba damuwa ina son zanyi magana da sistern ki" Jidda murmushi tace "It's Okayy" Leena ta girgiza mata kai ita ba zata tsaya ba Jidda a hankali ta mata magana me haka Leena zaki sa ya raina mu" Leena ta kamata gam idan Jiddah ta fara tafiya itama sai ta bita idan ta tsaya itama sai ta tsaya, Jiddah tace "ke me haka? Ki tsaya kiji me zai ce Miki" daga haka ta karɓe Ledan hannun Leena tayi gaba da sauri shi kuma ya samu daman shan gaban Leena, Leena ta ɓata fuska kamar zata yi kuka amma hakan bata bari ya nuna a fuskar ta ba yace "Leena right?" Bata ce masa komai ba ji take kamar ta kwashe a guje ta shige gida yace "I'm sorry na tsayar da ke kuma kamar you're not comfortable" to her surprise ya karɓe watan hannun ta ta saya sakeke tana kallon sa yace "Your passcode?" ji tayi kawai ta faɗa sannan tayi realizing ashe faɗa masa tayi, sakake tana kallon sa ya gama sa numbern sa sannan yayi dialing tana ji wayan sa yayi ringing a aljihun sa sai ya kashe sannan ya mika mata wayan yana murmushi yace "Thank you so much" ta karɓa watan tana jin haushin Jidda ta wuce sa, tana shiga Jiddah ta kwashe da dariya tace "Leena me kike yi kamar wata gwaɓuwa? Kinga reaction ɗinki kuwa? Haba zaki sa maza su raina ki wallahi" Leena tayi shiru tana kallon Jidda ita yau gaɓa ɗaya ta rasa me yasa ta zama wani iri ne ko dan Abunda Sadeeq ya mata ne Oho, ita dakyar ta bari aga hawayen ta balle aga gazawan ta tana cikin wannan tunanin taji Muryan Sadeeq na sallama da sauri ta ɗaga kai ta kalli jidda kan kace me ta tashi da gudu ta wuce cikin dakin. Strickly yana kallon Jiddah yace "yaushe zata koma?" tace "Dama kwana uku zata yi, jibi kenan zata koma" yace "tell her ta shirya kayan ta gobe zata koma" Jidda ta wani kalle sa tace "akan me Ya Sadeeq?" yace "saboda gobe zan koma itama dole ta koma gobe" Jiddah tace "toh dan zaka koma gobe sai ya zama na lalle itama goben zata goma? Toh tare ma kuka zo ne?" yace "wannan kuma ku kuka sani, dan na gama magana" Jiddah na masa wani kallo tace "Ni ban gane takuratan nan da kake yi ba, idan ma wani abun ne a ran ka gwara ka faɗa dan wannan ba solution bane" ya watsa mata wani kallo ta ɗauke kanta tana kunshe dariyar da ya taso mata. Sai bayan Magrib Sadeeq ya bar gidan kuma har ya koma be haɗu da Leena ba da gangan taki fitowa sai da taji tafiyar sa sannan ta fito ta ɗauki some snacks ɗin da suka tsaya ɗazu ta haɗa tea tana sha ta kalli wayan ta jin yana ringing taga numbern wannan mutumin ɗazun ne toh ita me zata ce Idan ta ɗauka, stranger ne fah a haka har ya katse kuma tun ɗazu yake addaban ta da kira, Jidda ta shigo da sallama Leena ta amsa ta karasa ta zauna kusa da Leena tana kallon ta tace "Leena meyasa baki fito kun gaisa da Ya Sadeeq ba?" Leena ta turo baki taki cewa komai tace "Har yanzu kina nan a Leenan ki na baya sai dai wancan ba ta da saurin kuka ita ɗin jarumai ce" Leena tayi murmushi bata ce komai ba duk sukayi shiru sai can Jiddarh tace "Leena Uncle ɗinki fa ɗazu da yazo fah yayi booking muku flight Leena ta kalle ta sai kuma ta tsunkuyar da kai kasa tace "I'm sorry Leena haka yayi requesting toh ba zai saurare Ni ba sai sa kawai na basa info" Leena that was speechless kawai wani wajan take kallo Jiddah ta kamo hannaun ta tace "I'm sorry dear, beside yana son ki samu enough time ɗin rubuta WAEC ɗinki ne" Leena tace "Allah sa hakan shi ya fi alkhairi". Leena ta kwanta amma kwata kwata bacci yaki ɗaukan ta, ta jawo wayan ta Whatsapp ta shiga nan taga messages ɗin wannan mutumin har guda 10 kamar tayi skipping sai kuma ta buɗe ta shiga tana ta kallon message ɗin da ya mata kamar haka "Hello Leena, you're my long-time crush! I've been watching your videos on Instagram. My name is Muhammad Faisal Arab, I'm 35 years old, living in Maitama, Plot 12, Street 5. I work with NNPC. I graduated from the University of California, Los Angeles (UCLA) with a degree in Petroleum Engineering. I did my master's degree in Energy Policy from Stanford University. And, I completed my PhD in Renewable Energy from the Indian Institute of Technology (IIT) Delhi.
I want to be honest with you; I'm not here to play games with your heart. Sincerely, I love you so much and I want to marry you. I'd love the opportunity to get to know you better and show you my feelings. If you're willing, could you tell me a little about yourself, where you live, and a bit more about your life?" Tayi ta kallon hoton sa kamar tana son gano wani abu, kawai ganin kiran sa tayi ya shigo tayi picking takai kunnen ta.....
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


_By Jiddatul-khayr
Chapter 13



Thank you so much, my dear readers, for reading my book🫂🫧!  I'm grateful to those who've added my novel to their reading list📖💕. May Allah bless you abundantly and provide for your needs, so you can keep enjoying my stories without any distractions (like running out of data 😊)! 🙏📚❤️

Around 8am Leena ta fito duk jikin ta amace ta samu Jidda already tana kan breakfast ta karasa ta zauna Jidda ta kalle ta tace "Dalla ki sake ranki, idan kina haka ne Ya Sadeeq zai ci-gaba da miki abinda ba baki so" ta turo baki Jidda tayi dariya ta haɗa mata tea ta zuba mata chips ɗin a plate Leena ta fara ci kenan akayi knocking zata tashi Jidda ta rike ta tace "Ke dalla ki daina wannan shashanci, ki daina abu kamar kina tsoro" Leena ta koma ta zauna Jidda tace "who is it" yace "Malama idan zaki zo ki buɗe, kizo ki buɗe" tayi dariya tace "har yanzu be sauka ba kenan" ta karasa ta buɗe masa ta matsa masa sai daya shiga sannan tace "ina kwana Ya Sadeeq" yace "Fine" ya karasa cikin parlorn ya zauna akan kujera Jidda ta karasa inda suke karyawa ta zauna Leena Satan kallon sa tayi suna haɗa ido tace "Good morning" yace "Morning!" daga haka ya cigaba da dannan wayan sa sai kuma yace "Look! Kina wasting mana time fah" sai sannan ta kalle sa Jidda tace "Leena be quick" ta gyaɗa mata kai ta tashi tace "I'm done" Jiddah ta shiga ɗaki ta fito mata da jakkan ta, Bolt ɗin da sukayi order ya karaso duk suka fito Jidda ta raka su har waje Sadeeq ya shige gaban motar, ita Jiddah ta buɗe mata bayan motar ta mata raɗa a kunne Leena tayi murmushi. Bayan sun isa Sadeeq ya ɗauki jakkan sa dana Leena suka karasa cikin airport tun da sukayi magana a gidan Jidda har yanzu ba wanda yace da ɗan uwan sa uffan, suna zaune suna jiran a kira su, Leena taji watan ta yana ringing ta ciro wayan a jakka gannin Muhammad ne ke kiran ta yasa ta ɗan saci kallon Sadeeq taga ita yake kallo tayi silencing wayan ta mayar jakka. Bayan jirgi ya tashi Leena ta fara jin bacci saboda rashin bacci da bata samu da wuri ba jiya, bacci ya ɗauke ta har kanta ya karkace ta ɗan ɗaura a shouldern Sadeeq  ya gyara mata yadda ba zata takura ba, gaba daya trip ɗin nan Leena na bacci sai da za suyi landing ne ta farka ganin ta tayi ashe tayi balance a jikin sadeeq yasa ta tashi da sauri ta ɗan sace kallon sa taga wani gurin yake kallo daban. Bayan sun sauka ya ɗauki jakkan sa da nata suka samu waje suna jiran Sultan sai gashi ya iso yana murmushi ya fito ya buɗe booth yana kallon Leena yace "Baby girl" tana murmushi ta gaishe sa ya amsa mata da fara'a yana kallon Sadeeq yace "kai kuma ba magana ne?" Sadeeq yayi kamar be ji sa ba Sultan yayi dariya yace "Wato yau kuma da halin ka ka dawo". A daidai kofan su Leena suka tsaya ta sauka Sultan ya sauke mata kayan ta a booth tana kallon sa tace "Thank you" kamar zata tafi kuma sau ta karasa inda Sadeeq yake tace "sai anjima, thank you" sai sannan ya lalle ta yace "My pleasure" daga haka ta shiga gida tana gaishe da masu gadi. A compound ta haɗu da Mummy ta zata fita kenan tace "Good morning, Mummy" ko kallon ta bata yi ba balle ta amsa ta karasa sashen su ta shiga da sallama Ammi ta fito a kitchen baki buɗe tana kallon ta, ta sake jakkan hannun ta da gudu taje ta rungumi Ammi tace "Ammi nayi missing ɗinki" Ammi tace "zuwa ba magana Leena" Leena ta bata fuska tace "Uncle Sadeeq ne wai dan yau zai dawo wai sai dai mu dawo tare" Ammi tace "ai shikenan". Da yamma Leena ta tafi part ɗin Hajiya tana shiga taga Rayyan yana zaune akan kujera yana danna wayan sa ta karasa cikin parlorn ta zauna a opposite ɗin sa tace "Ya Rain" sai sannan ya ɗaga kai ya kalle ta tace "ina wuni" yace "Lafiya Leena" sai kuma ya mayar da hankalin sa kan Abunda yake yi a waya Leena ta kuma cewa "Baka je aiki ba yau? Baka da Lafiya ne?" yace "I'm fine, aiki kuma ina hutu ne" ta gyada masa kai kawai Hajiya ta fito Leena taje ta gudu ta rungume ta "Hajiya tace "Ni fa Leena kaman kina girma hankalin ki yana baya, toh karya Ni kike son kiyi" Leena na dariya tace "A'a". Yau wajan kwana huɗu da zuwan Leena gida, kiran da Muhammad yake mata har ya wuce misali, Ammi har sai da ta tambaye ta wai waye ne, bata boyewa Ammi komai ba, hakan yasa wata Sa'id idan ya kira taki ɗauka sai Ammi tayi da gaske take ɗauka. Wata Rana Leena na zaune tana karatun WAEC dinta kawar ta zahra tayi sallama Leena ta fito a ɗakin ta ta buɗe mata kofar Leena tace "wai dama da gaske Zahra zaki zo?" tace "Ke tare nake da yaya na ban keypoint din biology" Leena tace "toh shigo mana, suka karasa ɗakin Leena, Leena tace "gashi! amma dan Allah ki samu ki karasa da wuri dan ban gama amfani da shi ba" zahra tace "In shaa Allah, Ke Leena wallahi wannan step Mum ɗin taki bata da kirki" Leena tace "Meya faru?" tace "shigowa fah da nayi ta zageni tas" Leena tace "sai hakuri Nima ban tsira ba balle Ammi na". ta raka ta har bakin gate zata dawo sai ga Rayyan zai fita tace bari ta gwada kin masa magana to her surprise taga be mata magana ba ta gyaɗa kai wato idan har bata masa magana ba shi ba zai mata ba. Da daddare Leena na karatun WAEC ɗin da zasu fara gobe, Ayaan ya shigo dakin da wayan Leena ke ringing ta karɓa ganin Muhammad ne yasa takai kunne ta gaishe sa ya amsa yace "Leena meyasa baki son kira na?" tayi shiru yace "ina damun ki ko?" tace "Saboda exams ne a gaba na" yace "well, ina son ganin ki Leena" tayi shiru ita duk ta kagu ya kashe wayan tace "Um" yace "jibi in shaa Allah zan zo Baby" da sauri tace "Meyasa?" yace "baki son ganina ne?" tace "A'a ba haka bane?" yace "toh ki sanar ma Ammi zan zo gashe ta tunda ke baki son nazo na Ganki" sai kuma jikin ta yayi sanyi kullum sai ya kira kuma kullum da kalan iskanci da take masa tace "I'm sorry, ba haka bane" yace "it's okay, sai munyi waya gobe" yana kashe kiran ko 3 minutes be yi da kashe wayan ba sai ga message ɗin sa ya shigo yana wishing inta success, da safe bayan ta gama breakfast tana zaune still akan dining din ta gagara tashi Ammi tace "Meke damun ki ne wai Leena?" tace "Ammi wai fah Muhammad ne" Ammi tace "meya faru da shi?" tace "wai zai zo ya gaishe ki" Ammi tace "shine kike ta nuku nuku? Toh Allah kawo sa lafiya" sai ta tashi tace "Ammi barin tafi" Ammi ta mata addu'a. Bayan Leena ta dawo daga exams, ta cire kayan jikin ta ta wuce toilet tayi wanka sannan ta fara sallah, tana cikin sallah wayan ta ya fara ringing tana idarwa ta jawo wayan duk tunanin ta Muhammad ne sai taga bakon numbern sake kiran ta akayi tayi picking ta kai kunne sallama akayi ta amsa tana mamakin jin muryan sa, toh ko ba shi bane, tana cikin tunani taji yace "ki fito ina kofar gida" tace "toh" ta dauki hijab dinta ta saka tana mamaki ta buɗe gate nan idon ta ya gasgata mata cewa kunnen ta ba karya ya mata ba ta karasa jikin motan tace "Ina wuni Uncle sadeeq" be amsa mata ba sai papers ɗin hannun sa ya mika mata yace "kiyi going through zasu taimake ki" ta amsa tace "Thank you" motar Rayyan ta gani yana tahowa daga haka ta koma ciki da sauri gudun kar su hadu, mamaki ya cika Leena toh daman yana da numbern ta ne, da wadannan tunanin ta shiga parlor
End Ads